Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
******************************
Yau kwana zee baby uku asaudiya har yau bata farkaba zuwa yanzu Abu Rahman ya fara tsorata da lamarin ga yan uwanta sun damu sosai ya rasa meke masa dadi. da misalin karfe biyar na yamma Hassan da hussaini zaune bakin gadon zee baby Amina gefe Abu Rahman na zaune kusanta. cikin hukuncin Allah na'urorin jikinta suka dauki ruri ta fara motsi sai ga likitoci sun shigo suna dubata idanunta ta bude ahankali tana kallon dakin da jama'ar gabanta yayi mugun faduwa ta zazaro idanuwa ganin wa inda suke tsaye cikin tashin hankali da firgici ta bude baki zatayi magana taji yana cewa" Alhmdllh ta farka sauran lfy ta dawo haiyacinta idanu ta rumtse dan batason ganinsa arayuwarta sai yanzu ta tuno cikin jirgi yana rike da ita Kenan idan hakane bata Nigeria tana saudiya tunda ga likitocin larabawa tsaye kanta gabanta ya fadi ta shiga tunanin mijinta mahbeer tana Addu'ar Allah yasa yana lafiya bayan sun gama dubata doctor yace" Alhmdllh ta dawo haiyacinta ayanzu batada matsala normal take. Abu Rahman yaji dadi sosai yaje ya rungume zee yana farin ciki yan uwanta ma haka idanu ta bude ta kallesu tana murmushi tace" gaskiya naji dadi yaushe mukazo da ummita nan.Abu yace mata"ke daya nakawo namiki magani itama tana zauwa. "ai babu damuwa ko bata zoba zanyi zamana daku. dadi sosai yaji har Amina da yan uwan zee baby sun zata gaske take. Saida suka kara kwana aka kara duba lafiyarta batada wata matsala washe gari aka salamesu suka tafi gida. suna zuwa zee tasaki jikinta kamar batada damuwa.
saida tasaka yan uwanta ajiki zuwa dare ta keb'e dasu tamusu huduba ta zugesu ta hadasu da Abu Rahman tace acikin jirgi taji yana zancan zai kashemu mu uku kuma daman boye musu tayi ya kashe ummi ne ya satota sukazo ai kuwa suka fara kuka tace ba kuka zasuyi ba su dubo takardun dukiyarsu kakaf zatayi musu dubara su koma, nagerai idanko basuso ai zai kashesu ne. sun yarda sun hau kai sun zauna shiko Abu Rahman baisan meke faruwa ba da misalin karfe goma Na dare zee tana rungume jikin Amina suna zaune a parlo Abu bayanan su Hassan suna can suna neman dukiyarsu zee ta kalli Amina ta fashe da kuka tace"yau sauran kwana uku Fahad ya kasheki mu jibi zai kashelu
Allah sarki ummina ana k'asa abunne arikice ta dagota "kina nufin ya kashemun diyar tamu daya da muka haifa.? eh agabana ya mata yanka rago wayyo ummina ganinin zuwa gareki nida yan uwana da kakata bamuda hanyar kubuta babu Wanda zai cecemu duk saudiya Dole mu mutu jibi kuka Amina takeyi sosai ta rungume zee" kibar cewa haka Dole zamu rama abunda ya mana kuma nasan yada zamu gudu bazamu zauna k'asar bama mukoma k'sar mahaifinki zan rikeku amana tunda ke kinada mijinki gashi yace zai kuma d'aura miki aure cikin satinan. da sauri zee tace da gaske zaimu wani aure ai dayaci durin uwarsa dan iskan tsoho najadu kawai. idanu Amina ta zaro gira zee ta d'aga mata "zaki bimu Nageria muzauna.? " zanje wlh tunda duk yanda na zauna dashi yakeson kasheni bayan ya kashemun diyata daya ina Hassan da hussaini suzo nasan inda dukiyarku take. fitowa sukayi dan sun nema sun rasa.
"gamu. mik'ewa tayi Zee tace "kakata bani wayarki na kira mijina. wayar ta bata taja hannunsu suka fita. zama na gyara na saka number mahbeer dan inada ita akaina nakira har sau uku amma bata shiga gabana naji ya tsananta faduwa. ta Sardauna na saka itama akwai akaina. tanata ringing bai d'agaba sai da na kira sau uku tana dabda tsinkewa ya daga. cikin sansanyar muryasa mai amon dadi yayi sallama. bansa lokacin da na lumshe idanuwana ba nayi kwance. muryashi na tsinto yana cewa" idan baza'ayi magana ba zan kashe. kuka naji ya kufcemun bansan daliliba cikin shashekar kuka nace"My Sardauna Nice kanwarka zainab ina ta Kiran mahbeer bana samunsa yana lfy ko.? lokacin Sardauna yana akwance saman makeken gadonsa cikin bedroom baisan lokacin da ya zamo daga kan kujera ba jikinsa na kerrrma
yace"my sweet zee babyna kina ina ne.?" yayana ina saudiya dan Allah kazo ka fitar damu nida yan uwana kaji.?" Alhmdllh yi shiru bari kukan banason kukanki wlh ganinan zuwa ki kasance cikin shiri. ashagwab'e nace My Sardauna nah.?" Na'am my zeener menene.?" kazo inason ganinka Sardauna nah na fada cikin kukan shagwab'a" oh my god don girman Allah matata bari tadamun hankali zanzo cikin satinan ki kwantar da hankalinki yi shiru sai nazo kibani labarin wani dan iskane yasa ceki ya kaimun abar kaunata saudiya ciwon zuciya yakusa kasheni. " My Sardauna nah wlh Abu Rahman ne." OK kwanta maza ki huta zan kiraki anjima yanzu gida zani kiss ya sakar mun ta wayar ya tsinke kiran.
idanuna na lumshe gabobin jikina duk sun saki Sardauna nake gani.
a idanuna tsikar jikina sai yamm takeyi ina mimmik'ewa wani irin yanayi nakeji tashi nayi nabi bayansu akofar wani d'aki muka hadu Amina ta kwaso takardun dukiyarmu har na ummi muka dawo parlon muka zauna ta tatara kan takardun ta bani naje na boye na dawo wayar ta amsa tayi Kiran wata number bugo daya ya daga. tayi sallama ta masa bayanin komai da irin hanyar da takeso ya mata zasu bar k'asar amma kowa yanada passport d'insa ya tambaya su nawane zee ta amsa ta masa bayani har Sardauna Kenan su biyar yace to abashi kwana hudu gobe zaizo ya amshi kudadan da passport d'insu. sosai sukayi farin ciki Abu Rahman sai wajan karfe daya yadawo zee ta taresa cikin murna yanajin dadin sauyawarta sosai nan suka baje ana hira yake basu labarin karshan wata zashi dauko ummi Raiyan zee ta musu nuni karya yakeyi ya kasheta sun kuma gamsu da maganarta amma basu nuna meba sukaci GABA da hirasu da ciye ciye sai bayan da sukayi sallah Asubah kowa ya kwanta zee wayar suka kashe dan kar Sardauna ya kira Abu ya gani su shiga bala'i shiyasa ta kasheta.
*Nigeria* kowa Sardauna cikin farin ciki mara musaltuwa ya warci key d'in motarsa ya fito Nisha lokacin na parlo tana kallon TV dan batajin bacci taji Sardauna ya dauketa yayi sama da ita yana juyi yana dariya itama dariya takeyi ta makaleshi" my Dr cikina zai kulle babynka na motsi fah. direta tayi yana murmushi Nisha cike da mamaki tace"my Dr wai meye kasamu haka na dadi Allah yasa my dear aka samu.? " itace aka samu amma tana saudiya yanzu ta kira Oya muje gida yanzu ko kin zauna na dawo.? cikin farin ciki ta rungumeshi tana kukan dadi "Alhmdllh Allah Abin godiya masoyiyyata ta dawo lfy wayyo. sakinsa tayi taje ta shirya ta fito suka tafi. cikin farin ciki yake driving Nisha na kwance jikinsa har suka isa gidan. a parlo suka iskosu basu kwanta ba da gudu yayi kan daddy yana ihu gabaki dayansu idanu duka tsura masa jikin dadi ya fada yana dariya" Alnishirunku iyayena. Allah ya baiyana zainab yanzu ta kirani tana saudiya. cike da mamaki sukace" waye ya kaita saudiya.?" wlh tace Kakanta ne kuma abun farin cikin ma ta samu lfy ta dawo haiyacinta ras. tsaye ummi Raiyan tayi ta fashe da kuka tace"shikenan itama ya rabani da ita.Sardauna ya Mike ya koma gunta yana lallashinta ya mata bayanin da zee ta masa ajiyar zuciya ta sabke ta zube k'asa, ta kalli gabas tayi Sujada tana beka godiyarta ga Allah ghaisha taje ta ta tayata daddy ya shiga Kiran yan uwa yana musu albishir cikin farin ciki Nisha itama sosai take farin ciki dan tasan zee tana
zauwa idan taji labarin komai bazata zauna da Sardauna ba. Daddy yace"Dr gobe ka fara shinrin tafiya ayi maza arabosu da k'asar banaso wani abu yasamu momy. ummi tayi dariya tace"wlh baby daide take dashi zata san duk yanda tayi suka kubuta daga hannunsa kafin zuwan Sardauna. murmushi daddy yayi yace"Rayyan yau kece harda dariya masha Allah su tuwusai ma dariya akeyi minata harda su rawa zatagata su Hassan da hussaini Nisha da hafeeza na mata dariya Najib jikinsa yayi sanyi dan yanzu ya gano mutumin nan da ya masa tambayoyi shine yasace zee gudun kar Sardauna ya hada masa jini da majina yayi shiru. sai karfe shabiyu Sardauna yama iyayansa sallama
Suka tafi gida.suna zuwa sukayi shirin bacci amma Sardauna saida ya raba dare yana sallah yana bika godiyarsa wajan ubangiji. sai karfe biyu ya Mike ya hauro gadon ya rungumo Nisha. ai fah wannan dare ta taba taji dan tunda ya fara cacakarta bai saurara mataba sai asubah taci kuka har tagaji. sai bayan da sukayi sallah ya rungumeta yana lallashinta har sukayi bacci. Nisha kam anbugu
**************************
Bayan kwana biyar
cikin ikon Allah Sardauna ya gama shirin tafiya Wanda a yaune ya daga k'asar ta saudiya Nisha tasha kuka a Airport daket ghaisha da ummi suka lallasheta suka dawo gida Sardauna kullum cikin waya suke da zainab tana fada masa komai har dukiyarsu sun kwashe an gama shirya musu tafiya shi suke jira kowa yayi waya da zee agida amma babu Wanda yayi kokarin fada mata mutuwar mahbeer kullum cikin waya take da ummi tana fada mata muguntar da zasuwa Abu Rahman ummin tayi ta kuka tace sudai barshi su taho karsu cutar dashi duniyace ta ishesa ko yaya yake mahaifintane shi din Dole zee suka barshi. dan har yanzu baisan sun yashe komaiba zasu bar k'asar ba. gashi Sardauna ya daga k'asar saudiyar domun kawosu sai muce Allah ya kaisa lfy Amin.
More Hausa novels
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Zazzafan Rabo Part One Complete Hausa Novel
By Aisha Umar Indabawa
Ni Da Yaya Sadiq Book 1 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Dafin Harshe Book One Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.