Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
By Azizat
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Author: Azizat
Chapter 85 of 161
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,689 words Chapter 2 1,523 words Chapter 3 1,583 words Chapter 4 1,696 words Chapter 5 1,682 words Chapter 6 1,693 words Chapter 7 1,594 words Chapter 8 1,673 words Chapter 9 1,663 words Chapter 10 1,668 words Chapter 11 1,678 words Chapter 12 1,698 words Chapter 13 1,687 words Chapter 14 1,699 words Chapter 15 1,656 words Chapter 16 1,634 words Chapter 17 1,681 words Chapter 18 1,675 words Chapter 19 1,655 words Chapter 20 1,613 words Chapter 21 1,669 words Chapter 22 1,655 words Chapter 23 1,671 words Chapter 24 1,650 words Chapter 25 1,677 words Chapter 26 1,696 words Chapter 27 1,598 words Chapter 28 1,699 words Chapter 29 1,694 words Chapter 30 1,659 words Chapter 31 1,683 words Chapter 32 1,309 words Chapter 33 1,691 words Chapter 34 1,697 words Chapter 35 1,553 words Chapter 36 1,588 words Chapter 37 1,682 words Chapter 38 1,680 words Chapter 39 1,677 words Chapter 40 1,649 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,698 words Chapter 43 1,676 words Chapter 44 1,625 words Chapter 45 1,633 words Chapter 46 1,675 words Chapter 47 1,693 words Chapter 48 1,668 words Chapter 49 1,688 words Chapter 50 1,647 words Chapter 51 1,653 words Chapter 52 1,568 words Chapter 53 1,689 words Chapter 54 1,699 words Chapter 55 1,669 words Chapter 56 1,578 words Chapter 57 1,564 words Chapter 58 1,660 words Chapter 59 1,694 words Chapter 60 1,415 words Chapter 61 1,653 words Chapter 62 1,690 words Chapter 63 1,685 words Chapter 64 1,618 words Chapter 65 1,652 words Chapter 66 1,674 words Chapter 67 1,687 words Chapter 68 1,699 words Chapter 69 1,644 words Chapter 70 1,698 words Chapter 71 1,691 words Chapter 72 1,671 words Chapter 73 1,689 words Chapter 74 1,679 words Chapter 75 1,677 words Chapter 76 1,678 words Chapter 77 1,655 words Chapter 78 1,683 words Chapter 79 1,696 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,694 words Chapter 82 1,697 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,668 words Chapter 85 Reading now Chapter 86 1,666 words Chapter 87 1,677 words Chapter 88 1,694 words Chapter 89 1,667 words Chapter 90 1,700 words Chapter 91 1,670 words Chapter 92 1,670 words Chapter 93 1,655 words Chapter 94 1,640 words Chapter 95 1,607 words Chapter 96 1,668 words Chapter 97 1,659 words Chapter 98 1,689 words Chapter 99 1,675 words Chapter 100 1,614 words Chapter 101 1,610 words Chapter 102 1,700 words Chapter 103 1,683 words Chapter 104 1,657 words Chapter 105 1,698 words Chapter 106 1,700 words Chapter 107 1,695 words Chapter 108 1,656 words Chapter 109 1,683 words Chapter 110 1,699 words Chapter 111 1,699 words Chapter 112 1,641 words Chapter 113 1,696 words Chapter 114 1,626 words Chapter 115 1,695 words Chapter 116 1,691 words Chapter 117 1,698 words Chapter 118 1,645 words Chapter 119 1,673 words Chapter 120 1,691 words Chapter 121 1,635 words Chapter 122 1,694 words Chapter 123 1,689 words Chapter 124 1,688 words Chapter 125 1,673 words Chapter 126 1,692 words Chapter 127 1,686 words Chapter 128 1,697 words Chapter 129 1,660 words Chapter 130 1,691 words Chapter 131 1,674 words Chapter 132 1,670 words Chapter 133 1,693 words Chapter 134 1,691 words Chapter 135 1,687 words Chapter 136 1,672 words Chapter 137 1,691 words Chapter 138 1,657 words Chapter 139 1,687 words Chapter 140 1,650 words Chapter 141 1,695 words Chapter 142 1,607 words Chapter 143 1,699 words Chapter 144 1,676 words Chapter 145 1,698 words Chapter 146 1,684 words Chapter 147 1,664 words Chapter 148 1,696 words Chapter 149 1,674 words Chapter 150 1,680 words Chapter 151 1,697 words Chapter 152 1,628 words Chapter 153 1,618 words Chapter 154 1,688 words Chapter 155 1,664 words Chapter 156 1,692 words Chapter 157 1,584 words Chapter 158 1,644 words Chapter 159 1,646 words Chapter 160 1,618 words Chapter 161 1,797 words

Shekara ɗaya da rabi kenan da fara aikin sa bayan ya kammala degree da kuma Law school ɗin sa. Barrister Auwal Usman Abubakar kenan saurayi ɗan ƙwalisa. Yana da kyau, ilimi, tsabta ga uwa uba kamala.

Cikin shekaru huÉ—u da Zaytoonah ta haihu abubuwa da dama sun faru. Ciki kuwa har da chanjin yanayi da su Iya su ka tsinci kan su. Rana É—aya Alhaji Rabi'u ya zo ya ce ya ba su sati biyu su tattara su bar gidan Muntari domin shi ya riga ya saida gidan. Iya ta buÉ—i baki tana Allah wadarai da halin sa amma ya nuna ko ajikin sa har da ce ma ta ai tun farko a gidan T J take amma kwaÉ—ayi ya sa ta komawa gidan Muntari. Abun wasa su ka É—auka sai da sati biyun su ka cika aka kawo mu su notice kan cewa su fita daga gidan ko kuma dai a haÉ—a su da hukuma.
Iya sai da ta yi kuka lokacin da aka ce mu su an ƙara mu su kwana uku. Ta kira gida tayi ƙorafi, hatta mahaifin Rabi'un ta kira shi ta sanar da shi abinda ɗan sa ke shirin yi amma sai ya nuna ma ta ai da gaskiyar sa tunda dai babu Muntari a gidan ba su da ikon zama su uku kacal a wannan makeken gidan gara a siyar idan ya so ayi jari da kuɗin a dinga juyawa kafin Muntari ya dawo. A lokacin Iya ta gane cewa cin amana ba shi da alaƙa da addini ko yare domin kowa na iya yi. Tun kafin ya zo zancen sai da gida ya riga ya dena tura mu su kuɗin da ya ke ba su duk wata. Abinda ma Iyan ba ta sani ba shine tuntuni Maryam 'yar Mukhtari Mommy ke biya ma ta kuɗin makaranta ba wai Rabi'un ba kamar yadda ta ke tunani.

A waɗanda Iyan ta kira cikin 'yan uwanta da ta san sun ɗan yi Boko shine aka ba ta shawara akan su kai ƙaran Rabi'u saboda a bi mu su hakkin su. Da ta yiwa Hanne magana Hanne ta ce ita ba ta da kuɗin ɗaukan lawyer itama tun da aka rufe Muntari ita ke fama da biyawa kanta kuɗin makaranta da sauran hidimomi kuma yanzu da ta ke ajin ƙarshe ma tana buƙatar kuɗi ga kuma kasuwancin na ta ya ja baya.
Bayan dogon nazari da Iya ta yi sai ta tuna cewa ai Maryam ma tsohuwar Lawyer ce ko ba ta taimaka mu su bama za ta haɗa su da wanda zai taimaka mu su. Kamar yadda har yanzu girman kai ya hanata baiwa Maryam haƙuri balle har ta jata a jiki hakan ya sa ta kira Maryam a waya tana ma ta maganar halin da ake ciki da kuma taimakon da ta ke so ta mu su.
Maryam ta san komai gameda abinda ke faruwa saboda Hanne ta gaya ma ta har ma sun tsaida matsaya kan abinda za ayi.

Bayan Maryam ta gama sauraron bayanin Iya sai ta ce " ba ni da hurumi da dukiyar Muntari, da dukiyar Tijjani ne zan iya yin komai akai amma wannan ba hurumina ba ne. Idan ba ki manta ba, farkon lokacin da aka rufe Muntari na zo miki da wata magana kan abinda Rabi'u ya ke shirin yi amma kika zageni tatas kika nuna nine ummul aba'isil duk abinda ya faru har kike iƙirarin Rabi'u ɗan uwa na ƙwarai ne, to gashi yau Allah ya bayyana gaskiya tunda dai abinda na ke gudu mu ku tun farko sai da ya faru. Kuma..."

Iya ta kashe wayar dan ba za ta iya cigaba da sauraron maganganun Maryam ba. Tabbas maganarta babu ƙarya a ciki tunda anyi hakan amma a lokacin haushin Maryam da ta ke ji ya sa ta ƙi sauraron shawaran da Maryam ta kawo balle har ayi aiki da shi, bata ma yarda da zargin Rabi'un da ta ke yi ba a lokacin. Abinda kuma ba su sani ba shine tuntuni Rabi'u ya sa aka chanjawa Muntari Prison. Da farko a Kaduna ya ke amma yanzu dukkan su babu wanda ya san inda aka maidashi. Shi yanzu ma burinsa bai wuce Muntari ya mutu ba ko kuma dai ya cigaba da zama a kurkuku har mutuwar sa. Baya tunanin ko da wasa zai iya maidawa Muntari dukiyar sa a yadda yake jin sa yanzu ne ya san jin daɗin rayuwa.

Maganar komawa Ringim ta yiwa Hanne sai Hanne ta ce "Maryam ta ce mu koma gidan Hamma Tijjani. Jiya wanda su ke zaune a ciki suka tashi yau za ayiwa gidan kwaskwarima gobe sai mu koma"

Iya ta sauke ajiyar zuciya tunda dai an samu maslaha dan dama niyyarta Humairah ta koma wajen Maryam ne saboda karatunta ita kuma sai ta koma Ringim.

A haka Hanne da 'yarta, Humairah da kuma Iya su ka koma gidan Tijjani wanda Hajjo ta zauna da. Kasancewa dukkan su mata ne ya sa Mommy ta ce Auwal ya koma gidan saboda tsaro bai so ba amma kuma ba yadda ya iya.

Cikin ikon Allah Hanne ta kammala karatunta har ta yi bautar ƙasa a Nasarawa state da ta dawo kuwa zawarawa da samari su ka ma ta chaaaa. Tun shekara ɗaya da rufe Muntari ta je kotu aka warware auren su. Aikin koyarwa ta samu a wani makarantar Sakandare ta gwamnati, ta yi shekara tana aiki kafin ta yi aure, ta auri Wani Lecturer da ke KadPoly mutumin Zaria ne amma a Kaduna ya ke zaune da matar sa ɗaya. Ita dai Hanne tana zaune a gidan sa na Zaria yana zuwa ma ta a weekend ko ita ta je. Aiki ma yake nema ma ta da ta samu a Kadunan sai ta dawo chan amma yanzu samun aikin gwamnati na da wahala. Da ke ba sa shiri da matar sa Zahra shiyasa ma ba ta takura da komawa Kadunan ba dan zamanta a Zaria ya fi ma ta kwanciyar hankali.

***

Iya na zaune a falo tana kallo lokacin da yai sallama ya shigo falon. Humairah tana kwance a three sitter sanye ta ke da riga mai hannun shimi ja sai baƙin jeans, kanta babu ɗankwali ta sha kitson brazillian wool wanda aka ƙarashi ya sauka har tsakiyar bayan ta, abu ɗaya da ke tauye mata zama cikakkiyar Fulani kenan a idon mafiya yawan jama'a saboda Allah bai bata gashi ba. Gata fara doguwa sirirya mai dogon hanci zubin Fulani amma gashin kam suɗal ya ke, yaƙi yin gaba kullum dai hakan nan ya ke. Akwai lokacin da ta yi ta kashe kuɗi wajen siyan magungunan ƙara gashi su Chebe and co, amma da gashin ya ƙi responding sai ta shareshi ta koma saka brazillian wool da kuma wig duk da kuwa abunda Hamma Auwal ɗin ta ya ƙi jini kenan. Ta saka headphone a kunne tana sauraron waƙa yayinda idonta ya ke bin kowani layi na rubutun labari da ta ke karantawa a waya.

"Ban hanaki zama a cikin gida haka ba?" Auwal ya daka ma ta tsawa.

Ta yi saurin cire headphone É—in dan ba ta ji mi ya faÉ—a ba inuwar sa kawai ta gani "Hamma sannu da zuwa, ya office?"

"Ki je ki rufe kan ki sannan ki chanja riga ko kuma ki saka hijabi"

"Hamma zafi ake yi" ta zumɓuro baki tana shagwaɓa.

Bai kulata ba ya wuce É—aki saboda a gajiye ya ke baya son magana...

Kamar yadda su ka saba al'adar su ta cin abinci tare yau ma dukkan su biyar suna zagaye gaban tray suna cin shinkafa da miyan sauce É—in manja wanda ya ji busashahiyar kifi.

Tsabar rigima maimakon su nitsu su ci abinci kowa ya ci gaban sa sai kaga wannan ya tsakuri gaban wannan wannan ma yayi hakan. Wani ƙaton lomar kifi Hashir ya ɗauke daga gaban Hadid sai Hadid ya riƙe cokalin yana faɗin "put it down" Hashir ya sa hannu yai saurin ɗauke kifin zai kai baki sai Hadid ya riƙe hannun.
"GrandMa Hashir wants to take my fish"

Kafin ta yi magana Salman ya sa yatsa ya talli fiskar Hashir sannan ya yiwa Hadid yana faɗin kowa ya ci gaban sa baya son rigima. Dama Uncle Salman ne maganin su a gidan dan Uncle Auwal baya taɓa su amma Salman har xanesu yanayi.

Hadid ya tashi ya dawo gefen Mommy ya zauna ya fara cin abinci yana yiwa Hashir gwalo. Sai shima Hashir ya taso ya zo gefen Mommy ya zauna ya fara cin abinci yana nunawa Hadid Harshe. Su ka koma ba ma abincin su ke ci ba sai gwalo da zare ido da su ke yiwa juna. Sai da Salman ya daka mu su tsawa kafin su ka nitsu.

Duk rigiman su Mommy ba ta iya dukan su ko ta ce za ta basu punishment. Tausayi su ke ba ta, yaran kaman ba za su yi rai ba watannin farko na haihuwar su saboda Zaytoonah ta haifesu ne lokacin da take fama da Post traumatic stress disorder (PTSD) ƙarshe lokacin da ake yiwa Zaytoonah therapy yaran kam Madara aka koma basu. Ashe ba mutuwar Zuhayr kaɗai ya girgiza Zaytoonah ba. Long time effects na tsoratarwa da kuma abubuwan da Ben yayi ta yi ya shafi ƙwaƙwalwar Zaytoonah. Idan abinta ya tashi mantawa ta ke yi Ben ya mutu hakanan ma Zuhayr ɗin ta shima ya mutu.

End of Chapter 85Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next