Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Bazan sake bata miki raiba ghaisha tazo ta zauna bakin gadon ta rumgumosu tana lallashi Dan zee wani irin kukane take mai daci sai daket ghaisha ta lallabata tayi shiru ghaisha ta kalli nisha"maza tashi kije ya maidake gida cikin sanyin jiki ta Mike zee takin ko kallonta abin ya daga mata hankali Dole ta fice ghaisha saida tasa zee tayi wanka da kanta ta shiyarta tsaf cikin abaya tasa hijab ta kamo hannuta suka fito parlo lokacin bakin sun dawo daga part din Daddah gun ummi zee ta nufa rumgumeta tayi Aisata tace"amaryamu bayan auranki tare zamu niger murmushi tayi batace komaiba dariya sauran sukayi suna yaba kyawun zee baby duk da suma ba baya bane buzayene jajur dasu gashi har baya a mota Nisha ta isko Sardauna fuskarsa, murtik tsoronsa ya cika mata zuciya tana shiga ya tashi motar cikin sanyin murya tace"yayamu kayi hakuri idan na batama rai kallonta yayi yaga itafa batada laifi har gidansu akazo akace Ana sonta murmushi ya sakar mata "no Nisha baki batamun ba zainab ma Dan batada lfy ne ba fushi take dakeba kisaki ranki amaryata kinji? ajiyar zuciya ta sabke taji dadi sosai sama sama suke hira har yakawota gida akofar gida ya ajiyeta ta fito ta shiga gida yaja motarsa gudu yake shararawa sosai saboda an fara kiran sallah yana zauya alwalla yayi ya nufi masallaci, bai fitiba saida akayi sallah isha tare suka fito da mahbeer part d'insu ghaisha suka nufa da sallama suka shigo parlon Daddah tace"wlh Sardauna bakada kirki gida cike da baki dangi amma baka zuwa part Dina sai kaga dama ko dariya yayi ya Saki hannu mahbeer yaje ya rumgumeta"tuba nake uwar gidana dariya suke tuwusai tace"gaskiya muma fushi Muke ismaghi ne suka shigo da Daddy yace"Faisal ja'irin yarone bai taba zuwa niger ba tare zamu kuyi amarci acan sakin Daddah yayi ya nufin gunsu ya rumgume ismaghil"to uncle zanje mahbeer yayi dariya yaje kusan zee ya zauna wacce take jikin ghaisha manne tanabin kowa da idanu Dan ita jima takeyi auran ya fice mata arai fuskarta mahbeer ya kalla cikin tausayawa yace"zeena sannu ya jiki fuska ta yamutsa daket tace da sauki duk abin dake faruwa kan idanun Sardauna tsaki yaja ya nufi kan dining zee mik'ewa tayi daga jikin ghaisha "momy ina zaki "ummi kwanci zanyi "ah sai kinci abunci mahbeer maza jeka bata abunci da Sauri ya Mike ya kama hannuta suka nufi kan dining ya zaunar da ita suna zuwa Sardauna ya Mike ya fasa cin farfesun ya bar gun daket yasamu taci farfesun kazar kadan sai yaga duk ta canza masa to sanin halin mutum mai
jinnu sai hakuri har bedroom ya rakata ta kwanta ya fito ummi sai murmushi takeyi sosai ta yaba da samun sirikin kwarai gabaki dayansu suka nufi kan dining akaci akasha Daddy yau farin ciki yake gasu tare da family Almahadee magawata hira akace cikin farin cikin da anushuwa mahbeer sai yage baki yakeyi bangaran zee da Sardauna kuwa sunacan kowa zuciyarsa babu dadi ahaka har zee tayi bacci Dan ko ina na jikinta ciwo yake mata mahbeer sai shabiyu ya koma. part d'insu yayi wanka yayi shirin kwanciya amma saida yayi sallah yama zee Addu'ar samun lfy ya kwanta yana Addu'a yaji Ana kecewa da wata irin dariya akowane bangon daki anacewa "wlh gwara ko kayi Addu'a Dan kana bukatarta ko ajikinsa yaja blanket ya shige yana Addu'arsa har bacci ya daukesa bangaran Sardauna sallah yayi saida ya dauki dogon lokaci sai karfe biyu ya gama yayi Addu'a ya shafa ya Mike ya cire jallabiya yasaka kayan bacci ya Haye saman bed yaja blanket yana juyi alokacin babu abinda yakeso sama da yaji zee baby cikin jikinsa, ya rumgumeta gam yayi bacci wayarsa, ya dauka ya kirata, amma wayar akashe tsaki yaja yayi wurgi da wayar"oh my god haba my kanwata meye na miki da zafi haka, wlh nasan da karna kiraki ne kika kashe wayarki to me yasa, kika zabarmun Nisha idan kinsa bakison hakan wlh babu digon sonta na soyayya sai na yan uwantaka da darajarki taci da kuma yaba hankalinta da nayi tsaki yaja, yana dafe da goshinsa yana juyi har barawon bacci ya kwashesa da mafarkin zee baby, asuba ta gari
*************************************
*Bayan kwana uku*
Yau take juma'a To fah yau take sallah ga angwaye da amare yau take ranar daurin aure Wanda za'a daurasa bayan sallahr juma'a wlh fadar irin taron da yake cikin wannan gida to bata lokacine bikine fa yau ake na kece reni wlh idan kama zee kallo daya bazakaso ka dauke idanunka akantaba ghaisha da ummi sun yi mata uban gyara da shiri kanwar mijin maijidda yaya Sardauna ce ta cancada mata kunshi da kitson wlh fadin irin kyawun zee bazai faduba gashi ta saki jikinta tabar tunanin Sardauna tun washe garin ranar tayi watsi dashi ta kashe wayarta, ta maida hankali kan abunda yake gabanta kowa yaga kunshin zee da kitsonta sai ya yaba mata mahabeer da yagani saida ya rike hannuta yayi ta lasar kunshin tana masa dariya bangaran nisha ma ta hadu ba karya itako kanwarta Salma ta mata saboda itama gwanace wajan kitos da kunshi yau bakin Nisha baya rufuwa sai washe shi takeyi dan wani ubansu Dinner ne aka shirya karfe biyar za'a tafi gidansu Nisha fah shima cike yake suna sai kidan kwaryar akeyi Nisha daga cikin sai rawa take ita da kawayanta suna ihu sai zuga nisha suke saboda tayi mutikar yin kyau material din ya amsheta gidan Abdulmutallab yau babu masayar haki shagali fah ake sosai harda masu kidan kwaraya sai casu akeyi ciki na kutsa domin samo labari ghaisha na hango cikin wata uwar shadda gizna blue color sai kai komo takeyi bedroom naga ta nufa tundaga kofa nake jiyo ihu zee na hango tsakiyar su hafeeza dan tayi gayar kawayansu na makaranta ga, zainab itama da kawayanta amma sunada aure zee ce cikin wani dankareren material ruwan toka kanta ba dankwali an mata meke-up ta zuba sinare ajikinta kamar bad a kudiba aka saya wuya da hannu da yatsotsinta tilar hancinta da kasan lebanta duk ta sauya musu zinare wlh idan kaganta zaka zaji babu ta biyunta akyau kidane ke tashi sai cashewa suke maryama matar Nuhu ce tsaya tana koya musu irin rawar da za'ayi gun dinner zee sai dariya takeyi haka ghaisha ta shigo ai maryama kamar ta nutse a k'asa zee dariya take harda rike ciki "Aunty wlh kinban dariya ghaisha ta girgiza kai "maryama zo dama ke nake nema idan kin gama koya musu rawar maijidda tayi dariya "ai aunty muna hanaki kikaki sum sum ta fice zee tace"ummina ina ummi dariya ghaisha tayi " gatacan gun yan kidan kwarya tana dauka awaya dariya zee tayi ghaisha ta fice zainab tace"wow matar yaya wlh ina tsoron daga gun dinner ya wuce dake Brahim estate dariya sukayi ta hararesu ta Mike tana rawa cikin wani shegen Salo da iya taku dan tana mugun son wakar gwanja mata ku taka rawar ganin ido mata kununa farin ciki dariya suke mata itako ko ajikinta dan tanada damuwa dannewa ne takeyi ta wayance dan batasan takamemen damuwarta ba bangaran nisha ma abun ba'a cewa komai itama sunacan suna cashewa ko gajiya rawa batayi da kawayenta abin ya rabu abiyu wasu gidan Umma hauwa wasu gidan ghaisha haka dangi aka rabu ana hidima ko wane gida raguna da saniya aka yanka sai girke girke ake zee Ana hanata saida ta saci jiki ta fito gun yan kidan kwarya ghaisha ce da gudu tazo ta janyeta su hafeeza da intisar 'ya'yan kawu Saminu da su haulat sai casu suke zainab ma da tsohon cikinta sai takawa take ummi Raiyan na musu barin kudi tana dariya
More Hausa novels
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
Dafin Harshe Book One Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel
By Oum Yasmeen
A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
A D U N I Y A Ta Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
A Sanadin Son Ki Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Search across the available chapters.