Soyayyanovels
Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
By Real Ladingo
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel

Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel

Author: Real Ladingo
Chapter 65 of 130
About 7 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,685 words Chapter 2 1,656 words Chapter 3 1,426 words Chapter 4 1,678 words Chapter 5 1,658 words Chapter 6 1,660 words Chapter 7 1,540 words Chapter 8 1,682 words Chapter 9 1,488 words Chapter 10 1,684 words Chapter 11 1,352 words Chapter 12 1,481 words Chapter 13 1,490 words Chapter 14 1,658 words Chapter 15 1,664 words Chapter 16 1,361 words Chapter 17 1,446 words Chapter 18 1,594 words Chapter 19 1,440 words Chapter 20 1,595 words Chapter 21 862 words Chapter 22 1,587 words Chapter 23 936 words Chapter 24 1,007 words Chapter 25 1,624 words Chapter 26 548 words Chapter 27 1,952 words Chapter 28 1,599 words Chapter 29 1,281 words Chapter 30 1,465 words Chapter 31 1,117 words Chapter 32 1,166 words Chapter 33 1,496 words Chapter 34 1,495 words Chapter 35 1,191 words Chapter 36 1,505 words Chapter 37 1,475 words Chapter 38 1,632 words Chapter 39 970 words Chapter 40 1,565 words Chapter 41 1,516 words Chapter 42 1,101 words Chapter 43 1,209 words Chapter 44 1,672 words Chapter 45 1,520 words Chapter 46 1,612 words Chapter 47 1,543 words Chapter 48 1,654 words Chapter 49 1,192 words Chapter 50 1,699 words Chapter 51 1,476 words Chapter 52 1,648 words Chapter 53 1,617 words Chapter 54 1,636 words Chapter 55 1,432 words Chapter 56 1,581 words Chapter 57 1,631 words Chapter 58 1,206 words Chapter 59 1,393 words Chapter 60 1,279 words Chapter 61 1,241 words Chapter 62 1,639 words Chapter 63 1,506 words Chapter 64 1,619 words Chapter 65 Reading now Chapter 66 1,475 words Chapter 67 1,600 words Chapter 68 1,589 words Chapter 69 1,675 words Chapter 70 1,603 words Chapter 71 1,692 words Chapter 72 1,515 words Chapter 73 1,429 words Chapter 74 1,552 words Chapter 75 1,635 words Chapter 76 1,554 words Chapter 77 1,590 words Chapter 78 1,500 words Chapter 79 1,567 words Chapter 80 1,518 words Chapter 81 1,656 words Chapter 82 1,634 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,643 words Chapter 85 1,435 words Chapter 86 1,628 words Chapter 87 1,694 words Chapter 88 1,601 words Chapter 89 1,576 words Chapter 90 1,659 words Chapter 91 1,655 words Chapter 92 1,536 words Chapter 93 1,559 words Chapter 94 1,457 words Chapter 95 1,655 words Chapter 96 1,677 words Chapter 97 1,557 words Chapter 98 1,692 words Chapter 99 1,558 words Chapter 100 1,525 words Chapter 101 1,533 words Chapter 102 1,651 words Chapter 103 1,695 words Chapter 104 1,597 words Chapter 105 1,580 words Chapter 106 1,627 words Chapter 107 1,681 words Chapter 108 1,700 words Chapter 109 1,636 words Chapter 110 1,621 words Chapter 111 1,471 words Chapter 112 1,637 words Chapter 113 1,685 words Chapter 114 1,674 words Chapter 115 1,638 words Chapter 116 1,629 words Chapter 117 1,674 words Chapter 118 1,513 words Chapter 119 1,674 words Chapter 120 1,653 words Chapter 121 1,623 words Chapter 122 1,605 words Chapter 123 1,584 words Chapter 124 1,634 words Chapter 125 1,675 words Chapter 126 1,537 words Chapter 127 1,639 words Chapter 128 1,693 words Chapter 129 1,496 words Chapter 130 1,209 words

Karfe goma sha daya zee ta farka daga bacci ta Mike ta shiga bathroom tayi. wanka ta fito ta cacada kwalliya tasaka Riga da siket na less baki mai ratsin fari ta murza daurin dankwali tafesa turare ta bude kofar ta fito parlo "wow wannan hadaddan parlon nawane da gudu ta isa tana dariya ta fada saman kujera mik'ewa tayi taje ta kunna Tv cikinta ya murda yunwa aikuwa ta nufi d'akin mahabeer ta murda ta shiga yana cikin shiri kusansa ta tsaya" my heart yunwa nakeji baki ya tab'e " ke baki iya gaisuwa bane? " baki ta turo" to ina kwana " banaso ai roka nayi kije kan dining an kawo abunci kallonsa nayi sama da k'asa cike da mamaki yada yake shan kamshi bai wani damu daniba ban sake magana ba na fice adakin na nufi kan dining na hada tea inasha yazo ya zauna ya hadawa kansa tea ko kallo bai isheniba naci farfesun kayan ciki na dawo parlo nayi zaune Kenan naji knocking naje na bude su hafeeza ne da haulat na rumgumesu ina dariya muka dawo parlo hafeeza tace" wow sister wlh kinyi kyau fah mahabeer ya ISO suka gaishesa ya amsa ya fice warsa hafeeza tace" ki rakashi mana zee tace" kuji yarinya da sa ido anki baza arakaba dariya sukayi zee ta saki jikinta suna hirasu ta duniya ko aka bata damuba dan tunda taji muryar Sardauna take cikin farin ciki da annashuwa

gidan Sardauna suna cikin bacci misalin karfe goma Kiran waya ya tasheshi idanusa ya bude ahankali ya sabkesu kan Nisha na manne dashi tana bacci hannu ya zaro ya janyo wayar yaga ghaisha ce picking yay ya kara akunnesa" hello momyna good morning dariya tayi daga can" morning Autana murmushi ya saki yana shafa kan Nisha" momyna nayi kewarki sosai"oh Sardauna tashi ka bude kofar parlo ga kayan breakfast nan so uku ana zuwa angaji da bugawa baku budeba asama kuke ko? " momyna muna k'asa bari yanzu na fito dariya tayi ta tsinke Kiran murmushi yasaki ya ajiye wayar ya dago da Nisha " oh Nisha amotsa mana idanu ta bude ta kallesa da sauri ta rufe idanunta ta boye kanta kirjinsa murmushi ya saki ya janyeta daga jikinsa, ya sabko " to bara nazo nayi miki wanka da kaina sai naga iya kunya ai da, sauri ta Mike ta sabko ta shige bathroom da gudu ta rufe kai ya girgiza ya fice daga dakin yana fitowa ya nufi hanyar parlo ya murza key ya bude Najib ne da kulolin abunci cikin wani katon gwando hanya ya bashi" shigo shigowa yayi direct kan hadaddan dining table d'insu ya nufa ya jera Sardauna na kallonsa yana gamawa yace" bro ina kwana hararasa yayi " banaso dariya Najib yayi " to nide na tafi binsa yayi suka tafi ya rufo kofar yana shiga bedroom yaga wayam Nisha ta tsere dakinta, kai ya girgiza ya shiga bathroom ya watso ruwa ya fito daure da towel ya. goge jikinsa ya murza mai ya gyara gashin kansa Nisha ce ta shigo da sallama ta hade cikin shadda gizna ruwan toka dinkin doguwar Riga tayi kyau ganin Sardauna haka ya tsoratata da Sauri tayi baya dariya ta bashi ya kirata"Nisha zo mana ina zaki matsoraciya kece dai zaki daukeni ki gama kwana kwanarki bata sauraresa ba ta gudu parlo ta zauna saman lumtsuma lumtsuman kujerun parlon sai raraba idanu take dan mugun tsoron girman Sardauna take taya za'ace wannan garjejen katon ya hau samanta Sardauna dariya Nisha take bashi to ita nufita haka zasuyi ta zama kafada ya makale ya shirya cikin wani danyan boyel blue colour yayi masifar yin kyau mutika fitowa yayi

yana baza kamshi tana zaune aparlo gunta ya nufo kanta ak'as tace" Yayamu ina kwana ya jikin da fatan ka warke "Alhmdllh tashi muyi breakfast mik'ewa tayi suka nufi kan dining Neesha ce ta hada masu komai Sardauna tea ya sha yaci farfesun kadan Nisha ma bata wani abun kirkiba mik'ewa yayi yaje yasha magunguna ya fito lokacin Neesha na zaune "to zan leko gida nazo "to ka gaishemun dasu ghaisha da ummi "zasuji ko zakije kai ta girgiza dan tasan fada yayi murmushi yayi ya fice ta Mike ta kunna TV tana zaune sai ga su intisar haba tayi farin ciki sosai nan suka zube suna hira intisar tace" ya na ganki kamar ba'ayi komaiba" ke wlh bazan iyaba Nadiya tace"aikuwa da sauranki Tab intisar tace" wlh yau ki saki jiki kibasa hakkinsa yayamu abinso ga kowa kije kina manne manne aradu ya karo aure idanu Nisha ta zaro tuni kwalla ta cika mata ido " wannan ai ba magana bace yaushe zakice haka ai bashida ra'ayin mace biyu kuma ni inajin sonsa bazan iya zama da wataba yaya Faisal nawane dariya sukayi " to kibasa abunsa danme jiya da yacemiki idan kina bukata ki fada kikace bakiso ai dan ya gwada kine" to naji yau bazan bashi abunsa ba tunda ina hutun sallah yau da asubah na fara amma da na gama zan bashi abunsa bushewa sukayi da dariya suna bata shawarwari ta kulla da mijinta ai yanzu ba'a wasa da rike miji duk su basu aureba amma suna karanta litatafai yanda, zasu kula da mazajansu jikinta yayi sanyi ta kuma dauki nasiyarsu tace zata kula da yayanta insha Allah haka sukaci gaba da hirasu cikin farin ciki intisar tanaso tacema Neesha mahabeer takeso kuma bata cire ran samun saba amma tana shakka yada Neesha keson Zainab duk itama yar uwartace amma kishin son mahabeer ya rufe mata idanu bata kallon zee yar uwa burinta ta samu mahabeer dan tasan larabawa ba wani iya tatalin mijiba sukayi kuma lami garesu basu fiye dadiba niko nace Hamm intisar bakisan wacece zee baby ba

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Bangaran mahabeer lokacin da ya fito daga gidansa direct gidansu Aunty amarya ya nufa dan jiyake idan baiga khalisat ba zuciyarsa zata buga lokacin da yaje mutane yagani akofar gidan azaune basufi su biyarba parking yayi ya fito ya nufi gunsu ya gaishesu yana tambaya ko lfy wani mai suna dauda yace"Alhaji abun babu dadin fadi mariya ce tayi mutuwar wulakanci tana ihu tana haushin kare ga wasu tsutsotsi na fita ajikinta har ranta ya fita kowa kin zuwa suturata yayi wai bata shuka alheriba aduniya muma dan natane bakin mu biyar Dinan mune muka kaita makwancinta mahabeer abun ya girgizashi mutika yace" Allahu Akbar Allah ya jikinta da rahma yanzu ina khalisat" wlh bamu saniba yau kwana biyu da gudu tace ita bazata iya da wari ba ta gudu gun dangin mahaifinta kansa mahabeer ya dafe" Ya Allah yanzu ina zan sameta suna cikin magana sukaga khalisat ta sabko cikin adedeta sawu tana kuka tarame tayi baki abin tausayi gunta mahabeer ya nufa da kallo ta bishi" khalisat Ashe Aunty ta rasu Allah ya jikinta dan Allah zaki yarda ki aureni da sauri

ta kallesa"ni kuma? " eh ke idan kin amince ki ban amsa zan dawo idan zafin mutuwa ya sakeki dan ya barta ta shiga ciki tace" eh idan nasameka zan aura bani hanya na wuce cikin farin ciki ya matsa mata ta wuce ya nufi motarsa ya shiga yaja yana farin ciki tunda ya ganta hajiyarsa ke motsawa jiyake kamar ya fadamata atiti su dauda da kallo suka bishi har ya bacewa ganinsu khalisat na shiga ta zube gaban inna tana kuka "ai kinga irin rashin tarbiyar da kikaba yarki niko ta bani tata amma insha Allah ni bazan kasance hakaba yanzuma nasamu me sona idan iyayansa sun amunce zan auresa nayi rayuwa mai kyau da kallo suka bita da kallon mamaki inna kanta cike take da nadamar ruyawa da tayi abaya mahabeer daganan gidansu ya nufa a parlo ya isko su ghaisha da baki kusanta ya zauna yana gaishe da su minata da tuwusai ghaisha ta kallesa tana murmushi ta shafi kansa" mahabeer ina momyna ka baro mun ita murmushi yayi" tana gida ummi Raiyan taji dadin ganin mahabeer sai taga kamar zainab tagani shiko mahabeer abin aransa yanaso ya fadama ghaisha shifa yanzu khalisat yakeso zai aureta ya hadata da zee amma yayi shiru har su daidaita da khalisat shi yama Mance da mutuwar aunty amarya suna cikin hira Dr Sardauna ya shigo da sallama gun ummi Raiyan ya nufa ya zauna ya gaisheta kansa ta shafa tana murmushi "Faisal ina Aisha da fatan kun tashi lfy" Alhmdllh ummi dariya yan parlon suka musu ya Mike ya nufo gun ghaisha ya gaishe da bakin suna masa tsiya barin damarta ya zauna ya kwanto jikinta" mamana ina kwana dukansa tayi"ja'irin yaro yau kaban wahala kabar yar mutane da yunwa har goma dariya mahabeer yayi Sardauna ya dago da kansa" bro ina kwana" lfy ya kwanta murmushi ya saki baice komai ba ghaisha ta shafi kansa "Allah ya muku albarka ya shige muku gaba a alamuranku dariya sukayi suka amsa Amin suna rumgume da uwarsu kamar wasu jarirai ummi Raiyan saida taji hawaye yazo mata dama kewar zeey ta isheta haka sukaci GABA da hira ghaisha na musu nasiyar zama da mace sai hakuri tumba mahabeer saboda tasan yarinta na damun zee baby sai an hada da hkr

End of Chapter 65Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next