Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
By Azizat
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Author: Azizat
Chapter 18 of 161
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,689 words Chapter 2 1,523 words Chapter 3 1,583 words Chapter 4 1,696 words Chapter 5 1,682 words Chapter 6 1,693 words Chapter 7 1,594 words Chapter 8 1,673 words Chapter 9 1,663 words Chapter 10 1,668 words Chapter 11 1,678 words Chapter 12 1,698 words Chapter 13 1,687 words Chapter 14 1,699 words Chapter 15 1,656 words Chapter 16 1,634 words Chapter 17 1,681 words Chapter 18 Reading now Chapter 19 1,655 words Chapter 20 1,613 words Chapter 21 1,669 words Chapter 22 1,655 words Chapter 23 1,671 words Chapter 24 1,650 words Chapter 25 1,677 words Chapter 26 1,696 words Chapter 27 1,598 words Chapter 28 1,699 words Chapter 29 1,694 words Chapter 30 1,659 words Chapter 31 1,683 words Chapter 32 1,309 words Chapter 33 1,691 words Chapter 34 1,697 words Chapter 35 1,553 words Chapter 36 1,588 words Chapter 37 1,682 words Chapter 38 1,680 words Chapter 39 1,677 words Chapter 40 1,649 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,698 words Chapter 43 1,676 words Chapter 44 1,625 words Chapter 45 1,633 words Chapter 46 1,675 words Chapter 47 1,693 words Chapter 48 1,668 words Chapter 49 1,688 words Chapter 50 1,647 words Chapter 51 1,653 words Chapter 52 1,568 words Chapter 53 1,689 words Chapter 54 1,699 words Chapter 55 1,669 words Chapter 56 1,578 words Chapter 57 1,564 words Chapter 58 1,660 words Chapter 59 1,694 words Chapter 60 1,415 words Chapter 61 1,653 words Chapter 62 1,690 words Chapter 63 1,685 words Chapter 64 1,618 words Chapter 65 1,652 words Chapter 66 1,674 words Chapter 67 1,687 words Chapter 68 1,699 words Chapter 69 1,644 words Chapter 70 1,698 words Chapter 71 1,691 words Chapter 72 1,671 words Chapter 73 1,689 words Chapter 74 1,679 words Chapter 75 1,677 words Chapter 76 1,678 words Chapter 77 1,655 words Chapter 78 1,683 words Chapter 79 1,696 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,694 words Chapter 82 1,697 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,668 words Chapter 85 1,554 words Chapter 86 1,666 words Chapter 87 1,677 words Chapter 88 1,694 words Chapter 89 1,667 words Chapter 90 1,700 words Chapter 91 1,670 words Chapter 92 1,670 words Chapter 93 1,655 words Chapter 94 1,640 words Chapter 95 1,607 words Chapter 96 1,668 words Chapter 97 1,659 words Chapter 98 1,689 words Chapter 99 1,675 words Chapter 100 1,614 words Chapter 101 1,610 words Chapter 102 1,700 words Chapter 103 1,683 words Chapter 104 1,657 words Chapter 105 1,698 words Chapter 106 1,700 words Chapter 107 1,695 words Chapter 108 1,656 words Chapter 109 1,683 words Chapter 110 1,699 words Chapter 111 1,699 words Chapter 112 1,641 words Chapter 113 1,696 words Chapter 114 1,626 words Chapter 115 1,695 words Chapter 116 1,691 words Chapter 117 1,698 words Chapter 118 1,645 words Chapter 119 1,673 words Chapter 120 1,691 words Chapter 121 1,635 words Chapter 122 1,694 words Chapter 123 1,689 words Chapter 124 1,688 words Chapter 125 1,673 words Chapter 126 1,692 words Chapter 127 1,686 words Chapter 128 1,697 words Chapter 129 1,660 words Chapter 130 1,691 words Chapter 131 1,674 words Chapter 132 1,670 words Chapter 133 1,693 words Chapter 134 1,691 words Chapter 135 1,687 words Chapter 136 1,672 words Chapter 137 1,691 words Chapter 138 1,657 words Chapter 139 1,687 words Chapter 140 1,650 words Chapter 141 1,695 words Chapter 142 1,607 words Chapter 143 1,699 words Chapter 144 1,676 words Chapter 145 1,698 words Chapter 146 1,684 words Chapter 147 1,664 words Chapter 148 1,696 words Chapter 149 1,674 words Chapter 150 1,680 words Chapter 151 1,697 words Chapter 152 1,628 words Chapter 153 1,618 words Chapter 154 1,688 words Chapter 155 1,664 words Chapter 156 1,692 words Chapter 157 1,584 words Chapter 158 1,644 words Chapter 159 1,646 words Chapter 160 1,618 words Chapter 161 1,797 words

"Sai ki yi kuma ai 'yar baƙin ciki. To ni dai ba zan ci soyayyen ƙwai ba ki min wani abun mai ɗan romo-romo"

Ta wuce É—akinta tana tura ciki.

Wani abu ya daki zuciyar Maryam. "Ciki" ta furta a fili. Da ƙyar ta samu ta ƙarisa soya doyan da ta ke ta kwashe ko tattara wajen ba ta yi ba ta wuce ɗakinta. Gado kawai ta hau ta kwanta.
"Kenan ni ne ba na haihuwa" ta furta hawaye na gangaro ma ta.

T J ya buɗe ƙofa ya shigo, tuntuni ya shirya yana ɗakinsa yana marking assignment ɗin ɗalibai. Daya gama ne ya fito dan ya karya kafin ya wuce school, rashin ganin Maryam a falo da kitchen ya sa shi shigowa ɗakinta.

"Dear are you Ok?" Ya tambaya yana taɓa goshinta.

"Hajjo na da ciki" ta faÉ—a tana kallon sa

"Ya Ilahi! Ashe ban faÉ—a miki ba. About three weeks ago ta ce min ba ta da lafiya shine na raka ta asibiti aka ce ciki gareta. Ni dai Addu'a na Allah ya sa ba SS ba ne, ba na son 'ya'ya na su yi wahala kaman na Sadiq"

Ido kawai ta zuba mishi tana kallon yadda yake koro bayanai.

"Indai ta haihu aka samu AS inaga planning za ta yi mu raini abin da ta haifa"

"Saboda kar na cinye muku baby tun bai zo duniya ba shine ake ɓoye min cikin?"

"Subhanallahi! Maryam wani irin magana ne wannan? You know that's not true. Wallahi mantawa na yi"

"Mantuwa? Barkindo Mantuwa? For three weeks ka san cewa matarka tana da ciki amma ka manta ba ka gaya min ba. You are not good at lying dan haka kar ka fara. Ba ka son gaya min saboda ni mayya ce zan kama kurwan É—an ku"

"Innalillahi. Maryam please..."

Ranan kam duk yadda ya so ya fahimtar da Maryam mantuwa yai ba ta saurareshi ba. Da shi da ita ɗin ba wanda ya yi breakfast. Da rana da ya dawo ma dai abun duk ɗaya ne. Kusan sati tayi tana fushi dashi. Abunda ya lura shine ba wai dan bai faɗa ma ta bane kaɗai dalilin fushin na ta har da stigma na rashin haihuwa da ba ta yi ba har yanzu. A haka dai yai ta lallaɓata har su ka shirya gaba ɗaya. Ranan da su ka shirya ma saboda albishir daya kawo ma ta ne na form daya siya ma ta na Law school da ke Abuja. Yana ma ta Albishir ɗin ta yi tsalle ta rungumeshi har da bashi sweet kiss a lips ɗin sa, daga ranan kuma faɗan su ya zo ƙarshe...

Ana gobe Maryam za ta je Abuja yin registration aka turowa T J letter cewa ƙanin Kakan sa wato Alhaji Isa ya rasu. Wannan ya sa Maryam ce kaɗai ta tafi Abuja shi kuma ya wuce Ringim. Kwana ɗaya yai Washegari ya dawo saboda ayyuka da su ke gaban shi.

Bayan komai ya kammala Maryam ta fara karatu a Abuja, ɗaki T J ya kama ma ta ya biya hayan shekara ɗaya har ta gama Law school ɗin. Sunyi akan zai dinga zuwa ma ta duk weekend idan ya samu sarari ko ba weekend ba ya ce zai dinga leƙo ta.

Cikin Hajjo na wata takwas Inna Saratu ta zo ta É—auketa wai za ta yi haihuwan gida. Ita anata nufin wai za ayiwa Hajjo da abunda za ta haifa maganin Mayu saboda kar Maryam ta kama kurwan su.
Shi dai T J tunda ta ce Iya ma ta amince da tafiyar ya ce Allah ya kai su gida lafiya. Da ya san abinda ake shirin yi kenan da ko Iyan ce ta zo da kanta ba zai bari Hajjo ta bi ta ba. Shi dai tunda ta tafi ya ke addu'ar Allah ya sa ta haihu lafiya kuma a samu AS ba SS ba.

Hajjo kam tunda su ka tafi ƙauyen su ake ta ɗura ma ta jiƙe-jiƙe ana ma ta hayaƙi. Da farko ta nuna ba ta so amma Innarta ta ce ba ta isa ba dan ba zai yiwu ta dinga haihuwa Maryam na cinye 'ya'yan ba. Yadda T J ke da dukiya ya kamata ace ta haifa ma sa 'ya'ya dayawa, idan kuma duk su ka mutu ai ta tashi a tutar babu kenan. Da haka Hajjo ta yi shiru aka cigaba da magani.

Ta dawo daga class a gajiye sai taga ƙofar ɗakinta a buɗe ta shiga da sauri dan jiya-jiya T J ya bar Abuja ya koma Zaria.

"Lafiya ka zo?" Ta faÉ—a a É—an tsorace bayan ta ganshi zaune yana rubutu.

Ya taso ya rungumeta ya ce "jiya na yi mafarki mai daɗi shine na ka sa haƙuri na ce dole na zo na baki labari, kinga kema sai ki sa cikin addu'ar ki"

"My Love za ka sa heart attack ya kama ni. You should've waited zuwa wani weekend É—in idan ka zo sai ka gaya min mafarkin ai"

Ya girgiza kai yana ƙoƙarin cire ma ta gyalenta
"Baby Idan mafarkin nan ya tabbata i'll be the happiest man on earth"

Jin hannunsa a ƙugunta yana shirin since zaninta ya sa ta yi dariya ta sa hannunta ta zagaye wuyansa ta ce " gaya min gaskiya. Labarin mafarki ne ya kawoka ko kuma wani abun daban?"

"Labarin mafarki mana, amma zan fi jin daÉ—in ba da labarin idan na..."

Ya kai baki zai kissing É—inta ta sa hannu ta tare bakin " Love za ka barni na yi karatun nan kuwa. Karatun fa akwai wahala and you're not helping"

Ya janye hannunta ya manna ma ta light kiss ya ce "mu je na baki laƙanin riƙe karatu"

Ta yi dariya ta ce " I love you Shehu Tijjani"

"Wayyo zuciyata" ya faɗi yana dafe ƙirjinsa ta kai ma sa dundu ya riƙe hannun ya jawota ta faɗa jikinsa.

"Allah ya sa mafarkin da na yi ya tabbata"

"Wani irin mafarki ne wannan?"

"Wai kin haifa min Cute Princess mai kamar ki"

Ta yi murmushi dan harga Allah ta ji daÉ—in maganar da ya ce.

"Amin" ta furta ƙasa-ƙasa.

Kan katifar ɗakin ya mu su masauki yana faɗin ƙila Allah ya basu Princess yau...

Kwana tara da fara magani wata yammacin ranan Talata Hajjo ta fara ciwon ciki bayan ta sha jiƙon da aka ba ta. Wasa-wasa ciwon cikin ya tsanan ta daga baya sai naƙuda gadan-gadan aka kira wata Tsohuwa ungozoma. Ba ƙaramin wahala Hajjo ta sha ba kafin nan ta haihu amma ɗan ba rai dan har kaman ya fara ruɓewa alaman ya kwana biyu da mutuwa. Tun kwana uku da su ka wuce ta dena jin motsin cikinta amma ba ta faɗa ba.
Hajjo ta yi kuka sosai dan ko rasuwan Sadiq iya kaci. Ita kan ta yarda magungunan da ta ke ta ɗirkawa ne ya kashe ma ta ɗanta tunda lafiya-lafiya ta bar Zaria. A ranan aka aika Ringim su kuma su ka tura wasiƙa zuwa Zaria. Wasiƙar ba ta isa ga T J ba sai washegari.
Shima ya ji mutuwar a jikinsa sosai. A ranan da ya je Ringim ya ke jin labarin komai dan an taho da Hajjo Ringim, ya kuwa zage ya zuzzubawa Hajjo da Innarta masifa. Ya kuma furta kalmar da ta girgiza Hajjon da Innar na ta

"Duk ranan da aka ƙara kawo maganin Maita ko aka kira wani mai Magani wa Hajjo a bakin aurenta. Idan ba za ta iya zama da ni ba ta karɓi ƙaddararta zan iya sawwaƙa ma ta tun yanzu" yadda yai ta faɗa sai da Goggo ta sa baki yai shiru.
Abun takaicin ma ko gawar É—an sa bai gani ba. Daga Ringim straight Abuja ya wuce ko da wuni É—aya ne gara ya je ya ga Maryam dan ya san yadda ya ke jin sa ita kaÉ—ai ce za ta iya kwantar ma sa da hankali.
Itama ba ta ji daɗin mutuwar ɗan Hajjo ba, ta kuma ƙara tabbatarwa kan ta lallai ba ƙaramin Jahilci ke damun Hajjo da mahaifiyarta ba. Sun Jahilci zamani kuma sun Jahilci addini...

A wasu lokutan da Inna ta kawowa Iya ziyara ne ta zugata akan ta je ta zauna a gidan T J dan ta rinƙa kula da Hajjo idan ba haka ba kuwa Yadda Maryam ta shanye T J ba za ta bari ya haihu da kowa ba tunda gashi har sau biyu tana kashewa Hajjo 'ya'ya.
Iya ta san ba Maryam ce ke kashe 'ya'yan Hajjo ba amma kuma tsanar Maryam ya sa ta hau kan maganar.
Sati biyar da Hajjo ta yi a gida da za ta koma Zaria sai gashi Iya ta tattara kaya itama su ka yi tafiyar tare.

T J ya shiga ruÉ—u lokacin da Iya ta ce za ta zauna da su na wani lokaci. Ba yadda ya iya haka ya tattara kayan É—akin sa ya kai É—akin Maryam ya bar wa Iya É—akin sa.
Bayan kwana biyu da Iya ba ta ga Maryam a gidan ba ne ta tambayi Hajjo ina Maryam ta ke Hajjo ta ce ma ta wai karatu ta ke yi a Habuja.
T J na dawowa ta haushi da faÉ—a wai ya É—aurewa Maryam gindi ta tafi yawon karuwanci.

"Karatu ta tafi Iya kuma na shekara É—aya ne kawai"

"Karatun Uwar ka. Mata ta tafi karuwanci ka ce ta je karatu. Wani irin karatune daya ƙi ci ya ƙi cinyewa shekara da shekaru. Daɗin abin ma ba ta haihuwa balle aje a ɗauko ɗan shege a kawo maka gida. Allah dai ya shirya"

Ransa ya sosu da maganar Iya amma ba abinda zai ce haka yai shiru ya barta ta yi ta masifa har ta gaji ta yi shiru.

Zuwan su Iya ya sa ya rage kaiwa Maryam Ziyara. Maryam ba ta kawo komai ba dan ta É—auka yana ba ta space ne dan ta samu ta yi karatu sosai.

Bai gaya ma ta Iya ta dawo gidan sa da zama ba dan baya so hankalinta ya tashi , yana jiran perfect time ne da zai gaya ma ta wanda ba za ta É—aga hankalinta sosai ba.

End of Chapter 18Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next