Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Misalin karfe tara na safe zaune suke kan dining suna breakfast Sardauna ya zubama Nisha idanu saki murmushi yada nisha takecin nama kasa cikin rawar jiki kamar wani zai amshe mata kai ya girgiza"my Nisha kici mana ahankali waye zai amshe miki ya fada yana murmushi kallonsa tayi tana kid kif da idanunta sun kawo ruwa"my sweetheart kabarmun dariya wlh jinake kamar wani zai amshemun fah"yi hakuri ba mai amshe miki my Nisha ya fada yana jan hancinta bata sauraresa ba saida taci cinya da kirji ta hada tea mai uban kauri tasha mik'ewa Sardauna yayi" my nisha na tafi ba rakiya da cup d'in tea dinta ahannu ta rakoshi har har kofar parlo rumgumota yayi ya mata kiss agoshi "maza aje aci kaza yaja glass kofar ya fice itako ta dawo tana dariya ta zauna aparlo tana shan tea ta Mike taje ta dauko cinyar kaza ta zauna tanaci,
Gidan Mahbeer cikin shiri ya fito yana waya" ki kwantar da hankalinki khalisata yau insha Allah zan turo iyayena bari na lallaba yar rigimar ya tsinke kiran kofar bedroom din zee ya tsaya yana bubugawa kofar ta bude " wai meye zaka dameni ba wani anfani kakemunba shigowa dakin yayi "zo kiji
mana my zee magana zamuyi ni banason fada baki ta tab'e hannuta ya kama suka zauna bakin gado yana rike da hannuta"kanwata yar kirki Dan Allah temako nakeso kimun please hannuna na janye na zuba masa idanu cikin tsiwa nace temakon me zanma? " yauwa so nake muje gida kicewa su Daddy kece kikeson na Kara aure na auri khalisat tausayi take baki kinga nama Daddy maganar yakiya yace ko mata sun kare bazan auretaba kuma bai yarda namiki kishiyaba ki temaka mun kallonsa nayi cike da mamaki" yo idan ka aureta ya zaka mata kaida bakada anfanin komai? " wlh ko kusanta na tsaya tashi take gau kecedai bata tashi agabanki murmushi nasaki" gud my heart muje to ai farin cikinka nawane zan temakama rumgumoni yayi yana dariya "nagode kanwata zan kasance mai muku adalci jikina na amshe ina dariya" ai ba komai bari na shirya cikin gagawa na shiyar cikin wani ratsatsan less pink colour mai adon duwatsu baki Riga da siket na daure gashina da ribbon na murza daurin dankwali jaka da takalmi duk pink color mahbeer rumgumota yayi "kanwata kinyi kyau sosai wlh murmushi nayi"nagode mijin mace biyu dariya yayi yaja hannuna kuka fito takalmina mai shegen tsini akafata wayata na dauka a parlo muka fito ya rufe kofar muka nufi rumfar ajiye motoci "wow mijin mace biyu gidanmu akwai kyau dariya yayi muka shiga mota yaja muka nufi get mai gadi ya bude masa ya fice ya harba motar kan titi zee baby sai surutu take masa yana dariya Dan yana jin farin ciki yada zee baby ta yarda ya auri khalisat gudu yake sosai kan titi yan mintina kadan suka kawosu kofar gidan iyayan nasu honr yayi aka wangame masu katon get suka shige cikin sa'a kuwa Daddy na nan akusa da get Mahbeer yayi parking suka fito hannuta ya kama suka nufi part d'insu Daddy.............. ✍🏻
💃🏻Yar lelen Janaf ce🤙🏻
*💖💖👩🏻🦱ZEE BABY👩🏻🦱💖💖*
MALLAKAR UMMU FAREESA NE
*DAN ALLAH KARKU FITARMUN DA BOOK WAJE*
*👉🏻38*
....da sallama suka shigo parlon suna rike da hannu junansu Daddy da ghaisha da ummi Raiyan duk suna parlo zaune Daddy na shirin tashi ya gansu ya koma ya zauna ghaisha tace" oyoyo momy zee ta janye hannuta ta nufi gun ghaisha ta fada jikinta tana dariya"ummina ina kwana Daddy ina kwana dariya suka Mata mahbeer ya iso ya gaishesu ya zauna kusan Daddy zee tashi tayi ta koma kusan umminta ta rumgumeta tana mata kiss"ummina nayi missing dinki ina kwana murmushi tayi ta shafi kanta" baby kin tashi lfy? " Alhmdllh ummina ina so hafeeza? ghaisha tace" tana school Daddy ya kalli mahbeer "mahbeer naji dadin yada ka rike Amana Allah yama Albarka mik'ewa to ni zan fita sai ka tashi mutafi nanah ta rugu gunsa daukarta yayi" autar gida ya kike dariya tayi" ina lfy dady mahbeer ya kalli zeey baby da take sabgogin gabanta yace" zainab kima Daddy bayani abinda kikace kinaso ko?
jikinta ta janye ta Mike tazo gaban Daddy ta sunkuya cikin ladabi tace" Daddy dama yaya mahbeer ne kuma tayi shiru Daddy ya koma ya zauna" monyna dama me fadi maganarki kai tsaye meye yamiki kuka ta fara" ni banaso na hada fitina kar zumunci ya baci" haba momyna dawaye zumunci zai baci ai ni idan ya miki wani Abu kikaki fadi wlh kin cuceni Dan Ke amanace wajena har mahaifiyarki wlh nafi sonki Akan yarana ke yar zumunace maza fadamun meye ya miki mahbeer ya kalleta gabansa na faduwa" zainab bangane inda kika dosaba fah cikin kuka tace" yo dama ina zaka gane tunda baka ganewa wlh Daddy dama khalisat ce yakeso yar gidan anty amarya shiyasa tunda mukayi aure bai taba sabke hakkin da Allah ya Dora masaba kullum saiyace bashida lafiya amma wai zai Kara aure ashe nice bayaso shine yace wai muzo insa baki ku yarda ya auri khalisat bayan auranta idan sun gama cin amarcin ya fara kulani niko saboda biyayyar aure duk da na tsani kishiya to ya zanyin tunda inason mijina Dole nace muzo na rokeka ta
matsa gaban Daddy ta rike kafafunsa tana kuka"Daddy don Allah kubarsa ya auri khalisat ko ya fara sabke nauyin da yake kansa wlh banaso Allah yayi fushi dashi ummi Ranyan hankalinta yayi mugun tashi sanin karfin sha'awar yartata Allah kukane ya kufce Mata ta Mike da gudu tayi kan yarta ta janye zee daga gun Daddy ta rumgumeta Daddy mutuwar zaune yayi "bakinsa ya kasa furta komai saboda Bacin rai da kunyar abunda d'ansa yayi gashi ummi Raiyan taji hankalinta ya tashi ance ba'ason yarta za'a mata kishiya mahbeer hankalinsa ya tashi ya bude baki zaiyi magana ghaisha ta zabga masa Mari" wlh mahbeer kabani kunya mune zaka tozarta abaka amanar yarinya ka ajiyeta tsawon wata da kwanaki babu wani labari Dan shiga hakki karamun kaninka Sardauna yafika hankali da tunani shiyasa son yaron yafita daban azuciyata duk basu shiru da zainab wlh na tabata da shine bazai tozartamu ba haka to wlh sai ka saketa yanzu gun ummi ta nufa "Raiyan kiyi hakuri don Allah ki ajiye hankalinki insha Allahu momy zataji dadin aura"khadija wlh banji haushi tashin hankalina dayane da tace bai sabke mata nauyiba yarinyar tanada karfin sha'awa banaso ta fada halak amma babu komai Dan uwanatane shine yaje ya daukota kuma nasan halinta kumasa uzuri amma inaso ashirya mana tafiya zan tafi da baby saudiya tsaye daddy ya Mike ya wanke mahbeer da Mari yana wuci" wlh mahbeer kaci Amanata na dauki yar kanena mafi soyuwa azuciyata na hadaku aure ganin yada ka Nuna kaunarta gareta amma kaci amana har kasa mahaifiyarta kuka Dan bakada kunya ka daukota kakawota ta roki iyayanka ka Kara aure ka ajiyeta baka bata hakkinta yanzu da yarinyar mai shige shigece taje tabi maza fah nagode mahbeer gun
ummi Raiyan yazo" Raiyan kiyi hakuri babu inda zaku komai zai wuce tunda baya Sonta zan raba auran zan aura da ita inda za'a rikemun ita da mutumci hannu zee ya kamo yazo gaban mahbeer ya kalleta" momy tsakaninki da Allah tunda kukayi aure babu abinda ya shiga tsakaninku dashi cikin kuka kanta ak'asa tace" wallahi Daddy babu komai kowa adakinsa yake amma daddy ku yafe masa karkuyi fushi dashi Wlh nayafe masa" Alhmdllh mahbeer inaso yanzu kasaki zainab wlh ko namaka mugun baki iya rikicewa ya riki jikinsa na rawa yace" Daddy Dan Allah ku saurareni kuji uzurina wlh ina son zainab bazan iya sakintaba hannuta ta fizge ta nufi gun mahbeer tana kuka ta rumgumeshi" yayana Mahbeer karka sakeni riketa yayi gam idanu iyayan suka zuba masu cikin tsawa Daddy yace" idan kana sonta da ka sabke nauyin da yake kanka bazan bari diyar Dan uwana ta cutuba ghaisha tace " kwarai kuwa wlh idan baka saketaba baki zanma yanzu wlh kabamu kunya kasa munji kunya agaban mahaifiyarta" ghaisha kutsaya kuji.. " bamason jin komai saketa yanzu kaje ka auri kowacece ma tunda ka bujire mana kansa ya Sada cikin sanyi jiki ya janye zee daga jikinsa yace" zan muku biyayya tunda haka kuka zaba amma zee in a so ki fadi gaskiya tsakaninki da Allah gun ghaisha ta nufa "ummi dama idan yazo guna sai yace bayada lfy amma agun khalisat ras yake"Hasbinallah Dan ubanka saketa ko na maka mugun baki cikin rawar baki yace" kuyi hakuri Daddy wlh bazaku ganeba amma wlh banida lafiya amma shikenan Zainab na sakeki Saki daya ya fada yana share hawayen fuskarsa ya fice zee kuka take kamar ranta zai fita ghaisha ta rumgumeta tana lallashinta Daddy yace "insha Allah momy Alkhairi zai biyo baya Allah yasa haka yafi alheri lallashinsu sukayi har ummi Raiyan suka kwatanta mata ilar
zamansu baya sabke mata hakkinta zata iya bin maza gashi har yana shirin Kara aure aurema da annoba Allah kadai yasan abinda yasa hakan ya faru Dan ubangiji shikeda ikon yin komai alokacin da yaso kai Daddy ya jinjina yana tuno mafarkin da yayi jiya shiyasa daga tashinsa yaba masu aikin gidan sadaka yayi sallah Allah ya baiyana masa fassara mafarkin gashi ya gani saida yaga hankalin ummi Raiyan ya kwanta ta gamsu da bayanin da suka mata ya Mike ya musu sallama yaje ya gaishe da su Daddah yake fada musu abunda ya faru fada suka masa akanme zai sa ya saketa bayanin mafarkin ya musu amafarki ubangiji ya Nuna masa mahbeer Sam ba abokin rabonta bane kaddara ce ta aure kawai ta hadasu sallama ya musu ya fice Dan yanaso ya biya gidan malam kabiru ya masa tambayoyi daket ghaisha ta shawo hankalin zee tayi shiru da kanta ta kaita har bedroom ta kwantar da ita ta zauna tana shafa mata kanta da maganganu masu dadi na lallashi har tayi bacci ta fito ummi ta Saki jikinta ganin sun nuna sun fita jin ciwon abinda mahbeer yama zee Daddy suna fita da direbansa gidan malam kabiru yaje yana kofar gida tare da Almajiransa ya fito
More Hausa novels
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Zazzafan Rabo Part One Complete Hausa Novel
By Aisha Umar Indabawa
Ni Da Yaya Sadiq Book 1 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Dafin Harshe Book One Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.