Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
yasa ta saka hannu ta dauki plate mai soyayen dankalin turawa da kwai da cinyar kaza asoye ta koma gun zamanta abayar jikinta tacire ta ajiye tayi zamanta da dogon wando da guntuwar rigarta gashinta ya sabka har gadon bayanta rabi ya rufe mata fuska anutse yakeci har ya gama hamdala yai ya Mike yaje toilet ya wanko bakinsa da hannusa danna wata yar na'ura yayi ba'afi muntuna biyar ba aka fara shigowa ganin Dr wata latijuwa ta fara shigowa acikin girmamawa zee baby ta gaisheta ita ya fara dubawa nabiyu ko namijine saurayi Wanda zuciyarsa dab take da bugawa sosai Dr Sardauna yai masa fada ya rubuta masa maguguna yace zai kwantar dashi har kwana biyu ta ukku ce da ta shigo wata zankadediyar budurwace asuma ke damunta Dr Sardauna na tsaka da dubata zee takeson mata rashin kunya babu gaira babu dalili ta fara zaginta ganin basu kulata ba ta iskosu tayi tsaye kansu fur ta hanashi yaba yarinyar kulawa saboda bayason surutu Dole ya dago ransa abace" ke matsa kiban guri jikinsa ta matso ta rumgumeshi ta fara kukan shagwaba " wlh Dr bazaka dubata ba danme zaka rika tabata nadamar kawota hospital yai amma da ya tuna zai kunsa mata bakin cikin da bazata iya mantashi ba wuyanta ya damko ya kifa mata Mari ya hankadata wani daki ya murza key yaci gaba da aikinsa saida ya duba mutum sama da ashirin tun tana ihu da buga kofa har tagaji ta bari sai karfe sha biyu ya samu ya huta su Daddy sunzo amma yace ya mata magani Allura bacci ta awa biyar yamata bazasu samu ganintaba Mahabeer sawunsa biyu Dr Sardauna yace sai yamma zata farka Dole ya hakura ya koma gun aiki, Dr Sardauna ya shiga duba marasa lafiyar dasuke kwance a asibitin duk da yasa an dubasu amma yabi su daya bayan daya yana dubasu cikin fara'a yake duba kowa yana kara musu kwarin gwiwa hakan nama marasa lafiyan dadi ba kadan ba
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
karfe daya da rabi ya fito daga masallaci yin sallah Office ya bude ya shiga ya dauki abayarta ya bude ya wurga mata " maza tashi kiyi sallah kafin watan cin ubanki ya kama yanaji ta rama k'asa k'asa yana ciza bakinsa ya jinjina kai fitowa tayi taje tayi Alwalla ta shimfida dadduma sai Allah ya isa take masa" kuma yanzu zanyi Addu' Allah ya hadaka da cutar dan kanoma ka kasa zaune ka kasa tsaye ko kallo bata isheshiba tsadaddan agogon hannusa ya kalla saura minti ashirin yashiga tiyata wacce itace ta hanashi cin uwar zee baby soyake sai ya fito bayan mintina goma akayi knocking din kofar ya bada izinin shigowa Dr Ruma ce ta shigo da sallama sai wani lankwasa take amma cikin taitayinta dan tasan halin Dr Sardauna " doctor mun gama shiryama komai lokaci yayi Dr Nabil yace na kiraka ka fara fuskarsa ahad'e yace " Ok bai sake maganaba ta juya zata tafi " kallon banza zee tama Ruma " ke bazawara wlh kunji dai kunya ke yanzu haka kike yawon tsakiyar maza idan ba salon iskanciba da tallaar jiki kalli wani breast dinki duk ya saki sai kace mai shayarwa koda yake bazawarce ai dukda hausarta bawai ras take yintaba amma Ruma ta fahimta idanu Dr Sardauna ya zaro kallonta ruma tayi dan batason raini " ke yarinya shiga taitaiyinki kowama dan iskane zan tataka ki anan " kut wa zaki taka ki taka uwarki dai shegiya mai kirar agwagwa gadan gadan Ruma ta nufo zee baby wacce take zaune ko motsi ba taiba dan ta shiryawa ruma yada zata kadata Dr Sardauna yace" Ruma jeki wlh batada hankaline maganine aka kawota batasan me take fadiba jin yada Dr yakirata anutse abunda bai taba mata ta tsaya ta juyo tana kallonsa fuskarta dauke da murmushi sai wani fari take da idanu" ok Dr babu damuwa tunda batada hankali amma da na nuna mata iyakarta ai bata rufe bakiba zee baby ta watsa mata mari ta makaleta sai yakushinta take da cizo duk inda tabi ta kare zee ta tare karfi Ruma tasa saboda girmansu ba dayaba zee siririya ce Ruma akoshe take babbar macace tana dab da murkusheta zata danne zee aikuwa tayi sauri ta janyo kafar Ruma sai ji kake dim Ruma ta fadi kasa wanwar samanta zee ta Haye idanu Dr Sardauna ya zaro waje ya kauda kansa dan Ruma kusan tsirara take siket din ya tatare mik'ewa yayi cikin sauri dan sai cizonta take itako sai jibgar zee baby takeyi babuji babu gani yazo ya dauke zee baby cak daga saman ruma sai wutsul wutsul take tana dukansa rumgumeta yayi gam ya matseta ya ruko hannnuta da take dukansa yana murzawa ahankali yana buga bayanta sai ashar take durawa Ruma ganshinta ya tatara mata da ya rufe mata fuska ya kalleta "wlh idan bakimun shiruba zaki sani tantiriya fitsarariya kawai. shiru tayi ta tura kanta kirjinsa tana gunguni ya kalli Ruma " dr yi hakuri jeki zanci ubanta dakyau wlh sai na rama miki ai na gayamiki mahukaciya ce mik'ewa tayi cike da kunya ta fice amma azahiri dukan da tama zee yafi wanda zee baby ta mata ita dauriya tayi
More Hausa novels
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Zazzafan Rabo Part One Complete Hausa Novel
By Aisha Umar Indabawa
Ni Da Yaya Sadiq Book 1 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Dafin Harshe Book One Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.