Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
By Azizat
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Author: Azizat
Chapter 109 of 161
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,689 words Chapter 2 1,523 words Chapter 3 1,583 words Chapter 4 1,696 words Chapter 5 1,682 words Chapter 6 1,693 words Chapter 7 1,594 words Chapter 8 1,673 words Chapter 9 1,663 words Chapter 10 1,668 words Chapter 11 1,678 words Chapter 12 1,698 words Chapter 13 1,687 words Chapter 14 1,699 words Chapter 15 1,656 words Chapter 16 1,634 words Chapter 17 1,681 words Chapter 18 1,675 words Chapter 19 1,655 words Chapter 20 1,613 words Chapter 21 1,669 words Chapter 22 1,655 words Chapter 23 1,671 words Chapter 24 1,650 words Chapter 25 1,677 words Chapter 26 1,696 words Chapter 27 1,598 words Chapter 28 1,699 words Chapter 29 1,694 words Chapter 30 1,659 words Chapter 31 1,683 words Chapter 32 1,309 words Chapter 33 1,691 words Chapter 34 1,697 words Chapter 35 1,553 words Chapter 36 1,588 words Chapter 37 1,682 words Chapter 38 1,680 words Chapter 39 1,677 words Chapter 40 1,649 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,698 words Chapter 43 1,676 words Chapter 44 1,625 words Chapter 45 1,633 words Chapter 46 1,675 words Chapter 47 1,693 words Chapter 48 1,668 words Chapter 49 1,688 words Chapter 50 1,647 words Chapter 51 1,653 words Chapter 52 1,568 words Chapter 53 1,689 words Chapter 54 1,699 words Chapter 55 1,669 words Chapter 56 1,578 words Chapter 57 1,564 words Chapter 58 1,660 words Chapter 59 1,694 words Chapter 60 1,415 words Chapter 61 1,653 words Chapter 62 1,690 words Chapter 63 1,685 words Chapter 64 1,618 words Chapter 65 1,652 words Chapter 66 1,674 words Chapter 67 1,687 words Chapter 68 1,699 words Chapter 69 1,644 words Chapter 70 1,698 words Chapter 71 1,691 words Chapter 72 1,671 words Chapter 73 1,689 words Chapter 74 1,679 words Chapter 75 1,677 words Chapter 76 1,678 words Chapter 77 1,655 words Chapter 78 1,683 words Chapter 79 1,696 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,694 words Chapter 82 1,697 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,668 words Chapter 85 1,554 words Chapter 86 1,666 words Chapter 87 1,677 words Chapter 88 1,694 words Chapter 89 1,667 words Chapter 90 1,700 words Chapter 91 1,670 words Chapter 92 1,670 words Chapter 93 1,655 words Chapter 94 1,640 words Chapter 95 1,607 words Chapter 96 1,668 words Chapter 97 1,659 words Chapter 98 1,689 words Chapter 99 1,675 words Chapter 100 1,614 words Chapter 101 1,610 words Chapter 102 1,700 words Chapter 103 1,683 words Chapter 104 1,657 words Chapter 105 1,698 words Chapter 106 1,700 words Chapter 107 1,695 words Chapter 108 1,656 words Chapter 109 Reading now Chapter 110 1,699 words Chapter 111 1,699 words Chapter 112 1,641 words Chapter 113 1,696 words Chapter 114 1,626 words Chapter 115 1,695 words Chapter 116 1,691 words Chapter 117 1,698 words Chapter 118 1,645 words Chapter 119 1,673 words Chapter 120 1,691 words Chapter 121 1,635 words Chapter 122 1,694 words Chapter 123 1,689 words Chapter 124 1,688 words Chapter 125 1,673 words Chapter 126 1,692 words Chapter 127 1,686 words Chapter 128 1,697 words Chapter 129 1,660 words Chapter 130 1,691 words Chapter 131 1,674 words Chapter 132 1,670 words Chapter 133 1,693 words Chapter 134 1,691 words Chapter 135 1,687 words Chapter 136 1,672 words Chapter 137 1,691 words Chapter 138 1,657 words Chapter 139 1,687 words Chapter 140 1,650 words Chapter 141 1,695 words Chapter 142 1,607 words Chapter 143 1,699 words Chapter 144 1,676 words Chapter 145 1,698 words Chapter 146 1,684 words Chapter 147 1,664 words Chapter 148 1,696 words Chapter 149 1,674 words Chapter 150 1,680 words Chapter 151 1,697 words Chapter 152 1,628 words Chapter 153 1,618 words Chapter 154 1,688 words Chapter 155 1,664 words Chapter 156 1,692 words Chapter 157 1,584 words Chapter 158 1,644 words Chapter 159 1,646 words Chapter 160 1,618 words Chapter 161 1,797 words

Maman Tope ke da aiki amma ta nemi uzuri saboda an kwantar da wata 'yarta a Asibiti. Shiyasa aikin yai wa Zaytoonah yawa dan girkin da za ta yi har da ma su aikin gidan gaba ɗaya. Baccin safe da ta yi ne ma ba ta farka da wuri ba, dan da ta tashi sai gani ta yi ƙarfe shabiyu har da minti tara.

Tana kitchen É—in yaran su ka dawo, duk cikin su Suhailah ce ta shigo ta ma ta oyoyo kafin ta wuce wajen yayyen ta da tuni su ka kunna TV suna kallon wani favourite show É—in su.

Tana gama soya nama ta kashe gas ɗin ta bar kitchen ɗin da sauri. Tun da ta tashi a bacci kitchen ta wuco saboda sauri to kuma yanzu wani fitsari ke cinta dole ta ajiye girkin ta kashe gas ɗin ta tafi ɗaki. Da ta je fitsarin ma sai da ta tsaya ta gyara jikin ta sosai saboda dama tana tareda baƙo. Ta fito daga banɗaki kenan ta ji ihun Suhailah a ƙasa, ba shiri ta fito a guje.

A kitchen ta samu yaran suna tsaye wajen Suhailah da ke zunduma ihu saboda man da ya tsartu ma ta a jiki.
Zaytoonah ta yi kan ta da sauri tana tambayar miya faru amma babu wanda ya kulata saboda Suhailan kuka kawai take yi.

Ta san dai idan mai ya tsartu wa mutum tun lokacin suna yara Mommy na amfani da gishiri ko kamu ta mutsutstsuka wajen, idan kuma akwai Zuma sai ta shafa mu su.
Da sauri ta buÉ—e roban gishiri ta É—ebo ta fara shafawa Suhailah a wuya da hannun ta.
Raziya na cewa ta barta a kai ta Asibiti. Sai da ta gama shafa ma ta ta É—auki Suhailah a kafaÉ—a su ka fito a kitchen É—in dai dai nan kuma Justice ya shigo gidan.

"Miya faru?" Ya faɗa yana karɓan Suhailah a hannun Zaytoonan. Yarinya kuma ganin Daddyn ta kawai sai ta ƙara sautin kuka.

Raziya ce ta yi saurin faÉ—in " Yunwa ta ke ji shine ta shiga kitchen wajen Anty ita kuma ba ta kitchen É—in kuma ta bar Mai mai zafi a wajen sai ya zubowa Suhailah a jiki"

"Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun" kawai ya faÉ—a yai hanyar waje bayan ya yiwa Zaytoonah wani kallo.

Bayan fitar su da ƙyar Zaytoonah ta iya saita kan ta ta shiga kitchen ta goge wajen da man ya zuba ta ƙarisa girkin a gurguje.

Bayan ta gama girkin zama ta yi a falo ta yi tagumi tana jiran dawowar su.
Ta sani naman da ta soya ta ke son zubawa a miya yarinyar ta je ɗauka ta ga ƙaramar kujera a wajen alamar shi ta hau saboda tsayin ta ya kai wajen. By mistake ne ƙila hannunta ya bugi frying pan da ke gefen bowl ɗin da ta zuba naman shine Man ya tsirtu ma ta sauran kuma ya malale a ƙasa.

Kusan awa biyu da fitar su sai gashi sun dawo abin mamaki har da Hajia Ghazala dan ita ce ma ke riƙe da Suhailan wacce ke riƙe da ice cream tana sha hankali kwance an shafa ma ta magani a wajen da man ya zuba raɗaɗin da ta ke ji ya ragu.
Ko kallon Zaytoonah bai yi ba ya wuce sama.

Sai da ta sauke ajiyar zuciya kafin ta bi bayan sa ba tareda ta yiwa Hajia Ghazala magana ba.

Kai tsaye É—akin sa ta shiga dan ba ta gan shi a falon sa ba.

"Daddyn Raziya ka yi haƙuri, wallahi ban san za ta shiga kitchen ɗin ba i just..."

"Ƙarfe nawa Zaytoon ba a gama abincin rana ba?. Idan ke ba za ki iya girkin ba ina Atika? ina Silifat?. Aikin mi su ke yi da ba za su yiwa yara abinci ba"

"Ka yi haƙuri ranka shi daɗe. Maman Tope ta nemi uzuri kuma ni ne na ce kar Atika ta zo saboda..."

"Kar a sake barin Yaran nan da yunwa" ya katse ta.

HaÉ—iye sauran bayanin da ta yi niyyan yi ta yi tareda faÉ—in " Insha Allahu hakan ba zai kuma faruwa ba"

Fita ta yi daga É—akin jikin ta a sanyaye.

Ba za ta ba shi laifi ba dan ta san kowanni Uba 'ya'yan sa ke zuwa farko sama da kowa amma at least ya kamata ya ba ta damar kare kan ta, watan ta É—aya kenan a gidan kuma yau ne na farko da aka samu akasi irin wannan dan miyasa ba zai ma ta uzuri ba? Dan miyasa zai ba ta laifi ba tareda ya saurareta ba...
2/11/21, 10:04 PM - ****: 53

Bismillahir Rahmanir Rahim

*Raziya*

"Yaran nan dai kin san marayu ne. Tsakani da Allah Zainan ki ke ko Zaytoonah ya za ki mu su horo da yunwa?. Yunwa fa!

" Idan ki ka muzguna mu su ma dai kin san makomar ki a wajen Allah wuta ne.

"Gaba da baya yaran nan 'yan gata ne ya kamata ki san wannan, dududu yaushe ki ka zo gidan nan amma har kin fara carelessness akan yara ƙanana kamar ba ki san zafin haihuwa ba"

Duk maganar da Hajia Ghazala ta ke yi Zaytoonah ba ta tanka ma ta ba, amma furucin ƙarshe ya sosa ma ta rai.

"Ba na tunanin kina da hurumin shigo min ɗaki ba tareda izini ba. Tunda ban gayyace ki ba ki ɗau zawarawan ƙafafuwanki ki bar min ɗaki kafin na yi abinda ranki zai ɓaci"

"Ba laifin ki ba ne ai, laifin wanda ya ajiye ki a gidan ne. Amma ki sani duk lokacin da kika walaƙanta min 'ya'ya jikin ki ne zai gaya miki"

"Out!" Ta faɗa tana nuna ma ta ƙofa.

Hajia Ghala ta buÉ—e baki za ta yi magana sai kuma ta fasa ta ja dogon tsaki ta bar É—akin.

Sai da Hajia Ghazala ta fita daga É—aki hawayen da ta ke tarewa su ka zubo.
Ba ta san zafin haihuwa ba? Ai ko ba ta taɓa haihuwa ba ba za a gaya ma ta wannan maganar banzan ba, balle kuma ta haihu, ta san wahalan ɗaukan ciki, haihuwa da reno.

Sai da ta share hawayen ta sannan ta É—au waya ta kira Mommy suna gaisawa ta ce Dan Allah Mommy ta sa Salman ya kawo ma ta yaran gobe.

"Zaytoonah Lafiya dai ko"

"Lafiya Mommy kawai na missing É—in su ne, dan Allah ki sa Salman ya kawo su ko kwana biyu ne su min"

Ta so ta yi jayayya amma yanayin da Zaytoonan ta yi magana ya karya ma ta zuciya. Al'amarin uwa da É—a sai a hankali. Ita kan ta ma kewar Zaytoonan ta ke yi duk da kuwa kullum sai sun yi waya.

"Shi kenan gobe Salman zai kawo mi ki su"

"Na gode Mommy"

"Adaeze sai dai ki cigaba da haƙuri fa. Sha'anin aure sai ka yi haƙuri sosai da kuma addu'a kafin ka samu nasara. Ki dage da addu'a dan Allah kuma ki rage saurin fushi kin ji"

"Yes Mommy"...

Hajiya Ghazala na barin É—akin Zaytoonah falon Justice ta shiga luckily kuma ta same shi yana zaune yana shan kankana.

"Sannu da aiki"

"Abu Razz ni da 'ya'ya na kuma sai ka min godiya"

"Ki kira Atika ta zo aiki kafin Silifan ta dawo"

"Na riga na kira ta ma tana hanya yanzu haka"

"Na gode" ya faÉ—a yana maida hankalin sa ga TV da ke falon.

Shiru ya ɗan ratsa madaidaicin falon na sa na lokaci kaɗan kafin Hajia Ghazala ta fara magana " na ce Ranka shi daɗe sai dai ka ƙara haƙuri fa, ka san Antyn na su akwai shiririta, akwai yarinta a tattare da ita. Na ma mata magana kuma ta gane kuskurenta gaskiya, ta ce na ƙara ba ka haƙuri dan ta ga ranka ya ɓaci sosai"

"Jazakillahu khairan"

"Amin" ta faÉ—a tana faÉ—aÉ—a murmushin ta.

Sai da ta É—an zauna na wasu mintuna kafin ta bar falon fiskarta wasai dan ta samu abinda ta ke so.
Ba ta bar gidan ba sai da Atika ta iso. Lokacin ma ta gama girka abincin dare wa yaran.

Tana isa gidan ta ko hutawa ba ta yi ba ta kira Hajia Abu ta labarta ma ta ƙarya da gaskiya na abinda ya faru. Tuni Hajia Abu ta hau faɗa kamar Ghazalar ce Zaytoonah sai da ta gama faɗan ta ce tabbas za ta ɗau mataki akan Zaytoonah.
Hajia Ghazala ta haɗa da cewa " Wallahi Hajia Galadima bai yi dacen mata ba kwata-kwata idan ba ayi da gaske ba yaran nan ba ƙaramin wahala za su sha ba a wajen ta, tunfa ba a je ko'ina ba kenan. Shi kuma kin san Galadima sanyin shi yayi yawa ba komai ya ke iya magana akai ba"

Hajia Abu ta cika ta yi fam tana faÉ—in koma mi Zaytoonah ta zo da shi za ta taka ma ta birki...

Zaytoonah tunda ta gama waya da Mommy ta tashi ta sawa ƙofarta key. Da Hajiya Ghazalar da Justice da ma yaran duk haushin su ta ke ji. Ba ta sake fitowa ba har sai washegari ko abinci ba ta ci ba.
Washegari sai kusan ƙarfe goma ta fito ta nemi abin karyawa.
Bayan ta cika cikin ta tukunna ta koma sama ta shiga ɗakin Justice ta gyara ma sa. Da ke akwai ƙaramin lambu a ta bayan gidan duk weekend da safe Justice a nan ya ke zama ya yiwa flowers bayi ya gyara wajen.

Da ta gama ta koma ɗaki ta kira Salman a waya wanda ya ce ma ta suna hanya zuwa ƙarfe shabiyu za su iya isowa.

A ranta ta yi alƙawarin ba za ta kuma karambani yiwa kowa girki ba har kuwa da shi mai gidan. Ai kafin zuwanta abincin su Atika ya ke ci dan haka ya cigaba. Tunda ya nuna baya so ta dinga barin ma sa yara a yunwa gara ta tsame hannun ta daga lamarin girkin gidan tunda dai ita ba ta kai a ma ta uzuri ba.

Ta zo saukowa ta hango Justice yana shigowa dan haka ta fasa ta koma É—akin ta. She just cant stand him bayan abinda ya ma ta jiya.

End of Chapter 109Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next