Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Zee na rungume jikin ummi da lemon tsami ahannunta tana tsotsa. Nisha ta shigo da sallama.
Zeey ta amsa ummi tace"gida zaku ko..?"eh ummi yaya ne yake kiranta."baki ta turo gaba "ni wlh yau bazan koma ba ku tafi kawai."ummi tace "yi hakuri baby tashi ku tafi."kuka ta Saki tana rungume ummi"wlh ni ajikin ummina zan kwana bazan jeba."ummi ta kalli nisha"jeki kiramin Dr din yazo ya dauketa da karfi.
Fita nisha tayi tana murna tana zuwa gun Sardauna tace"yayamu zainab sai kuka take wai yau bazata tafi ba sai gobe.
"Murmushi yayi dama tausayin ta kwana ita daya yake.
"OK tayi kwancirta baiwar Allah."daddy ya girgiza kai maryama dariya tayi.
ghaisha ta rike baki"autana zo kaji mana."mik'ewa yayi ya dawo gun ghaisha.
Kunnansa ta kama ta murda da karfi ya Saki ihu, umma hauwa tace"sakarma yarona kunne ai gaskiya ya fada.
"Yauwa ummata ya fada yana mik'ewa ya nufi dakinsu ummi.
Ammi ta rike baki tace"khadija wlh rayuwar gidanku tayi ko my larabawa bazamu gwada muku kaunar junaba.
Dariya yan parlon sukayi. Hassan da hussaini sukaje suka rungume daddy suna kukan murna kawu Saminu ansha manyan kaya sai washe baki ake ya zauna kusan daddy ya janyo hussaini"daga yau karku sake kukan rashin mahaifinku ko yana raye mune nan iyayanku dan haka karku sake kuka kunji..? "Kai suka daga sunajin wani irin dadi na ratsasu.
Ghaisha katan kwalla take gogewa ita da Ammi.
😆niko nace kawu Saminu kai dai kawai ka kwashi gara balarabiya.
Sardauna da sallama ya murda kofar.
Ummi ta amsa zeey luf tayi kamar tana bacci Sardauna ya gaishe da ummi yace"Baby tayi bacci ko.? Dariya ummi tayi"yau kaji rigima takeji Ana zata kwana."kai ya Sosa "ummi ta kwana din dan Allah akulata sosai ummi sai da safe ya fada yana kallon zeey.
Aikuwa da, Sauri ta dago tana shashekar kuka tana dagama Sardauna hannunta ya dauketa.
Nufota yayi"Baby zaki bini gidan kin fasa kwana da ummi Oya task mu tafi abinmu kinci wani Abu ko."jikin ummi ta koma tana boye fuskarta"Yayana katafi bazan jeba da, ummina zan kwana.
Murmushi yayi ya juya yana shafa sajan fuskarsa ya fice.
Ummi tace "Baby kin iya fitina ko? baki ta tura tana kara rungume umminta tana tsorsar lemon tsami.
Sardauna yana fitowa yama iyayansa, sallama. Daddah yau antuno da Faisal sai matsalar kwalla take mairan karfe yana lallashinta yan parlon suna musu dariya barinma Ammi gani take rayuwar kamar Asudiya. Sardauna ya fara tsokanarsu"kai tsaffi idan soyayya zakuyi ku tashi ku tafi part dinku.
daddy ne ya Mike ya kora Sardauna.
Aikuwa da gudu Sardauna ya fice yana dariya,Nisha tama iyaynsu sallama tabishi.
Koda ta fito har ya shiga mota ya kunna sigari yana bata hayaki baki da hanci idanunsa lumshe yana tuna babynsa abar kaunarsa.
Saida yaji Nisha ta zauna kusansa ta rungumeshi tana sabke ajiyar zuciya.
Baice mata komai ba ya ya gyara mata kwanciya jikinsa yama motar key ya fizgeta ya nufi get yana horn megadi ya bude masa ya fice aguje yana zugar sigarinsa yana driving da hannu daya dayan yana shafa bayan Nisha.
My Nisher menene naga kamar kina cikin damuwa Oya my nishana fadamun..?"my Dr bana jin dadine my dear mun barota agida gashi bansan kwana nawa zatayi ba."ki kwantar da hankalinki kwana biyu zatayi ta danji gumin ummi banason ta kwana ita daya ga zazzabin da take kwana dashi,nafi so ta sami kulawa sosai kafin ki sallameni jibi.
Nisha ta ciza bakinta tana kisima abinda ta tsara na batar da zee cikin ruwan sanyi.
ta dago tana kallonsa hawaye ya wanke mata fuska,"my Dr mu koma adaukota ni na hakura ko da ga nan zuwa haihuwarta ne zan jure rashinka amma bazan jure rashin zeena ba."farin ciki ya ciki Sardauna ya saki murmushi.
My nishar ina sonki wlh halinki yayi arayuwa ya fada yana rungumeta gam yana kissing dinta saida motar ta kusa kwace masa.
Wayyo sweetheart zaka kashemu fah.
Burki ya take yana dariya"matsoraciya ya fada yana driving cikin kwarewa nisha, tana manne jikin Sardauna suna hirasu cikin anushuwa har su kazo gidansu.
Bayan kowanne yayi wanka yayi shirin bacci suka zauna a parlo.
Nisha ta hado masa coffee yana sha yana danna laptop tana makale jikinsa.
Saida ya kira zeey yaji lafiyarta,lokacin tayi bacci ummi ce ta dauki wayar yake tambarta jikin zeey ba zazzabi tace"babu tasamu tayi bacci saida ta mata tausa.
Yaji dadin zee bata da zazzabi,Nisha ma ta amsa sukayi hira da ummi.
Yau su Nisha ansami Sardauna sai wani riritashi take.😆 yo kwana 9 zeey baby ta kasa ta tsare Kiri Kiri take hana Nisha rabar Sardauna.
Karfe shabiyu suka tafi suka kwanta bedroom din Sardauna na nan k'asa.
Kwance suke manne da juna suns tostsar bakin junansu sosai Sardauna yake kasheta da salonsa bakinsa ya zare a nata yace"My Nishana na baki wani baby ko..? "Ya fada yana cire mata rigar baccinta ya cire boxes dinsa ya fara karanto Addu'ar saduwa da iyali ya nemi hanyarsa ya shige.
Idanu nisha ta lumshe lokacin da taji Sardauna ya shige jikinta batare da bata lokaciba ya fara sukuwa saman Nisha cikin kuzari da iya sarrafa mace dan amugun bukace yake shiyasa yake cacakarta sosai cikin kuzari.
Nisha ta sabke ajiyar zuciya tana shashekar dadi idanunta lumshe tanajin dadin yada Sardauna yake cacakarta,bakinta na rawa tace"Way...yo.. Da..di.. Sweetheart ka..Ka.. Ra..mun..da..kyau Ashhhh uhmm.............✍🏻🤣to Allah yasa ki daure dan kinsan mutimun naki baya cin kadan ya hakura.😆Asuba ta gari.
No Editing🤦🏻♀
*10/February/2020*
*💖💖👩🏻🦱ZEE BABY👩🏻🦱💖💖*
MALLAKAR UMMU FAREESA NE
*DAN ALLAH KARKU FITARMUN DA BOOK WAJE*
*Book 2 👉🏻14*
....Washe gari.
Nisha daket ta anfanu saboda ba karamin aiki Sardauna ya mata taci kuka kamar ranta zai fita dan bai saurara mata ba sai da yaji ya rage zafi sosai.
Shiyasa har Sardauna ya tafi aiki tana baccin wuya shi dariya ma ta bashi.
Sardauna yana fita sai da ya biya gida yaga zee dinsa tana bacci an samu tayi breakfast Kafin ta koma bacci, shiyasa ya tafi aiki cikin farin.
Nisha sai karfe goma shadaya ta farka tayi wanka ta fito parlo.
Kan dining taje taci ka cikinta ta dawo parlo ta zauna kenan taji knocking.
Ta mike ta nufi kofar ta bude.
Nadiya da intisar tsaye suna murmushi"wayyo yar uwa da kawata ku shigo."shigowa sukayi suna dariya,ta rufe kofar suka nufi gun kujerun parlon.
Kitchen taje ta kawo musu lemo da ruwa da kayan motsa baki.
"Kwana dayawa ya jin dadinku."suka hada baki"ke zamu tambaya.
intisar tace "wai ina zainab ya jikin nata.?" Wlh da sauki jiya mun barota agida."intisar tace"wlh naji dadin auran Abbanmu da ummi ba ruwanta muma zamuyi kanni larabawa.
Dariya sukayi Nadiya tace"Nisha kinga kuwa yada kika ciko kikayi kiba ko har kin kumshi na sati biyu."dukanta tayi"ke ko kawata bakida kirki ciki yanzu har na huta kafin lokacin zainab ta sauke kinga sai asami mai kula da Dr Sardauna.
Nadiya tace"albishirinki.?Nisha tace"goro fari tas tana dariya.
intisar tace"zanyi aure a kano Dr yakub zan aura har iyayansa sunzo anyi tambaya daman son mahbeer ne ya rufemun idanu tunda na rasashi dole zan auri wani."ta fada tana hawaye.
Nisha tace"intisar kiyi hakuri Allah ya tabbatar da Alkhairi,Nadiya kefa..?" wlh har kinban dariya ni da kinsan Dr Nabeel ne ai kimana fatan Alheri kwananan komai zai kankama insha Allah."nisha tayi dariya "to Allah ya kaimu.
Intisar tace"wlh yanzu ina mugun son Dr Yakub ya iya love da tatali.
Dariya sukayi.
Intisar tace"Nisha dan Allah ku kara had'e kanku da, zainab wlh ba ruwanta ni yanzu har kunyarta nakeyi lokacin da na rika mata basarwa da kallon banza sai gashi ya barmana duniyar ma."Nisha tace"wlh lfy muke zaune babu wata matsala.
Nadiya tace"yauwa Allah ya kara muku zaman lfy."nisha tace"Amin ta tsiyaya musu lemo ta basu sunasha suna hira suna Kara dorata ahanya da bata shawarwari yanda zata rike mijinta su zauna lfy,duk haushinsu takeji kawai tadai biye musune dan ko hauka take bazata yarda su San asalin wacece ita ba.
Haka sukayi ta hirasu wasa da dariya sai yamma wajejan karfe uku suka tafi.
----------------------------------------------------------
Bayan sallah la'asar.
Sardauna na zaune cikin hadaddan Office dinsa yana busa sigari yana duba tsadaddan agogon hannunsa.
Wayarsa ce ta dauki ringing ya kalli screen din wayar yaga sunan Bandar na yawo.
Dauka yai yayi picking ya akara akunne.
Tamkar bayason magana yace hello dan duniya too days kun bata kai da mara's kunyar yaron nan Ahmed."Dr gamu fa acikin hospital tun bayan azuhur,shukurah ce zata haihu wlh har yanzu shiru."
Da alamar damuwa Sardauna ya furta" Ya Allah!! to ai ban saniba gani nan fitowa wlh naga kiran babanta amma ban dauka ba."
Ya fada yana mik'ewa ya kashe sigarin ya kwashe wayoyinsa ya zuba cikin aljihu ya fito.
Yana fitowa ya nufi bangaran yan haihuwa da hajiya hafsa ya fara cin Karo sai Ma'aruf Bandar ya hango yayi zaune yayi tagumi.
Gurunsu ya nufa da sassarfa.
Yana zuwa ya gaishe da Alhajin cikin girmamwa.
Bandar ya taso sukayi masahaba.
Dr nabeel ne ya fito shida Ruma.
"Dr shiga kaga matar awuyace take" dakin Sardauna ya shiga.
Bai jimaba ya fito yana goge zufa ya kalli,iyayanta "Dady sai ku sa hannu dan bazata iya haihuwa da kanta ba sai anyi mata CS muje kusa hannu babu lokaci."
Bandar jikinsa har ruwa yake ya rike Sardauna.
Ma'aruf yace"muje nasaka hannu Allah yasa ayi a sa'a"
Sardauna suka bi Office dinsa.
Alhji Ma'aruf ya saka hannu.
Sardauna ya cire agoginsa ya ajiye da zobe da wayoyinsa baki daya suka fito bandar harda kuka.
Sardauna bai saurareshi ba ya shige dakin tiyatar da aka kai Mashakura iyayanta suka bita da Addu'ar nasara.
Cikin ikon Allah da yardasa Sardauna yama mashakura aiki ya ciro mata yarta katuwa fara kyakyawa jajir da ita kamarta da Bandar sak tamkar copy dinsa babu abinda ta rage na Bandar.
Bandar kallo daya yama yarinyar ta shiga ransa ya hana kowa ita gashi sai tsala kuka takeyi.
Karfe bakwai aka fito da mashakura dakin hutu har yanzu bata dawo haiyacinta sosai ba.
Iyayanta sai albarka suke sakama Sardauna Bandar kamar ya goyashi.
Bayan sallah magarib Sardauna ya samu ya tsere gidansu.
More Hausa novels
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Zazzafan Rabo Part One Complete Hausa Novel
By Aisha Umar Indabawa
Ni Da Yaya Sadiq Book 1 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Dafin Harshe Book One Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.