Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Cike da mugunta ya yaketa daga tsaye ta fadi" Ashhhh Allah ya isa mugu ban yafeba bai mata maganaba dan bashida lokaci da harara ta bishi " wlh indai haka zakayi rawu ka hadu da wahala kwarton banza na mata ko ina kana yawo da mata kunji kunya kai dasu ransa yayi wani irin baci amma bai yi magana ba ya cire agogon hannusa da zobunan sa har biyu Wanda fadar tsadarsu bata lokacine ya ajiye ya dauki Rigar aiki yasaka yanaji tana masa tijara ya fice ya murza mata key daga waje yana Addu'ar Allah karya sa ta masa, wata bannar dakin tiyatar ya shiga, zee jin ya rufeta ta koma ta hau kujerasa ta zauna sai dube dube take taga abin barna tunawa tayi fah dama yana binta bashi kar yaje ya ilatata hakura tayi da barnar tayi zamanta dam tsoro fal zuciyarta don yanzu ma batasan nufinsa ba wayoyinsa ta shiga dubawa dukansu ya kashesu ajiyewa tayi, gilashin sa ta saka ta dauki rigarsa ta sanyi sai futinanan kamshi take rumgume rigar tay akirjinta tana shakar dadadan kamshinsa idanu ta lumshe nan bacci ya dauketa saman kujerasa dama ga gajiyar damben da tayi, karfe biyu da minti talatin da bakwai cif cif Dr Sardauna ya fito daga daga d'akin tiyata ya cire rigar yaba Dr Nabil yana goge zufa ya barsu da sauran aikin yana fitowa suka hadu da Mahabeer " Dr namu ya babyna?" my bro wlh yanzu na fito daga tiyata kuma yanzuma saura awa biyu ta farka " ok bari na koma bayan la'asar zan dawo dan Allah ka kulamun da ita kafasan amaryace murmushi Dr Sardauna yai " sai fa yaune za'a sa muku ranar har tazama Amarya Ok idan ta farka kafin ka dawo zan kulama da ita rumgumeshi Mahabeer yayi yana godiya ya sakeshi" na tafi Daddy yace yana kiranka akashe?" eh da zan shiga tiyata ne na kashesu ya fada yana nufar Office d'insa Mahabeer ya tafi, key ya saka yabude ya shiga ya rufo tana kwance saman kujerasa ta rufo fuskarta da rigarsa bacci take cikin nutsuwa haushine ya turnikeshi duk girman Office din tarasa gun kwanci sai kujerasa da yake zama toilet yashiga yajima sosai kafin ya fito yana murmushi mugunta ya nufi gunta kusanta yaje ya tsaya yana kallonta kirjinta duk awaje tunda ta fitar da abaya lokacin da zasuyi dambe da Ruma daga ita sai yar karmar riga pink colour da wando dogo komai nata awaje surata mai cike da kyawun kallo baki ya tabe k'asa yai da murya zainab yau zaki san kin shiga gonata saida na hadaki da girman Allah karki kuma yarda kishiga sabgata amma kika ki kin sa narasa abubuwa masu mahimmaci awayoyina kinso hadani da macan da nafiso aduniya kin ciramun Suit kala ukku Wanda nafi kauna amma ni zan barmiki dafi mai zafi shegiya mai ruwan karuwai dubi yada take shegiya mai ruwan yar tsana wlh sai nabarki da dafi mai zafi cikin zuciyarki daga yau zamuyi hannu Riga dake figigiya kawai ficiciya dake sai fitsara da fitina kusanta ya matso ya zauna ya janye rigarsa idanu ya zaro ganin gilashinsa ya cireshi rigarta da rabin kirjinta ke waje ya hannu ya gyara mata bakinsa yakai kusan kunneta ya kirata" zee baby Oya bude idanunki zan nuna miki banbancin fari da baki dayake bata nauyin bacci idan ba shaye shaye tayi ba idanunta ta bude ahankali jin ni'imataccen kamshinsa kusanta yasa ta dago idanu hudu sukayi dashi zabura tayi da sauri ta zauna gira ya daga mata yana murmushi " barka da warhaka tantiriya tambayoyi zanyi miki guda ukku daya bayan daya ki amsamun kafin ki amshi hukunci da zai zauna miki azuciya ya hanaki sukuni cikin tsiwa tace " to matsa na, sabkar maka daga kujeraka kokarin sauka take ya sanya tattausan hannuwansa duka biyu ya maidata ya zaunar buge masa hannu tayi mari ya zabga mata ya tsareta da shanyayun idanusa fuskarsa babu wasa" dan ubanki ni sa'ankine zaki rika bugemun hannu me zanji awanan busashan jikin naki Oya dago idanunki ki kalleni ya fada yana kai hannusa wuyanta yana shafawa ya riko hannuta guda yana murzawa cikin wani irin salo yar naji gashin jikina na mik'ewa wasu kwayoyi nake gani cikin fitunanun idanunsa ban gama dawowa daga tunani ba naji amon murasaki mai fitar da amon dadi yanace min" inaso ki amsamun tambaya ta farko kafin tabiyu da ta uku suzo daga nan sai hukunci da zai tarwatsa kwanyarki yaki fita azuciyarki meye dalilinki na fasamun wayoyi da ciciramun kayan jiki da farfasamun turarukana da maiyuka yada yake mun tambayoyin cikin nutsuwa tamkar mai mai mun rada yana shafar wuyana da fuskata da yake ga hannuna da yake murzawa naji jikina ya fara saki ga kasala ta sabko mun sanyi ya fara ratsani mafaka nake nema kamshinsa ya adabeni ga ya tsare ni da rikitatun idanunsa yace karna kuskura na dauke idanuna daga kallonsa abinda yafi rudar da ni Kenan sai lumshe idanu nake nayi kasa da kaina tsawa ya buga mun da karfin gaske saida hantar cikina ta kada na dago na kalleshi" dan ubanki Oya bani Amsa duk da naji tsoransa mutika ga yanayin da na shiga amma na dake na dauke idanunta daga kallonsa muryata ta fara canzawa nace" Dr Sardauna bari kaji dalili...........
*💖💖👩🏻🦱ZEE BABY👩🏻🦱💖💖*
*DAN ALLAH KARKU FITARMUN DA BOOK WAJE*
*👉🏻13*
....na farko kaine ka zalumceni kamun dukan mutuwa har na suma shiyasa nama barna saboda bana yafiya idan an cuceni sai na Rama naba fada ina son kwace hannuna da yake murzawa duk gabobin jikina sun Saki kin sakina yai ya kara kusantoni niko sanyi nakeji sai lumshe idanu nakeyi murmushi mugunta yasaki" gud naji amsar farko sai tabiyu meyasa kika dauki wayar matata kika zageta uwa uba kika ce ni dan iskane bin mata nake meyasa kikaso ki rabamu meye dalilin ki Oya amsa?? ya fadi yana kamo k'uguna da hannu biyu yana murzawa cikin wani Dan iskan salo duk na rikice daket na tataro jarumta " kaga malam ni fa ba yar iska bace da zaka rika tabani baki ya bugemun da karfi" ni dan iskanne amma ke bakida matsayin da zanyi iskancin dake, Dan baki kai maceba Oya bani amsar tambayata meyasa kikeso Raba ni da sweet babyna kinsan irin son da nake mata kikaso rabamu jinayi raina yayi mugun baci bansan lokaci da na kaimasa duka akirjiba kai tsaye babu shaka nace" taci uwarta Dan kutumar ubanta ba baby ba dai yar tsana kuma ban saniba banida amsa idan kasheni ma zakayi to yi niyah? banza ya mata sanin bugu bayayi mata Dan fusrkarta tayi jajur saboda Marin da yarika gabramata baki ya ciza " gud to meyasa kike neman fada da mata idan kinga suna mu'amula dani meye dalilinki bani amsar dukansa na fara akirjinsa babu ko dar nace" banida amsa dan haka idan zaka kashenine to sai kasa niyah?? murmushin gefen baki yayi ya kamo fuskata bakinsa ya Dora akunnena yai magana k'asan makoshi cikin wata irin murya" ok bakida dalili amma idan kin ganni da mace kike haukacewa kirasa nutsuwarki har sai kinyi yada kikaga ta bar inda nake na lura Sam bakison ganina da wata mace kina sona ne ko me?? Ya fada yana sakin fuskata ya dagamun gira ya Kara rike k'ugunta Dan so yake yamata Alluran da za'ace tabbas mahaukaciyarce yasa mata kasala har tsawon wata biyu yaga iya shegenta da fitsara da rashin tsoro agigice na dago kaina na kalleshi raina abace " wa'iyazubillah wlh bana kaunarka gwara naga gawata da na soka Allah gwara na mutu bansan soba ko a akaddarata zan roki Allah Ubangiji kada ya doramun kaddara da zata hadani dakai da sunan soyayya wlh na tsaneka Dr Sardauna baka cikin irin mutanan Da zanso har nakoma ga Allah ni Zainab wlh nafi karfinka a soyayya wlh bazan taba somka ba kuma da kakecewa ni busasar macace babu abinso ajikina cikakun maza masu lfy irin su Ya Mahabeer su sun san cikakar mace bazasu fadi hakaba kai har yanzu bakasan macaba shiyasa kaje ka jajabo mai kirar Aladu mace ba fasali gindimdim wlh da nasoka gwara naso kare jikake tass ya sharara mata mari hudu ajere yana huci sakinta yayi ya Mike tsaye " nine kike hadawa da kare nine kika tsana haka Ashe kiyayar da kikemun takai haka nine kike gayawa magana mai daci haka matar da zan aurace kike kushewa haka nine ba Namiji ba Wallahi na fasa horon da zan muki na sauya Salo Alluran da yazo da niyar mata har kala ukku ya cirosa tanaga Allura hankalinta yayi kololuwar tashi amma ta dake yau ta dauki niyar duk abinda zaiyi saidai ya mata kuma taji dadin yada ransa ya baci yake tsuma kallonta yai yagane tsoron Allurane fal aranta murmushi yai cikin wani irin voice yace" ki ajiye hankalinki na fasa miki da naso na miki wata shegiyar Allura wace zaki kai tabonta har lahira dafinta na tare dake azuciyarki zaki daina duk wani iskanci amma yanzu zan samiki dafin da yafi wannan Allura watsar da Alluran yai yana kallonta "na rantse miki da Allah idan yau ayanzu baki furtamun kalmar soba ni badan halak bane duk da bana kaunarki kamar yada baki kaunata duk na gama ganoki haukan banza kike wlh sona ya miki mugu mugun kamu amma zaki fada da bakinki zan miki hukunci mai tsauri wanda zai zauna azuciyarki daram bazai taba fitaba zan Nuna miki ba kowane namiji ba zaki kalla ido da ido ki fada masa abunda kikaga dama ba kuma ya barki hararasa
More Hausa novels
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Zazzafan Rabo Part One Complete Hausa Novel
By Aisha Umar Indabawa
Ni Da Yaya Sadiq Book 1 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Dafin Harshe Book One Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.