Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
"Yauwa hajiya dariya tasake hauwa ta Mike ta amshi ledar hannusa tana masa sannu suka nufi bedroom hayatu ya kalli zee baby"kanwata wlh mahabeer yamun shigar sauri Nisha tace"wai yaya meyasa kake hakane"ke zan ci ubanki mace dan namiji daya akayita cikin tsiwa zee baby tace" wlh dan my heart akayini hayata kake kowa wlh kar mufara yar rashin mutumci dakai nafika iyawa ta fada tana mik'ewa ta nufi bedroom Nisha ta bita acan sukaci gaba da hirasu har hussaina yazo kiransu cin abuncin dare, ko akan dining sai harara hayatu takeyi saboda irin kallon da yake mata ana gamawa ta Mike bata tsaya hiraba, kiran mahabeer tayi suke hirasu, Dr Sardauna yana zuwa gida wanka yayi yayi sallah isha ya nufi part d'insu ghaisha duk suna zaune a parlo har mahabeer da sallama ya shigo kusan ghaisha yaje ya dora kansa cinyarta ya rufo idanunsa kansa ta shafa"Dr lfy kuwa fuska ya yamutsa ya shagwab'e mata Daddy yace"Dr wa ya taboka ne"Daddy babu kowa kawai dai banajin dadin jikina ne dariya mahabeer yayi "Dr namu fadi gaskiya banza yamasa ghaisha tace"tashi muje kaci abunci nawwara tace"yayamu sai karika Abu irin na yara idanunsa ya bude ya watsa mata mugun kallo da gudu tabar gurin ta nufi Daddy jikinta yana tsuma Aunty amarya tace"Dr karka firgitamun diya ghaisha ta kamashi ya Mike suka nufi dining sai dariya suke musu dan idan tana tatalinsa ko nawwara auta bata samun haka
serving dinsa tayi ta zauna itace take bashi abaki sai yamutsa fuska yakeyi dan sam yau bayajin dadin zuciyarsa daket ta lallabashi ya dan ci farfesun nama rago kadan dan dama tasan halinsa bayacin abunci da dare mai yauni zaide ci nama kadan yasha frut kadan sai coffee kallonsa tayi cikin sigar lallashi"autana waye ya tabamun kai shagwab'e mata yayi"ghaisha ni auran ne ya fita araina Allah da sauri ta rufe masa baki "haba bokan turai Namijin duniya karkasa azagi mahaifinku mana a garin Katsina meye tamaka yarinya mai hankali dan Allah kayi hakuri mata sai ana hakuri dasu haka tayi ta lallabashi da maganganu masu dadi akan cewa karma yakuma tasa maganar ta janyosa suka dawo parlo lokacin mahabeer na hira da zee baby Dr ya musu sallama ya nufi part d'insu yana shiga yayi zamansa a parlo yana kallon TV yana busa sigari sweet baby ce ta kirasa tsaki yaja saida ta kira sau ukku ya daga cikin masifa ya fara magana"wai uban me zaki bani da wannan daran kibarni zan nemeki haba dan Allah kitt ya tsinke Kiran yaci gaba da kallonsa yanajan tsaki haka mahabeer ya iskoshi yana masa hira sama sama yake amsawa dan yau haushin kowa yakeji neman inda zai huce haushinsa yake, mashakurah tunda ya mata tsawa tayi kwance tana kuka sai kiran sunansa take tana Kiran sunan wani mutum sai tsine masa, albarka take tana masa Allah ya isa duk tafice haiyacinta
su zee suna uwar daka akwance sai hirasu suke ita da Nisha suna dariya har karfe kusan daya na dare bacci ya dauki Nisha zee baby sai juyi takeyi tana lumshe idanu da ta tuno yada ta riko k'ugun Dr Sardauna da yada yasata cikin jikinsa yana mata masifa da kuma da rana yada ya tsotsi bakinta da yada yake murza mata breast yana mata magana cikin zazakar muryasa komai NASA cikin kwarewa ahankali ta furta"Dr Sardauna Jarumin maza ta fada tana lasar baki ta fara matsar kafafunta tana mimmik'ewa har bacci ya dauketa cike da mafarkin Sardauna suna wata irin rayuwa mai dadi, Dr Sardauna kwance yake saman makeken gadonsa sai juyi yake yanajan tsaki yana rike da cikinsa yana cizon lips d'insa na k'asa har karfe biyun dare Dole ya Mike ya sabko daga kan bed d'in yana tangadi ya nemo magani yasha sai zufa take keto masa ta ko ina ya rarafa ya kwanta daket bacci ya sa cesa, Asubah ta gari,
*********************************
*bayan kwana ukku*
tunda zee baby ta dawo gidansu Nisha rayuwarta take hankali kwance babu takura sai hayatu da ya tisata GABA duk inda tayi idanunsa na kanta ko ya rika neman zama kusanta ko yace zai tabata ko kusa bata yada akwai ranar da ta wankeshi da mari tana kitchen tana soya kwai taji ya rikota tana juyowa ta sharara masa mari ta tofa masa yawu tayi masa, kwakwaran kashedi tun ranar bai sake ko kallonta ba sai aboye ita da Nisha yawo suke fita sune gidan zainab gidan kawu saminu gidan Ibrahim yayansu Nisha gidan Nuhu gidan maijidah yayar Dr Sardauna wacce yakebi idan kagansu kamar tagwaye gidan Nuhu suje su hadu da su hafeeza suna iya shege maryama tayi ta musu dariya dan ita batada matsala agidan zainab ne zee baby suka hadu da wata makwabciyar su zainab yan matace mai sunan habiba kallo daya zee ta mata tasan tana shaye shaye aikuwa ta faki idanunsu Nisha tajata gefe tana mata tambaboyi aikuwa nan take ta amsa mata lokacin zee babu kudi agunta nan take takira mahabeer ta kafa masa kuka Dole yazo ya iskota ya tsaya kofar gida duk gidan yana zuwa tunda abokinsa ne hadeem din kudi tace ya bata zata sayi kayan kwalliya nan take ya bata dubu ashirin ya tafiyasa duka taba habibi tace ahado mata kayan maye masu tsada aikuwa habibi taje ta hado mata na dubu goma taci dubu goma to zee cikin dare tasha ta kwale tayi ta haukanta sai asuba tayi bacci ban garan Dr Sardauna ko da mashakurah ya dan sabko saide yanzu baya yawan kiranta irin nada yana bata dai kulawa kadaran kada han ne shi har yau baima san zee bata gidaba
yau ta kama monday tun karfe 7:00am Nisha tayi shirin tafiya makaranta zee na sharara barcinta dan kwana biyu bata bacci saboda kwayoyin da take ci da sirot da take sha, karfe tara Dr ya fito cikin shirin zuwa Office yau cikin suit bakake ya hade Wanda suka fito da asalin farinsa da kyawunsa da kwarjininsa gilashi bakine manne kan fuskarsa sai zuba uban kamshi yakeyi da sallama ya shigo parlon dukansu suna kan dining har mahabeer karasowa yayi ya gaishesu ya yabi iyayansa daya bayan daya ya rumgumesu yaja kujera ya zauna tea ghaisha ta hada masa mai kauri yasha agaugauce ya Mike dan
Jiransa akeyi kiss yama ghaisha"mamana sai na dawo Daddy yace"Faisal nifa gunsa yaje yana sakin murmushi ya masa kiss din nanah tace"yayamu zan bika daukarta yai ya mata kiss" ki zauna dai autarmu nawwara ta dawo daga school kuyi wasa Mahabeer ya Mike Dr Sardauna ya kallesa "bro yau da wuri zaka fitane?? " eh wlh muje ka ajiyeni amotarka yau banajin tuki baki Dr ya tab'e Daddy yace ikon Allah motocin shiga har ukku gareka amma kace motar k'aninka zaka shiga ficewa yayi yana dariya"wlh Daddy zolayarsa Nike ni gun zainab zan biya ma wayarsa ta dauki ruri ajiye nanah yayi ya ficewarsa yana amsa waya Daddy yace"Mahabeer yau kaje ka kawomun momyna? " to idan na taso daga gun aiki zan biya na daukota ya fice shima Daddy ya Mike yaje yayi shirin fita Kamfani Dr Sardauna na fita ya shige mota yau wata Jeef ce fara wuleliyarta ya fita da ita
✨✨✨✨✨✨✨
More Hausa novels
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Zazzafan Rabo Part One Complete Hausa Novel
By Aisha Umar Indabawa
Ni Da Yaya Sadiq Book 1 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Dafin Harshe Book One Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.