Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Nisha bayan ta ghaishe da iya yansu ta nufi gurin yan mata amare , tana shiga suka mata caa suna yaba dinkin material suna tambayarta meyasa ta saka material na dinner yanzu tace ra'ayinta suka yi dariya suka ci gaba da hira kawanyen Hafeeza da na intisar sunata tsara yada komai zai tafi daidai dan intisar dinner dinta a Kano za'ayi yau komin dare.
Sardauna ne ya fito ya nufi farfajiyar gidan taku yake cike da izza da takama hannunsa daya cikin aljihu dayan rikeda waya manne akunnesa yana waya da Ahmed ya hango wasu yan mata cikin rumfa sun zuba masa idanu.
Kai ya dauke yanajan tsaki ya nufi gun motarsa yana amsawa Ahmed ya hango motar Bandar ta danno cikin gidan , jinginuwa yayi jikin motarsa har suka fito shida mashakura Bandar ya hango Sardauna gurinsa suka nufo.
"Gaisuwa baban Amarya."murmushi Sardauna yayi mashakura ta gaishesa ya amsa Bandar ya bashi Amatullah ya mata wasa ya bashi ita,Bandar yana mashakura ita"ki shiga ciki sai zuwa dinner zaki ganni."murmushi ta sakar masa ta shige ciki.
Sardauna yace"Ahmed yake ta kirana muje nasan dama Amarya aka kawo."eh ai can na fara kai ta gaida umma Ahmed."hannu suka hada suna dariya kowa ya shiga motarsa atare suka fice daya bayan daya.
Sardauna suna fita yana driving idanunsa sun kada sunyi jajur ya kunna sigari yana bata hayaki ya dauki wayarsa ya danna wata number ba suna ya kara akunnesa.
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
Duk inda kuke tunani biki to fa bikin gidansu Sardauna yakai saboda komai anyishi acikin tsari da ilimi da misalin karfe sha biyu akayi walima Wanda anane aka saka atamfa anyi wa'azi mai ratsa jiki da tab'a zuciya Hafeeza da intisar saida sukayi kuka barema intisar da zata garin da ba uwa ba uba babu wani nata sai mijinta walima tayi sosai anci ansha amare ansha kwaliya su Saudatu uwar amarya ba laifi anci kyau haka ghaisha dasu maijidda su zainab da su zeey atamfar tayi mata kyau sosai nisha ma ba laifi.
Da misalin karfe uku na yamma daidai aka d'aura auran Hafeeza da Ahmed intisar da Yakub auran da ya sami halarta manyan mutane daga garuruwa daban daban,dan kofar gidan Abdulmutallab motocine reras ajere babu adadi babu irin motocin da babu yan Kano ma sunada yawa haka bangaran su Ahmed ma kofar gidan Daddy da cikin gidan to fa ba'a cewa komai saboda Al'ummah wlh ba'a cewa komai Daddy tare yake sosai da manyan mutane dan kallo daya zakama yawancin jama'ar kasan sunci sun tada kai.
Bangansu Sardauna ba'a cewa kumai wani rantsatsan yadi ne milk colour sukayi su uku Wanda fadar kudun yadin da irin dukunan da kyau din da sukayi ba'a cewa komai bayama Sardauna yayi mashahurin kyau.
Bayan daurin aurene Sardauna daket yasamu Yakub yayi hakuri dan ya nace sai Sardauna yabisa Kano.
Misalin karfe hudu su Yakub suka juya Kano tare da Amaryasu intisar wacce taci kuka sai daket Sardauna da kansa ya sakata mota tare da kawayanta biyu da umma hauwa da maijidda da ummi Raiyan sune suka tafi kaita dakin mijinta dama akwai mutum uku acan da basu karaso ba yan gyaran daki, zee ma tasha kuka sosai daket ghaisha ta jata suka koma ciki.
Canma hafeeza ta tsorata sai kuka take daket aka shiryata cikin ratsatsan material saboda lokacin zuwa dinner yayi.
Tun karfe hudu daidai Nisha tadauki jakarta tabar gidan ta tafi gurin cikar burinta.
Kallo daya zakama gidan kasan gidan yan dabane.
Aparlo ta iskoshi zaune yana waya da wani dungumeman takalmi akafarsa yana shan ganye.
Nisha ta bushe da dariya tace"Gazaguri bakada mutumci."dariya yayi yace"hajiya Aisha ai ban kikiba.
Jakarta ta bude zip ta ciro mask da uban damin kudi"ga irin fuskar Sardauna kayi maza kaje ka kawota mu aiwatar da aikinmu ka aikamun shegiya lahira."amsa yayi suka bushe da dariya ya Mike, ya saka mask din sai ga fuskar Sardauna ta baiyana.
"Yauwa yanzu abinda zakayi ka cire wannan shegen takalmin ka saka na mutumci."bai saurareta ba ya fice yana dariya"kijira yanzu zamu kauda, shegiya.
Zaman tayi ta cire mayafin jikinta ta zauna tana bude jakarta ta ciro reza dan tayi niyyar sai tama zee aski kafin su kasheta,sai dariya take tanajin farin ciki.
Gazaguri yana fita ya ciro waya cikin aljihunsa yana magana ya shiga mota yaja ya fice daga gidan.
Yan zuwa dinner duk an fara tafiya Hafeeza ansha kyau ba karya mashakura tayima zee kwalliya tayi uban kyau na mamaki dinki Riga da siket ne wanda suka mata cif cif.
Zeey ce ta fito waya manne kunneta tana magana ta nufi kofar get tayi kyau ba na wasa ba cikinta da ya fito ya kara mata kyau anutse take tfy da wani uban takalmi mai tudu akafarta "Yayana pls kazo mutafi dinner din mana wlh duk an tafi.
Dagacan yace "Baby kawai ki tafi ai mu har munzo ki biyo sauran jama'a." kuka ta fashe masa tana bubbuga kafa tana tafiya har ta danyi nisa da get bata saniba , cikin shashekar kuka tace "Yayana wlh na fasa zuwa tunda ka dauki matarka kuka tafi ni kabarni agida kanacan yan mata na kallonka Yayana wlh zazzabi ya zubomin yanzu don Allah kayi hakuri gazo gareni pls Yayana."Kitt ya tsinke mata Kiran.
Sake fashewa tayi da kuka"wayyo na shiga uku menayi ma Baby Sardauna zai samin ciwon zuciya Yayana dan Allah kayi hakuri menayi maka da zafi haka."ta fada tana tafiya sam batasan inda take saka kafarta ba jiri ya fara dibarta kawai taji an janyota anturata cikin mota.
Dan sauran kuzarinta da ya rage ta tataro ta kurma ihu aka rufe mata bakinta motar aka fizga da karfin gaske ana sharara gudu............✍🏻
No Editing🤦🏻♀
*13/February/2020*
*💖💖👩🏻🦱ZEE BABY👩🏻🦱💖💖*
MALLAKAR UMMU FAREESA NE
*DAN ALLAH KARKU FITARMUN DA BOOK WAJE*
*Book 2 👉🏻17*
...Gudu motar take shararawa saman titi,zeey ta haukace ma mutumin da yake rungume da ita tana kuka suna kokowa tace"don sonka da Annabi ka sakeni ni matar aure ce bai kamata ka dauko ni ba har kana hada jiki dani kuma ma meye na muku da kuka satoni."
ta karasa maganr cike da rudani maganarta ce ta tsaya mata cak.
Jin yanayin jikin Sardauna tare da mamakin jin kamshin Sardauna ya baibaye mata hanci ga wata kyakywar runguma da ya mata saman kirjinshi yana shafa bayanta. jikinta na rawa ta dago,da kanta ta kalleshi aikuwa idanunsu ya sark'e da juna yana sakar mata murmushi.
Cike da murna da shagwaba ta fashe da kuka ta rungumeshi kam kam tana dukan bayansa,"My Sardauna nah wlh dama nasan bazaka taba barin Babyn ka ta shiga matsalaba wlh nasani Yayana meyasa kamun irin wanan wasan meyasa kaso kasani arudani kace bazaka zoba muje gun dinner sai na fadama ghaisha da ummina da daddy kasakani kuka."ta fada tana shashekar kuka tana dukan kirjinsa tana goga fuskarta atashi.
Tsawa ya daka mata amma yana rungume da ita ya mata kyakyawan riko yace"dallah can malama ima mutane shiru."amutikar tsorace na dago na kalleshi ganin yanayinsa ya tsoratani sai yanzu na lura da shigarsa ta yan daba da yayi amma ganin babu wasa afuskarsa yasa nayi shiru jikina na rawa na lafe kirjinsa na rungumeshi ina hadiye kukana tsoronsa ya cikamun zuciyata.
Ban sake koda kwakwaran motsiba ina cikin jikinsa har naji mota ta tsaya naji muryan direban nacewa"Yallabai kuje ganinan zuwa ina kallon kumai tanan kafin nazo na koya mata hankali."murmushi ya Saki ya bude motar ya fito ya sunkuya yaciccibi zeey ya mannata kirjinsa yana tafiya.
Lafewa nayi jikinsa tsoron Yayana ya cikani.
Muna zuwa kofar parlon. Naga Najib ya karaso gurinmu.
Sardauna yace "yauwa ka dauki komai anuntse."Ok bro."
Ya ajiyeni ya bude dakin ya tunku doni yada bazan fadi ba ya dakamun tsawa"wuce muje,sai me muna shigowa naga Nisha atsaye da gudu na nufeta.
"My dear yau duk Yayana ya canza min kema yana miki abinda yakemin."na fada ina k'ok'rin rikota ta goce zan kifa saman cikina naji Sardauna ya rungumoni da Sauri yana sauke numfashi.
Nisha tace"Gazaguri taya zaka rungumeta ka temaketa bayan nafiso naganta tana magagin ciwo ta bugu da kujera tsinanan cikin jikinta ya zube agabana kafin ka aikamun yar isaka lahira."
Rumtse idanu Sardauna yayi yana kara shigar da zee jikinsa yana shafa bayanta zuciyarsa na masa kuna,cikin hanzari ya tataro nutsuwarsa ya dan ture zeey daga jikinsa yada bazata fadiba yana binta da wani mugun kallo ya koma wajan nisha ya tsaya ya rungumo nisha murya k'asa yace kiyi hakuri zan rungumeki na yan dakiqai kafin mu aikata lahira ai abinda yasa kikaga na temaka mata so nakeyi taji irin tsanar da kika mata da irin yada kika kulamata tugu da shairi ko ban kyauta ba."ya fada yana bata wani dan iskan kiss Wanda ta nemi nutsuwarta ta rasa ta rukumkumeshi tana jin wani iri amugun tsorace tace"ya naga kazama Sardauna na sak gazaguri ka koma mijina muryaka ta canza ka Kara girma tamkar Sardauna kamshinka na Sardauna komai nasane."ke yi asannu karta gane ba Sardauna bane baki cika burin kiba."
"Kuma fa hakane ta fada tana janye jikinta taje ta dauki reza ajakarta ta nufi gun zeey,wacce take tsaye duk ilahirin jikinta kerrrma yakeyi zufa na keto mata ta ko fitsari ya kufce mata sai tsiyaya yake.
ina hawaye sun gama wanke mata fuskarta ta nuna nisha da Sardauna tace"Yayana me na muku me zakumin yanzu Yayana zaka ita cutar dani Nisha me namiki da kike cewa zaki kasheni kuma agaban Yayana."bata rufe baki ba Nisha ta dauketa da mari sai da tayi tagal tagal zata fadi ta rike kujera.
Nisha tace "dan ubanki zainab na tsaneki tsana mafi muni wlh yau agabana zaki mutu sai na kasheki keda abin cikin ki.
Kinsan me.? Hummm nice nan na hada miki tugu akan zubewar cikina kuma nice nasha maganin da kaina domin cikin ya zube na bakanta miki nasa miki bakin jini cikin dangi nasaka Sardauna ya sake ki amma Allah bai yiba babu yada banyi na zubar da cikin jikin ki ba bai zube ba.
More Hausa novels
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
Dafin Harshe Book One Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel
By Oum Yasmeen
A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
A D U N I Y A Ta Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
A Sanadin Son Ki Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Search across the available chapters.