Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
By Azizat
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Author: Azizat
Chapter 63 of 161
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,689 words Chapter 2 1,523 words Chapter 3 1,583 words Chapter 4 1,696 words Chapter 5 1,682 words Chapter 6 1,693 words Chapter 7 1,594 words Chapter 8 1,673 words Chapter 9 1,663 words Chapter 10 1,668 words Chapter 11 1,678 words Chapter 12 1,698 words Chapter 13 1,687 words Chapter 14 1,699 words Chapter 15 1,656 words Chapter 16 1,634 words Chapter 17 1,681 words Chapter 18 1,675 words Chapter 19 1,655 words Chapter 20 1,613 words Chapter 21 1,669 words Chapter 22 1,655 words Chapter 23 1,671 words Chapter 24 1,650 words Chapter 25 1,677 words Chapter 26 1,696 words Chapter 27 1,598 words Chapter 28 1,699 words Chapter 29 1,694 words Chapter 30 1,659 words Chapter 31 1,683 words Chapter 32 1,309 words Chapter 33 1,691 words Chapter 34 1,697 words Chapter 35 1,553 words Chapter 36 1,588 words Chapter 37 1,682 words Chapter 38 1,680 words Chapter 39 1,677 words Chapter 40 1,649 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,698 words Chapter 43 1,676 words Chapter 44 1,625 words Chapter 45 1,633 words Chapter 46 1,675 words Chapter 47 1,693 words Chapter 48 1,668 words Chapter 49 1,688 words Chapter 50 1,647 words Chapter 51 1,653 words Chapter 52 1,568 words Chapter 53 1,689 words Chapter 54 1,699 words Chapter 55 1,669 words Chapter 56 1,578 words Chapter 57 1,564 words Chapter 58 1,660 words Chapter 59 1,694 words Chapter 60 1,415 words Chapter 61 1,653 words Chapter 62 1,690 words Chapter 63 Reading now Chapter 64 1,618 words Chapter 65 1,652 words Chapter 66 1,674 words Chapter 67 1,687 words Chapter 68 1,699 words Chapter 69 1,644 words Chapter 70 1,698 words Chapter 71 1,691 words Chapter 72 1,671 words Chapter 73 1,689 words Chapter 74 1,679 words Chapter 75 1,677 words Chapter 76 1,678 words Chapter 77 1,655 words Chapter 78 1,683 words Chapter 79 1,696 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,694 words Chapter 82 1,697 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,668 words Chapter 85 1,554 words Chapter 86 1,666 words Chapter 87 1,677 words Chapter 88 1,694 words Chapter 89 1,667 words Chapter 90 1,700 words Chapter 91 1,670 words Chapter 92 1,670 words Chapter 93 1,655 words Chapter 94 1,640 words Chapter 95 1,607 words Chapter 96 1,668 words Chapter 97 1,659 words Chapter 98 1,689 words Chapter 99 1,675 words Chapter 100 1,614 words Chapter 101 1,610 words Chapter 102 1,700 words Chapter 103 1,683 words Chapter 104 1,657 words Chapter 105 1,698 words Chapter 106 1,700 words Chapter 107 1,695 words Chapter 108 1,656 words Chapter 109 1,683 words Chapter 110 1,699 words Chapter 111 1,699 words Chapter 112 1,641 words Chapter 113 1,696 words Chapter 114 1,626 words Chapter 115 1,695 words Chapter 116 1,691 words Chapter 117 1,698 words Chapter 118 1,645 words Chapter 119 1,673 words Chapter 120 1,691 words Chapter 121 1,635 words Chapter 122 1,694 words Chapter 123 1,689 words Chapter 124 1,688 words Chapter 125 1,673 words Chapter 126 1,692 words Chapter 127 1,686 words Chapter 128 1,697 words Chapter 129 1,660 words Chapter 130 1,691 words Chapter 131 1,674 words Chapter 132 1,670 words Chapter 133 1,693 words Chapter 134 1,691 words Chapter 135 1,687 words Chapter 136 1,672 words Chapter 137 1,691 words Chapter 138 1,657 words Chapter 139 1,687 words Chapter 140 1,650 words Chapter 141 1,695 words Chapter 142 1,607 words Chapter 143 1,699 words Chapter 144 1,676 words Chapter 145 1,698 words Chapter 146 1,684 words Chapter 147 1,664 words Chapter 148 1,696 words Chapter 149 1,674 words Chapter 150 1,680 words Chapter 151 1,697 words Chapter 152 1,628 words Chapter 153 1,618 words Chapter 154 1,688 words Chapter 155 1,664 words Chapter 156 1,692 words Chapter 157 1,584 words Chapter 158 1,644 words Chapter 159 1,646 words Chapter 160 1,618 words Chapter 161 1,797 words

Ɗakin da aka kwantar da Zaytoonah ya fara zuwa bayan ya gama jin bayani daga wajen wani police. Ance ma sa ba ta ji ciwo sosai ba Mr Smith ne ya ji ciwo sosai. Amma ganin ta kwance an ɗaure ma ta goshinta da ya bugu da bandeji sai hankalin sa ya ƙara tashi. Zama da yai yana kallon ta bai san lokacin da hawaye ya fara zubo ma sa ba.
"She's too young to die" ya faÉ—i a ran sa.

Ko da matsayin da ya bawa Zaytoonah matsayine na ƙanwa, baya fata ya rasata kamar yadda ya rasa Alinah. At first bai ɗauka za su yi wani shaƙuwa ba a iya shekarun da ya ɗiba da za su yi aure amma gashi tun ba aje ko'ina ba ta shiga ran sa sosai.

Ben ne ya dafa kafaÉ—ar sa ya katse ma sa tunanin da ya ke yi.

"She wont die right?" Ya faÉ—a bayan ya juyo ya kalli Ben É—in wanda ya tsura ma sa ido yana ma sa kallon So da tausayi gameda haushin wai hawayen da ke zuba a idon masoyin sa hawaye ne saboda Zaytoonah.

Ko ba ta mutu ba ya so ace ta nakasa sosai abinda yai niyya kenan, amma sai gashi buguwa kawai ta yi a kan ta. Da ma ita ce ta ji ciwon da Mr Smith ya ji.

"She wont die" ya furta da sigar lallashi yana rungumeshi, shi kaÉ—ai ya san miya ke ji da wannan runguma da ya samu a wajen Zuhayr.

A Asibiti Zuhayr ya kwana kuma ya ci sa'a Zaytoonah ta farka chan tsakar dare. Kwana biyu ta yi a asibitin su ka sallameta amma Mr Smith kam zai É—an jima. An fara investigation amma babu wani result da aka samu mai gamsarwa dan wanda yai aikin ya daidaici inda babu CCTV ne yai wannan aika-aikar...

*Team Ben ina ku ke ne? muna gayyatar ku querry*

*Idan kuna son sanin formula da Zuhayr ya bawa Zaytoonah please comment i'll love to share😀*
2/11/21, 10:04 PM - ****: 28

Bismillahir Rahmanir Rahim

*deflowering*

Duk wani kulawa Zuhayr yana bawa Zaytoonah. He felt guilty gameda abinda ya faru, hakan ne kuma ya sa sati ɗaya da ta warke sosai ya ɗauketa da kan sa su ka je masallaci sallar Tarawih. Wanda su ka san shi tunda ba ƙaramin murna su ka yi da ganin sa ba. Ba irin wa'azin da ba a ma sa ba amma ya janye jiki da masallaci. Lokacin da yai sallah a masallacin kuma sai ya ji wani ni'ima ya ratsa shi. Bayan an idar da sallah Sheikh Hassan ya gayyace su zuwa shan ruwa gidan sa washegari.
Tunda su ka je gidan Sheikh Hassan sai ya zamana kusan kullum sai dai su je shan ruwa wani gida, har gidan Faisal Khan sun je. Azumi yana saura kwana uku ko huÉ—u ta yiwa Zuhayr magana akan suma ya kamata su gayyaci mutane shan ruwa gidan su tunda suma sun je gidajen mutane. Yayi na'am da shawaran dan haka su ka shirya yadda tsarin zai kasance. Kusan indai mutum na attending masallacin nan to suna gayyatar sa indai zai samu damar zuwa.
Ranan Azumi ashirin da tara aka zo aka yi liyafa a gidan Zuhayr. Liyafa ce da aƙalla families gida ishirin da takwas su ka zo daga ƙasa mabanbanta amma zaman Las Vegas ya haɗa su an zama ɗaya. Da ke tunda aka yi maganar sai aka tsayar da shawara akan kowa zai kawo abu daga gidan sa ya zo da shi, sun ce kar nauyi yai wa Zuhayr yawa duk da kuwa sun san Zuhayr ɗin yafi ƙarfin haka.

Mata da yara na gefe guda ana cin abinci ana hira yayinda suma maza ke chan gefe suna na su. Abincin kusan serve yourself ne kowa ya ɗebi abinda zai iya ci. A wajen Zaytoonah ta sha labarin Alinah a wajen wanda su ka san ta. Kowa faɗan kyawawan halayen ta ya ke yi da yadda su ka sha mamakin mutuwarta tashi ɗaya, mutuwa ma mai muni wato kisan kai. Wasu har lokacin ba su yarda Alinah kashe kan ta tayi ba ganin irin yadda ta ke da riƙo da addini, sun fi yarda da cewa kasheta aka yi aka nuna kaman kashe kan ta tayi.

Bayan anci abinci aka haɗu aka yi sallar jam'i a wajen da aka idar aka yi sallama ana taya juna murnan ganin wata da aka yi saboda sun ji labari ance an gani a wasu wajajen ciki har da ƙasar Saudiyya.

Lokacin da Zahra matar Faisal Khan za ta tafi ne ta bawa Zaytoonah wani dogon envelop ta raÉ—a mata kalmar ALINAH a kunne. Zaytoonah ta amshi envelop É—in jikinta na rawa.
Bayan kowa ya watse ta yi sauri ta shiga gida inda ta bar Zuhayr yana taya ma'aikatan sa tattare wajen da aka ɓata.

Tana zama akan gado ta buɗe envelop ɗin hannunta har rawa ya ke yi. Hoton da ta fara gani na wata farar Balarabiya ce tana tsaye tana murmushi, tana sanye da riga shirt brown sai dogon skirt baƙi ta yi rolling da baƙin gyale ta juya bayan hoton ta ga an rubuta sunan Alinah Amir Jones da kuma iya shekarun da tayi a duniya. Ta rasu tana da shekara ashirin da shida.
Hoto na gaba ma na Alinah ce amma da kayan Indiyawa ita da Amarya Zahra Ayyub. Hoton gaba ma A wajen auren Zahran ne cikin jama'a ma ta ke. Sai hoto na gaba an ɗauka su huɗu, ita da Zuhayr sai kuma Zahra da Faisal Khan shima duk a auren su ne. Hoton ƙarshe kuma ita da Zuhayr kaɗai su ka ɗauka a wajen auren still. Wani Jarida ta gani kaman an wrapping ɗin hoto da shi ta duba headline ɗin jaridar ta ga an rubuta *MUSLIM WOMAN COMMITTED SUICIDE OVER GAMOPHOBIA*
Ta yi saurin jawo wayarta ta duba ma'anar kalmar Gamophobia.
Hoton da aka naɗe da jaridar ta ɗauko hannun ta na rawa saboda a juye ya ke. Tana buɗewa ta yi saurin rufe bakinta jikinta na ƙyarma bayan ta ajiye hoton akan gado.
Alinah ce a cikin bathtube wanda ruwan ciki gaba É—aya ya rikiÉ—e ya koma jini.
Innalillahi kawai ta ke ta maimaitawa tana jin tsoro na shigarta. Da ana cewa kisan kai ta É—auka hanging kan ta tayi ashe ma mutuwa mai girgiza hankali ta yi.
*She bled to death* abinda aka rubuta a jaridar kenan bayan ta koma kan jaridar ta karanta labarin.

Muryan Zuhayr da ta ji yana haurowa sama ne ya sa ta tashi da sauri ta fita daga É—akin da gudu. Saura stairs biyu ya haura sama ta iso ta rungumeshi sosai haÉ—eda fashewa da kuka. Dole ya damu da rashin son jin labarin Alinah, wani irin damuwa ne zai sa mutum ya kashe kam sa, ya yanka hannun sa ya dinga gani har jinin sa ya tsiyaye.

"Miya faru?"

"I'm sorry Zuhayr, i'm really sorry"

Da ƙyar ya samu ta nitsu ta dena kuka kafin ya janyeta daga jikin sa ya rakata har ɗaki. Ben na bayan su yana wani huci idon sa yayi ja. Yanada plans dayawa gameda yadda zai yi ya hallaka Zaytoonah kuma ba zai gushe ba sai ya ci nasara akan ta.

Bayan ya rakata É—akin ne ya ga hoton da ta gani, bai ce komai ba sai ma janye jikin sa da yai daga Zaytoonah ya ma ta sai da safe ya wuce na sa É—akin. Yana shiga É—akinsa shima É—in jikinsa ne ya hau rawa saboda abinda ya gani ya tono ma sa tsohon gyambo da ke zuciyar sa har yau ya kasa warkewa.

Washe gari ranan Sallah haka su ka tashi sukuku, kowa da tunanin da ya ke yi a ran sa. Waya da su ka yi da 'yan gidan su ne ma ya sa Zaytoonah ta samu farinciki.

A rana ta ukun Sallah su ka je gidan su Kakan Zuhayr saboda an ma sa waya Mr Haddish ba lafiya. Sun je sunyi kwana biyu su ka dawo saboda jikin na sa da sauƙi...

***

Yau ne rana ta farko da ta koma makaranta saboda hutu ya ƙare. A nan ɗpoet ce.

Zaytoonah was so captivated with the fact cewa mutum É—aya zai iya abubuwa dayawa haka. A cikin taÉ—in da su ka yi ne watarana ta sanar da Farha tana son koyon rawan ballet saboda ta cikawa Mommynta burinta na zama ballerina.

"So what's stopping you?" Farha ta faÉ—a tana tauna chewing gum

"Its too late, i'm going to be seventing in 3months time"

"So?"

Zaytoonah ta kalleta da mamaki.

"That's not a reason"

"I'm fat" Zaytoonah ta faɗa daga ƙarshe

Farha ta fashe da dariya, dariya sosai harda riƙe ciki.

"Kinga kalmar ƙiba idan tana damun ki ba abinda za ki yi a rayuwar ki. Look Zaytoonah babu abinda siriri zai yi da mai ƙiba ba zai yi ba sai dai idan bai yi niyya ba"

Zaytoonah ta baza kunne tana sauraron how confident Farha ta ke magana gameda abubuwan da mutum zai iya idan ya sa kan sa. Bayan sun gama hiran ta ba ta assignment akan idan ta je gida tayi tunanin mi take so ta zama bayan zama Barrister...

Kwana biyun nan Zuhayr yana sintiri tsakanin Vegas da ƙauyen su Kakan shi saboda jikin na sa da ya tashi. Duk yadda ya so Mr Haddish ya bar gidan gona ya zo babban asibiti a cikin gari a duba shi ya ƙi cewa ya ke yi wai ya san ɓata lokaci za ayi amma shi ya san ya kusa mutuwane kawai.

Bayan gajeruwar jinya da Mr Thomas Haddish yai sai rai yai halin sa. Rana ce da ta sa Zuhayr kuka saboda tsananin son Kakan sa da ya ke yi. Har da Zaytoonah aka je burial amma ita kam ko wajen akwatin gawan ba ta je ba lokacin da ake zaman wake. Da za aje bisine shi ma ba ta je ba saboda tsoron gawa ta ke yi, ko a TV aka nuna akwatin gawa ko mutum cikin likkafani to haka za ta yi ta jin tsikar jikinta na tashi. Wani lokaci har mafarkin abin sai ta yi.

End of Chapter 63Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next