Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
ta danna ta Kara akunnata da sallama. murmushi ya Saki ya amshi sallama" my Neesher ya kk ya babyna...? daga can ta Saki murmushi tace" my Dr muna lfy sai rashinka wlh Dr wani mugun mafarki nayi amma ba komai nayi Addu'a. Sardauna yace "matar Dr namefa ai dai ba akan cikina dake bane ko...? " wayyo sweetheart bari kadawo zan fada maka yaushe zakazo" gobe insha Allahu ki daure kizo tarbar mijinki nayi missing dinki kinji mamar babyna..?" Zanzo mijina I love u my Dr. murmushi yayi ya sakar mata kiss ta wayar sukaci gaba da hira. jikin zee baby ko ina b'ari yakeyi wani irin mahaukacin kishine ya rufeta nan take zazzabin ya dawo mata yada taga Sardauna yanama Nisha tasan ita kadaice azuciyarsa kukanta ta danne tayi Addu'a ta shafa ta kwanta saman
Dardumar tana rawar sanyi amma batayi kukaba batada hujjar yin hakan. Sardauna sun jima suna hira da Nisha kafin suyi sallama ya dago yaga zee kwance tana rawar sanyi da Sauri ya zabura ya sabko ya nufo gunta yana zuwa ya dauketa yaji jikinta zafi rau saman kujera ya nufa da ita ya zauna yana rungume da ita idanuna na lumshe dan nayi alkawalin bazanyi kuka ba kuma bazan Nuna kishiba magana ma bazan masaba zan hakura na jure har muje gida na fadawa mahbeer duk irin iskancin da yayimun"my zainab bude idanuki kici abunci kisha magani ban musaba na bude ya bani tea nasha
yaci gaba da bani abunci abaki na amsa ko kallonsa banba har ya gama bani yaban magani nasha duk ina jikinsa ya Mike ya ciremun kayana ya barni sai pant da bra ya kwantar dani shima ya kwanta ya kashe wutar dakin ya daukeni ya Dora kirjinsa ya rufemu da bargo yana shafar bayana ahankali yana dannamun jikina ko motsi banyi ba nazame masa kamar gumki birkitoni yayi ya mannani jikinsa ya matseni sosai ya tallabo kaina yana huramun iskar bakinsa" my bugun numfashina zainabata my Abulena menene. shiru banyi maganaba" sweet baby kimun magana meyasa kika mareni saboda zafin kishinki zainab kina masifar sona sona yamiki mugun kamu meyasa kikaso shiga duniya saboda na kusanceki zainab ina mugu mugun sonki ina kaunarki wlh da kekikemun son da nake miki wlh yanzu da kinbar duniyar dan bazaki iya jure abun da na jureba. idan munje gida duk abinda kikaji kika gani kiyi tawakali ki amshi kaddara. Wani mugun haushinsa ya kamani amma bance komaiba na nutsa kaina kirjinshi ina fitar da wani irin numfashi tamkar numfashina zai tsaya
Sardauna jin yada zee numfashinta yake sama da k'asa yasa ya dagota "zainab wai meyasa kikemun haka yanzu don girman Allah meye na miki na Bacin rai kalli yanda numfashinki yake neman daukewa. yana rufe bakinsa zainab ta sume masa cak numfashinta ya dauke akidime ya zauna tana rungume jikinsa ya kwantar da ita ya sabko ya lalubi makunin wutar dakin ya kunna ya dauki robar ruwa ya kurbi kadan ya hauro gadon ya dauketa ya rungume ya tallabo kanta ya Dora bakinsa ahancinta ya fesa mata ruwan ahancinta da karfi ajiyar zuciya ta sabke da karfi numfashi na fita da Sauri amma idanunta alumshe hamdalah yayi ya kwantar da ita ajikinsa ya rungumeta gam yaja bargo ya rufesu yana tofa mata Addu'a yana shafa bayanta da gashinta ya tallabo kanta ya Dora bakinsa anata yana Kara busa mata numfashinsa tana Shaka sosai dan idanunta biyu tayi alkawalin karyatashine zata Nuna masa bata sonsa bata kishinsa tun tanajin yada yake hura mata numfashinsa tana shakar kamshin bakinsa har bacci ya dauketa shima ahaka bacci ya daukesa bakinsu cikin juna bacci suke sosai manne da juna da sun dan motse cikin bacci sai sufara tsotsar bakin junansu suna tande yawun junansu suna manne kamar zasu koma cikin junansu. Asubah ta gari.
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
*Washe gari* a *Nigeria* da misalin karfe hudu na yamma Nisha tana zaune. a parlonta tun jiya acikin farin ciki take irin yada Sardauna ya nuna itace azuciyarsa😂niko nace Nisha bakida wayo har kin manta abunda kika ga Sardauna yayima zee Rabia ta kira sai gata" hajiya gani. " Rabia kawomun kaza ai inada Sauran ta rana. Ko? " eh bari na kawo miki. ta koma kitchen sallamar matar nan taji akanta atsaye atsorace Nisha ta kalleta ta Mike tsaye" Ma'alumah ta ina kika shigo zama tayi tana dariya. "Aisha Allah ya shiryeki ina knocking fa kikace nashigo abude kina cewa Rabia ta kawo miki kaza. murmushi Nisha tayi tace" wlh na shafa ya gida. " lfy lau Aisha yau mijinki ke tasoyawa su shigo kano gobe karfe shabiyu ya maganar mu ta jiya ko kin fasa ramuwar.? " wlh ma'alumah ban fasaba ai nafara dorasa ahanya nace nayi mugun mafarki
Bakiga yada ya rudeba. Rabia ta kawo mata kazar a plate ta gaishe da ma'alumah ta juya Nisha ta faracin naman" ma'aluma bismillah. murmushi tayi ta dauka tanaci tace" yauwa ai naji dadin yada kika masa yanzu amshi wannan. Nisha ta amsa tace" na meye...? " ki zuba alemo gobe da safe kisha kafin kutafi Kano suna sabka ki fara tarbar Zainab ki rungumeta kina kukan kissa kinsan shegen kishine da ita zataji haushin tabatan da kikayi zatayi yunkurin gucewa sai
ki fadi da gangan wlh daide lokacin cikinki zai zube kuma Sardauna zai Dora laifin kantane yaga kamar da gangan tamiki to turba ta biyu zan doraki ne bayan munyi nasara zubar da cikinki. Dariya Nisha tayi "ai indai zai
saketa na yarda cikin ya zube nasan zan samu wani nan kusa dariya sukayi suka tafa sukaci gaba da hirasu suna shewa. can gida kuwa Daddy bayan sallah isha yana zaune ghaisha tace" Abban Sardauna goben harni zamu tarbo su momy? murmushi yayi" khadijah ai zama zakuyi nida tuwusai zamu da saminu da nuhu da hafeeza sai Aisha. ihu hafeeza tayi ta Mike da gudu taje ta fada jikin daddy. " thanks my daddy zan gano su hassan da hussaini. Dariya ummi Raiyan tayi minata tace" wato abun yar wariyace ko. " kudai yi hakuri Najib yace" daddy Nima su Ahmed da bandar zanbi suma suna zuwa" to Allah ya kaimu goben Ashe Kano tanada baki gobe.dariya sukayi hafeeza ta dagashi ta nufi daki ta kira, Ahmed taji da gaskene suna zuwa Kano.
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
*Saudi Arabia* tun bayan da sukayo breakfast Wanda daket Sardauna yashawo kanta ta yarda taci ya mata wanka ya bata magani Tasha wlh kallonsa batayi ba duk abunan da yake mata duk yabi ya tada hankalinsa ta fada masa abinda ya mata shiru tai masa Dole yayi banza shima da ita ya rungumeta ya rufesu da bargo ya matseta gam jikinsa. Tayi kamar tayi bacci 😆zee baby kenan Sardauna na bacci ta janye jikinta ta saka kayanta ta gudu part dinsu Ammi suma duk baccin suke jikin Ammi ta shige ta rungumeta tana kuka Mara sauti har bacci ya kwasheta ahaka dan jikinta akwai zafi duk Tasha magani ga yanda zuciyarta take harbawa da karfin gaske.
Haka suka wuni tunkur har dare zee taki yarda Sardauna ya ganta babu yadan baiba Ammi tace"ya rabu da ita ai Dole zasu zauna acikin jirgi tare. wajan su jannat da manal tun yamma sukazo suna tare da zee bedroom suna hirasu amma zee koda wasa bata fada musu abinda Sardauna ya mataba Sardauna dan yaba zee haushi ya kira Jannat suna hira aikuwa taji haushin dan tana jiyo dariyarsu toilet ta shige taci kukanta dan kal manal ta gani ta fito ta shiga sha'aninta tanaji ya amshi number Jannat yace zai mata wata kyauta ta musamman su hussaini ma dariya sukeyi suna tsokanarsa wai ko ta uku zaiyi da kawar. zee. Hamraz karfe goma na dare ya dawo suka shirin tafiya. karfe shadaya suna Airport harda su manal zee tana rungume dasu suna kukan rabuwa barinma Jannat da taji son Sardauna yamata dirar mikiya dan Sam batasan mijin zee bane cikin kuka Jannat tace" habibty inason yayaki.zee tayi tsayar da kukanta tayi murmushi tace gashi can ki fada masa ko kibari idan ya kiraki ki fada masa maybe ma shima sonki yakeyi tunda ya amshi numberki. cikin farin ciki Jannat ta rungume zee takai kallonta gefen su Sardauna karaf idanunsu ya sark'e da juna murmushi ya sakar mata zee tayi saurin kauda kanta dan tana lure dasu. zuciyarta na bugawa da karfin gaske
zata fadi jannat ta riketa suka zauna Ammi tace"yau bakijin jikinki zainaba kanta ta boye jikin Ammi tana fitar da numfashi da Sauri Sauri hawaye ya wanke mata fuska robar ruwa kusan ammi ta dauka ta bata tana sha sosai Tasha ta cire bakinta Sardauna na lure dasu hankalinsa duk atashe ya dai daurene. Manal tace"wlh kamar nabiku k'asarku jannat tace "wlh. nidai sai naje kwananan insha Allahu.inason Sardauna Zee idanunta ta rumtse tanajin maganar Jannat tamkar an soke mata kibiya aeuciya tun tana jinsu har bacci ya dauketa. can ko gidan Abu Rahman karfe shabiyu Allah ya bashi ikon farkawa daga baccin da yakeyi ya tashi ya fito yana addu'a dan tunaninsa bai bawani jimaba amma sai me yana fitowa yaga abinda yadaga masa hankali komai na gidan afashe Kiran Ammi ya shiga yi da Hassan da zainaba amma ba kowa da gida ya nufi gun dukiyarsa bakomai wayam ya duba wayoyinsa babu laptop babu komai babu da gudu yana ihu ya nufo harabar gida yana cewa"ayau sai nakasheki zainaba shegiya tsinaniya megadi kaima kasheka zanyi yana zuwa kan megadi
More Hausa novels
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Zazzafan Rabo Part One Complete Hausa Novel
By Aisha Umar Indabawa
Ni Da Yaya Sadiq Book 1 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Dafin Harshe Book One Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.