Soyayyanovels
Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
By Real Ladingo
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel

Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel

Author: Real Ladingo
Chapter 11 of 130
About 7 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,685 words Chapter 2 1,656 words Chapter 3 1,426 words Chapter 4 1,678 words Chapter 5 1,658 words Chapter 6 1,660 words Chapter 7 1,540 words Chapter 8 1,682 words Chapter 9 1,488 words Chapter 10 1,684 words Chapter 11 Reading now Chapter 12 1,481 words Chapter 13 1,490 words Chapter 14 1,658 words Chapter 15 1,664 words Chapter 16 1,361 words Chapter 17 1,446 words Chapter 18 1,594 words Chapter 19 1,440 words Chapter 20 1,595 words Chapter 21 862 words Chapter 22 1,587 words Chapter 23 936 words Chapter 24 1,007 words Chapter 25 1,624 words Chapter 26 548 words Chapter 27 1,952 words Chapter 28 1,599 words Chapter 29 1,281 words Chapter 30 1,465 words Chapter 31 1,117 words Chapter 32 1,166 words Chapter 33 1,496 words Chapter 34 1,495 words Chapter 35 1,191 words Chapter 36 1,505 words Chapter 37 1,475 words Chapter 38 1,632 words Chapter 39 970 words Chapter 40 1,565 words Chapter 41 1,516 words Chapter 42 1,101 words Chapter 43 1,209 words Chapter 44 1,672 words Chapter 45 1,520 words Chapter 46 1,612 words Chapter 47 1,543 words Chapter 48 1,654 words Chapter 49 1,192 words Chapter 50 1,699 words Chapter 51 1,476 words Chapter 52 1,648 words Chapter 53 1,617 words Chapter 54 1,636 words Chapter 55 1,432 words Chapter 56 1,581 words Chapter 57 1,631 words Chapter 58 1,206 words Chapter 59 1,393 words Chapter 60 1,279 words Chapter 61 1,241 words Chapter 62 1,639 words Chapter 63 1,506 words Chapter 64 1,619 words Chapter 65 1,517 words Chapter 66 1,475 words Chapter 67 1,600 words Chapter 68 1,589 words Chapter 69 1,675 words Chapter 70 1,603 words Chapter 71 1,692 words Chapter 72 1,515 words Chapter 73 1,429 words Chapter 74 1,552 words Chapter 75 1,635 words Chapter 76 1,554 words Chapter 77 1,590 words Chapter 78 1,500 words Chapter 79 1,567 words Chapter 80 1,518 words Chapter 81 1,656 words Chapter 82 1,634 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,643 words Chapter 85 1,435 words Chapter 86 1,628 words Chapter 87 1,694 words Chapter 88 1,601 words Chapter 89 1,576 words Chapter 90 1,659 words Chapter 91 1,655 words Chapter 92 1,536 words Chapter 93 1,559 words Chapter 94 1,457 words Chapter 95 1,655 words Chapter 96 1,677 words Chapter 97 1,557 words Chapter 98 1,692 words Chapter 99 1,558 words Chapter 100 1,525 words Chapter 101 1,533 words Chapter 102 1,651 words Chapter 103 1,695 words Chapter 104 1,597 words Chapter 105 1,580 words Chapter 106 1,627 words Chapter 107 1,681 words Chapter 108 1,700 words Chapter 109 1,636 words Chapter 110 1,621 words Chapter 111 1,471 words Chapter 112 1,637 words Chapter 113 1,685 words Chapter 114 1,674 words Chapter 115 1,638 words Chapter 116 1,629 words Chapter 117 1,674 words Chapter 118 1,513 words Chapter 119 1,674 words Chapter 120 1,653 words Chapter 121 1,623 words Chapter 122 1,605 words Chapter 123 1,584 words Chapter 124 1,634 words Chapter 125 1,675 words Chapter 126 1,537 words Chapter 127 1,639 words Chapter 128 1,693 words Chapter 129 1,496 words Chapter 130 1,209 words

ni nafita ma harakarta sai kayi kokarin hanata karta kuskura tashiga sabgata,nima ok? " insha Allah bata shiga ba amma ai kiné take tsoro ya zakace bazaka tsawatar mataba? baice komaiba ya dauki dadduma ya shimfida ya tayar da sallah la'asar har ya gama Mahabeer Na tsaye dan ya fahimci Sardauna yaji haushin abunda yamasa yana gamawa ya Mike wayarsa ta dauki ringing suna Daddy ya gani ya dauka yai picking ya kara akunnesa yana kallon Mahabeer ya daga masa gira " hello Daddy" dan uwaka zo yanzu ina parlo kitt ya kashe wayar " my brother karana takai muku ko? Hannusa Mahabeer ya kama suka fito suka nufi part d'insu Daddy da sallama suka shigo parlon zee baby na jikin Daddy tana matsar kwalla kusan Daddy ya zauna " Daddy gani? " meyasa da nace karka tabamun momy ka doketa momy wani irin duka ya miki? " Ammin wlh bankaremun hannuwa yayi ya daureni a karfan gadon hospital ya rika harbani wai sai yaga bayana wai ni annoba ce ya makoremun wuya saida na suma baci ba sha haka ya barni har likintan abonkinsa saida yamun kuka saboda tausayi tunda ta fara magana Dr Sardauna bai dagoba ya kalleta har takai karshen maganar tana kuka kowa ya tausaya mata Daddy ya dagata " ke Hafeeza maza kuje tayi wanka ta canza kaya tayi sallah tazo tafadi abun da takeson ci ko wani irine yanzu za'a nemoshi momy kuje kiyi wanka nine zan rama miki karki damu dariya tayi cikin farin ciki tabi Hafeeza suka nufi bedroom d'insu cikin fada Daddy ya fara magana" Faisal nine zaka rainawa hankali ka daureta kana bugo saboda zalumci yarinyar da uwarta tabaka Amana k'asakantar da kansa yai "Daddy ayi hakuri bazan sakeba nafita harakarta insha Allah idan tayi ba daidaiba ga Mahabeer

zai tsawatar mata jikin Daddy yayi sanyi marin da yayi niyar masa ya fasa dan yasan Sardauna yanada ladabi " to naji ka kiyaye ba ruwanka da ita Mahabeer yace "Daddy tafi tsoransa ai Dole sai ana dan tsawatar mata mai ran karfe yace wannan haka yake Daddah tace" ko zata zauna part dinmu? Hauwa tace" da dai ta zauna gun yan matan ghaisha tace" hakan zaifi Aunty amarya tace" gaskiya abarmana kuma fah inaga Dole Faisal ne zai tsawatar mata Mahabeer naga bayason laifinta Daddah dariya sukayi Dr Sardauna tafiyarsa yayi dan maganarsu ko ajikinsa dan yayi Alkawalin baya shiga harakarta mutikar bata shiga tashiba Abu daya zaigani ya horata shaye shaye, suna shiga bedroom khalisat ce ta hada mata ruwan wanka taje tayi wanka tajima sosai kafin ta fito dauré da towel ta goge jikinta tas Hafeeza ta dauko mata Riga da siket na atamfa har taso tayi musu ganin karamin dinkine kuma tanada son kayan atamfa ta amsa, ta saka tayi masifar kyau atamfar ja ce anmata adon fari dinkin Riga da siket mai karmin hannu yayi mata kyau cuf ya mata da yake Hafeeza batada jiki itama amma saide kowa da irin dirinsa hafeeza ta kalleta" sister kinyi kyau sosai? " shukran bani dadduma nayi sallah shimfida mata tayi tasaka hijab ta tayar da sallah, suna zaune har ta gama ta kalli khalisat " meye sunanki? " khalisat yar uwata Hafeeza" ita na sani kece ban saniba ai ke babbace kin grimemu sosai mekike jira bakiyi aureba? kunya ta kama khalisat har hafeeza ma

mik'ewa hafeeza tayi " sister muje parlo fuska ta yamutsa " ni kwanciya zanyi ina shantocina ne ko suna gun Ahukhuya? " gasunan ajere waiwayawa tayi murna ta kamata taje ta bubude komai da ta dauko sunan har kwayoyinta da sirot dinta na kwalba gudun kar su gani yasa bata fidoba duk da tana matse karamar jakarta ce bata ganiba wayarta na ciki " my khalisat muje parlo muyi hira ko ta fadi tana kallon hafeeza tare suka fito parlon ba kowa duk sun kama gabansu sai ghaisha kade tana waya khalisat taje jikinta ta kwanta zee baby ta tureta" gani yarinya ke katuwa dake ai nima ummi tace dariya hafeeza tayi khalisat tayi murmushi " my zee zo ki kwanta to ta Mike ta matsa mata tako zauna ta dora kanta cinyar ghaisha tana waya gashin zee ta shiga shafawa zee tana murmushi ummina dawa kukeyin waya nima inaso akiramun ummina dariya su khalisat sukayi yada zee take shagwaba saida ta gama wayar ta kira lumber ummi Raiyan bugo daya ta daga da sallama suka gaisa da ghaisha taba zee baby " hello ummina wallahi nayi kewarki sosai? " Zainaba nima nayi kewarki dan Allah ki zauna lafiya da kowa kinji yarinyata? tafada tana goge kwalla" ummina insha Allah ai satine kadai zanyi na dawo gareki murmushi Raiyan tayi " ina Mahabeer dazu ya kirani mun gaisa har Dr ma baki na tabe " suna lafiya ummi sun jima sosai suna hira kafin suyi sallama taba gaisha wayar" ummi ina Ahukhuya? ya fita zai dawo kinji kai ta daga sukaci gaba da hirasu

Dr Sardauna bayan ya fita part d'insu ya koma ya canza shiri cikin kananun kaya wanda sukayi masifar kyau ya fito ya nufi gidansu Ahmed dan ya isheshi da kira yazo yamasa Allura zazzabi ke damunsa yana zuwa yayi parking akofar gida ya tura get ya shiga gidan har parlon su Ami ya shiga da sallama tana zaune" Dr ne ince mutumin ya takuraka ko? " ami babu komai dama da kullum sai nazo indai ba aiki yana ciki ko" yana part dinsa mik'ewa yayi ya mata sallama ya nufi bangaran Ahmed yana parlo sai nishi yakeyi " dallah can ragon namiji kawai tashi mutafi asibiti zama yayi kusansa ya dafa jikinsa zafi radau " Dr Wlh inajin jiki fah " tashi muje dai mik'ewa yai dama jallabiya ce jikinsa suka fito rikeshi yayi suka fita har kofar gida suka shiga mota sa hospital din Dr Sardauna suna zuwa yashiga masa gwaje gwaje ya saka masa drip da ya sha magani ganin magarib ta gabato ya shiga toilet ya dauro Alwalla ya fito " namijin duniya na tafi masallaci kai ya daga masa yana mamakin tsokanar da Sardauna yake masa yau ba shegen miskilancin sa, tunda ya tafi bai dawoba saida akayi sallahr isha'i ya dawo har lokacin drip din bata kareba ya zauna ya kira mashakurah suna hira su ta soyayya sai shagwaba take zuba masa yana lallabata" sweet baby wlh inaso na ganki amma agajiye nake yanzu ina komawa gida sai bacci " karka damu Dr nima inason ganinka amma nafi bukatar ka huta na ajiye shagwabar " ok thanks sweet bye ya tsinke Kiran Ahmed ya zuba masa idanu" ni fah Dr naga kamar son da kukewa juna yayi yawa ku ragema yan baya mana banza yamasa ya Mike ya karawa, drip d'in gudu minti biyar ta gama yacire masa, " malam ina magana fah? " banda lokacin ka " to naji wai naga da araga mana maguguna ya hada masa" Oya mutafi

tunda kaji sauki Dole ka rainamun wayo fitowa sukayi Dr Sardauna sai gaishesa ake yana amsawa sama sama Dan bacci yakeji ga baisha sigari ba tunda ya dawo daga kano, ko amota iskacin Ahmed yayi tama Sardauna amma bai ko kallesaba bare yasamu arzikin magana har suka iso kofar gidansu Ahmed ya fito " Dr namu sai gobe idan na gama wartsakewa zanzo nama kanwarmu sanu da zuwa baimasa maganaba yaja motarsa ya tafi Dan lokaci yaja karfe kusan tara gudu yayi sosai yana zuwa yayi honr aka bude masa get ya shige parking space ya shiga ya faka yana fitowa part d'insu ghaisha ya shiga da sallama ya shigo parlon duk su hallara Ana hira zee baby na kusan Mahabeer zaune sai sangarta take zuba masa dannkwayoyin da taje yanzu taciyo aboe sun fara mata aiki shiko sa lallabata yakeyi su Daddy namusu dariya kusan Daddy ya zauna ya gaishesu " Dr Ashe baka gidan" wlh Daddy Ahmed ne ba lafiya muna hospital amma yanzu da sauki tunda taji shine danma karta kallesa ta boye kanta jikin Mahabeer dhiko baisan Allah yayi ruwantaba ghaisha tace" ayya Allah bashi lafiya Ashe shiyasa yau bai lekoba tashi kaci abunci tunda ya shigo khalisat ta zuba masa

End of Chapter 11Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next