Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
By Azizat
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Author: Azizat
Chapter 157 of 161
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,689 words Chapter 2 1,523 words Chapter 3 1,583 words Chapter 4 1,696 words Chapter 5 1,682 words Chapter 6 1,693 words Chapter 7 1,594 words Chapter 8 1,673 words Chapter 9 1,663 words Chapter 10 1,668 words Chapter 11 1,678 words Chapter 12 1,698 words Chapter 13 1,687 words Chapter 14 1,699 words Chapter 15 1,656 words Chapter 16 1,634 words Chapter 17 1,681 words Chapter 18 1,675 words Chapter 19 1,655 words Chapter 20 1,613 words Chapter 21 1,669 words Chapter 22 1,655 words Chapter 23 1,671 words Chapter 24 1,650 words Chapter 25 1,677 words Chapter 26 1,696 words Chapter 27 1,598 words Chapter 28 1,699 words Chapter 29 1,694 words Chapter 30 1,659 words Chapter 31 1,683 words Chapter 32 1,309 words Chapter 33 1,691 words Chapter 34 1,697 words Chapter 35 1,553 words Chapter 36 1,588 words Chapter 37 1,682 words Chapter 38 1,680 words Chapter 39 1,677 words Chapter 40 1,649 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,698 words Chapter 43 1,676 words Chapter 44 1,625 words Chapter 45 1,633 words Chapter 46 1,675 words Chapter 47 1,693 words Chapter 48 1,668 words Chapter 49 1,688 words Chapter 50 1,647 words Chapter 51 1,653 words Chapter 52 1,568 words Chapter 53 1,689 words Chapter 54 1,699 words Chapter 55 1,669 words Chapter 56 1,578 words Chapter 57 1,564 words Chapter 58 1,660 words Chapter 59 1,694 words Chapter 60 1,415 words Chapter 61 1,653 words Chapter 62 1,690 words Chapter 63 1,685 words Chapter 64 1,618 words Chapter 65 1,652 words Chapter 66 1,674 words Chapter 67 1,687 words Chapter 68 1,699 words Chapter 69 1,644 words Chapter 70 1,698 words Chapter 71 1,691 words Chapter 72 1,671 words Chapter 73 1,689 words Chapter 74 1,679 words Chapter 75 1,677 words Chapter 76 1,678 words Chapter 77 1,655 words Chapter 78 1,683 words Chapter 79 1,696 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,694 words Chapter 82 1,697 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,668 words Chapter 85 1,554 words Chapter 86 1,666 words Chapter 87 1,677 words Chapter 88 1,694 words Chapter 89 1,667 words Chapter 90 1,700 words Chapter 91 1,670 words Chapter 92 1,670 words Chapter 93 1,655 words Chapter 94 1,640 words Chapter 95 1,607 words Chapter 96 1,668 words Chapter 97 1,659 words Chapter 98 1,689 words Chapter 99 1,675 words Chapter 100 1,614 words Chapter 101 1,610 words Chapter 102 1,700 words Chapter 103 1,683 words Chapter 104 1,657 words Chapter 105 1,698 words Chapter 106 1,700 words Chapter 107 1,695 words Chapter 108 1,656 words Chapter 109 1,683 words Chapter 110 1,699 words Chapter 111 1,699 words Chapter 112 1,641 words Chapter 113 1,696 words Chapter 114 1,626 words Chapter 115 1,695 words Chapter 116 1,691 words Chapter 117 1,698 words Chapter 118 1,645 words Chapter 119 1,673 words Chapter 120 1,691 words Chapter 121 1,635 words Chapter 122 1,694 words Chapter 123 1,689 words Chapter 124 1,688 words Chapter 125 1,673 words Chapter 126 1,692 words Chapter 127 1,686 words Chapter 128 1,697 words Chapter 129 1,660 words Chapter 130 1,691 words Chapter 131 1,674 words Chapter 132 1,670 words Chapter 133 1,693 words Chapter 134 1,691 words Chapter 135 1,687 words Chapter 136 1,672 words Chapter 137 1,691 words Chapter 138 1,657 words Chapter 139 1,687 words Chapter 140 1,650 words Chapter 141 1,695 words Chapter 142 1,607 words Chapter 143 1,699 words Chapter 144 1,676 words Chapter 145 1,698 words Chapter 146 1,684 words Chapter 147 1,664 words Chapter 148 1,696 words Chapter 149 1,674 words Chapter 150 1,680 words Chapter 151 1,697 words Chapter 152 1,628 words Chapter 153 1,618 words Chapter 154 1,688 words Chapter 155 1,664 words Chapter 156 1,692 words Chapter 157 Reading now Chapter 158 1,644 words Chapter 159 1,646 words Chapter 160 1,618 words Chapter 161 1,797 words

Rashin zuwan Humairah duba shi bayan kowa ya zo ya ƙara kashewa Auwal jiki. Kenan da gaske fa ta dena son shi.

Bai iya kwana a Asibitin ba kusan ƙarfe tara na dare aka sallameshi ya koma gida...

"Anty Zaytoonah kinaga ba zan faÉ—awa Hamma gaskiya ba. Ina tsoron kar wani abu ya sameshi"

"Kul, ki bari ya zo da kan sa ya nemi soyayyar ki"

"Anya zan iya?"

"Ke ki ka sani ai" Zaytoonah ta faɗa tana ɗaukan jakan ta. Tun kusan minti bakwai da ta wuce Galadima ya kira akan ya zo ɗaukan ta amma ta taɗi, yanzun ma Mommy ne ta ƙwala ma ta kira shine ta fita...

Tana shiga mota ta samu Galadima na amsa waya. Daga yadda ya ke maganar ta gane da mace ya ke wayar. Ta takure gefe ta sha kunu amma kuma duk hankalin ta na kan maganar da ya ke yi.
Sai da su ka kusa isa gida tukunna ya gama wayar. Ya kamo hannun Zaytoonah zai riƙe ta yarfe hannun.
Ƙyaleta yai sai da su ka isa gida kafin ya tambayi lafiya ta ke haɗa ma sa rai dan shi bai ɗauka wayar da ya ke ne ma ya sa ta fushi ba tunda ya san faɗan su na rashin barinta ta zo gida washegarin ranan da su ka sauka ya riga ya wuce.
Wata matar ƙanin sa ce ta kirashi ta ke ma sa ƙorafin wai ƙanin shi zai ƙara aure kuma bai gaya ma ta ba sai yanzu da biki ya saura wata ɗaya.

"Baby miye matsalar ki? Na san dai lafiya lau dai ki ka baro su Daddy"

"Na ce ma ka ina da matsala ne? Duk da dai ka koma aikin counselling to ni ban nemi service É—in ka ba. Akai wa Mata ma su matsalar aure"

"Ke baki da matsala da ni kenan"

"Allah ya rabani da matsala"

Galadima ya ɗan haɗe rai ya ce "tunda ba ki da matsala dama akwai wata 'yar bautar ƙasa da aka kawota office ɗina. Na ga yarinyar akwai hankali, inaga kawai zan kawo miki ita ta taya ki zama"

"A wa É—in?"

"Ke mana"

"To ka kawo mana, ni ina ruwana. Ba 'yar bautar ƙasa ba ko 'yar bautar duniya ce ka kawo ta mu gani. Ba matar da za ta bani tsoro a gidan nan"

Wucewa ta yi ɗakinta ran ta a jagule. Yaran suna Fada, Alinah kuma ta barta wa Mommy. Tana shiga ɗaki ta fiddo da wayarta daga jaka ta shiga kiran Ahmad ƙirjinta na bugawa da ƙarfi-ƙarfi.

Ba a É—auka ba sai a bugu na biyu sannan aka É—auka.

"Maman 'yan biyu lafiya?" Ya faÉ—a yana sake duba agogon hannun sa.

"Ahmad wace Corper ce a office É—in ku?"

"Corper kuma?"

"Yes, na ji ance an tura wata Corper office É—in Justice"

Ahmad ya ƙyalƙyale da dariya.

"Ahmad ya kake dariya, ka gaya min mana"

"E" ya faÉ—a lokacin da ya tsagaita dariyan "akwai wata tsaleliyar budurwa da aka kawo mana ita kwanan nan. Yarinyar nan ga kyau ga diri, irin figure 8 É—in nan"

Zaytoonah ta yi saurin dafe ƙirjinta da ke ma ta zafi.

Shirun da Zaytoonan ta yi ne ya sa shi jin tsoro, kar dai ta shiga matsala saboda abunda ya faÉ—a. Dan ya riga ya gane kishi ne ya sa ta bugowa.

"Maman 'yan biyu Uncle baya karɓan 'yan bautan ƙasa a office ɗin sa"

Sai alokacin ƙwaƙwalwarta ya fara aiki. Tabbas lokacin da ta ke koyon aiki a wajen dayawa da farko sun ɗauka bautar ƙasa ta zo yi shine ma su ke mamakin zuwanta tunda sun san Justice baya karɓa sai daga baya su ka gane she's already a Barrister ma ba wai half baked Lawyer ba ce. Chamber ɗin sa na Zaria kam ana karɓa amma banda na Abuja.

Hannu Galadima ya sa a ƙungunta ya jawota jikinsa.
Saurin katse kiran ta yi jin muryan Ahmad na faÉ—in Hello Hello. Juyowa ta yi tana kallon sa tareda turo baki.

"Na É—auka ai kin ce ba kya tsoron kowacce mata"

"Justice Yunus da yanzu jini na ya hau mi za ka ce?"

"Sai na ce wagga mata akwai cika baki, amma shegen tsoro gareta"

"Ni ba na tsoro" ta faÉ—a tana nuna kan ta

"Kawai dai ina tausayin wacce za ta shigo ne, dan dai na riga na gama sanin sirrin ba abinda za ta zo da shi"

"Mi zai hana mu ƙarisa chan a nuna min sirrin"
Ya faÉ—a yana kissing wuyan ta. Zaytoonah ta yi murmushi.

***

Washegari Humairah ta kira Zaytoonah ta sanar ma ta ai bayan tafiyarta Auwal ya kirata a waya.

Zaytoonah na naÉ—e boxers É—in Justice da ta wanke ta yi saurin ajiye shi gefe ta ce "ba ni labari mi ya ce mi ki?"

"Anty Zaytoonah na kwabsa fa sosai. Wallahi tausayi ya bani shine na fallasa komai"

"Kinci gidan ku Airah"

"Kai Anty"

"To mi zan ce bayan kin ɓata mana show"

"I'm just pulling your legs, ban gaya ma sa gaskiya ba sai da ya faÉ—i sirrin da ke zuciyar sa"

"Da gaske?"

"Allah, barin ma tura miki ki ji dan na recording wayar da mu ka yi"

Bayan Zaytoonah ta kunna recording É—in ta saurara sai ta ji tausayin Auwal ya kamata.

Tambayar Humairan yai akan miyasa ba za ta aure shi ba. Ita kuma ta ce ma sa saboda baya son ta, ita ba za ta iya auran wanda baya son ta ba.

"Kina ganin ba na son ki ne?"

"Hamma ba ka sona, ba ka taɓa cewa kana sona ba, ba ka taɓa nuna min so ba, kullum kusheni ka ke yi"

"Wannan shine hujjar?"

"E"

"Ki yi haƙuri Aysherh. Indai irin soyayyar nan da ki ke yi da samarin ki ne ba zan iya yi mi ki shi ba. Ina son duk wata soyayya da zamu yi to ya kasance cikin gidan mu ne"

"Kenan Hamma kana sona?"

"A matsayin ki na ƙanwata ina son ki, a matsayin ki na matar da na ke son aura ina miki albishir da samun soyayya idan kin shigo gidana"

"Hamma ni dai idan ba ka ce kana sona ba ba zan amince ba"

"Aysherh please" ya faÉ—a da sassanyar murya.
Zaytoonah was his first love. Lokacin da ya rasata a farko da na biyu zuciyar sa ta shiga cikin ruɗani. He was completely shattered, ya jima yana jinyar zuciyar sa. Ba zai ce yana yiwa Humairah irin son da yai wa Zaytoonah ba amma yana son ta. Tunda Mommy ta ma sa magana akan idan har zai bi shawaran ta to ya nemi Humairah sai kuma a hankali ya fara ƙoƙarin cire Zaytoonah a ran sa. Sannan ya fara koyawa kan sa kallon Humairah a matsayin macen da zai iya aura ba wai a matsayin ƙanwar sa kaɗai ba. It takes time kafin yai adjusting, sai dai rawan kan Humairan ke ɗan sace ma sa gwiwa.

Lokacin da ya ga ginin sa yai nisa ne ya fara tunanin gabatar da kan sa wa Humairan sai kuma ta yi wani sabon saurayin da ya manne ma ta, itama kuma ta ke É—an ji da shi. Hakan ya É—an sa shi dakatar da niyyar sa ya zuba ma ta ido ya ga gudun ruwan ta.

"Zan aure ki ne dan ina son ki Aysherh" ya faɗa daga ƙarshe da muryan sa mai rauni...

***

Kamar yadda aka saka wata biyu bayan Azumi za ayi biki hakan ta kasance kuwa dan ba a chanja ba. Zuwa yanzu Humairah da Auwal sun sasanta kan su dan har hira ya ke zuwa wajen ta tunda ta koma gidan Mommy da zama yanzu tun dawowar Daddyn su.

Shirye-shiryen biki ake ta yi gadan-gadan wanda duk ƙarfin abun Mommy ne da Zaytoonah ke yi. Daddy na ƙoƙarin neman aiki ne yanzu tunda ya rasa gurbin koyarwar sa a ABU. Sai dai kuma abinda bai sani ba tuni Galadima ya shige ma sa gaba wajen ganin an dawo ma sa da aikin sa.
Mutumin da yai degree har uku ba abun yar wa ba ne lokaci guda.

Muntari shima yanzu ba abinda ya ke dan komai na shi ya tafi, har yanzu kuma Alhaji Rabi'u bai waiwaye su ba, suma kuma sun kasa yin maganar sa balle su tunkare shi.

Auwal dai da kansa ya ƙarisa ginin gidan sa amma Mommy ta ɗauki nauyin duka furnitures ɗin gidan. Cikin ƙanƙanin lokaci aka gama komai na gidan.

Sati uku kafin biki Humairah ta koma Bauchi ta je ta yi sati biyu wajen Ummi kafin ta dawo bayan ta sha gyara.

Duk yadda Zaytoonah ta so ta zo bikin da wuri bai yiwu ba sai ranan Jummu'a da safe da za ayi walima ta dira a gidan su. Galadima na fama da mura, Hashir da Falaq na zazzaɓi gaba ɗaya babu yadda za ta yi ta bar su a wannan hali. Jikin Falaq ya ɗan yi sauƙi amma Hashir kam dai sai a hankali, ta dai taho da shi a haka. Mafarin zazzaɓin ma ruwan sama ne aka yi, Zaytoonah na bacci a ɗaki yaran su ka fita compound ɗin gidan su ka yi ta wasa cikin ruwa.

Duk da Zaytoonah ta so ayi wani hidima na burgewa ko da dinner ne ko kamu amma Daddy ya hana. Ranan Alhamis Humairah ta yi friends day sai kuma Jummu'a aka yi walima Asabat kuma aka É—aura auren *Barrister Auwal Usman Abubakar* da kuma amaryar sa *Aishah Tijjani Abubakar*...
2/11/21, 10:04 PM - ****: 76

Bismillahir Rahmanir Rahim

*Forever with you, my love*

End of Chapter 157Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next