Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Sardauna yana fita ya shiga mota ya kama hanyar hospital. hankalinsa atashe Dan yana tausayin yaron da iyayansa yaron yakai matakin karshe ba lallai bane ya rayu dandai komai daga Allah ne. shine mai rayawa shine mai kashewa. yana zuwa yayi parking ya fito ya rufe motar yayi cikin asibitin direct room din da yaron yake ya nufa yana shiga yaga mahaifiyar yaron na rusar kuka da gudu ya isa yaron na bulbula aman jini Sardauna ya shiga bashi temakon gagawa amma ina shakuwa biyu yayi cak numfashinsa ya tsaya idanu Sardauna ya rumtse da karfi ya bude ya kalli nabeel mahaifin yaron yace" ya mutu ko? Sardauna yace" saide Allah ya Baku hakuri Ameer ya cika tayaya yaro karami ya kamu da ciwon zuciya kuma Baku dauki matakiba tun da wuri Nan take mahaifiyar yaron ta fadi asume mijinta ya dauketa ya shimfide kan gado Sardauna ya shiga bata temakon gagawa tana farkawa Sardauna ya musu gaisuwa ya fice Dan wani irin tausayi suke bashi ga mutuwar yaron ta tsaya masa arai Office d'insa yaje ya zauna ya kunna sigari yanasha Sam yau yarasa irin yanayin da yake ciki dadi ko akasin haka.mik'ewa yayi ya fito ya nufi harabar hospital d'in. bangaran zee baby bata tashi ba sai kusan karfe biyar na yamma ummi tayi ta tashinta taki tashi wanka tayi sallah la'asar ta saka Riga da siket na atamfa ta fesa turare ta daure gashinta da ribbon ta fito parlo ba kowa ummi da ghaisha sun tafi gidan daddah sai nanah da nawwara suna kallon Tv tashar MBC 3 Zee ta zauna saman kujera tace" nawwara ina"ummi Raiyan da ghaisha babyna yazo.?" Anty zainab suna gidan daddah. baki ta turo " ni bansan gidanba dariya suka mata. "Kai anty gashinan da kin fita mik'ewa tayi tsaye tace" to bari naje. ta nufi hanyar da taga kowa na shigowa ta bude ta fito ta fara tafiya kanta babu ko Dan kwali kuma ba'ayi katari ba ta hadu da kowa ma'aikatan gidan babu Wanda ya ganta wata yar karamr kofa ta hango can ta nufa dan naciki zai bude ya fita amma nawaje bazai budeba sai an bude masa ko yanada key da gudu tayi gun gun kofar lambu ta tsinkayo amma rashin sanin meye taki isa ita tsoroma gurin ya bata ta bude yar karamar kofar ta wuce kawai sai gata kofar gida motoci nata ficewa dariya tayi ganin motane nata wucewa tace" yanzu ina zanga ummi da ghaisha Anan jama'a sai kallon zukekiyar kyakyawar yar balarabiya sukeyi itako dariya take tana hirata ta nufo saman titin wata bakar mota ta tsaya gabanta ya janye glass d'in motar ya Saki murmushi idanu ta tsura masa tanaja da baya " zainab ina zaki zo muje na kaiki gun babynki yana kiranki jin yace haka ta, dawo jikin motar tana dariya" to muje can gurin magani yake ko yana ina.? " muje kigani. ya fadi yana murmushi ya bude mata motar ta shiga ya rufo yaja motar aguje yabar gurin..................✍🏻
*ZEE BABY*
*👉🏻48*
....kallon mutumin da yake kusanta zaune tayi taga yana kama da ummi Raiyan sosai gemunsa ta kama tana dariya.shikuma idanunsa Akan kofar katafareran gidan da zainab ta fito yar kofar da ta fito irin tasu ta larabawa ce. mamaki yakeyi dama Faisal din masu arzikine haka. zee ta dawo dashi daga tunanin da ya tafi Dan har sunyi nisa bai saniba yaji tana cewa "kaima D'an ummi Raiyan ne ko. kaima my babyna zai baka abunci abaki ni shine yake bani mahbeer mijina ya mutu amma har yanzu basu kaina naga mutuwar ba bare tabani mijina mahbeer mudawo ko zamu yanzu. ta kalli balaraban mai tuka motar tace" kai ka kamu gun mutuwa ta bamu mahbeer mijina sai mu bar mata wannan ta Nuna Fahad Abu Rahaman burki mutimun ya taka da karfi yana dariya Dan yasan abunda zainab ta fadi da Abu Rahman najin Hausa da tuni ya matsa kusanta "zainab ai bayajin Hausa kekuma yanzu bazaki gane Arabic ba sai kin dawo normal. da harshan larabci ya fadama Abu Rahman abinda zainab ta fadi idanu yazaro ya matsa gefe dariya tayi tace"meye kake matsawa muji to kaga babyna yanada kirki daddy yace shima mijinane fah kuma ni bansa ma inda zanga mijin ba. Abu Rahman yace"Turki metace ne.?duk abinda ta fadi ya zaiyane masa tun shigarta motar.gabaki daya tausayinta ya kamashi Sam bai taba tunanin abun haka tazama ba bai taba son zainaba ba kullum burinsa yaga karshanta Dan yasan itace kezuga
umminta ta bujire masa har tabaro k'asar haihuwarta amma tunda yaganta cikin wannan halin yaji ya fasa cutar da ita ya kalli Turk yace"abinda za'ayi yanzu muje muyi shirin tafiya nayi alkawalin kaita amata magani har
ta warke zan bawa mahaifiyarta farin ciki duk nasan yanzu sai sunshiga damuwa ina anfanin dukiyar da aka Tara babu temako gashi suna babban gidan an hada jin dadin duniya amma sun kasa fitar da ita k'asar waje Dan haka muje yanzu mu kama hanyar kano. "to shikenan Allah bata lfy shiyasa ai bayan nagama bincike na kiraka nasanar dakai komai kuma kaga ta yada nayi bincike na cikin sirri har muka gama babu Wanda yasanmu shima Najib din kaga bayan muntafi kano zai fadi ga yada akayi ko tsoro ya hanashi fadin gaskiya tunda kaga bazai taba tunanin daga gareka bane. "insha Allahu nagama cutar da yarinyata zan bata farin ciki sosai Allah yaba zainaba lafiya. "Amin zee baby da idanu take binsu da batasan me suke cewa ba sai dariya takeyi kai Abu Rahman ya girgiza cike da tausayinta yana mai nadamar abun da yama mahaifiyarta da mahaifinta tabbas yasan idan zainaba tasan shine yasa aka kashe mata mahaifinta kasheshi zatayi Dan yarinyar akwai bakar zuciya ahaka har suka isa masaukinsu hotel Turk ya shiga da motar ya yayi parking yana budewa zee ta fara kuka sai tabishi Abu Rahman ya riketa "tsaya yazo chocolate zai kawomiki. yo ita ba larabci ta saniba shiyasa bata ganeba dukansa ta fara harda cizo tana ihu
ya saketa Turk bai jimaba sai tashi da akwatinsu ya bude bayan mota ya nasa ya shiga"ah yadai kuka taso dawo gaba yi shiru. tashi tayi ta tsalaka ta zauna ah gaba gun Turk yaja motar yabar cikin hotel d'in zee ta kalleshi tana goge hawayenta. "gun babyna zaka kaini ko.? eh can zamu amma sai kun hau jirgin saman keda kakanki. dariya tayi ta juyo tana kallon Abu Rahman yacema Turk "amma ina zamu samu abaya ta suturta jikinta.? "wannan ba matsala bace muje kano tunda jirgin sai gobe ma zaizo wlh abun yayi mutikar bani mamaki da Al'ajabi yada kace insha Allahu yau tsakanin Raiyan da zainaba sai kaci nasara samun daya acikinsu gobe dasu zaka saudiya wlh ban yarda ba amma sai gashi cikin hukuncin Allah kasamu daya kamu naji dadin yada kacanza shawara. " ai nacema kafin nazo nasaka amun Addu'a Akan Allah yabani nasara akansu kuma Nima kwanana uku ina Addu'a nasan hakan araina jikina ne yabani zansamu daya daga cikinsu shiyasa tun shekaran jiya nacema muyi ta zurganiya har muyi masara. haka sukayi ta hira zee sai kallonsu takeyi sosai Turk yake sharara gudu na uban mamaki Ana kiran magarib lokacin sunyima katsina nisa sosai awani dan kauye suka tsaya sukayi sallah zee sai hiramin Abu Rahman ya bata ta nada akanta tayi sallah lokacin ta fara musu kuka tana kiran baby dinta daket Turk ya lallabata tayi shiru yaja motar suka dauki hanyar Kano.
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
can gidan kuwa su ghaisha da su minata basu tashi dawowa ba saida aka fara kiran sallah magarib suka dawo kowa shiga yayi sallah ummi tana shigowa d'akin taga babu zainab ta duba bathroom batana Alwalla tayi ta fito tayi sallah zatonta tana dakin hafeeza bayan tayi sallah taje taga ko tayi sallah taga wayam batanan parlo ta fito ba kowa su nawwara ghaisha ta jasu suyi sallah dakin ghaisha ta nufa akofa, suka hadu. " khadijah baby tana gunki.?" wlh batanan ina take. nawwara tace" momy ai mun turata gunku gidan daddah tunda yamma. idanu suka zaro hankalinsu atashe ghaisha ta wankawa nawwara Mari"Dan gidanku yaushe kika taba ganin anbarta ta fita ko hospital Sardauna idan zai kaita sai an rufe mata fuska duk Dan karta koyi fita waje. ummi da hankalinta yayi kololuwar tashi ta rike ghaisha" kiyi hakuri bari dukanta. ghaisha taja hannunta suka fita gidan daddah suka nufa. babu inda basu subaba lungu da Sako babu zee gabaki dayansu suka fito ghaisha ta kira dadday ta fada masa hankalinsa atashe yabaro masallacin ummi har ta fara kuka Sardauna daddy ya kira yana tambayarsa ko yana tare da momy ai basai lokacin da ya tsinke wayarba ya baro masallacin yazo ya shiga mota ya nufi gidan. lokacin da yazo kaf girman gidan babu inda ba'a nemi zee baby babu Sardauna hankalinsa atashe yace" yo duk kuna inane saboda Allah kuka barta ta fito ina anfani masu gadi da ma'aikatan gidan har zainab ta fita babu Wanda yaganta to wlh duk sai kunbar gidan kuma duk wani mai aiki
na gidanan wlh ya fita tun ban ilatakuba. Daddy ya rikeshi" haba Dr meye nasu aciki kaga mai aikinmu sabuwa ce ba wacce kasani bace tana kitchen batasan abunda ya faruba megadi yace wlh bata nan ta wuceba to me wanki ma bai ganta ba haka mai ba shifkoki ruwama bai gantaba su ghaisha suna gidan daddah. jikinsa ya janye ya nufi Swimming pool saida ya zagaye ko
ina suka biyoshi suna kara dubawa babu ita cikin ruwan ya fada yayi nema har yagaji babu zainab fitowa yayi hankalinsa atashe jikinsa sai rawa yakeyi ga ummi da ghaisha na kuka daddy na basu hakuri part d'insa yaje ya canza kaya ya fito ya shiga mota ya fizgeta ai tun kafin ya isu megadi ya bude masa, kofa ya fice aguje. Kai tsaye gidansu hayatu ya nufa gudu yake shararawa ikon Allah ne ya kaishi gidan akofar gidan yayi parking ya fito Kenan hayatu ya dawo daga masallaci aguje ya nufi gunsa ya harba masa Kafa saida ya fadi ya damkoshi ya rika wanka masa Mari kafin me ya hada masa jini da majina ya damki wuyansa ya wurgashi cikin mota yashiga ya fizgi motar
More Hausa novels
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Zazzafan Rabo Part One Complete Hausa Novel
By Aisha Umar Indabawa
Ni Da Yaya Sadiq Book 1 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Dafin Harshe Book One Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.