Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
sonka gashi Nisha ta nuna itama sonka take Dole zan kaurace muku kuyi soyayyarku My dear Nisha nagode da adalcinki gareni da har kikaji zaki iya barmun Sardauna da banida miji wlh koda banida miji bazanso mijinki ba ai da kunya kuma ni bana ra'ayin mai mata inada mugun kishi bare Sardauna da yau daya sonsa yamun mugun kamu sonsa ya shigeni sosai har nakejin idan banyi nisa dashiba akwai matsala baba Astagafirullah ya Allah kayafemun ka ciremun son Sardauna ka maidomun son mijina mahbeer Sardauna yafi karfina yau zuwa zanyi nayi shaye shaye naje yawona da gidan casu na cashe nasha kwaya da sirot na more na tafi gidansu manal da jannat na boyema Sardauna har yagaji ya tafiyarsa Nigeria ni bazan koma k'asar haussa ba tunda Sardauna yafi karfina Nisha. Ki ajiye hankalinki Sardauna nakine ni ko da banida miji bazan shiga rayuwarki ba da masoyinki mahbeer kazo gareni nafasa cewa ka sakeni wlh nasan kana sona baza ka gujeniba dan dan uwanka ya kusanceni da zaran Sardauna ya gaji da nemana bai ganni ba yabar saudiya zan dawo gareka mijina yaya Mahbeer zan nuna maka zallar so da kauna my Ahkuyana takai karshan maganar tana sakin wani irin kuka mai cin rai dama duk maganar da take cikin kuka takeyi limozin ta tsinkayo tun kafin ta ISO ta daga hannu tana isowa ga banta tayi tsaye tana dingisawa tana cije baki ta ISO gaban motar. aka bude mata ta shige motar direba yaja suka tafi a motar duk mafi yawa takarune zee a kusan wata balarabiya mai tsohon ciki take zauna tana kuka wiwi balarabar ganin zee itama balaraba ce ta janyota jikinta tana buga bayanta tace" yarinya me aka miki ya kika fito babu Nikab yi shiru ki fadamun............... ✍🏻
🤾🏻♀Yanzu Aka fara muje zuwa⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀
*ZEE BABY*
*book 2 👉🏻3*
...."jikin macan na shiga sosai ina kuka ban mata magana ba. " bazaki fadamun wa ya tabaki ba..? cikin shashekar kuka nace" Yayana ne ya dokeni ummana bata gida tana gidan biki gurinta zani yanzu. "to yi shiru bari kukan kin masa laifine shiyasa ya dokeki bari kukan kinji.?kai na daga mata nayi shiru. dagoni tayi ta gogemun hawayena. ta bude Jakarta taciro Nikab ta bani nasaka tana mun hira sauran jama'ar sai kallonmu suke. cikin tsiwa nace" wai dan durin uwarku me kuke kallo ajikinmu shegu yan iska. duk kunciki mana mota da tsami baki ta rufemun da sauri tana girgiza kai. "kul ki kuma zagi babu kyau. " to naji ai naga sun zuba mana idanu kamar mujiya ne. kai ta girgiza shiru nayi ban sake maganaba har mukazo inda zata sabka nayi mata godiya ta sabka niko ba azoba inda zan sabka dan gidansu manal zani. ana isa unguwar tun daga nesa nace" nan zan sauka motar ta tsaya na fito ahankali saboda zafin da nakeji agabana ina sabka na basu kudinsu na tsallaka titi ahankali na nufi layin gidansu manal. akofar gidan.
na tsaya ina danna Bell din gidan ba'a jima ba aka bude Radah ce murmushi na sakar mata na shigo rungumeni tayi ta rufo gidan tanajin dadi ta sakeni tayi ciki da gudu tana Kiran manal kai na girgiza nabita abaya. bangaran Sardauna zee na fita kamar da 30 minute ya farka yana lalubanta bata jikinsa ya kalli kofa yaga abude kai ya girgiza ya saki murmushi yanajin wani mugun farin ciki na ratsashi sabkowa yayi daga saman gado ya shiga bathroom yayi wanka ya dauro alwalla ya fito ya zura jallabiya sai istigifari yake irin yada yayi bacci baiyi sallah ba akan lokaci kan darduma ya hau ya tayar da sallah. bayan ya gama yayi ta neman gafarar ubangiji yama dan uwansa Addu'a da matansa Allah basu zaman lfy Allah yasa zee ta amshesa hannu bibbiyu. ya shafa Addu'a ya Mike dan wata irin yunwa yakeji saman kujera ya nufa ya janyo table yaci naman kazar kadan yasha lemo ya Mike yaje ya dubo zee da jikinta yaji ko bata zazzabi. wayarsa ta dauki ruri dauka yayi
yai picking ya kara akunne. "hello my Neesher ykk ina babyna nayi missing dinku. " My Dr i miss u jinake kamar ka shekara. murmushi ya saki" my Neesher ai muna tafe gobe insha Allahu zuwa jibi zamu isa. " my dr ka gashemun da my dear kace nayi missing dinta pls." zataji wlh baccin gajiya nayi shiyasa yau ban kiraki ba. " babu komai ai ni nakiraka babynka na kewarka. " ki shafamun shi dakyau da nazo zan bashi kwarin gwiwa. zan kiraki anjima. " OK sweetheart bye murmushi yayi yaji ta tsinke kira. Kiran daddy yayi lokacin yana Office ya dauka suka sha hira ya kashe ya kira ghaisha lokacin suna parlo ita da ummi Raiyan da su tuwusai da minata ta dauki Kiran ta kara akunnata. Sardauna ya shagwab'e" hello momyna i miss u. daga can tace" i miss too my son ina momy...?"
Tana lfy bacci take momy ki gaishemun da ummi zan kiraki an jima. " to su tuwusai Na gaisheka. " kice zan kira anjima bye i love u ghaishata ya tsinke Kiran
yana wani irin farin ciki ya ajiye wayar ya dauki turare ya fesa yaje gaban dressing mirroir ya gyara gashinsa yana wakar" wayyo zainabu abu Abuleta yar balarabar yarinya Wanda yace zainabu Abu ai kamar yace Sardauna Faisal duk Wanda yaso zainabu Abulena ai kamar yasoni duk Wanda baison Zainabu Abulena to wallahi Sardauna baya kaunarsa Abulena yar yarinya my gidan dadina Abu. Haka fah yari rika waka yana sakin murmushi ya gyara gashinsa ya fito ya nufi part d'insu Ammi suna parlo suna kallon TV ya shigo da sallama murmushi dauke fuskarsa. Ammi ta amsa ta rike baki" oh wannan yaran ai sai a barku wuni guda babu ko lekowa tun safe. kusanta Sardauna ya zauna yana dariya Hassan da hussaini sukace" Yayamun Dr ina yini yau sanmu yafi akirga muna tashinku amma shiru gashi za'ayi la'asar. kallonsu Sardauna yayi" wlh yan biyu gajiya ce shiyasa nayi bacci sosai to ina mutuniyar ko tana ciki akwance.Ammi ta dokesa abaya" kunji ja'irin yaro yo mu ai kai muka gani bari ni naje na ganta miji dadi idan bazata zoba. Sardauna yace wallah bata can koda na tashi bata d'akin. ya fada hankalinsa atashi yana mik'ewa tsaye. ai dukansu suka tashi tsaye.suna hada baki.
Wajan cewa"kana nufin ta fito...? Sardauna amutikar kidime yace" wlh ta fito kofarma abude na ganta ya fada yana nufar d'akunan yana duba ko ina jikinsa har tsuma yakeyi su Hassan hankalinsu ya tashi suka bazu yawon nemanta lugu da sako na gidan suka koma part d'in Sardauna ciki da bai babu zeey baby Ammi kuka ta fara" na shiga ukku ina zainaba ta tafi. Sardauna dabas ya zauna ya dafe kansa zuciyarsa na wani irin mahaukacin bugawa da karfin gaske jikinsa na rawa ya furta"My bugun Numfashina yaushe ne zaki barni na huta yaushe zaki bari muji dadin rayuwarmu pls karkiyi nisa dani wallahi ayanzu bazan iya rayuwa babu keba bazan iya ba sam bazan juri nisanki gareni ba pls ki fito don Allah. Ammi ganin yada jikin Sardauna yake rawa yana sambatu abun ya tsora tata sosai kusansa ta zauna ta rungumushi jikinta tana lallashinsa ta kalli hussaini tace" lokacin da kuke garin nan ina kukaga zainab na zuwa su waye kawayanta...? Hassan yace "yauwa Alhmdllh wlh sai yanzu na tuna Ashe fa ana muka girma kawayanta Manal da Jannat koda yaushe tare
suke basa rabuwa kuma ko dama idan tsiyarta ta motsa tana kwana biyu uku bata gida can take zuwa. ai da Sauri Sardauna ya janye jikinsa ah na Ammi ya Mike zuwat dan sai yanzu ya tuna Ashe zainab haihuwar jiddah ce tasan garin ciki da bai.ya rike hassan. "muje gidan pls muje na dawo da ita gareni tun kafin Abu Rahman ya farka daga baccinsa tabbas zai baza hotonta yana nemanta ak'asar wlh ba lalai bane musamu barin k'asar saboda inada tabbacin har Airport sai yakai hotonanku ah hanaku barin k'asar hakan yana nufin Abuna zata fada tashin hankali tare d'aku dan nasan bazai barku ba. Niko bazan iya jure rashinta ba. Ammi ta dauki waya ta kira Hamraz bugo daya ya daga da sallama Ammi tace"Hamraz akwai babban tashin hankali zainab bata gida gashi ja'irar yarinyace zata iya barin Jiddah mu nemeta mu rasa kasan ko idan Abu ya farka wlh kashinmu ya bushe don Allah kazo zamu nemanta gidan kawayanta ko ma dace.dagacan yace"Subahanallahi to ganinan yanzu. Kiran ta kashe ta kalli Sardauna ta kamo hannunsa ya zauna. "yi hakuri muma acikin damuwa muke idan Abu ya tashi bamu bazamu bar k'asar ba. insha Allah batayi nisa ba kansa ya dora kafadarta yace"na amshi kaddara duk yada tazo Allah ya tsaremun zainaba ta aduk inda take insha Allahu ayau
More Hausa novels
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Zazzafan Rabo Part One Complete Hausa Novel
By Aisha Umar Indabawa
Ni Da Yaya Sadiq Book 1 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Dafin Harshe Book One Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.