Soyayyanovels
Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel
By Real Ladingo
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel

Zee Baby Part One And Two Complete Hausa Novel

Author: Real Ladingo
Chapter 85 of 130
About 7 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,685 words Chapter 2 1,656 words Chapter 3 1,426 words Chapter 4 1,678 words Chapter 5 1,658 words Chapter 6 1,660 words Chapter 7 1,540 words Chapter 8 1,682 words Chapter 9 1,488 words Chapter 10 1,684 words Chapter 11 1,352 words Chapter 12 1,481 words Chapter 13 1,490 words Chapter 14 1,658 words Chapter 15 1,664 words Chapter 16 1,361 words Chapter 17 1,446 words Chapter 18 1,594 words Chapter 19 1,440 words Chapter 20 1,595 words Chapter 21 862 words Chapter 22 1,587 words Chapter 23 936 words Chapter 24 1,007 words Chapter 25 1,624 words Chapter 26 548 words Chapter 27 1,952 words Chapter 28 1,599 words Chapter 29 1,281 words Chapter 30 1,465 words Chapter 31 1,117 words Chapter 32 1,166 words Chapter 33 1,496 words Chapter 34 1,495 words Chapter 35 1,191 words Chapter 36 1,505 words Chapter 37 1,475 words Chapter 38 1,632 words Chapter 39 970 words Chapter 40 1,565 words Chapter 41 1,516 words Chapter 42 1,101 words Chapter 43 1,209 words Chapter 44 1,672 words Chapter 45 1,520 words Chapter 46 1,612 words Chapter 47 1,543 words Chapter 48 1,654 words Chapter 49 1,192 words Chapter 50 1,699 words Chapter 51 1,476 words Chapter 52 1,648 words Chapter 53 1,617 words Chapter 54 1,636 words Chapter 55 1,432 words Chapter 56 1,581 words Chapter 57 1,631 words Chapter 58 1,206 words Chapter 59 1,393 words Chapter 60 1,279 words Chapter 61 1,241 words Chapter 62 1,639 words Chapter 63 1,506 words Chapter 64 1,619 words Chapter 65 1,517 words Chapter 66 1,475 words Chapter 67 1,600 words Chapter 68 1,589 words Chapter 69 1,675 words Chapter 70 1,603 words Chapter 71 1,692 words Chapter 72 1,515 words Chapter 73 1,429 words Chapter 74 1,552 words Chapter 75 1,635 words Chapter 76 1,554 words Chapter 77 1,590 words Chapter 78 1,500 words Chapter 79 1,567 words Chapter 80 1,518 words Chapter 81 1,656 words Chapter 82 1,634 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,643 words Chapter 85 Reading now Chapter 86 1,628 words Chapter 87 1,694 words Chapter 88 1,601 words Chapter 89 1,576 words Chapter 90 1,659 words Chapter 91 1,655 words Chapter 92 1,536 words Chapter 93 1,559 words Chapter 94 1,457 words Chapter 95 1,655 words Chapter 96 1,677 words Chapter 97 1,557 words Chapter 98 1,692 words Chapter 99 1,558 words Chapter 100 1,525 words Chapter 101 1,533 words Chapter 102 1,651 words Chapter 103 1,695 words Chapter 104 1,597 words Chapter 105 1,580 words Chapter 106 1,627 words Chapter 107 1,681 words Chapter 108 1,700 words Chapter 109 1,636 words Chapter 110 1,621 words Chapter 111 1,471 words Chapter 112 1,637 words Chapter 113 1,685 words Chapter 114 1,674 words Chapter 115 1,638 words Chapter 116 1,629 words Chapter 117 1,674 words Chapter 118 1,513 words Chapter 119 1,674 words Chapter 120 1,653 words Chapter 121 1,623 words Chapter 122 1,605 words Chapter 123 1,584 words Chapter 124 1,634 words Chapter 125 1,675 words Chapter 126 1,537 words Chapter 127 1,639 words Chapter 128 1,693 words Chapter 129 1,496 words Chapter 130 1,209 words

yasa musu albarka ya zauna can ciki kuwa kawu Saminu ne ya nemawa dansa Faisal auran zainab Daddy ya bashi Ana take kawu saminu ya ciro dubu dari biyu kash ya bayar Sadaki da huhun goransa guda uku ya ajiye daddy ya amshi kudin ya waribdubu Hamsin ya bashi sauran yace" albarkar aure mukeso ba kudiba Dole Saminu ya amshi sauran sadakin yabawa Nuhu ya rike maitmran karfe yaji dadin hakan nan babban liman da kansa da sauran malamai da alwalin ango da na amarya aka daura Auran Faisal da zainab Akan sadaki nera dubu Hamsin nan mai sanarwa ya fara cewa" jama'a ku amsa fatiha an daura auran Faisal Da Zainabu Abu mai tagwayen suna Akan Sadaki nera dubu hamsin lakadan ba ajalan ba tazama shi yazama ita karaf akunen Sardauna saboda lasifikace ake maganar da ita zuwat ya Mike tsaye jikinsa yana rawa liman suka musu Addu'ar Allah yabasu zaman lafiya daddy yasake bara addu'a akayi musu nan aka shiga Rabo goro da kudi huhun guda daddy yaba liman da kudi nera dubu Hamsin jama'a sai albarka suke samusu saida mutane suka rarage su daddy suka fito Sardauna na hango su daddy ya nufo gunsu daddy ya hangoshi ya tsaya yana murmushi" masha Allah Dr Sardauna ango dariya sukayi yana isowa ya fada jikin daddy ya Saki kuka tamkar karamin yaro jikinsa sai rawa yake daddy yace" haba Faisal jarumin jarumai ya kuma yau kake kuka kaida zakayi farin ciki momy Allah yayi tazama mallakinka fatana ka kulamun da ita ka rikemun ita Amana Allah ya dubomu ya bata lafiya kwana biyu abun nata duk ya rikice amma ba komai mun barma Allah ikonsa yi shiru Dr namu wani kukan ya Saki ya rungume daddy gam Dan ya tunamasa da mahbeer" daddy meyasa kuka auramun matar yayana ni danace zan zabar mata miji nagari murmushi daddy yayi yana buga bayansa "kaikuma kayi yaya da sonta kabar maganar aduk duniya ayanzu babu Wanda zan iyabama zainaba kulawa ta musamman ba kosawa idan ba kaiba Nuhu yazo yana murmushi yace"ai zainab dakai tafi cancanta Saminu yace" yanzu sai mutafi gida Faisal ka ajiye hankalinka D'ana mairan karfe yace ja'iri yanaso kissa murmushi Nuhu yayi ya kama hannusa Kawu Saminu yarakasu har gun motar Sardauna ya bude ya shiga Saminu yace"my son kayi tuki cikin nutsuwa kaji kansa

ya d'aga Nuhu ya rufe masa kofa Sardauna yayima motar key yaja ya tafi daddy sai murmushi yakeyi suka shiga mota suka tafi. acikin Nutsuwa Sardauna yake driving yarasa wani irin yanayi yake ciki farin ciki ko akasin haka sigari ya dauka ya kunna ya fara bata hayaki baki da hanci kai tsaye hospital ya nufa saboda yau bai lekaba akwai yaron da zai duba jiya da tunaninsa ya kwana, can gida kuwa bayan an dawo daga sallahr juma'ah suka Mike kowa yaje yayi sallah, zaune suke saman dinning su maijidda sai kwasar gara ake ummi tayi tayi da zee taci abunci taki ta kafa, musu kuka sai babynta yazo yau bata ganshi ba ko ya mutune duk ta fitinesu. Neesha tace" kiyi hakuri zaizo ai ghaisha tace" momy zo ga wayata ki kirayi mijinki da kanki nasan zuwa yanzu an daura auran da Sauri Neesha ta kalli gashi dariya zee tayi ta Mike taje gun ghaisha ta zauna ta amshi wayar su daddy ne suka shigo da sallama Hauwa ta Mike"Dan uwa ya da fatan an daura murmushi daddy yayi Nuhu ya bata goro farare tas ba kadan ba cikin farin ciki Hauwa tace Alhmdllh Saminu yace"Alhmdllh tazama matarsa fatanmu Allah yabata lafiya cikin farin ciki suka gabaki dayansu suka ajiye spoons sukace amin suka Mike zainab ta rungume zee maijidda tace Allah ya baki lafiya maryama tace" zainab Amaryar Sardauna Nisha uwar gida ghaisha farin ciki ya hanata magana Nisha har wata zufa take keto mata tayi ta maza ta goge tana murmushi ta nufi gun zee ta rungumeta" Alhmdllh my dear zan rikeki Amana Allah yabaki lafiya yau kin zama matar babynki ko? ta fadi tana murmushi kallonta zee tayi tana murmushi " ke ni matar mahbeer ce ba babyna ba maijidda tace" ai an daura muku aure dashi jikinta ta janye ta nufi gun daddy tana dariya" daddy wai babyna munyi aure yo mahbeer din fa hannunta ya kama idanunsa ya ciko da kwalla yace" momy kinci abunci dariya tayi" daddy wlh bazanci ba sai my babyna yazo yabani abaki wayarsa ya ciro daga aljihu ya lalubo number Sardauna bugo biyu ya d'aga yabawa zainab" amshi momy yi masa magana maza yazo ya baki abunci amsa tayi ta Kara akunne ashagwab'e tace"my babyna kazo kabani abunci nasha magani tun d'azu nake kuka ko me yace mata tayi dariya tana tsalle tace"💃🏻yeeee mijina kazo yanzu wayar ta bekama daddy tana ta murmushi ta nufi bedroom da gudu da idanu suka bita cike da tausayinta su daddy kan dining suka nufa ghaisha ta bisu ta hada musu abunci ummi yawan surutun zainab ya fara damunta dannewa takeyi sai take ganin yar tata kamar ta haukacene Neesha fakar idanun motane tayi tabi bayan zainab bedroom tana shiga zee na fitowa da ledar magani ahannunta shiyasa sukayi Karo Nisha ta mayar da ita ciki ta rufo kofar "my dear don Allah ki saurareni. zee ta bita da kallo tace" meye ne ni gun babyna zani riketa Nisha tayi ta fashe da kuka zee ta kalleta............... ✍🏻

*ZEE BABY*

*👉🏻47*

....waye ya bugeki kike kuka ki tafi gidanku mana ina mijinki ko kema ya mutu ni sakeni na tafi gun babyna mijina yace yanzu zaizo Kara rungumeta Neesha tayi "my dear nifa yar uwarki ce Dan Allah karki hada miji dani dariya zee tayi ta banbareta da karfi tana hararanta"yo ai bansan mijinki ba.waye? "Sardauna nane babynki ina sonsa dayawa please da kin dawo haiyacinki karki zauna dashi kinji yar uwata?" Ni baruwa daddy yace mahbeer ya mutu yanzu my baby ne mijina ina sonshi hararata Nisha tayi"hmmm ai nasan son bakya daide ne da kin warke zaki tsaneshi Dan haka banida damuwa tunda baya sonki dariya zee" bawani yana sona wai ina son yake ne wlh ni ban sanshi ba Nisha tace" to idan kinaso kisanshi kibar kula babynki kibar bari yana baki abunci ko magani sai na gwada miki so amma idan kina kula babynki bazaki San so ba fauu kakeji ta dauke Neesha da Mari ta damke mata wuya" my babyn nawa zakice nabar kulawa kuji yar mutuwa Nisha ta tsorata kokarin amshe kanta takeyi" tsaya zee kiji yi hakuri nufina kirika kulashi sakeni kije gunsa yana jiranki hankada ta tayi tana hararata" shegiya yar mutuwa haka kawai zakice nabar my babyna naki bana barinsa so din yaci mutuwar uwasa kuji shegiya ta fadi tana ficewa da gudu mik'ewa Neesha tayi Dan taji buguwar fashewa tayi da kuka" wayyo nashiga uku

na lalace ya zanyi da raina Allah kabata lfy tabarmun mijina Allah kabani juriya da hakuri har su rabu Allah yasa karta tonamun asiri Dan ba hankaliba gareta ayanzu zata iya fada musu bathroom ta shiga ta wanko fuskarta ta gyrata ta Saki ranta ta fito zee ta hango zaune kusan zainab tana rike da mahbeer D'an zainab tana masa wasa maijidda ta girgiza dan tana mugun tausayin zainab zee ta kalli ummi Raiyan tace" ummi kalli mahbeer Dina suke cewa ya, mutu murmushi ummi tayi" baby kirabu dasu ai gashinan ghaisha murmushi tayi" momy wannan ai d'ankine fah fuska ta kwakwab'e ta b'are baki ta fara kuka ghaisha tace"oh Allah to yi hakuri mijinki ne. shikenan ko? Kai ta daga tana dariya. Nisha ce ta iso ta zauna akusanta" my dear kinga mahbeer dinki ko? " ni baruwana dake yanzu kikace nabar.. baki Nisha ta rufe mata tana murmushi " my dear ba fah nace kibar mahbeer gashinan ahannunki umma Hauwa tace"sakar mata baki tana sakinta ta Mike da mahbeer ahannunta ta isa gurin ghaisha ta zauna tana hararan Nisha tace" haka kawai sai kice nabar my baby ki nuna mun so. idanu suka zubawa zeey cike da tausayi Dan zatonsu mahbeer karami take nufi babu wanda ya gano.ghaisha tace" yi hakuri bazaki bar babynki ba. Sardauna ya shigo da sallama Maijidda ta Mike tana cewa"Dan kanina fuska ya game mata" ni wlh kunya nakeji idan kin kirani kaninki Dan Allah kibar fadin haka. rungumeshi tayi"aikuwa yaro sai hakuri shekara biyu na baka murmushi yayi ya tsinketa awuya ba shirui ta sakeshi" mugu kai sai mugunta bani gorona to? baki ya tab'e baiyi magana ba suka iso gunsu ghaisha yayi jimulla ya gaishesu zeey ta kallesa tana kwakwabe fuska " my babyna ina ta jiranka murmushi ya sakar mata ta Mike ta kaiwa zainab

End of Chapter 85Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next