Soyayyanovels
Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
By Real Ladingo
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel

Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel

Author: Real Ladingo
Chapter 10 of 130
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,685 words Chapter 2 1,656 words Chapter 3 1,426 words Chapter 4 1,678 words Chapter 5 1,658 words Chapter 6 1,660 words Chapter 7 1,540 words Chapter 8 1,682 words Chapter 9 1,488 words Chapter 10 Reading now Chapter 11 1,352 words Chapter 12 1,481 words Chapter 13 1,490 words Chapter 14 1,658 words Chapter 15 1,664 words Chapter 16 1,361 words Chapter 17 1,446 words Chapter 18 1,594 words Chapter 19 1,440 words Chapter 20 1,595 words Chapter 21 862 words Chapter 22 1,587 words Chapter 23 936 words Chapter 24 1,007 words Chapter 25 1,624 words Chapter 26 548 words Chapter 27 1,952 words Chapter 28 1,599 words Chapter 29 1,281 words Chapter 30 1,465 words Chapter 31 1,117 words Chapter 32 1,166 words Chapter 33 1,496 words Chapter 34 1,495 words Chapter 35 1,191 words Chapter 36 1,505 words Chapter 37 1,475 words Chapter 38 1,632 words Chapter 39 970 words Chapter 40 1,565 words Chapter 41 1,516 words Chapter 42 1,101 words Chapter 43 1,209 words Chapter 44 1,672 words Chapter 45 1,520 words Chapter 46 1,612 words Chapter 47 1,543 words Chapter 48 1,654 words Chapter 49 1,192 words Chapter 50 1,699 words Chapter 51 1,476 words Chapter 52 1,648 words Chapter 53 1,617 words Chapter 54 1,636 words Chapter 55 1,432 words Chapter 56 1,581 words Chapter 57 1,631 words Chapter 58 1,206 words Chapter 59 1,393 words Chapter 60 1,279 words Chapter 61 1,241 words Chapter 62 1,639 words Chapter 63 1,506 words Chapter 64 1,619 words Chapter 65 1,517 words Chapter 66 1,475 words Chapter 67 1,600 words Chapter 68 1,589 words Chapter 69 1,675 words Chapter 70 1,603 words Chapter 71 1,692 words Chapter 72 1,515 words Chapter 73 1,429 words Chapter 74 1,552 words Chapter 75 1,635 words Chapter 76 1,554 words Chapter 77 1,590 words Chapter 78 1,500 words Chapter 79 1,567 words Chapter 80 1,518 words Chapter 81 1,656 words Chapter 82 1,634 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,643 words Chapter 85 1,435 words Chapter 86 1,628 words Chapter 87 1,694 words Chapter 88 1,601 words Chapter 89 1,576 words Chapter 90 1,659 words Chapter 91 1,655 words Chapter 92 1,536 words Chapter 93 1,559 words Chapter 94 1,457 words Chapter 95 1,655 words Chapter 96 1,677 words Chapter 97 1,557 words Chapter 98 1,692 words Chapter 99 1,558 words Chapter 100 1,525 words Chapter 101 1,533 words Chapter 102 1,651 words Chapter 103 1,695 words Chapter 104 1,597 words Chapter 105 1,580 words Chapter 106 1,627 words Chapter 107 1,681 words Chapter 108 1,700 words Chapter 109 1,636 words Chapter 110 1,621 words Chapter 111 1,471 words Chapter 112 1,637 words Chapter 113 1,685 words Chapter 114 1,674 words Chapter 115 1,638 words Chapter 116 1,629 words Chapter 117 1,674 words Chapter 118 1,513 words Chapter 119 1,674 words Chapter 120 1,653 words Chapter 121 1,623 words Chapter 122 1,605 words Chapter 123 1,584 words Chapter 124 1,634 words Chapter 125 1,675 words Chapter 126 1,537 words Chapter 127 1,639 words Chapter 128 1,693 words Chapter 129 1,496 words Chapter 130 1,209 words

yada naga ya dawo lokaci guda amma na boye tsoron ina kallonsa nace " baru ba gareta rigar kuma sanyi nakeji ai ganin ya nufoni gadan gadan yasa na Mike aguje naje na janyo rigar nasaka ina tsinemasa albarka Dan sanyi nakeji yanzu zazzabi na iya kamani bakin gadon na zauna wayoyinsa ya dauke yasa aljihu "Oya muje ya fada yana bude plate din abuncin yaga wayam idanu ya zaro ya kalleni baisan ta ina dariya ta zomasa saida yayi yai nadamar yinta Dan zata ita rainasa niko wata muguwar kunyace ta kamani nan take na fashe da kuka nayi kansa ina dukansa akirji ina masa Allah ya isa me yagani ajikina na dariya saida nagaji da dukansa Dan kaina na fada saman kirjinsa na rumgumesa ina kuka tamkar ummi ta rasu Dan ina mamakin jarumtarsa ga kunya ta cikani kansa ya dafe yanajin ciwon Amanar da Daddy yace ya basa Mara tarbiyya nan tanason hadasa masa hawan jini janyeni yayi daga jikinsa ya kama hannuna muka zauna bakin gado baimun magana ba ya kama goshina yana murzawa gurin kumburin tin karfi " wayyo ummina zai kasheni wlh Dama banzo kasarnan ba mugu azalumi janyota yayi jikinsa ya matseta da kyau saida ya murje gun tas ya koma kafin ya saketa yana zubar da miyau ya Mike tsaye baimata magana ba ya bude kofar ya fice toilet

naje na wanko fuskata na biyo bayansa suna tsaye akofa suna magana da Dr Yakub nesa dasu na tsaya ina cika da batsewa yakub yace" kanwarmu sannu ykk? ayatsine nace "ni banajin Hausa dariya yayi Dr Sardauna yabashi hannu sukayi musabaha har gurin mota ya rakomu suka sallama baya na bude zan shiga tsawar da yamun tasa na dawo gaba na zauna tsaki yaja yama motar key suka fice daga asibitin yana hawa kan titi ya fara sharara gudu tunda ya fara driving ko kallona baiba wayarsa ya dauka ya kira wata lumber bugo daya aka daga cikin zazakar mursa ya fara magana cikin wani voice mai dadin gaske fuskarsa kamar bashi bane yake cicin magani " hello sweet babyna ykk? ko me tace ya Saki murmushi " lokacin bana kusa to ya gajiya Nima ganinan ahanya sosai yake hira suna zuba love tamkar bashiba ne mai tsamarnan niko sanyi nakeji sosai na fara jin zazzabi hakorana sun fara haduwa giri guda kallonsa nayi driving dinsa yake da hannu daya cikin nutsuwa yana wayarsa hankali kwance baki na ciza Dan wlh duk uwar wuyar da ya bani sai na Rama yauma Dan banida lafiyane sanyi ya adabeni gashi banida wani abun da zan rufa narasa ya zanyi ganin wayarsa yake kawai na matsa jikinsa na kwantar da kaina kirjinsa na zagaya hannuwana ta bayansa na rumgumesa gam na cusa kaina kirjinsa ina sabke ajiyar zuciya har tsawon minti uku sosai naji dadin hakan sanyi ya fara raguwa hannuna na dora saman wuyansa ina shafawa ashgwab'e na kirasa"Dr Sardauna ko gezau baiba yaci gaba da wayarsa yana driving d'insa duk da ta matseshi sosai ya bar tane saboda zafin da yaji ajikinta saida ya gama wayarsa ya ajiye wayar ya gangara yai parking can k'asa k'asa cikin daddar muryasa dan shi bai fiye taratsiba yace" wlh nidai an hadani da jaraba Dan ubanki ni sa'an kine meye zaki bani kike, kiran sunana bakin yaune kikeda damar hakan gobe ko ance ki nufi inda nake wlh bazaki zo dan ni bana yinki sam ya fadi yana janyeta jikinsa niko dama raguwace wajan zazzabi banida hakuri kuka na saka masa na Kara shigewa jikinsa" Dan Allah mai Suna Abbu kayi hakuri sanyi nakeji na fada ina karkarwa tsaki yaja ya tabe baki inda yake ajiye magani ya duba cikin sa'a ya samu ya dauka ya ballo biyu ya dago kanta ya bata ya bude gora ruwa ya kafa mata abaki Tasha kallon maganin takeyi kamar tace ya kara mata dan yau daya da bata taunaba batajin dadi rikeshi nayi gam ina goga fuskata saman wuyansa ina hucin zazzabi Dan nasaba alallabani kamar yada ummi takemun gashi ajirgi ma Ahukhuya ya lallabani k'asa nayi da murya, " mai sunan Abbu ka lallabani idan banida lfy lallabani akeyi na fada, ina had'e face d'inmu ina hawaye bakin cikin yama Dr Sardauna yawa bugemun baki yayi ya ingijeni " ke Dan ubankin tashi ki koma bayan mota ki kwanta yar iska jarababiya rashin tarbiyar zaki Nuna akasar Hausa jarababiya kawai zakici uwarki jikina ba na banzaye mata bane irinki naji zafin maganar sosai amma babu yada na iya saboda

ina bukatar gumi wlh har suma nakeyi idan haka ta faru banyi zuciyaba nasake dawowa jikinsa na rikesa gam ashagwab'e nace" Dr Sardauna kayi hakuri ceton raine zakayi wlh Nima idan ba doleba babu abin da zan da wannan lusarin jikin naka mai sufar mata niko na fadane Dan na bata masa azahirima bantaba ganin cikeken namiji mai cikar halita irinsaba wani Bacin raine yazo masa baisan lokacin da ya sharara mata mariba ya harbata ya matan da wata Amana janyeta ya wurgata baya " ni zan nunamiki ni Dr Sardauna bana cikin lusaran maza sai nasaki kinfadi haka da bakinki idan hakan bata faruba kice ni ba dan halak bane yau kinci darajar mahaifina amma kijirani wlh sai kinyi nadamar fadin hakan kuma daga yau bake bani idan kika sake shiga sabgata wlh zakiyi nadamar zuwanki duniya yar iska mashayiya ya fada yanama motar key ya fizgeta da karfi yana sharara gudu ransa abace yana kisama irin azabar da zai mata wacce itace ta karshe tabbas yasan daga ita bazata sake fatan shiga rayuwarsa ba Dan ya tsani yarinyar bata da tarbiya bata cikin irin mutanan da yake hulda dasu jiyake kamar ya tatara ya koma gidansa,Wanda bayada niyar hakan sai bayan yayi aure,

Naji ciwon maganganu da ya fadamun amma naji dadin yada yaji ciwon lusarin da nace masa murmushi nayi nima ina tsara yada zan Rama abun da yamun da karfi nace " Dr Sardauna na tsaneka bakada kirki yada ya karawa motar gudune yasa nayi mugun tsorata naja bakina nayi shiru Dan fah duk abinda nake masa wlh inajin tsoransa kwanciya nayi na rufe idanuna narasa mekemun dadi duniyar ma naji ta isheni amma da na tuna sati dayane zanyi sai naji farin ciki driving yake ransa abace sigari ya kunna yanasha cikin nutsuwa tunda na farajin kaurinta na kife kaina na toshe hancina ban yada yagane banason warin ba, haka dai har muka shigo garin Katsina abinda yasa ko na gane waya naji yanayi akofar wani makeken get muka tsaya yayi honr mai gadi ya bude masa ya danno hancin motar cikin gidan masha Allah duk suna tsatsaye harabar gidan parking space ya shigar da motar yai parking Mahabeer yanufo gunsu fitowa yayi gani iyayan NASA yasa ya bude mata motar ya bata hannu kin kamawa tayi ta murguda baki ta fito ai tana hango Mahabeer ta nufi gunsa tana dariya shima dariyar yakeyi ya ware mata hannayansa ta fada kirjinsa tana farin ciki Dr Sardauna ko kallo basu isheshiba ya wucesu Khalisat da ke tsaye kusan ghaisha ganin Sardauna ya nufo gun ta zuba masa idanu ta dan kallesa ta lumshe idanunta tana sabke ajiyar zuciya, gunsu Daddy ya nufa zee baby ko sai tabara takewa Mahabeer ashagwabe tace" Ahukhuya nayi missing dinka wancan mugun yayi ta dukana azaba iri iri ran Mahabeer yayi mugun baci ya kamo fuskarta yana shafawa idanunta masu mutikar haske ta zuba masa tana wani marerecewa " my zeena kiyi hakuri karki sake shiga sabgarsa kinji Rabin raina? " insha Allah my Ahukhuya na? dariya sukayi atare Daddy yace" Mahabeer kawota mana taga dangi mai ran karfe yace barni da ja'irin yaroAunty hauwa sai farin cikin takeyi jitake kamar Faisal dinne, gun jama'ar suka Iso kowa kallonta yakeyi saboda tsabar kyawunta da kuma tsantsar kamar da sukeyi da Dr Sardauna kan Daddah tayi da gudu itako toni ta fara kuka ta tuno da danta Faisal rungume juna sukayi Najib dariya yake harda rike cikin Dr Sardauna ko tunda sukazo ya gaidasu dama shi ba sabgar mutane yafi shiga ba to wannan abunda zee baby tamasa yau yasa yaji yanason kara nesa da kowa shigewarsa, part d'insu yayi itako zee baby dariya takeyi tana buga bayan Daddah har tayi shiru ta saketa ta nufi gun Daddy ta rumgumeshi ta saki kuka tun karfi agigice yace momy waya tabaki cikin shashekar kuka tace" Ammin wlh ku kirasa ku tambayesa kuji azabar da yamun yau kasheni ne baiba wai ni annoba ce cikin dangi baya ko jin nauyin sunan da nake dashi gaba daya jama'ar suka dauki salalami " aikuwa Dr bai kyautaba bakonka Annabinka ne gaskiya amasa magana ran Daddy amutikar bace ya rika waigawa inda zaiga Dr Sardauna babu alamarsa parlon suka nufa baki dayansu kafa yaran suka gudu gudun kar aturasu kiransa ya sabke akansu Mahabeer ya nufi part d'insu gun Sardauna ransa amutikar abace.....

🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀kuci GABA dabin yar mutan Niger domin kuji yada labarin zai tafi cikin wani yanayoyi da dama na rayuwar duniya Wanda Azahirima na faru

*ZEE BABY*

*DAN ALLAH KARKU FITARMUN DA BOOK WAJE*

*👉🏻7*

....kofar d'akin Dr Sardauna ya murda ya shiga da sallama ya fito daga wanka kenan daure da towel yana goge jikinsa ya amsa sallamar Mahabeer ya iso kusansa" Faisal meyasa baka tausayin Zainab yarinya cefa saida lallaba ba dukaba wlh bata da lfy tunda muka baro Saudia zazzabi take da amai amma kamata duka ko yaya take fah yar uwarka ce jinin kace bakada maraba da ita gata marainiya tunda Mahabeer ya fara magana Dr Sardauna bai kallesa ba murdaddan jikinsa ya shiga gogewa ya bude wardrobe ya ciro jallabiya fara sai kamshi take zubawa tamkar yanzu ya fesa mata turare ya saka jikinsa yaje gaban dressing mirror ya taje gashinsa Wanda yake kwance luf tamkar ka kitsa Dan Tara gashi yake tamkar yada indaiwa sukeyi ya dauki turaransa mai masifar kamshi da tsada ya fesa wlh zakace balarabene sak bai shafa mai ba" Faisal dakai fah nake magana? duk da yaji zafin abin da Mahabeer yamasa ga Wanda zee ta masa, ya juyo fuskarta dauke da murmushi " sorry my brother bazan karaba

End of Chapter 10Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next