Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
*bayan kwana ukku*
tunda zee baby da Dr Sardauna sukayi fada da Alkawalin fita daga harakar juna yau har kwana uku to sun cika alkawali babu mai shiga sabgar kowa tun ranar zee ko kallonsa bata yada ta sake ba tayi watsi da lamarinsa kamar yada shima ya watsar da ita a salima idan sunji murya junansu kowa k'okianrin barin gurin yake shiyasa yanzu zee bata fiye zama parlo ba da dare dama dasafe kafin ta tashima ya tafiyasa gun aiki shiyasa basu fiye gamuwaba tun daga ranar har yau basu hada idanuba kowa yama zuciyarsa alkawalin hakan shiyasa ta maida hankalinta gun Mahabeer suke zuba soyayyarsu tana masa sangarta iri iri yana biye mata Dr Sardauna ya maida hankalinsa gun sweet babynsa dan tana bashi tausayi yanda take mutuwar sonsa, yaune wa'adin da malam kafi madubi yama Aunty amarya yaune zata amso magani da sharudan da zai gindaya mata, tun safe tacewa Daddy mamarta ba lfy yace ta shirya ya ajiyeta tace amotarta zata bai musaba, bayan sun gama breakfast taje ta shiryo, ghaisha na zaune aparlo Mahabeer na mata sallama yau ya makara da ya shiga gun zee ta tsayar dashi wai suyi hira sai daket ya lallabata ta koma bacci dama shine ya tasheta ya kawo mata tea tasha, Aunty amarya tafito rike da hannu nanah tace" Aunty ghaisha zan dubo mummy sai nadawo"kodai na tashi mutafi? " wlh ki zauna gidan ba kowa. idan kin samu lokaci sai ki tafi"to agaishemun dasu kafin nazo nanah zo mu zauna kafada ta makale Mahabeer ya dauketa yana dariya tare suka fito da Aunty Amarya har motarta ya rakata yana rike da nanah ya ajiyeta sukayi sallama ya shiga motarsa ya nufi get Aunty amaryama ta shiga motarta tayi mata key ta nufi get............✍🏻
💃🏻Yar ilu ce🤪
*💖💖👩🏻🦱ZEE BABY👩🏻🦱💖💖*
*DAN ALLAH KARKU FITARMUN DA BOOK WAJE*
*👉🏻21*
....atatare suka fita Mahabeer da Aunty ya dauki hanyar kamfaninsu itako ta dauki hanyar gidansu ranta fari tas take tuki nanah na mata surutu sai dariya takeyi akofar gidansu ta tsaya wani gidane me soron kofa kana gani kasan kwaskwarima ce yasha parking tayi tafito ta safke nanah ta rufe motar suka shigo tsoron kofar atsakar gida ta isko mamarta da Asiya "kai kawata amma samun aminiya irinki sai antona yanzu nabiyo na ajiye nanah na tafi gidanki muwuce wata yar dattijuwar matace ta washe baki "yaran albarka kuyi yada kukeso gidan mazajanku ku murza kambunku ahannu nima naci zamanina Mariya mahaifinki har yamutu idan nayi kurtu baya tsallakewa dan haka kema lokacin yayi da zaki kama mijinki uwar gidanki tazama shara ita da 'ya'yanta yazama baya ganin kan kowa da gashi sai ke wlh ina mamaki nifa mahaifin kafi boka malam kafi madubi shine yamun aiki sama da shekaru ashirin naci karena babu babaka amma ace har yanzu burinki bai cikiba aure wajan shekaru bakwai haba ai yaci mu yashesu muma mushege daula bushewa sukayi da dariya mariya taje ta rumgume mamarta "wlh hajiyata kibari komai yakusa zuwa karshe baza'ayi irin na Abban khalisat ba duk dukiya Ashe ta banki ce yaci bashi har muka kasheshi abanza ai wlh inajin takaici har yau sai na tsinewa Alhaji Musa albarka kara da kiyashi Muke Asiya tayi dariya tace daukar marar sani wlh nima tayaki nakeyi amma kibari wannan zamu yashi arziki kamar yada nake nan ina tande Haruna hajiya tace"Allah muku albarka ku tashi ku tafi nanah zo ki zauna gun kakarta ta nufa ta zauna suka miki suka mata sallama suka fito mota suka shiga Aunty amarya taja suka kama hanyar gun malam boka
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
lokacin da sukaje akwai jama'a sosai duk matane mazan kadanne guri suka nema suka keb'e har layinsu yazo suka shiga dan dak'in mai cikin da baranda wani irin wari yake kadawa amma basu damuba saboda sun saba zaune suke agabansa ya janyo katon madubi ya fara saddarabarunsa yace"mariya matso ki gani matsowa tayi idanu ta zaro ganin Sardauna khalisat a hagum d'insa dayar adamarsa sai wata da ba'a ganin fuskarta sai haske kawai goshinta yake ga fararan hakoranta tana sakin murmushi da wani katon ice ahannuta tana k'ok'arin buga musu khalisat da dayar yarinyar sai mashakurah tana kuka cikin wani hali agefe arikice tace"malam na shiga uku na lalace mace hudu to dan meyasa ba'a ganin wannan mai hasken fuskar kuma me yakawo aishi cikin harakokina bushewa yayi da dariya" tabbas zata shigo cikin rayuwarshi mutikar kika kuskure a sharudana idan kin cika kuwa yarki ce kadai sarauniya saboda Dole kaddara zata rabashi da wata wacce bansantaba kaddara ta Santa to iyayansa babu tunanin hadashi aure da yarki dan haka shi kansa yau da kinsan irin tsafi da wuyar da nasha kafin na samu lbrn da fitowar yaron kinsan yanada karfin ibada da Addu'a da sallahr dare duk lokacin da zan tun karesa cikin ibada yake dan haka ajiye hankalinki tashi Muje ki amshi maganin wani dan d'aki suka shiga wata babbar kwaryace da faifai arufe ya bude wani ruwane bakikirin aciki sai wani irin wari ke tashi hannu yasa ya tsamo ledoji gida uku abin Al'ajabi babu dugon k'azamin ruwan jikin ledar ya bata ta amsa "to ki kiyaye yau kwanansu goma sha daya cif ina tsafi akansu sharadin sune Jan leda ta farko ki tabatar kin zubawa mijinki maganin a abunci sau uku rak karki kuskura wani ya ganki kuma karki bari wani yayi anfani da kwanon da zaici abuncin mutikar kikayi haka ba ki bari yayi fashin cin abuncinba kuma wani bai gankiba wlh kin gama dashi ko cewa kikayi ya sama garin Katsina wuta sai yasa ko ya kwanta kimasa yankan rago wlh da kansa zai kawo wukar na biyu kuwa yaron da kikeso ya auri yarki wannan na farar ledar zatayi kokari ta barbada masa inda zai tsallaka amma shi bazan gayamiki illar saba sai kinzomun godiya sharadin shine ta tabbatar shine zai tsallaka da farko dan idan ba hakaba to fah Wanda ya tsallaka Hamm to idan shine ko da. Wani yabi bayansa to babu abinda zai samesa na uku shine tsanwar ledarnan ta jik'a maganin sai yayi kwana uku tarika wanke fuskarta sau uku arana tayi k'ok'ari suna magana koda so dayane har tsawon kwana talatin da tara to fah ranar aikinku zai kammala ki kiyaye karku kuskure barinma ke wlh idan kika kuskure to wannan ruwan kwarya sai yafiki daraja aduniya ki kiyaye aikinku akwai tsauri mutanan sunada taurin kai da karfin Addu'a nasha wuya hada maganinan anyi asara jarirai biyu saboda aikin ki da yarki don haka karki bari aiki ya b'aci ranar da kika cika kwana arba'in ba daya to wlh duk abinda Alhaji ya mallaka yazama naki kuma ranar za'a daurawa yarki aure da d'ansa sabanin haka saide a d'aura da wata kuma keko kare sai yafiki daraja zaki lalace ki tozarta aduniya dan dama na gayamiki sharadin kafin nayi tsafinan kikace kin amince karki dawo sai kwanaki sun cika "karka damu zan kiyaye yau ina farin ciki wannan k'aramin aikine babu mai wuya aciki duka zamuyishi fitowa sukayi Asiya tayi masa godiya ya kara jadada mata karta dawo sai bayan kwana talatin da tara tazo masa da labari mai dadi kudi ta Tule masa na uban mamaki suka fito suka tafi mota suka shiga suka tafi zuciyarsu fari kalla suka nufi gida,
******
Zaune yake cikin hadaddan Office d'insa saman lumtsumemiyar kujera sai juyi yake yana zugar sigari farin gilashi manne afuskarsa ya had'e cikin kananu kaya Wanda suka yimasa masifar kyau kwarjininsa ya fito sosai gashin kansa bakikirin sai sheki yakeyi ya dan sabko kadan bisa wuyansa wayarsa karama ta dauki ringin kin kallon wayar yayi lumsassun idanunsa ya lumshe ya daga kai sama ya feso da hakin taba knocking kofarsa akayi saida akayi sau uku ya bude idanunsa cikin zazzakar muryasa yace"yes turo abude bai karasa ba Ahmed ya shigo"wlh Dr Sardauna bakada mutumci dan kun hanani kanwarku shine yau kwana hudu baka jiniba baka nemeni ba, murmushi gefen baki Sardauna yayi"sorry Abokina wlh aiyuka sunmun yawa yanzu ko 20 minute banba da na fito daga tiyata wlh marasa lfy garemu dayawa kwana biyu sai dare nake zuwa gida ykk ya soyayya ka hakurane?? " ban saniba dan rainin hankali ai Dole zan barta tunda yayamu yamun fin karfi amma wlh ina son zee baby yar fara kyakyawa baki Sardauna ya table"wai kuwa Dr kasan wani Abu? " sai ka fada "hmm bandar fah alondon wlh yar mutane ya lalata ko ince suka lalata juna gashi abun ya damesa" Ahmed nifa kasan banason gulma kabar maganar yace sai yazo dukan wasa Ahmed ya kai masa"dallah can malin malin karkamun wa'azi hayakin sigari ya cika baki dashi ya fesa ma Ahmed "dan rainin hankali kai ko da yaushe idan mutum yazo gunka sai kamasa rainin hankali "Allah baka hakuri aboki daga fadin gaskiya, Kiran sallah azuhur aka fara Sardauna ya Mike ya dauro alwalla suka nufi masallaci Dr sai tsiya yakema Ahmed banza ya masa da Ruma suka hadu a harabar asibitin ta gaishesu adakile Dr Sardauna ya amsa suka wuce Ahmed"yace ya dai ko uwar guzuma na cikine mugun kallo Sardauna ya masa suka shiga cikin masallaci,
✨✨✨
More Hausa novels
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel
By Hafsat Bature
A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Zazzafan Rabo Part One Complete Hausa Novel
By Aisha Umar Indabawa
Ni Da Yaya Sadiq Book 1 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Dafin Harshe Book One Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.