Soyayyanovels
Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
By Real Ladingo
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel

Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel

Author: Real Ladingo
Chapter 109 of 130
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,685 words Chapter 2 1,656 words Chapter 3 1,426 words Chapter 4 1,678 words Chapter 5 1,658 words Chapter 6 1,660 words Chapter 7 1,540 words Chapter 8 1,682 words Chapter 9 1,488 words Chapter 10 1,684 words Chapter 11 1,352 words Chapter 12 1,481 words Chapter 13 1,490 words Chapter 14 1,658 words Chapter 15 1,664 words Chapter 16 1,361 words Chapter 17 1,446 words Chapter 18 1,594 words Chapter 19 1,440 words Chapter 20 1,595 words Chapter 21 862 words Chapter 22 1,587 words Chapter 23 936 words Chapter 24 1,007 words Chapter 25 1,624 words Chapter 26 548 words Chapter 27 1,952 words Chapter 28 1,599 words Chapter 29 1,281 words Chapter 30 1,465 words Chapter 31 1,117 words Chapter 32 1,166 words Chapter 33 1,496 words Chapter 34 1,495 words Chapter 35 1,191 words Chapter 36 1,505 words Chapter 37 1,475 words Chapter 38 1,632 words Chapter 39 970 words Chapter 40 1,565 words Chapter 41 1,516 words Chapter 42 1,101 words Chapter 43 1,209 words Chapter 44 1,672 words Chapter 45 1,520 words Chapter 46 1,612 words Chapter 47 1,543 words Chapter 48 1,654 words Chapter 49 1,192 words Chapter 50 1,699 words Chapter 51 1,476 words Chapter 52 1,648 words Chapter 53 1,617 words Chapter 54 1,636 words Chapter 55 1,432 words Chapter 56 1,581 words Chapter 57 1,631 words Chapter 58 1,206 words Chapter 59 1,393 words Chapter 60 1,279 words Chapter 61 1,241 words Chapter 62 1,639 words Chapter 63 1,506 words Chapter 64 1,619 words Chapter 65 1,517 words Chapter 66 1,475 words Chapter 67 1,600 words Chapter 68 1,589 words Chapter 69 1,675 words Chapter 70 1,603 words Chapter 71 1,692 words Chapter 72 1,515 words Chapter 73 1,429 words Chapter 74 1,552 words Chapter 75 1,635 words Chapter 76 1,554 words Chapter 77 1,590 words Chapter 78 1,500 words Chapter 79 1,567 words Chapter 80 1,518 words Chapter 81 1,656 words Chapter 82 1,634 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,643 words Chapter 85 1,435 words Chapter 86 1,628 words Chapter 87 1,694 words Chapter 88 1,601 words Chapter 89 1,576 words Chapter 90 1,659 words Chapter 91 1,655 words Chapter 92 1,536 words Chapter 93 1,559 words Chapter 94 1,457 words Chapter 95 1,655 words Chapter 96 1,677 words Chapter 97 1,557 words Chapter 98 1,692 words Chapter 99 1,558 words Chapter 100 1,525 words Chapter 101 1,533 words Chapter 102 1,651 words Chapter 103 1,695 words Chapter 104 1,597 words Chapter 105 1,580 words Chapter 106 1,627 words Chapter 107 1,681 words Chapter 108 1,700 words Chapter 109 Reading now Chapter 110 1,621 words Chapter 111 1,471 words Chapter 112 1,637 words Chapter 113 1,685 words Chapter 114 1,674 words Chapter 115 1,638 words Chapter 116 1,629 words Chapter 117 1,674 words Chapter 118 1,513 words Chapter 119 1,674 words Chapter 120 1,653 words Chapter 121 1,623 words Chapter 122 1,605 words Chapter 123 1,584 words Chapter 124 1,634 words Chapter 125 1,675 words Chapter 126 1,537 words Chapter 127 1,639 words Chapter 128 1,693 words Chapter 129 1,496 words Chapter 130 1,209 words

cikin sassarfa ya isa gareta ya zube gabanta ya kamota ya rungumeta cikin jinin, jikinsa na tsuma muryasa tana sarkewa ya furta"Ni...sha..ciki..na.. sai..da.. ya..zube."cikin fitar haiyaci tace"Dr kayi hakuri ni kaina da nasan lemon da my dear ta bani haka zata faru wlh bazan shaba.
akidime! ya Mike da ita ajikinsa" kina nufin lemon da kika shane..? amma ina ta suma bata motsi aguje ya fito da ita ya nufi gurin kwalin drinks din, yana kiran zee acikin tsawa da daga murya ya dauki sauran drinks din daide lokacin zee ta iso gabansu ganin Nisha cikin jini arikice tayi kanta tana sakin kuka atsawace Sardauna yace"karki kuskura ki tabata."

kallo daya zeey tama Sardauna jikinta ya dauki b'ari tsoronsa ya shigeta.....................✍🏻

Afuwa da rashin Editing mai kyau😢

*💖💖👩🏻‍🦱ZEE BABY👩🏻‍🦱💖💖*

MALLAKAR UMMU FAREESA NE

*DAN ALLAH KARKU FITARMUN DA BOOK WAJE*

*Book 2 👉🏻11*

..."Ashe Zainab zaki iya kissan kai ashe ba kaunata kike ba gudan jinina zaki kashe mun wato shiyasa kika ce bari ki kawo mata lemo dan kirabani da abin da nafi so meyasa zaki mun haka dan kinsa ina sonki bazan iya rabu dake ba zaki sawa Aisha maganin zubar da ciki me ta miki ko ni me na miki.

Arikice zee ta dago ta kalleshi jikinta na rawa ta fashe da kuka ta nufo gunsa"Yayana wanene ya cema maka zan iya kashe ko da saurone bare dan mutum waye yake kokarin rabani da kai da kuma yar uwata Yayana kar ka manta nayi Alkawalin mutikar ka juyamun baya arayuwa wlh sai na kashe kaina dan bazan iya rayuwa babu kai, ta fada jikinta na tsuma ta nufi gunsa da gudu.

Sardauna hankalinsa ya rabu a biyu amma mugun haushin zee da yake ji bai bari ta isa gareshi ba ya fice da Nisha a hannunsa.

Zeey ta barke da kuka ta nufi gun Rabia cikin masifa da gudun bala'i take kiranta.
Akofar dakinta sukayi karo.

Ta sharara mata mari ta damki wuyanta tana wuci. Arikice Rabia tace"me namiki dan Allah karki ilatani."zeey ranta ya gama bace
Tace"uban wanene ya sama Nisha maganin zubar da ciki mijina yake zargina ke daya ce agidan yar aiki kuma kinsan ita baza sha abinda zai mata ilaba ki fadamun ubanwa yasaki ta karasa maganar idanunta na fitar da jini dan ta gama zuwa karshan bacin rai.

Wasu irin bakaken kunamu ne ahannunta sunfi guda goma.
Rabia ta gama tsorata da, zee jikinta mugun kerrrma ya keyi bakinta na rawa tace"wlh Allah ban saniba ba ni bace ba Abu daya na sani jiya wata mata...daga wannan bata sake magana ba zeey taga ta fadi bata motsi jikin zeey ya dauki rawa da gudu ta shiga kitchen ta dauko ruwa ta zuba mata ta farka,tana zaro idanu.
Zeey tace"wata mata? " wlh ban saniba kawai kame kame ne.
Shakuta zeey tayi suka fito ta hankadata parlo.
"Wlh yau sai kin fadi dalilinki na zuba mata maganin zubar da ciki kike neman rabani da rayuwata.

Ta haye saman bene da gudu ta, dauko hijabi ta fito amma sama da k'asa babu Rabia ba dalilinta.

Ciki ta koma ta dauko key daya acikin motocin Sardauna ta nufi rumfar ajiye motoci ta shiga daya ta fizgeta tin karfi take horn.
Megadi yazo ya bude mata kofa ta fice aguje tana rusar kuka ta nufi hospital.

Lokacin da ta isa hospital Sardauna ne da kansa yake ba Nisha temakon gagawa cikin ikon Allah ta farfado sai barci take cikin ya gama zubewa bayan ta zubar da jini dayawa saidai Sardauna ya kara mata jini cikin sa'a akwai irin nata Sardauna kuka yake yana jin ciwon zubewar cikin yana mugun jin haushin zeey dan yayi niyar sai ya bata mata rai fiye da tunaninta sai ya ajiye sonta gefe ya hukuntata.

Zeey tsaye take akofor tana bugawa yana rungume da Nisha ya janye jikinsa ya Mike ya nufo kofar ya bude, zeey yaga tsaye idanunta jajur.
Sardauna ya had'e face yace"lfy malama..?"fashe masa nayi da kuka na fada jikinsa na rungumeshi"Yayana ina sonka kar ka gujeni karka doramin laifin da ba nawa ba wlh bani bace ba mai aikin gidan muce na tsare ta yanzu wlh har dukanta nayi ta fadamun gaskiya yanzu haka ta gudu bata gidan My Sardauna ina sonka karka tsaneni.

Sardauna kasa magana yayi bai kuma tureta daga jakinsa ba idanunsa alumshe yana sauke ajiyar zuciya, wani Abu ya cizo sa ya hankade zeey "karya kikeyi kece baki sona, dan haka nima zanyi nesa dake zan fita rayuwarki tunda baki sona kika sakawa matata maganin zubar da ciki na auna lemon na gani Kenan ke bazaki haihu daniba zainab kinsan ina sonki bazan iya ilataki ba shiyasa kika zubar mun da cikina ya fada yana barin gurin ya koma gun Nisha ya zauna.

zeey ta zube nan k'asa tana rusar kuka mai taba zuciya.
"Yayana zan mutu wlh zan mutu bazan iya jure rashin ka ba, wlh bani bace ba don Allah kamun rai karka rabu dani wlh zan kashe kaina mutikar ka juyamun baya Yayana meyasa kasaka mun dafin sonka azuciyata Wanda yakai matakin karshe kasan bazan iya rayuwa babu kaiba an fadama banajin ciwon mutuwar my Ahkhuya na ne wlh inajin zafin mutuwar sa fiye da tunanin ka kawai mugun sonka ne yake ragemun zafin mutuwarsa tun ranar da ka kusanceni a Saudiya Allah ya jarabeni da tsananin kaunarka amma saboda ka manta meye so har kake tunanin zan iya kashema gudan jinin ka kuma gudan jinin yar uwata Yayana shikenan na barma Allah komai kayi yanda ya dace na amashi kaddara ta fadi tana fitar da wani irin numfashi da sauri sauri idanunta na lumshewa dif numfashinta ya tsaya bata motsi.

arikice Sardauna ya taso"Ya Allah wai wannan wace irin masiface nake gani zainab babu damar kiyi Abu ba daidai ba atsawatar miki sai suma.
Ciccibarta yayi ya bude kofar ya fice ya nufi wani special room da ita ya kwantar da ita saman gado ya dauko ruwa a fridge ya kurbi kadan ya hau gadon ya shigar da ita jikinsa sosai ya tallabo kanta ya dora bakinsa, ahancinta ya fesa mata ruwan da karfi.

ajiyar zuciya ta sauke ta bude idanunta ta ganta kirjin Sardauna ta kura masa idanu kallon da ya matane yasa ta sada kanta k'asa ta cusa kanta kirjinsa tana zubar da hawaye ga wani irin sanyi da takeji zazzabi ya rufeta.

matseta yayi sosai yanajin hucin zafin zazzabi jikinta na ratsashi, ajiyar zuciya yake ya kankameta sosai yana shafa laulausan gashin kanta da ya zubo ya rufe mata fuskarta yana tatara mata gefe daya,ya janyeta jikinsa makaleshi tayi tana rawar sanyi.
Rankwafa wa yayi bakinsa saman kunnanta yana shafa fuskarta "ki sakeni zan hada miki magani bana son zazzabin jikinki ya kara fadar maganar cikin wani yanayi na shauki.
Sakinsa tayi tana nishi.
Ya mike ya sabka ya hada alluran ya shigar da ita jikinsa cikin mugunta ya tsira mata.

hadiye kukan ta tayi ta shige jikinsa sosai ahankali ta furta"Yayana ina sonka bazan iya rayuwa babu kaiba kamun adalci kar ka rabu dani pls Sardauna."
Makaleta yayi yana wani irin numfashi jiyake kamar ana kara masa sonta da kaunarta sam bazai iya rayuwa babu zainab ba.
k'asan makoshi yayi magana yada bazata jiba ya tura kansa k'asan wuyanta yana jujuya kansa"My Abulena kin gama da rayuwata sonki yamun mugun kamu bazan iya cutar dake ba gashi kin kashe rai amma na,saka miki idanu na kasa fadawa kowa saboda banaso amuzanta mun ke sorry amma dole zan hukun taki.

Zeey kuwa jinta jikin Sardauna ga, Alluran da ya, mata bacci ya dauketa,
sai saukar numfashinta Sardauna yaji.

Janyeta yayi ya sabka ya dauki waya ya kira ghaisha, ya fada mata komai amma baice zeey ba ce ta zubar yace itama bata da lfy zazzabi take ghaisha tazo ta kwana da ita shi jinyar Nisha yake.

Bajimawa kuwa su ghaisha sukazo duk dare yayi har ummi gani zeey ba wani buguwa tayi ba suka koma ghaisha kade ta tsaya gurin zeey sai daddah tace ita zata kula da Nisha amma Sardauna ya tsaya su kwana tare.

Sai can tsakiyar dare Nisha ta farka,Sardauna ya kaita toilet ya mata wanka da ruwan gumi ya canza mata kayan da yaje gida ya kawo, ya bata abunci taci da maguguna ya fada mata gaskiya cikin ya zube haka tayi ta kuka tana cewe zeey ta cuceta amma ta yafe mata dan Allah Sardauna karda ya taba zee ko ya mata wani Abun sai daket ya samu ta koma bacci shima ya kwanta.
Ashe abinda basu saniba Daddah ba bacci take ba idanunta biyu ta jisu tayi mamakin ya akayi zeey ta zubarwa da Aisha cikinta, ahaka har bacci ya dauketa.

Washe gari bayan Sardauna yaje gidansa ya dawo lokacin zeey taji sauki zazzabin Sardauna ya sallamesu amma basu tafi ba ita da ghaisha suna gurin Nisha wacce ta sake da zeey ta nuna babu wani Abu itace ke Jan zeey da hira tana nuna mata karta bari yan gida su sani taji dadin hakan damuwarta daya Sardauna baya kulata.

Da misalin karfe goma shadaya na safe dakin cike yake da yan uwa suna ta zuwa dubiyar Nisha kowa yaji zafin fitar cikin dan sunyi mutikar mamaki cikin wata biyar ya zube kai tsaye batare da tayi doguwar jin yaba ko ya nemi kasheta.
Zeey baby ce zauna kusan Nisha tana rike da hannunta zeey "my dear wlh inajin ciwon wannan zubewar cikin fiye da tunaninki.
Sardauna ne ya shigo da sallama karaf akunnensa idanu suka hada da zeey ya zafga mata harara.
kanta ta kauda zuciyara na mata daci kamar daga sama sukaji murya daddah tace"tsaninku da Allah acikin ku biyu waye ya zuba maganin zubar da ciki alemo da gangan.
Arikice suke kallonta gabaki dayan dakin suka hada baki wajan furta"innalillahi wainnahilahir Rajiun!!
Daddah tace"wlh dole mutum ya zuba maganin tsakanin Aisha da Zainab.

End of Chapter 109Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next