Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Maijidda tace"wlh ni dama nasan zainab bazata iya wannan abuba."zainab tace nima haka. Kowa na gurin ya shaidi zee har Nisha tace"wlh dama jikina ya gama bani ba ita bace Allah ya isa da akaso hadani da yar uwata ta fada ta Mike ta nufi gun zee suka rungume juna suna kuka.
Kowa yan dakin saida ya tausaya musu kawu Saminu yace"to kuyi hakuri Allah na tare daku Aisha Allah ya miki albarka ya kauma baki mai anfani.
Nisha ta sake samun matsayi cikin family kowa sai Albarka yake samata da yabon hankalinta.
Nuhu yace"wlh Aljani shedani ne yaso hadasa fitina tsakanin yan uwan juna Allah bai bashi sa'a ba."Sardauna ya zubawa matansa idanu cike da so da akaunar so bama zeey kamar ya kamota ya cinyeta yakeji ya matsu su tafi gida sai wani lumshe idanu yake yana shafa kwantacciyar sumar kansa.
Daddy yace"yanzu sai magana ta gaba shine Raiyan da Saminu kanin mijinta mun yanke zata aureshi taci gaba da zama karkashin inuwar dan uwan mijinta mun gama magana da ita da kuma mahaifiyarta ta kuma amince shima ya amince.
dariya yan dakin suka dauka baki daya zeey kuwa murna tasa tayi dan ihu tana cewa"yauwa daddy inaso ahadasu Allah ya basu zaman lfy da kwanciyar hankali.
Hassan da hussaini ma murna sukeyi Ammi tace"Alhmdllh ai shiyasa tun farko na amince haka Allah ya tsara mata aurqn yan uwa biyu meye ajikin wani jansi da baza'a aura ace sai balarabe dan uwanta kuma ai zubin larabawan gareku wlh naji dadin hakan yayi min dari bisa dari amma Raiyan nawa take da zatace bazata sake aure ba wanna zuri'a mai albarka Ubangiji ya kara hade kanku."suka amsa" Ameen.
Maijidda tace"kanina Allah ya kara tsarzmun kai duk Wanda zai cutar dakai mutum ko Aljan Allah ya shiga tsakanin ku dashi Allah ya baka wani kuma insha Allah cikin jikin zeeanab yafi karfinsu nan gani nan bari."Dariya Sardauna yayi yana kada kai.
Nisha takai ci da bakin ciki yasata ta Mike tabar gurin ta fice tana matsar kwalar bakin ciki rabuwa da cikinta saidai tayi kudirin zubar da cikin zeey idan yaso suma sai ace aljannanta ne suka zubar.
Haka taron ya watse cike da so da kaunar junansu daddah ta kama zee suka tafi part d'inta su ghaisha da su ummi suka koma ciki ummi Raiyan duk kunya ta gama kamata jin zata auri kanan mijinta sai sun ne sun ne take.
Su Sardauna suna gidan har bayan isha'i kafin suyi shirin tafiya zeey na rungume da Ammi ta kurawa Sardauna idanu sai lumshesu take dan wata irin jaraba ce take cinta sotake tajita a jikin Sardauna yana cacakarta da karfin gaske bakinsa ta kurawa idanu suna magana da Daddy kan sanya ranar auran Hafeeza da Ahmed.
Ghaisha tace"Allah ya kaimu goben hankali ya kwanta yanzu ai Autana zo kaji."Sardauna ya mike daga kusan daddy ya zura hannunwansa cikin aljuhu yana takunsa cikin isa da kasaita fuskarsa dauke da murmushi ya nufi gun ghaisha.
Nisha ta kureshi da idanu tanajin mugun sonsa na azalzalar zuciyarta sai lumshe idanu take.
Ya zauna kusan ghaisha ya kwanto jikinta"My momy gani."Autana Allah yama Albarka ya karemun kai ta fada tana shafa kansa.
"Ameen momana mu zamu tafi gida bacci nakeji kwana biyu banida nutsuwa.
"Bakomai ai gashi Allah ya warware komai cikin sauki tashi muje na hada maka coffee kasha ta fada tana janyeshi jikinta ta Mike ta mikar dashi suka nufi kan dining.
Hassan da hussaini mamakin shagwabar Sardauna suke sukayi ta musu dariya.
Daddy yace!"ai zaku gaji idan dai khadija da Faisal ne."Najibi yace"ni wlh kishi nakeyi.
Hafeeza tace" wlh nima."ummi tayi dariya"Aikuwa zakuyi tayi.
Nisha fa haushin kowa takeji kawai dai ta daurene ana raha dan kar agano ta.
Ghaisha kuwa saidai tama Sardauna wayo yaci abunci sosai ta tsiyaya masa fruit yasha tukun ta hado masa coffee da kanta ta kawo masa suka dawo parlo yana sha suna hira da daddy har ya gama ya kalli Nisha"Aisha ku tashi mu tafi gida.
Zuwat ta mike zee ta kura mata idanu tayi Saurin dauke kanta tanawa Ammi magana.
Sardauna ya mike ya nufi gurinsu ummi ya musu sallama suna musabaha dasu Hassan ya kalli zeey"baby tashi mutafi.
Buris tayi da shi saida Ammi ta mikar da ita tsaye bata kallesa ba ta nufi gun ummi ta rungumeta ta mata kiss ta rungume su hussaini suka yi sallama taje tama su daddy sallama da ghaisha Nisha ma ta musu suka tafi.
A cikin mota zeey tana baya Nisha na GABA ita da Sardauna tana rungume jikinsa yana shafa cikinta yana jin haushin rashin cikin sai ciza lips dinsa yake gefe tausayin Nisha yake.
Narke masa tayi ajiki"my Dr kayi hakuri baga wani mun samu ba agurin my dear ai duk dayane Allah nima zai bani wani insha Allah."Allah ya yarda my Neesher.
"Amin.
Wani bakin kishine ya tukaremun zuciyata naji kuka ya kufcemun nayi Saurin toshe bakina dan kar sujini na hade kaina da gwiwa inaji sunamun magana nayi shiru nayi banza dasu kamar bacci na keyi niko idanuna biyu har mu kazo gida muna zuwa yana parking na bude mota afusace na nufi ciki ko kallo basu isheni ba dan sam yau bana iya boye kishin Sardauna gwara nayi nesa dasu dan gudun kar nayi abin kunya da yar uwata mai kaunata.
Sardauna hankalin sa gurin zee Nisha tace"sweetheart me akama my dear naga kamar tana fushi.
"No ba fushi take ba ya fada yana rufe motar ya kama hannun Nisha suka nufo ciki.
lokacin zeey ta Haye sama.
Sardauna saida ya hadama Nisha ruwan zafi tayi wanka shida kansa ya shiryata cikin kayan bacci saida ya sakata bacci da salonsa Wanda ta zauce tana masa kukan dadi yada tsotseta tas shiko tausayin rashin cikin da tayi ne ga babbar matsalar da take ciki ta rashin mahifarta bazata sake daukan ciki ba yaji yana mugun tausayawa rayuwarta shiyasa yayi alkawalin bata farin ciki na har abadan ganin baccinta yayi nisa ya janye jikinsa ya lulubeta da blanket ya sauka ya fice.
Kai tsaye saman bene ya haura bedroom d'insa ya shiga yayi wanka yayi shirin bacci cikin wasu Riga da wando ruwan toka masu santsi ya fesa, turare yana baza kamshi ya nufi dakin zeey ya daukota.
Bangaran zee baby tana hawa sama ta shige bedroom d'inta ta fada saman bed ta fashe da kuka tana birgima saman gado tanajin wani irin daci da zafin kishi yana azalzalarta tsawon awa guda cur tayi tana kuka har zuwa yanzu taki dainawa.
Kofar ya murda ya shigo da sallama, yaji gunjin kukan zee arikice ya nufi gadon.
"Wayyo Allah!! My baby nine ko.? Ya isa da gudu ya dauketa cak ya rungumeta yana jijigata kamar jaririya"pls Mrs Sardauna kiyi hakuri na tuba jininki ya hau sosai ga sabon ciki ajikinki ga yawan zazzabi da amai yasa mun ke gaba ji yanzu ma jikinki akwai zafi kibar yawan damuwa na rantse miki da Allah zainab kece azuciyata sonki yayi fice karki taba tunanin akwai ta biyun ki azuciyata wlh kukan,ki da kinsan yada yake bata mun rai wlh bazaki yiba.
Kanta ya tallabo ya hade face dinsu yana shaka mata numfashinsa, cikin kasalaliyar murya mai cike da shaukin so yace "Babyna Oya fadamun me yasaka min ke kuka.? cikin shashekar kuka na kirasa"My Sardauna nah? "Na'am Mrs Sardauna pls ki temaki Sardaunan ki kibar kuka Oya Baby fadamun menene.? Ya fada yana tsotse hawayen fuskarta yana shafa bayanta"My Sardauna nah kishinka yake damuna narasa ya zanyi sonka yamun yawa bana son ganinka da kowace mace saidai kash, babu yada na iya yar uwata na sonka nima ina sonka itama ina sonta My Sardauna nah?na kirasa ina ririkeshi.
"Mmn tiwis don Allah kiyi hakuri ya fada yana mik'ewa rungume da ita ya sauka ya nufi toilet ya hada ruwan gumi yayi mata wanka tas tana zuba masa shagwaba da sangarta har ya gama mata ya,nadota cikin towel ya fito rungume da ita ya dorata saman gado ya goge mata jikinta ya shafeta da maiyuka masu kamshi ya,saka mata rigar bacci yar guntuwa ya fesheta da turare.
Ya kura mata idanu yada take turo baki.
Murmushi sakar mata ya dauketa cak yana rungume da ita suka sauko k'asa yaje kitchen ya dauko mata fresh milk,ya zauna parlo tana rungume jikinsa yana bata"My Abulena maza shanye babyna yunwa yakeji.
Dole na amsa inasha ina lumshe idanu dan wata muguwar sha'awarsa nake baki na turo gaba"Yayana? Idanu Sardauna ya kurama zeey yada take lumshewa ya gano zallar fitinar da take cinta.
agaguce yasamu ta sha fresh milk ya goya abarsa dan bata iya cin komai ya dauko ruwan gora guda marar sanyi suka haura, saman bene.
Suna zuwa dakin baccinsa ya shige ya murza, key tana goye abayansa sai kissing d'in wuyansa zuwa kunnensa take tana nishi tana shafar kirjinsa sai lumshe idanu yake."oh Baby nima akame nake.
More Hausa novels
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
Dafin Harshe Book One Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel
By Oum Yasmeen
A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
A D U N I Y A Ta Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
A Sanadin Son Ki Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Search across the available chapters.