Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
zamu ganta su hussaini suma Zama sukayi suka hadu suka rungume Sardauna suna jadadda masa baza ta wucce wannan gidanjan biyu ko bata can sunada yakinin
sunsan inda take. suna haka aka kira sallahr la'asar suka Mike suka dauro alwalla suka tafi masallaci Ammi ta itama ta Mike ta dauro alwalla tayi sallah, tana Addu'ar Allah yasa zainaba bata yi nisan kiwoba. bayan su Sardauna sun dawo daga masallaci suna zaune parlo Sardauna zazzabi ya rufesa Hassan ya kawo masa magani yasha ya kwanta. saman kujera suna jiran Hamraz. karfe hudu da rabi ya shigo parlon da sallama Sardauna zabura ya Mike zuwat, ko gaisawa Ammi bata bari sun yiba tace"Hamraz mutafi nemanta karfa tayi nisa cikin jimami yace"Sardauna ka ajiye hankalinka za'a ganta hussaini ina da ina take zuwa...? " gidan kawayanta muje nasan unguwar da gidajan munsha zuwa tare. "OK ku tashi muje wlh rashin ganinta matsalane babba tafiyarku zata sami matsala.hannu Sardauna ya ruke Amina ta Mike dama sun gama shirinsu tsaf suka fito Hamraz part din Suna shiga yace"ka canza kaya. Baiyi musu ba ya saka jallabiya fara tas mai kyau da tsada ya saka shirami suka fito su Ammi na farfajiyar gidan suka fito kofar gidan inda mota yake Hamraz ya bude musu suka shiga. Sardauna yana gaba kusan Hamraz. yama motar key yana tambayar inda zasu fara zuwa. Hussaini yace" unguwar Marhabah, gidansu Jannat, yace" OK yaja motar ya harbata kan titi Sardauna Addu'arsa daya Allah yasa su sameta acan gidan.
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
Bangaran zeey baby kuwa tana Sanya kanta parlon ta sukayi Karo da manal tana ihu ta fito tarbarata rungumeta tayi tana ihu" wayyo habibty ina cikin farin ciki sahiba ta dawo gareni dariya zee tayi ta janye jikinta tace" ai Saki karasani dama ba lfy bace dani ba. hannuta ta kama suka Isa parlo yan gidan duk suna zaune zee ta karasa da tafiyarta agwale ta zauna kusan mamar manal ta gaisheta" zainaba yaushe kuka dawo amarya Ashe aure aka miki a haussa..? Murmushi zee tayi ta sadda kanta k'asa Radah tace"wlh kin Kara kyau sosai kin murje. Manal ta kama hannu zee "tashi mu shiga yau akwai yawu agarin saudiya Ashe dariya yan parlon sukayi zee tabi manal suka shige bedroom suna shiga zee tace bari nayi sallah banyi sallah ba. Ta fadi tana shiga bathroom ta tube ta hada ruwan zafi ta shige cikin bath ta lumshe idanunta ta fashe da kuka"Wayyo Sardauna ya zanyi da rashinka na har abadan ya zanyi da masifar sonka wayyo Yayana Sardauna meyasa ka aikata haka gareni meyasa kayi zina dani bayan kasan haramunce gashi ina matar yayanka kuma gashi ka sakamun Masifafan Sonka azuciyata Yayana ka hallakar dani baki daya Dole zanyi nisa daku zanbar jiddah ayau komin dare zan nufi inda Baku taba tunanin zaniba zan kaurace muku har zuwa wani lokaci har naji na daina Sonka na koma gun mijina mahbeer. haka tayi ta sambatu a toilet bayan tasan hakan babu kyau amma bata cikin nutsuwarta saida taji ruwan ya surke ta fita ta kunna shower tayi wanka ta dauro alwalla ta goge jikinta ta fito da kayanta ahannu ta zauna bakin katifa tana sabke ajiyar zuciya tajima Kafin ta Mike ta saka kayanta ta hau saman darduma ta tayar da sallah. tana cikin yi aka kira la'asar tana sallama ta tashi ta tayar da sallahr la'asar bayan ta gama ta shiga kwararo Addu'a tana neman gafara ubangiji akan zinar da sukayi tana rokon Allah yasa taji ta daina son Sardauna
Allah yasa mahbeer kar ya tsaneta tana cikin kuka manal ta shigo da babban tire ta hado mata kayan ciye ciye dasu shayi ta ajiye tiran ta nufi gurin zee ta kamata ta tashi ta rungumeta"habibty meyasa kike kuka wani abu aka mini Dan Allah ki fadamun.?saida ta gaji da kukanta tace"manal Dan Alalh muje inda zan samu nutsuwa pls inaso nayi shaye shayen da ban taba irinsa ba aduniya. hannunta ta kamo suka zauna ta zuba mata shayi ta bata ta amsa ta kurba ta ajiye"to kici wani abu cikinki yayi yauni sai mu tafi inda zamu buya wlh yanzu An hanani shaye shaye amma akwai inda zamu samu. da Sauri zee ta Mike tashi mu tafi mutikar kina sona kina kaunata yanzu kikaini nasha na more saboda nasan ke tawace shiyasa na fara zuwa gunki Kafin naje gun Jannat. " OK mutafi cikin farin ciki zee ta rungume manal tana murna janye jikinta tayi ta dauko Nikab din zee itama ta Dora abaya Akan kayanta ta daurawa zee nikab dinta taja hannu zee suka fito parlo ba kowa duk sun shiga sallah"manal tace"kinga muje kawai ficewa sukayi
suna fita bakin titi suka tsaya jiran tax ko limozin basu jimaba suka samu tax suka shiga manal ta fada masa inda zai kaisu yaja motar ya tafi. bangaransu Sardauna suna zuwa gidansu Jannat Hamraz yayi parking Ammi ta fito da kanta ta danna bell din gidan cikin ikon Allah Jannat da take farfajiyar gidan tana waya aboye da saurayinta taji ana danna bell tazo ta bude tabi Amina da kallo Dan bata Santaba Ammi tace"kece jannat..? " eh nice. "to ni kakar zee baby ce kawarki ko tazo nan ihu tayi ta rungume ammi tace"Dan Allah tana ina muje ki kaini gunta bari nazo ta fadi tana shiga gida da gudu Ammi hankalinta ya tashi jin zee bata gidan Jannat ta fito cikin shiri taja Hannun ammi suka fito ta rufo kofar Dan asace ta fito Sardauna sabkowa yayi ya taresu"Jannat ina zainab don Allah karku boyeta idan kinsan inda take. " wlh nima yanzu naji amma muje bata wuce gidansu manal motar yakoma ya hade kansa da gwiwa zuciyarsa na mahaukacin bugawa Dan ya fara tsoron lamarin. har motar taja ta tafi Sardauna baima saniba Jannat tace" insha Allahu bata wuce gidansu manal ko batacan wlh nasan inda zasu ita da manal cikin farin ciki Sardauna ya dago yace"idan naga zainab ta dalilinki ayau bazan taba mantawa dakeba Hamraz idan anga zainab pls kasan yada zaka mun nasamu tafiya ayau da ita idan yaso goben su Ammi su bimu. "Sardauna kayi hakuri har goben kaifa doctor ne kasan yada zaka mata koda allauran baccine har goben kar abun yayi yawa su gane gudune za'ayi dasu" OK shikenan zanyi kokarin tsare abata. Dariya yaba kowa da tausayi duk suma sun damu daurewa suka kawai Jannat ko ko aka
Dan tasan halin kawayanta. suna zuwa kofar gidansu manal Jannat ta bude mota tafito ta nufi gidan tajima tana danna bell Kafin abude mata Radah tace" har sun fada miki ko.?" eh matsa kiga ta shige da guda. aparlo ta tsaya suka gaisa da mamar su manal tace" suna ciki tun la'asar basu fitoba. dariya Jannat tayi ta nufi ciki tana kiransu wayam ba kowa idanu ta zaro ta duba ko ina babu su babu alamarsu wayam ta fito" mamah basu nan tsaye tayi cike da mamaki tace"kaga shegun yara ko mashaya biyu sun hadu wlh duk inda suke sun tafi neman kwaya Dan Allah jeki nemosu koda yake duk dayane har ke dinma abokin barawo barawone Jannat ficewa tayi Dan tasan ba inda zata samu su zee sa gidan yar saude ta shiga mota Sardauna yace"bamu dace ba ko...?murmushi tayi tace"an fadamun inda suke Hamdalah sukayi da Addu'ar Allah yasa su sameta acan Hassan duk yaji ya sare Dan zee ta taba haka saida ta kwana hudu Kafin asameta.Hamraz yace "to yanzu ina mukayi kenan Jannat ta fada masa sunan unguwar. Hamraz ya zaro idanu yace"wannan lalatartar unguwar takarun Tab. Sardauna gabansa ya tsinke ya fadi idanunsa ya lumshe da Addu'ar Allah yasa su Sami zee acan Hamraz yaja motar ya dauki hanya Dan akwai Nisan bala'i can kusan fita daga garine. bangaran su zee kuwa suna gidan yar saude uwar shege da shegiya suna zuwa tunda taga zee taji zata samu kudi anan ganin zee adamuwa ta shiga mata dubaru ta fada mata matsalata kiyawa tayi saboda batason kallo mafi yawancinsu kowa duk sun kura mata idanu
Wata bakar mace dumkukuma mai budaddan hanci na hango zaune matasan yan mata na kewaye da ita saura duk sun kwale Manal tace" yar saude mu kibamu abinda ya kawomu. Zee tace wlh kuwa Dan na matsu naji na buge. Dariya yar saude tayi ta fito musu da kwayoyi da kwalaban syrup masu masifar tsada ta ajiye gabansu tana washe baki "manyan yara gashi amma fa akwai tsada. Manal tace ai kinsan ko nawane zan siya ta fadi tana bude kamar Jakarta ta ciro kamsa miyyah Riyadh guda biyu ta bata zee jikinta na rawa ta bude kwalbar syrup ta Kafa bakinta ta fara tultulawa cikinta manal ganini zee zata shanye duka ta riketa ta amshe "haba karki ilata kanki mana kibi komai asannu duk da bansan meke damunki ba. takai cine yasa na fashe da kuka na kwashi kwayoyin na watsa abaki" manal kibarni kawai ina cikin masifa ina cikin taskar rawu wlh. yar Saude tace" kina yarinyarki karama kizo asaki gari manal ni bansan kawarnan takiba kizo yanzu a nuna miki gari yar balarabiya. Zee tace "Dan Allah wani garine yafi dadi Wanda idan naje zan manta da damuwata. cikin murna tace "yauwa zan fada miki bari ajima akwai direban da zai kaiki garin ba ko sisinki. Manal ta shanye sauran syrup din zee amma bataci kwayarba sanin kwakwaluwarta karamace. zee cikin murna tace "Dan Allah ki kirasa zanje pls. "Ai yanzu kuwa zan kirasa zaki ganshi yazo waya ta dauka ta Mike ta shiga daki zee tabita da kallo ta kwashi wasu kwayoyin ta watsa abakinta ta tauna suna hira. da Manal tace ita dai bazata ba. Zee tana dariya Dan tuni zee syrup ya fara canza mata yanayi su Sardauna basu isa gidan ba sai da Ana kiran magarib wani irin lungunane Hamraz yayi parking abakin titi ya juyo ya kalli Jannat"ki sabka kuje da Ammi gaskiya bazan shiga lungun nanba. Sardauna yace "ai motar ma bazata shigaba nake gani Jannat fito mutafi suka
More Hausa novels
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Zazzafan Rabo Part One Complete Hausa Novel
By Aisha Umar Indabawa
Ni Da Yaya Sadiq Book 1 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Dafin Harshe Book One Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.