Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
By Azizat
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Author: Azizat
Chapter 1 of 161
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 Reading now Chapter 2 1,523 words Chapter 3 1,583 words Chapter 4 1,696 words Chapter 5 1,682 words Chapter 6 1,693 words Chapter 7 1,594 words Chapter 8 1,673 words Chapter 9 1,663 words Chapter 10 1,668 words Chapter 11 1,678 words Chapter 12 1,698 words Chapter 13 1,687 words Chapter 14 1,699 words Chapter 15 1,656 words Chapter 16 1,634 words Chapter 17 1,681 words Chapter 18 1,675 words Chapter 19 1,655 words Chapter 20 1,613 words Chapter 21 1,669 words Chapter 22 1,655 words Chapter 23 1,671 words Chapter 24 1,650 words Chapter 25 1,677 words Chapter 26 1,696 words Chapter 27 1,598 words Chapter 28 1,699 words Chapter 29 1,694 words Chapter 30 1,659 words Chapter 31 1,683 words Chapter 32 1,309 words Chapter 33 1,691 words Chapter 34 1,697 words Chapter 35 1,553 words Chapter 36 1,588 words Chapter 37 1,682 words Chapter 38 1,680 words Chapter 39 1,677 words Chapter 40 1,649 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,698 words Chapter 43 1,676 words Chapter 44 1,625 words Chapter 45 1,633 words Chapter 46 1,675 words Chapter 47 1,693 words Chapter 48 1,668 words Chapter 49 1,688 words Chapter 50 1,647 words Chapter 51 1,653 words Chapter 52 1,568 words Chapter 53 1,689 words Chapter 54 1,699 words Chapter 55 1,669 words Chapter 56 1,578 words Chapter 57 1,564 words Chapter 58 1,660 words Chapter 59 1,694 words Chapter 60 1,415 words Chapter 61 1,653 words Chapter 62 1,690 words Chapter 63 1,685 words Chapter 64 1,618 words Chapter 65 1,652 words Chapter 66 1,674 words Chapter 67 1,687 words Chapter 68 1,699 words Chapter 69 1,644 words Chapter 70 1,698 words Chapter 71 1,691 words Chapter 72 1,671 words Chapter 73 1,689 words Chapter 74 1,679 words Chapter 75 1,677 words Chapter 76 1,678 words Chapter 77 1,655 words Chapter 78 1,683 words Chapter 79 1,696 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,694 words Chapter 82 1,697 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,668 words Chapter 85 1,554 words Chapter 86 1,666 words Chapter 87 1,677 words Chapter 88 1,694 words Chapter 89 1,667 words Chapter 90 1,700 words Chapter 91 1,670 words Chapter 92 1,670 words Chapter 93 1,655 words Chapter 94 1,640 words Chapter 95 1,607 words Chapter 96 1,668 words Chapter 97 1,659 words Chapter 98 1,689 words Chapter 99 1,675 words Chapter 100 1,614 words Chapter 101 1,610 words Chapter 102 1,700 words Chapter 103 1,683 words Chapter 104 1,657 words Chapter 105 1,698 words Chapter 106 1,700 words Chapter 107 1,695 words Chapter 108 1,656 words Chapter 109 1,683 words Chapter 110 1,699 words Chapter 111 1,699 words Chapter 112 1,641 words Chapter 113 1,696 words Chapter 114 1,626 words Chapter 115 1,695 words Chapter 116 1,691 words Chapter 117 1,698 words Chapter 118 1,645 words Chapter 119 1,673 words Chapter 120 1,691 words Chapter 121 1,635 words Chapter 122 1,694 words Chapter 123 1,689 words Chapter 124 1,688 words Chapter 125 1,673 words Chapter 126 1,692 words Chapter 127 1,686 words Chapter 128 1,697 words Chapter 129 1,660 words Chapter 130 1,691 words Chapter 131 1,674 words Chapter 132 1,670 words Chapter 133 1,693 words Chapter 134 1,691 words Chapter 135 1,687 words Chapter 136 1,672 words Chapter 137 1,691 words Chapter 138 1,657 words Chapter 139 1,687 words Chapter 140 1,650 words Chapter 141 1,695 words Chapter 142 1,607 words Chapter 143 1,699 words Chapter 144 1,676 words Chapter 145 1,698 words Chapter 146 1,684 words Chapter 147 1,664 words Chapter 148 1,696 words Chapter 149 1,674 words Chapter 150 1,680 words Chapter 151 1,697 words Chapter 152 1,628 words Chapter 153 1,618 words Chapter 154 1,688 words Chapter 155 1,664 words Chapter 156 1,692 words Chapter 157 1,584 words Chapter 158 1,644 words Chapter 159 1,646 words Chapter 160 1,618 words Chapter 161 1,797 words

ZAYTOONAH COMPLETE
*...... ...... .......ZAYTOONAH*

Rubutawa.....Azizat
Wattpad@Azi_zat

*Free page*
*1- Mbom-uzo festival*

Bismillahir Rahmanir Rahim

1985

"Dear let's just leave, my mind is not at peace here" Abinda Caroline ta faɗawa mijinta kenan a karo na ba adadi tun zuwan su ƙauyen mijin na ta wato Okwuohia Village.

Kamar kullum haƙuri ya shiga ba ta akan ta bari su yi christmas a ƙauyen kafin su tafi. Wannan karan kam Caroline ta ƙi fir musamman saboda mafarkin da ta yi jiya da dare. Ganin yayi yayi ta haƙura ta ƙi ne ƙarshe ya nuna ma ta zai yi tunani a kai.
Caroline ta turɓune fiska ta ce ma sa matuƙar ya ƙi ba ta ƙwaƙwƙwarar amsa zuwa dare to za ta ɗauki 'yar ta su bar ƙauyen gobe da safe.

"Please Carol" ya faÉ—a yana haÉ—a hannuwansa biyu. Shigowar 'yar su ne ya dakatar da Caroline daga maganar da ta ke son yi.

Yarinyar da gudu ta shigo É—akin ta faÉ—a jikin mahaifinta tana haki saboda gudun da ta yi.

"Daddy i didnt miss the steps today. I'm ready for the festival" with so much excitement ta ke maganar.
Ta miƙe ta fara rawan Atilogwu wanda ta ke koya tun kwana shida da su ka shige. Tana yi mahaifinta na ma ta tafi yayinda mahaifiyarta ta haɗe fiska saboda yanayin da ta ke ciki na tsanar ƙauyen mijin na ta da duk abin da ke ƙauyen.

Bayan ta gama rawan ne ta fita da gudu akan za ta je ta yi wanka. Bayan fitar ta daga É—akin Patrick ya kalli matar sa ya ce cikin harshen turanci "ki bari ayi bikin Mbom-uzo sai mu tafi, idan mu ka tafi ba ayi bikin nan ba Nkiru ba za ta ji daÉ—i ba"

"Yaushe ne bikin?"

"Nan da kwana huÉ—u" Patrick ya faÉ—a yana fatan Caroline ta amince.
Sai da ta ja dogon numfashi kafin ta ce "ana gama biki za mu tafi" Patrick ya gyaÉ—a ma ta kai...

Kwanaki goma da su ka wuce Patrick da matar sa Caroline da tilon 'yar su Mary-Nkiru su ka zo ƙauyen Okwuohia wacce ta ke ƙarƙashin Obowo Local Government da ke jahar Imo. Sun zo ne da niyyar sai bayan Christmas za su koma gidan su da ke cikin Owerri. Wannan karan ne zuwan su Nigeria na farko tun bayan da su ka koma Ingila da zama, hakan ya sa Nkiru ke jin daɗin ƙauyen saboda rayuwa ce da ba ta taɓa sanin akwai shi ba sai da ta gani da idon ta. A Ingila aka haifeta kuma wannan ne karo na farko da ta bar ƙasar Sarauniya Elizabeth zuwa ƙasar iyayenta wato Nigetia.

***

Yana zaune akan madaidaicin teburin da ke ɗakin na sa yana ta ƙoƙarin lissafi aka shigo ɗakin.
"T J the mathematician" guntun saurayin da ya shigo sanye da uniform ɗin 'yan bautar ƙasa ya faɗa yana ƙoƙarin zama akan yaloluwar katifar sa da ke shimfiɗe a ƙasa.

"Eze welcome, how's the class?"

"Fine ooo, but my guy i don tire"

T J ya juyo ya É—aga ma sa yatsu huÉ—u.

Eze ya ce " 4 months is still long my friend"

T J yai dariya.

Bayan Eze ya chanja kaya ne ya fara ƙoƙarin haɗa gari dan bai yi girki ba kafin ya tafi. T J ya ce ya ɗau plate ya ɗeba abinci a tukunya. Eze yai ihu kafin ya ɗau plate ɗin da sauri ya fara ɗiban dafa dukan shinkafa da T J ya dafa.
Har ya gama ci T J bai bar lissafin da ya ke yi ba. Dama ya san ɗan ɗakin na sa indai ya samu lissafi to ba ya iya cin abinci har sai ya ga ya cracking na shi ya wargazata. Akwai ranan da ya fara da dare har Asuba bai iya samun amsa ba haka ya wuni ba abinci a cikinsa wai shi da cin abinci sai ya samu amsan lissafin nan. Haka Eze ya zuba ma sa ido har ƙarfe shida na yamma kafin ya samo amsar. Banda sallah ba abinda ke sa wa T J ya tashi a waje idan yana lissafi.

Ganin shirun yayi yawa ne ya sa Eze tambayar T J maganar tafiyar su ƙauyen Okwuohia nan da kwana uku.
Ba tareda TJ ya ɗago ba ya ce " wani ƙauye kenan?"
Eze ya ce ma sa ƙauyen da su ka je siyan manja sati biyu da su ka wuce. T j ya ce "ohoooo"

"Za mu je festival É—in ai ko?"

"Kai ni fa ba na son wajen da zan je a yanke min wuya"

Eze ya kwashe da dariya tunowa da yai da labarin da T J É—in ya bashi farkon zaman su.

Bayan T J ya fito daga camp wani ƙaramin ƙauye da ke chan wani lungu chan gaba da ƙauyen Amuzi, bayan ka bar ƙauyen Amuzi za ka yi tafiyar kusan awa biyu da rabi a ƙafa kafin ka kai ƙauyen. Su uku aka tura ƙauyen dukkan su babu Igbo a ciki, shi Bafulatanin Arewa sauran kuma ɗaya Bayarabe ɗaya kuma ɗan Jos ne yaren Angas. Gaba ɗaya ƙauyen ba musulmi kuma 80% ɗin su addinin gargajiya su ke bi sauran kaso ishirin ɗin kuma Christians ne.
Watarana T J ya fita da sassafe zai je ƙaramin primary school da ya ke koyarwa ya haɗu da wasu sun yi shigan jajayen kaya su na riƙe da sanduna wasu da ƙwarya, jikin su da fiskokinsu ya sha zane da farin alli, suna tafiya su na maganganun su na siddabaru. T J ya zo ta gaban su zai wuce ya ji an damƙo shi kafin ka ce me an fara dukan sa. Ƙarshe aka ɗaure shi aka kai shi gaban Dibia na garin (Boka) T J dai tun da aka ɗaure shi ya ke addu'a a ransa.
Dibia ɗin wani ƙazami da shi sai wari ya ke ya nufo T J da ke ɗaure yana riƙe da wani sanda wanda saman sandar wani ƙwarangal ɗin wata dabba ce akai an ɗaureta da jar ƙyalle. Tunda ya nufo shi T J ya fara karanto ayatul Kursiyyu da ƙarfi nan take sandar hannun Dibia ɗin ya kama da wuta. Dibia ya yarda sanda yana ihu yana surkulle chan ya ce a fita da T J domin gunki na fushi da shi, wai aje a yanka shi a tsakiyar gari. Aka fita da T J ana ihu shi kuma yana maimaita Ayatul Kursiyyu.

Sai da su ka iso tsakiyar gari aka fara shela akan za a yanka baƙo wanda ya ƙi bin dokar ƙasar su, dan haka ayi shaida, hukuncin kisa ce za ta zamo sakamakon duk wanda ke wasa da dokar Amadioha.

Cikin 'ya'yan sarkin ƙauyen akwai wanda ya fara karatu har yana matakin sakandare a Owerri, shi tuni ya jima da zama christian shiyasa ya yi watsi da al'adun su na gargajiya. Jin abinda ake faɗa ne ya sa shi fitowa da gudu dan ya san babu baƙi a garin sai 'yan Bautar ƙasa guda uku da aka turo sati ɗaya da ya wuce. Yana zuwa kuwa ya hango T J ɗaure ga wani daga cikin matsafan wajen ya riƙe wuƙa yana wulli da ita a sama yana surkulle.

Nnadozie ya ƙarisa ya fara magana akan su sake T J saboda shi baƙo ne bai san dokar ƙauyen ba. Aka ma sa chaa akan ba za a sake shi ba domin ya taka dokan ƙasa. Ranan da ba a fitowa da takalmi saboda biyayya ga mai girma Amadioha ya fito da takalmi kuma ba a fitowa waje sai rana ta fito shi kuma ya fito waje kafin rana ta fito, dan haka dole a kashe shi kuma babban Dibia ma ya ce gunki na fushi da T J.
Ganin dai ba za su fahimce shi ba ne ya sa ya ce idan su ka kashe T J to gwamnati za ta turo a hallaka mutanen ƙauyen gaba ɗaya. Wa su a ciki su ka fara kallon juna suna ƙusƙus amma wanda ke riƙe da wuƙan ya ce bai yarda ba. Ganin sun tsaya yanke shawara tsakanin su ya sa shi komawa gidan su ya sami Baban sa ya gaya ma sa idan har baya so gwamnati ta shafe ƙauyen su a doron ƙasa to ya je yai magana kar a kashe T J, domin T J wakilin Gwamnati ne. Da jin haka Sarki ya razana ya bi bayan Nnadozie su ka je wajen, wanda har lokacin ana ta muhawara akan ko a yanka T J ko kar a yanka shi.

Sarki yai magana nan aka tsaida zance akan T J zai bar ƙauyen saboda kar ya jawo mu su fushin Amadioha sannan za ayi sacrifice da jan Taure da farin Zakara.
Nnadozie ya kunce T J ya taimaka ma sa su ka koma masaukin su. Sai da su ka je ne sauran ke jajen abinda ya faru. Ashe headmaster na makarantar ya kira Bayo da Felix ya gaya mu su kar su fito yau saboda wani ritual da za ayi a ƙauyen. Su kuma sun ɗauka ya gayawa T J shiyasa ba su kula ba ma da safen da ya shirya ya fita. Shi kuma headmaster haushin T J ya ke ji kasancewar sa musulmi shiyasa bai faɗa ma sa ba.

Wannan abun da ya faru ya sa T J da Nnadozie su ka je su ka yi complain a Owerri nan aka mai da shi cikin Obowo local government kuma a nan a sakandare ya ke koyarwa ba primary ba.
Sauran abokan na sa ma daga baya guduwa su ka yi saboda gargajiyan ƙauyen yayi yawa ga wahala da su ke yi saboda rashin ruwa mai kyau.

Saɓanin wancan ƙauyen garin Obowo na da cika kuma yana da basic amenities da ake buƙata sai dai nan ɗin ma ba masallaci, dan Jummu'ah sai ya je Capital Owerri kafin yai sallar Jumu'ah. Kamsu Salawat kuwa haɗuwa su ke a ɗakin wani Bayarabe ɗan Kwara su na sallar. Akwai 'yan tsirarun musulmai da su ke garin wanda duk kasuwanci ya kawo su, akwai Hausawa akwai kuma yarabawa sai dai a wannan lokacin kan 'yan tsiraru su ke a garin ba su fi a irga su ba...

***

End of Chapter 1Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Login to Save Next