Soyayyanovels
Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
By Real Ladingo
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel

Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel

Author: Real Ladingo
Chapter 4 of 130
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,685 words Chapter 2 1,656 words Chapter 3 1,426 words Chapter 4 Reading now Chapter 5 1,658 words Chapter 6 1,660 words Chapter 7 1,540 words Chapter 8 1,682 words Chapter 9 1,488 words Chapter 10 1,684 words Chapter 11 1,352 words Chapter 12 1,481 words Chapter 13 1,490 words Chapter 14 1,658 words Chapter 15 1,664 words Chapter 16 1,361 words Chapter 17 1,446 words Chapter 18 1,594 words Chapter 19 1,440 words Chapter 20 1,595 words Chapter 21 862 words Chapter 22 1,587 words Chapter 23 936 words Chapter 24 1,007 words Chapter 25 1,624 words Chapter 26 548 words Chapter 27 1,952 words Chapter 28 1,599 words Chapter 29 1,281 words Chapter 30 1,465 words Chapter 31 1,117 words Chapter 32 1,166 words Chapter 33 1,496 words Chapter 34 1,495 words Chapter 35 1,191 words Chapter 36 1,505 words Chapter 37 1,475 words Chapter 38 1,632 words Chapter 39 970 words Chapter 40 1,565 words Chapter 41 1,516 words Chapter 42 1,101 words Chapter 43 1,209 words Chapter 44 1,672 words Chapter 45 1,520 words Chapter 46 1,612 words Chapter 47 1,543 words Chapter 48 1,654 words Chapter 49 1,192 words Chapter 50 1,699 words Chapter 51 1,476 words Chapter 52 1,648 words Chapter 53 1,617 words Chapter 54 1,636 words Chapter 55 1,432 words Chapter 56 1,581 words Chapter 57 1,631 words Chapter 58 1,206 words Chapter 59 1,393 words Chapter 60 1,279 words Chapter 61 1,241 words Chapter 62 1,639 words Chapter 63 1,506 words Chapter 64 1,619 words Chapter 65 1,517 words Chapter 66 1,475 words Chapter 67 1,600 words Chapter 68 1,589 words Chapter 69 1,675 words Chapter 70 1,603 words Chapter 71 1,692 words Chapter 72 1,515 words Chapter 73 1,429 words Chapter 74 1,552 words Chapter 75 1,635 words Chapter 76 1,554 words Chapter 77 1,590 words Chapter 78 1,500 words Chapter 79 1,567 words Chapter 80 1,518 words Chapter 81 1,656 words Chapter 82 1,634 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,643 words Chapter 85 1,435 words Chapter 86 1,628 words Chapter 87 1,694 words Chapter 88 1,601 words Chapter 89 1,576 words Chapter 90 1,659 words Chapter 91 1,655 words Chapter 92 1,536 words Chapter 93 1,559 words Chapter 94 1,457 words Chapter 95 1,655 words Chapter 96 1,677 words Chapter 97 1,557 words Chapter 98 1,692 words Chapter 99 1,558 words Chapter 100 1,525 words Chapter 101 1,533 words Chapter 102 1,651 words Chapter 103 1,695 words Chapter 104 1,597 words Chapter 105 1,580 words Chapter 106 1,627 words Chapter 107 1,681 words Chapter 108 1,700 words Chapter 109 1,636 words Chapter 110 1,621 words Chapter 111 1,471 words Chapter 112 1,637 words Chapter 113 1,685 words Chapter 114 1,674 words Chapter 115 1,638 words Chapter 116 1,629 words Chapter 117 1,674 words Chapter 118 1,513 words Chapter 119 1,674 words Chapter 120 1,653 words Chapter 121 1,623 words Chapter 122 1,605 words Chapter 123 1,584 words Chapter 124 1,634 words Chapter 125 1,675 words Chapter 126 1,537 words Chapter 127 1,639 words Chapter 128 1,693 words Chapter 129 1,496 words Chapter 130 1,209 words

Dadi batason rabuwa da yar tata amma da ta tuna rashin jinta gashi batasan me zai faru a gaba ba Dan rashin jin. Yar tata sai ahankali gashi tana Addu'a ba dare ba rana amma baby wani sauyi Zee baby ko suna shiga ta tube kayan jikinta tana rawa da juyi sai ihu takeyi tana dariya daga ita sai shegiyar rigar nan manal tace" my habibty wlh iskanciki gaba yakeyi fah fasa rawar tayi wata shegiyar tsayuwa akarkace tana kallonta shekeke tana murmushi " bari nayi bautar Allah na gama zanci durin uwarki la'ada waje yasin bathroom ta shige jannat ta kalli manal " wlh duk kece kika koya mata Hausa da zage zage gashinan akanki take sabkesu wlh dazu naji kunyar abun da ta fadi gaban baki? dariya manal tayi" naji amma shaye shaye wa ya koya mata Dan kaniyar mai da famiki shurba daga cikin toilet ta lailayo zagi ta dirka musu ta ciko Dan bokiti da ruwa ta bude kofar ta watso musu " sheguna ina jinku fah ta koma taci gaba da wankata ta dauro Alwalla ta fito tabude wardrobe dinta ta bude ta ciro Abbaya ta saka ta nade kanta da mayafin ta shimfida dadduma tayar da sallahr Azuhur, suko kayansu sukacire suka canza da nata suna mata Allah ya isa azuciya tana idarwa taji kiran la'asar ta tashi ta tayar suma Alwalla suka dauro sukayi sallah tana gamawa ta ci uwar kwalliya tasaka wata atamfa bakace mai ratsin fari dinki Riga da siket manal ce me musu dinki tare su ukku kullum to jannat ba'a barinta tana sawa agidansu saide idan ta fito gashinta ta sarce ta daureshi tayi masifar kyau kamar ka saceta sai dai dinkin ya fito da surata yan mazaunanta masu daukar hankali sai motsi suke tana kadasu gangan tana musu gwalo manal tace " dallah can figigiyar banza nacemiki ki faso gari kizama yar duma duma A dama dake kullum ke kamar kinashan ruwan zafi ta fesa turare

ta kallesu " wlh manal danayi jiki gwara daga haka nakara tsotsewa Dan uwarki ko ba jiki akwai kayan aiki ta juyo mata yan mazaunanta masu qira coca cola tana fito da harshe waje tana kadawa ihu suka saka " ku tashi muje parlo ku gaishe da Dan uwana kuma wlh sai kun duka har k'asa fitowa sukayi suna dariya gun mahabeer suka nufa ta zauna kusansa suko suka duka suna masa sannu da zuwa cikin fara'a ya amsa yace" ko zaku bimu Nigeria ne kai suka girgiza suna dariya Zee ta jinginu da jikin Mahabeer ashagwab'e tace" Ahukhuya nima bana zuwa fah ta Kara shigewa jikinsa tana turo baki aransa Adu'a yakeyi Allah yakawo masa dauki son yarinyar yamasa mugun kamu ga wata muguwar shawarta da yakeji janyeta yayi yana murmushin karfin hali " kanwata kiyi hakuri muje sati dayane zakiyi ki dawo ko ummi ya fada yana kallon ummi dariya tayi" eh sati daya zakiyi habibty ajiyar zuciya ta sabke" to naji amma da anyi sati zaka maidoni kuma ba gidansu wannan banzan gayan bane zan zauna ko ummi ta matso ta doketa abaya tun karfi take dukanta tana mata magana da larabci saida ta Saki Kara ta rukunkume Mahabeer tana kukan sangarta tare dukan yai yanaba ummi hakuri ransa babu dadi Dan yaji haushin bugun da take mata kamar yayi kuka yace" haba ummi Raiyan Zee yarinya ce fah lallabata zamuyi zata daina masa amma dukan yayi yawa sai ajimata ciwo ai idanu ummi Raiyan ta zuba masa cike da mamakinsa " haba Mahabeer yanzu ahakane zaku ku gyarata kana daure mata gindi wlh shiyasa naso yazo da kansa tun kafin su isa can taci gidansu la'ada waje cikin shashekar kuka tace" Ahukhuya kagani kullum sai ummi ta dokeni saboda wannan mungun mutumin wlh idan mukaje Nigeria mutikar na Ganshi akasar idona

idanusa kafin na dawo Allah na dauki Alkawarin sai na Rama abinda akamun akansa ta fada tana Kara rumgumesa tana kukan takaicin duk lokacin da zata zageshi sai ummi ta doketa kuma duka ba na wasaba shiyasa takejin duk duniya ta tsaneshi sama da komai Hasbinallahu Wani'imar Wakim kawai yake maimaitawa gashi bayason kukanta daurewa yayi yana bubbuga bayanta " yi hakuri kanwata nima bazan yardaba anaci miki mutumci yi shiru kinji ya leko fuskarta shiru tayi ta boye kanta kirjinsa samu yayi ya lallabata ya janyeta jikinsa Jamal da idanu yake binsu yanajin haushin yada idan tahau jikin Mahabeer yake janyeta baya bari ya rage zafi ba lallashinta ya shiga yi har ta Saki ranta suko su manal sunsha mamaki Dan sunsan Zee baby bata cika kuka ba a Al'amuranta kuka baya cikin tsarin rayuwarta ummi dai da idanu take binsu yau ta Mahabeer take ta Saki jikinta sai labari take bashi yako maida hankalinsa kanta sai dariya yakeyi Jannat na tayasu Dan Mahabeer ya burgeta bashida damuwa akwai fara'a
Saida akayi kiran sallah magrib suka Mike sukayi shirin zuwa masallaci suma su Zee baby suka tafi suyi sallah sai tsokanarta sukeyi wai taga Dan uwanta ta sheresu dariya tanusu batace dasu komaiba,

************
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*Nigeria* karfe shida na yamma Wata jibgegiyar motace fara sal da ita saman babban titin malali cikin nutsuwa yake driving waya manne akunnesa sai murmushi yakeyi cikin amon muryasa mai dadin gaske naji yace" sweet baby kiyi hakuri wlh kukanki na daga mun hankali kiyi shiru ganina fah saman hanya zanzo na ganki shikenen ko OK Oya fito gani na karaso ina Sauri kar lokacin sallah magrib yayi ya fada yana tsinke kiran saboda ya Iso kofar gidan honr yai mai gadi ya bude masa ya danno hancin motar gidan yana parking ta fitowa masha Allah wata kyakyawa na gani baka ce sosai amma tanada kyau amma ba doguwa bace ba kuma bata fiye gajarta ba tanada hanci dede misali da idanuwa dede gwargwado tanada gashi ba laifi bakinta Dan karamine saidai tanada yar kiba kadan agaskiya dai batada makosa tanada kyau yar 23 year tanda faram faram batada daurin kai saide ta fiye sanyin hali batada hayaniya duk da a turai tayi karatun Nurse har tsawon shakara ukku isowa tayi ta bude motar ta shiga da sallama

tana murmushi shima murmushin ya sakar mata " sweet baby uwar yan rigima ya gajiya bazaki bari ki hutaba kamar bamu hadu da safe ba ya cikin naki da fatan kinsha magungunan da na kawo miki kanta ta sada tana wasa da hannuta " nifa kinga matsalata dake dagowa tayi Dan tasan halinsa yanzu zaiyi watsi da lamarinta ya tafiyasa Dan Sam bayason shariya " my Dr yi hakuri ta fada tana kallonsa cikin dauriya Dan kwayar idanusa fusgar mutum sukeyi my Dr na kayi kyau sosai kamar na saceka ta fada cike da kunya " OK Oya fadamun me kike so kika tisani da kuka sai nazo kuma gani kina wani sunne sunne ko cikinne ? kanta ta kwantar saman kafadarsa tana sabke ajiyar zuciya "sweet babyna menene bakida lfy ne ? " my Dr na wlh idan nayi awa biyu ban gankaba banajin dadine amma yanzu banajin komai na warke ta fada cikin sanyinta murmushin gefen baki yai ya dagota kanta daga kafadarsa ya kura mata mayatattun idanunsa yanajin mugu mugun sonta da kaunarta na ratsashi Dan tarbiyyarta tayi masa tamkar ba aturai tayi karatu ba " my mashakurah wlh nima ina sonki nifa na ganki nace kinmun so sai me ki ajiye hankalinki Dr Sardauna nakine ke daya insha Allah kinji sweet babyna idanuta ta lumshe ta daga masa kai kiss ya mata agoshi " OK Oya shiga ciki kinji an fara kiran sallah kisha magani kinji? kai ta daga fitowa tayi tana daga masa hannu idanuta sun tara kwalla ya gani sairai idan yace ya lallasheta kuka zata saka masa shiyasa yaja motar ya fisgeta da karfi juyawa tayi ta tafi ta nufi cikin gida yana fitowa ya harba motar kan titi yana gudu sosai ya dauki hanyar kofar Marusa lowcos gudu yake shararawa sosai Dan ya samu sallah magarib, lokacin da yazo har an gama sallah honr yayi aka bude masa katoton get din gidan ya danna hancin motar gidan Ana harbar gidan yai parking ya fito gun mai gadi ya nufa agaguce yayi Alwalla ya nufi masallaci, bai fito daga masallaci ba saida akayi isha'i yana fitowa ya shiga bangaransu wow agaskiya ya hadu sosai d'akunane har biyar ukku daga farko biyu acikin wata yar kwana kwanar naga ya karya dakin karshene Nasa ya ciro key aljihunsa ya saka ya bude kofar wani ni'imataccen kamshi ya me fitowa tamkar yanzune akayi anfani da turarukan masha Allah nace saboda haduwar bedroom din wani royal bed makekensa d'akin ba tarkace amma zaka zata dakin amaryane ga wasu lumtsma lumtsuman kujeru na kayan jikinsa ya rage ya shiga toilet Yajima sosai ya fito daure da towel kirjinsa cike yake da gashi yana da fadin kirji sosai duk amunmurde yake tamkar yanacin karfe agaguce ya shirya ko mai bai shafaba yasa wando 3quater ya saka da Riga short ya fesa turare ya gyara sumar kansa tayi luf luf sai shegi take baka sudik wayoyinsa ya kwasa baki daya ya fito cikin kuzarinsa yake tafiya ko kofar bedroom dinsa bai rufeba ya nufi part dinsu ghaisha da sallama ya shigo parlon ghaisha na zaune Nawwara na jikinta yana shigowa ta Mike suna gaishesa yaran parlon hannu ya daga musu ghaisha tace" bokan turai baki ya turo kamar wani yaro zama kusanta ya kwantar da kansa saman cinyarta ashagwabe yace " ghgaisha nah wlh duk nagaji" sannu Dr Sardauna ai Dole tin safe sai yanzu tausa ta fara masa" yauwa mamana Allah kuwa ciwon jiki nakeyi dariyace ta kamasu Hafeeza ce dariya ta kufce mata khalisat ta zaro idanu ta Mike sadaf ta gudu tun kafin ya dago aikuwa ya zabura zai tashi ghaisha ta rikeshi suna ganin haka suka matso suna bashi hakuri banda hafeeza da khalisat da suka Ari ta kare ghaisha tace"maza ku tashi kusan nayi ai yasan wa tayi dariyar mik'ewa sukayi suka bar parlon baki ya ciza ya kalli ghaisha" yanzu Dan Allah mamana kina kallo khalisat mai zubin nunar rana itada yar iskan yarinyanan sukamin

End of Chapter 4Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next