Soyayyanovels
Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
By Real Ladingo
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel

Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel

Author: Real Ladingo
Chapter 63 of 130
About 7 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,685 words Chapter 2 1,656 words Chapter 3 1,426 words Chapter 4 1,678 words Chapter 5 1,658 words Chapter 6 1,660 words Chapter 7 1,540 words Chapter 8 1,682 words Chapter 9 1,488 words Chapter 10 1,684 words Chapter 11 1,352 words Chapter 12 1,481 words Chapter 13 1,490 words Chapter 14 1,658 words Chapter 15 1,664 words Chapter 16 1,361 words Chapter 17 1,446 words Chapter 18 1,594 words Chapter 19 1,440 words Chapter 20 1,595 words Chapter 21 862 words Chapter 22 1,587 words Chapter 23 936 words Chapter 24 1,007 words Chapter 25 1,624 words Chapter 26 548 words Chapter 27 1,952 words Chapter 28 1,599 words Chapter 29 1,281 words Chapter 30 1,465 words Chapter 31 1,117 words Chapter 32 1,166 words Chapter 33 1,496 words Chapter 34 1,495 words Chapter 35 1,191 words Chapter 36 1,505 words Chapter 37 1,475 words Chapter 38 1,632 words Chapter 39 970 words Chapter 40 1,565 words Chapter 41 1,516 words Chapter 42 1,101 words Chapter 43 1,209 words Chapter 44 1,672 words Chapter 45 1,520 words Chapter 46 1,612 words Chapter 47 1,543 words Chapter 48 1,654 words Chapter 49 1,192 words Chapter 50 1,699 words Chapter 51 1,476 words Chapter 52 1,648 words Chapter 53 1,617 words Chapter 54 1,636 words Chapter 55 1,432 words Chapter 56 1,581 words Chapter 57 1,631 words Chapter 58 1,206 words Chapter 59 1,393 words Chapter 60 1,279 words Chapter 61 1,241 words Chapter 62 1,639 words Chapter 63 Reading now Chapter 64 1,619 words Chapter 65 1,517 words Chapter 66 1,475 words Chapter 67 1,600 words Chapter 68 1,589 words Chapter 69 1,675 words Chapter 70 1,603 words Chapter 71 1,692 words Chapter 72 1,515 words Chapter 73 1,429 words Chapter 74 1,552 words Chapter 75 1,635 words Chapter 76 1,554 words Chapter 77 1,590 words Chapter 78 1,500 words Chapter 79 1,567 words Chapter 80 1,518 words Chapter 81 1,656 words Chapter 82 1,634 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,643 words Chapter 85 1,435 words Chapter 86 1,628 words Chapter 87 1,694 words Chapter 88 1,601 words Chapter 89 1,576 words Chapter 90 1,659 words Chapter 91 1,655 words Chapter 92 1,536 words Chapter 93 1,559 words Chapter 94 1,457 words Chapter 95 1,655 words Chapter 96 1,677 words Chapter 97 1,557 words Chapter 98 1,692 words Chapter 99 1,558 words Chapter 100 1,525 words Chapter 101 1,533 words Chapter 102 1,651 words Chapter 103 1,695 words Chapter 104 1,597 words Chapter 105 1,580 words Chapter 106 1,627 words Chapter 107 1,681 words Chapter 108 1,700 words Chapter 109 1,636 words Chapter 110 1,621 words Chapter 111 1,471 words Chapter 112 1,637 words Chapter 113 1,685 words Chapter 114 1,674 words Chapter 115 1,638 words Chapter 116 1,629 words Chapter 117 1,674 words Chapter 118 1,513 words Chapter 119 1,674 words Chapter 120 1,653 words Chapter 121 1,623 words Chapter 122 1,605 words Chapter 123 1,584 words Chapter 124 1,634 words Chapter 125 1,675 words Chapter 126 1,537 words Chapter 127 1,639 words Chapter 128 1,693 words Chapter 129 1,496 words Chapter 130 1,209 words

yana dafe da saitin zuciyarsa yana tari tin karfinsa jini ke fita kadan kadan har tarin ya lafa ya Mike ya goge bakinsa da handkerchief ya saita nutsuwarsa ya nufo gun taron fuskarsa asake ya shiga hall din zee sai hira takema mahbeer yana dariya tana ganin Sardauna ya shigo gabanta ya fadi sai take ganin kamar bashida lfy zama yayi yana kallon Nisha yana sakin murmushi "Nishana najima ko? "Yayamu baka jimaba kai zee ta kauda zuciyarta na mata kuna guri ya Kara ciki kawayen amarya Nisha Ana fili sai cashewa sukeyi Mc yace" to muyi abinda ya kawomu Ahmed ne ya Mike ya bada tarihin Ango Sardauna wani abun atafa wani ayi dariya Nisha kanta saida tayi dariya gurin da Ahmed yace Sardauna na tsoron tsawa da cida hall kowa ya dara shi kansa dariya yayi intisar ta Mike da kwalliya ta kece raini ta hadu iya haduwa diyar kawu Saminu itace ta bada tarihin Nisha raf raf raf aka dauki zee ma saida ta dara wai bera da mage sune tafi tsoro arayuwarta da mutum mai tsama Hadeem kuwa tarihin Mahbeer ya bada nanma ansha dariya sai Hafeeza ta bada tarihin zeey baby wai jama'a har rike ciki sukeyi masha Allah abin gwanin burgewa Mc yace suzo su yanka cake cikin nustuwa kowa ya kama hannun matarsa suka sabko cake din ya hadu sunayen amarya da angone da pic d'insu abun gwanin burgewa jama'a sun kewayesu Nisha ta, fara yankowa Sardauna yayi mata tsayi sosai cak ya dagata, tasaka masa, abaki aikuwa ihu da tafi zee idanunta ta rufe ta boye bayan mahabeer Sardauna ya yanko yaba Nisha aka tafa musu aka saki kida Maijidda da maryama suka jasu filin rawa Mahabeer ya yanko yaba zee ta amsa gun da ya bata mata baki ya duko ya lashe ya rumgumeta gam sai ihu ake ahaka tana rumgume jikinsa ta yanko ta bashi wani katone ta tura masa, duka sai dariya akeyi

su zainab da Salma suka jasu filin rawa jama'a kuwa, sai ciye ciye da tande tande akeyi acikin nutsuwa Sardauna ya rike k'ugun Nisha yana juyata su Ahmed sai barin kudi suke masa bandar ya bude bakin aljihu Nisha ko kunya ta cikata Dole ta manne jikin Sardauna ta boye kanta kirjinsa Nadiya kawar Nisha salon yayi mugun burgeta sai liki take musu tana jinjinawa, Nisha samun gwarzon Namiji irin Sardauna na mahabeer rike yake da zeey baby sai juyi suke zee sam bata haiyacinta bakin cikin yada Sardauna ya shigar da Nisha jikinsa yana juyi da itane ya daga mata hankali sai hawaye take gogewa da handkerchief kamshinsa na shigarta haka dangi su baibayesu ana watsa musu kudi su tuwusai da minata sai rawa suke dan dinner din Nigeria ya burgesu sai suka gaji dan kansu kowa ya koma mazauninsa aka ci GABA da gudanar da taro jama'a sai kara bankadowa suke su hafeeza girjin biki yau duk inda Ta wulga idanun Ahmed kanta bai taba zaton yarinyar haka Takeda tsariba yakub ko abokin Sardauna Wanda yazo daga, kano idanunsa kan intisar bandar ma yarinyar Ta tafi da imaninsa sosai saide yasan ba halin hakan masha Allah dinner yayi kyau sosai sai karfe bakwai aka tashi Sardauna ya saki ransa ya barwa Allah ikonsa yasan bawa baya wuce kaddarasa zee daurewa tayi ta saki ranta amma

Rumgumar da Sardauna yama Nisha da yada yake juyata filin taron,abin na ranata ta basar tunda batada hujja Sardauna na rike da hannu Nisha har gindin mota su Ahmed na biye dashi sai shishigema hafeeza yake motar aka bude musu suka shiga aka rufe musu Ahmed motarsu yaja hafeeza bandar na masa tsiya yakub ko yana tare da intisar saide bai samu yanda yakeso ba dan ita mutum dayane azuciyarta batajin zata daina sonsa har tabar duniya yanzuma dariya kawai take saboda Nisha ta wuce taki zuwa auranta direba yaja motar su Sardauna suka bar hotel d'in Nisha duk jikinta yayi sanyi tsoron Sardauna yashigeta yada Nadiya ta rika cemata wannan mijin bata taga yau bazai saurara mataba gashi gabjeje zaiyi kuzari gun sarrafa mace kallonta Sardauna yayi" Nishana meyasa kika fiye sanyi aguna amma ai ba haka kikeba ya fada yana leken fuskarta murmushi tayi ta dago"Yayamun ba komai kawai gajiyar rawar da kayi danine murmushi yasaki ya dora kanta cinyarsa " Ok to shikenan zan miki tausa dariya tayi ta sunne kanta acinyarsa gabanta na bugawa shiru yayi bai sake magana ya dauki wayarsa yana latsawa dan har yagaji da amsa kira, tsayuwar mota yaji kawai a kofar gidansu Nisha dagota yayi ya rufa mata dan kwalinta "Oya shiga gida a shiryamun ke sai kinzo idanu ta rika zarowa dariya ta bashi ya kanne ya bude mata motar ta fita tana daga masa hannu kai ya girgiza shima ya daga mata direba yaja motar suka tafi bangaran zee da mahabeer suna cikin mota direba na tukasu tayi lamo jikin mahabeer sai hawaye take ya rasa mai zai mata dagota yayi" zee menene sam yau naga kamar bakya cikin farin ciki ko bakida lfy ne Ahkuya d'inkine fah ya zama mijinki amma kike kuka cikin shashekar kuka tace"my heart farin cikine nakeyi kuma sai nakejin kamar na rasa wani Abu mai mahimmancin arayuwata amma wlh bansan meye ba ta fada tana kuka mai cin rai tausayi ta bashi dan ya lura kwana biyu bata cikin nutsuwarta hawayen fuskarta yake tsotsewa yana buga bayanta cikin sigar lallashi amma bata kyaleba Dole ya tallabo kanta ya had'e bakinsu yana tsotsa idanu ta rumtse sam bataso dolene yasa take barinsa shiru tayi ta lafe jikinsa yana tsotsar bakinta kamar zai cinyen mata baki yana cikin tsotsar yaji wani Abu kamar kibiya aharshensa sakin bakinta yayi da sauri yana kallonta hajijiya tana daukarsa idanu ta bude tana kallonsa "Ya mahabeer menene ta rikeshi" kinfi kowa sani idan bakyaso na tsotsi bakinki sai ki fada amma akan me zaki cijeni ya fada yana zaro handkerchief ya zubo wani irin jini bakikirin idanu zee ta zaro"wlh ban cijeka saboda me zan cijeka ta fada tana kuka bakinsa ya goge bai cemata komaiba har tagaji da kukanta tayi shiru ta rumgumesa har suka ISO gida direba na tsayawa ya janyeta jikinsa ya bude mota "jeki kallonsa tayi taga duk ya canza "my heart kayi hakuri kaji murmushi ya sakar mata itama murmushi tayi ta sabko ya bata Jakarta ta nufi gida shima fitowa yayi ya nufi part d'insu aparlo ya isko su Sardauna ya tatara duk wani Abu mai mahimmanci Najib na jida zaikai can gidansa su Ahmed sukace" yayamu sai yanzu aka ISO dariya yayi '' wlh kuwa Sardauna yace"bro kako maida kayanka ya fada yana murmushi kansa mahbeer ya shafa" wlh Dr namu har kasa naji kunya ai tun shekaran jiya nakai Hadeema yakai masa dukan wasa dariya Sardauna yayi "bro banga laifinka ba wlh Nina rashin lokacine kullum ina hospital kanaga kwananan har tsakiyar dare sai an kirani yanzu sai azo ama amare shiri dariya mahbeer yayi ya nufi bedroom d'insa bangaran zee baby tana shiga yan uwa aka mata caa Daddah tace "ja'ira amaraya ta rumgumeta "dariya zee tayi ghaisha tace da tuwasai da Minata
suje suyi mata wankan maganinan Daddah tace"ita zata mata dariya sukayi Dole suka bar Daddah ta nufi bedroom da ita ta cire kayanta suka shiga bathroom

ta wanke tas da ruwan magani yaji uban turare sai sheki da kyalli take da uban kamshi suka fito ummi ce ta goge yarta ya shafeta da maiyuka masu taushi ta tsatsara mata kwalliya ta kece raini wata arninyar doguwar rigace mai masifar kyau pink colour saide batada hannuwa ta saka mata ta nadeta da lufaya tanaso tayi mata al'adar larabawa amma bataso ace ta zage dayawa kan yarta fesheta tayi da turaruka masu kamshi ta zaunar da ita bakin gado hafeeza da zainab sai yabon kyaunta sukeyi bangaran Nisha tana shiga gida itama dangi sukabcaa akanta intisar da Nadiya na biye da ita itama wanketa akayi cikin ruwan turare sai kamahi da sheki take intisar ce ta cacada mata kwalliya itama lifayace aka nada Mata tayi masifar yin kyau zaune take bakin gado Nadiya sai kodata take intisar ta goge hawaye ta rumgume Nisha"yar uwata na tayaki murna kin samu cikar burinki ni nice nayi rashi Nisha ta kalleta" Ni intisar bansan inda kika dosaba wai waye kikeso hakane Dan Allah ki kasance mace mai kamun kai mutikar bashine ya ya furta miki soba to kiyi hakuri please yar uwata ta fada tana goge hawayen fuskarta" to shikenan nagode yar uwata zan daure ta fada tana dariya Nadiya tayi murmushi Dan ita tagano komai tun agon dinner hajiya fati ce ta shigo kanwar bashir" to amarya sai ki fito har Tara na dare tayi ga angwaye can sunzo daukar amaryarsu hannun Nisha ta kamo suka fito gaban umma hauwa'u ta Duke tana rusar kuka nasiya suka mata mai ratsa zuciya bashir ma ya shigo ya mata fada haka Nisha tana kuka aka fita da ita daga gidansu motocine har guda biyar na kece raini sukazo daukar Nisha tana kuka haka aka tafi da ita gidanta

End of Chapter 63Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next