Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Da sallam suka shigo parlon amsa musu sukayi yana ganin yayansa Nuhu ya nufi gunsa ya rumgumeshi " babban yaya amun afuwa kwana biyu ban zaunaba shiyasa ban lekaba tun jiya da nadawo ya gajiya dariya Nuhu yayi ya kara rumgume Sardauna jama'a parlon sai kallonsu suke su Daddah da Aunty hauwa da Maijidda itama yayar Sardauna ce sai zainab kanwar Sardaukar wacce akawa aure yanzu haka tsohon cikine da ita sai kawu saminu kanan Daddy ne masha Allah parlon cike da yan uwa sunzo ma zee baby sannu da zuwa tana jikin Aunty hauwa azaune tanajin sallamarsa ta dago kai ta kallesa ganin ko inda take bai kallaba yana harako kinsa da yayansa yasa ta watsar da lamarinsa taci gaba da zuba musu surutu tana basu labarin saudia Ahmed ko tunda suka shigo da yayi idanu hudu da zee baby yaji wani Abu na masa yawo gabansa na bugawa da mahaukacin karfi yana jinsa cikin wani shauki dan yarinyar tayi masa daga kallo daya ga yanayin shigarta siket ne baki bakin guiwa da Riga mai dan tsayi fara ce tas tazo mata har k'ugunta kirjinta dam acike tamkar su fasa rigar su fito babu abinda ya kara tafiyar dashi irin hips dinta da tillar hancinta da ta k'asan labbanta barimar sai walkiya takeyi gashin kanta har gadon bayanta Wanda ta canza masa kaloli rabi ja rabi grey Nuhu yace " Dr munzo sannu da zuwar kanwarka Ahmad ya karaso ya gaishesu duk su amsa Daddah tace" Ahmadu ya jiki kusanta ya koma dan tafi kusa da, zee baby " Daddah ina wuninku jiki da sauki sannu da zuwa nazo ya fada yana nuna zee baby Aunty hauwa tace " momy " ana miki magana juyowa tayi ta kalli Ahmed " wow dan gaye ka hadu kuwa kaima dan uwanmu ne ta daga masa gira dariya duka yan parlon sukayi Nuhu yace " momy abokin yayanki ne Sardauna juyowa tayi ta kallesu karaf suka hada idanu wani mugun kallon tsana da kyama yamata ya dauke kansa itako tunda suka hada idanu tarasa duk wani karfin jikinta lokaci daya taji wani sanyi na ziyartata kanta ta dauke daga kallonsa tunda shi tun kallon farko yayi watsi da ita yayi kicin kicin nutsuwarta ta tataro tace" Ammin naga yana ruwan yan gidanmu Sardauna baice komai ba bar musu gurinma yai gun ghaisha yaje ya zauna zainab ce kusanta ta gaisheshi ya amsa adakile dan shi haushin masu zauwa ganinta yakeji kansa ta shafa" Dr kaci abunci kuwa " wlh babu abinda naci mamana mik'ewa tayi ta kama hannusa suka nufi dining Nuhu yace " ghaisha keki
ke kara shagwaba Sardauna sai kace wani auta baki zee ta tabe taci gaba da sabgarta Ahmed na janta da hira shiko ya fakene yana kallon surata duk shi ba mutumin banza bane amma tunda yaganta yakejin yanayinsa na canzawa tun tana basar dashi har tasaki jikinta suna hirasu tana bashi labarin saudia suna musu dariya dan sosai ya biyewa shirmenta sai dariya yakeyi zuwa tayi ta dauko jallabiya sabowa fara tas mai shegen tsada har aledarta da turare mai azabar kamshi ta kawoma Ahmed yaji dadi sosai yan parlon sai dariya sukeyi khalisat tunda Dr Sardauna ya shigo ta nemi nutsuwarta ta rasa gudun kar ya kamata irin na jiya ta janye jikinta ta nufi bedroom d'insu ta fada saman bed ta fashe da kuka dan abun ya fara damunta ga kishi ya cika mata zuciya saboda zancan za'ayi maganar auransa da mashakurah da taji dasafe Daddy nayi Mahabeer da zee zancan ya dameta kuka takeyi sosai kamar daga sama taji mutum akanta Aunty amaryace wani mugun kallo ta mata batayi magana ta fita tasan ma'anar kallon mik'ewa tayi ta sabko ta bi bayanta Dr Sardauna na gama cin abuncinsa bai tsaya a parlon yana tafe yacewa Ahmed " kasameni a part d'inmu mik'ewa yayi ya kalli zee " kanwata zan dawo musha hira kinji dariya tayi " to yayana ina jiranka dariya yayi ya fice Aunty hauwa tace gaskiya yanada kirki tafi abonkin nasa son mutane kawu saminu yace kowa dai da irin halinsa amma Faisal yanada son mutane harakar da bata shafesa bace baya shiga zee baby bata ce komiba dan ta dauki niyar fita sabgar Sardauna dan batayin Wanda baya yinta shiyasa bata shiga hiraba gun ghaisha ta koma ta kwanta saman cinyarta kanta ta shafa " momy kinajin yunwa kai ta kirkiza dan sanyi sanyi takeji tun lokacin da sukayi ido hudu da Sardauna jikinta ya saki takejinta wani iri ko hira da tawa Ahmed daurewa ne takeyi " ko bakida lfy dariya tayi " ummina sanyine nakeji wlh kara rumgumeta tayi ta rufa mata hijab zainab dariya tayi lalle yar ummi idanuta ta lumshe sama sama take jinsu har bacci ya dauketa Daddah ta Mike " khadija kinmu kwace ko hafeeza tace daddah bari ma muje part d'inki musha hira " aikuwa da yafi tunda na rasa hajiya Zainaba takwarata tafiya sukayi Nuhu ma sallama ya musu ya fice dama shi daya yazo kawu saminu ma tafiya yayi tunda bai samu ganin Daddy ba sai matan suna hirasu, lokacin da Ahmed ya biyo Sardauna har ya shige part d'insu har ya tube yana daure da towel yana shirin shiga bathroom ya shigo Dr Sardauna ya kallesa yaganshi da jallabiya da turare yana murmushi yace" Abokina zauna na fito akwai labari mai dadi ya fada yana shigewa bathroom " wlh nima akwai labarin fito mu fadawa juna ya fada ya kwanciya saman bed d'in Sardauna........
*💖💖👩🏻🦱ZEE BABY👩🏻🦱💖💖*
*DAN ALLAH KARKU FITARMUN DA BOOK WAJE*
*👉🏻10*
....ya dauki lokaci kafin ya fito dauro da towel jikinsa na digar da ruwa kirjinshi ko ina gashine kirjinsa dake asama duk zubin jikinsa amunmurde tamkar mai cin karfe gaban dressing mirror ya tsaya yana goge jikinsa da karamun towel Ahmed ya kalleshi yana dariya " Dr Sardauna wlh dama aikin Soja katafi wannan katuntakar taka har ina mutum duk amunmurde wallahi har tausayin Mashakurah nake banza ya masa tamkar baijiba ya shafa maiyukansa masu masifar kamshi da Dadi ya taje gashin kansa " Dr dan Allah ka rage gashinan gashi kamar na mace " wai Ahmed meye damuwarka dani na hanaka ka aske nakane kuma da kakecewa haka sweet babyna ai ta isa nunawa sa'a ako ina bakaga yar duma duma bace ni kasan banason tsakuwar mace saboda gudun kisan kai dan wlh idan na... Bazata tashi ka gane ai ya juyo yana dagawa Ahmed gira amma fuskarsa ba wasa yayi magana bushewa da dariya Ahmed yayi " wallah Faisal Ashe bakada mutumci ya fada yana nunasa da dan yatsa kafadu ya dage irin ko ajikinsa wardrobe ya bude ya ciro shart fara yasaka da 3quatre ya shiga bathroom ya saka
"Wai nine kakewa boyo me zan gani idan ba katuntakarba" kai yaro raba kanka saboda tsaro karka firgita turare ya fesa ya taje sumar kansa ya kunna sigari yana bata wuta baki da hanci yazo ya zauna yana fuskantar Ahmed " nifa ba shan sigari nakeba duk ka cikani da wari mik'ewa yai yana murmushi " Ok tashi muje parlo muyi magana parlon suka dawo suka zauna saman wasu manyan kujero tamkar parlon Amarya wata makekiyar TV manne abango ya kunna Dr Sardauna ya fuskanci Ahmed " kai yaro albishirin ka zan angwance yanzu gaisha tace mun ya kamata aje gidansu sweet baby ayi maganar aure kasan tun haduwarmu naso ayi koma kafin ta koma gun karatunta Daddy yace najira sai Mahabeer ya tsayar da mata ahadamu to yanzu sun yanke hukuncin hadashi aure da zainab tare za'ahadamu yau zan je da kaina na fadawa sweet babyna takusa hutawa da ciwon ciki ya fada yana murrmushi " wai kace zamusha biki to Mahabeer ina ya samu zainab? " yar Agulla mana idanu Ahmed ya zaro hankalinsa atashe yakeye kallon Sardauna " wai kana nufin kanwata zee baby? " yes ita to meye idan ba na gidan ba wa zai kwasa ajinka amma ina tausa masa Allah ya basu zaman lafiya Ahmed jikinsa yayi sanyi" Amin abokina" to bani labarin da kace zaka bani" ai shikenan dama cewa zanyi wlh zee ta burgeni amma anwuce wajan sigarinsa yaci gaba da busawa suna hirasu Ahmed duk jikinsa
More Hausa novels
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Zazzafan Rabo Part One Complete Hausa Novel
By Aisha Umar Indabawa
Ni Da Yaya Sadiq Book 1 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Dafin Harshe Book One Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.