Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
A wani irin gajiye ya shiga bedroom ɗinshi yana faman lumshe blue eyes dinshi saboda baccin da yake ji,yana ƙarasawa ciki yasanya hannayenshi tare da ɗebe rigar jikin shi gaba ɗaya,ya azata asaman laundry basket dinshi,zame belt ɗin wandonshi yayi sannan ya zame shi daga jikinshi ya ajiye shi asaman rigar,ya rage daga shi sai shorts ajikinshi,
Komawa yayi tare da hayewa saman royal bed dinshi ya kwanta don ya ɗan runtsa,sosai ya miƙe saman gadon yana faman sauke ajiyar zuciya har bacci yayi awon gaba dashi,almost 6 mins sai ga sehrish ta fito daga cikin toilet ɗinshi,tunkarar gadon tayi saboda ta ɗauki mayafinta sai da ta kusa dab da gadon sannan idonta suka hango mata Boss Man ɗin nata kwance yana bacci,wani irin bugu taji zuciyarta tayi mata har sai da taɗan ja da baya tana kallonshi,hannu tasa tare da ɗan murza idanunta donta tabbatarwa idonta abunda take gani wai ko gizau ne,amma zahiran taƙara shaida cewa sgr ne da kanshi ya dawo,
Hankali kwance yake baccin shi,ya zagayo da left hand dinshi ta saman sumar kanshi,yayin da hannun damanshi ke asaman shafaffen cikinshi,
Ji tayi bazata juri kallon surar jikinshi ahaka ba saboda gudun jefa kanta cikin matsala,don ba ƙaramin fisgarta yake yi ba,kamar irin magnet din nan,
Har ta kama hanyar fita daga bedroom din nashi cikin sauri taji jelar gashinta na gogar hannunta,tsayawa tayi Cak tunawa da Mayafinta data ajiye asaman gadon nashi kafin tashiga gyara mashi toilet É—inshi,a hanzarce ta juya tana kallon inda ta ajiye mayafin,waro ido waje tayi cike da fargaba ganin yarda sgr ya mamaye mayafin nata gaba É—aya,ya kwanta asaman shi,tabÉ—ijan can
Tunani tashiga yi kodai ta tafi tabar mashi mayafin tunda ba iya É—aga shi zatayi ba,wata zuciyar kuma tace,idan ya farka ya samu mayafin naki asaman gadonshi bakya tunanin cewa zai iya zargin wani abu akanki?dole ya tuhume ki akan miya kawo mayafinki saman shimfiÉ—arshi,haka in kika fita ba mayafin wani ya ganki kin fito daga part dinshi haka fa,kiyi tunani sehrish barin mayafin risky ne,haka zalika daukarshi ma zai iya zama risky,
Runtse idanunta tayi tamkar ta fasa ihu saboda tsabar takaici,taji haushin cire mayafinta da tayi tun farko da bata jefa kanta cikin matsala ba,
Nan fa tashiga tunanin yarda za'ae ta dauke mayafinta batare da Sgr ya farka daga baccin shi ba,
cikin sanÉ—a sehrish ta soma tafiya a hankali tana tunkararshi a tsorace batare da sautin takon tafiyarta na fita ba,
Sai da tazo dai dai kusa dashi sannan tashiga cizon yatsa tana tunanin wai ma taya zata janyo mayafin daga jikinshi,Sehrish da kasada,
Hannu tasa tare da ɗan kamo mayafin daya leƙo daga bayanshi tana janshi a hankali don ya sulalo daga bayanshi,amma ko motsi wannan baiyi ba don ba ƙaramar danna sgr yayi mashi ba,gaba ɗaya nauyin jikinshi na akan mayafin taya zata iya janye shi!?
tun tana jan mayafin a hankali yana turjewa har takai ga hasala tashiga janshi da ɗan ƙarfi har sai da sehrish tashiga fitar da wani irin gumi a fuskarta,sakin mayafin tayi tana faman huci,duk da haka bata daddaraba,sai tasa hannu tare da dafa mattress ɗin ta haye saman gadon kaɗan daga gefenshi,hannu takai zata ruƙo mayafin karaf idonta suka sauka akan farar fatar ƙirjinshi,mayar da idonta tayi akan damtsen hannunshi,haryanzu akwai sauran zanen nan nashi na tattoo bai ƙarasa gogewa ba gaba ɗaya,tun farkon zuwanshi 9ja tare da zanen ajikinshi ya dawo kamar tambari ne na mukaminshi ba ƙaramin kyau yayi mashi ba,
Gaba daya sehrish ta shagala da kallon surar jikinshi,kafin tayi wani aune,Sgr yayi wani irin kwakkwaran juyi zai gyara kwanciyarshi,aikuwa gaba ɗaya ya haɗa da sehrish yayi juyin tare da sanya hannunshi yayi hugging ɗinta tighly a faffaɗan kirjinshi,duk a tunaninshi pillow ne ya rungumo hakanne yasa ya matseta sosai a ƙirjinshi kamar yarda ya saba rungume pillow in zaiyi bacci wani sa'in,tashin hankali da ba'a sama shi date,
Tabɗijancan,ƙiris ya rage sehrish ta saki fitsari saboda tsabar tsoran da taji,hankalinta yayi matuƙar tashi,saboda tasan mai zai biyo ba in sgr ya farka yaganta manne ajikinshi,yasan na jiya taimakon shi tayi gudun karya faɗi,na yau kuma mai zai kira shi!?meya kawota saman gadonshi da har ta faɗa jikinshi!?
yarda ya matseta a ƙirjinshi ko kwakkwaran motsi sehrish ba ta iya yi,ba ƙaramin ruƙo yayi mata ba,tunkan ya farka taga irin hukuncin da zai yi mata harta fara zubar da hawaye,kai tsaye kuma hawayen suke shafar fatar jikinshi,
sai faman shessheƙar kuka takeyi ƙasa ƙasa yayin da la66anta ke gogar fatar breast dinshi,gaba ɗaya Wannan jan bakin data shafa ya koma a fatarshi,sosai zanen lips ɗin sehrish ya fito raɗau tare da kalar jan bakinta maroon colour,duk bata lura da hakan ba,saboda la66an nata amanne suke a wurin,
Tana cikin wannan yanayin tajiyo takun tafiyar mutum a falonsa alamar ana tunkaro bedroom ɗinshi,hakan ba ƙaramin firgita sehrish yayi ba,nan take tashiga haɗiyar yawu a tsananin tsorace,
Muryar Abbansu tajiyo yana cewa"Wai har yanzu rafayet bai dawo bane?inaso naji ko sunyi waya da Mommynshi ne game da zuwanta Nigeria,'
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,"sehrish ce ta ambaci hakan acikin zuciyarta,"Shikenan na mutu wayyo Allah na,ya Allah ka kawomun ɗauki,daga wannan sai wannan......'bata ƙarasa zancen zucin nata ba tajiyo muryar Marshal Omar yana bashi amsa da cewa"Abba ashe muna da manyan baƙi cikin watan nan,don munyi waya da goggon katsina ma ta sanar dani cewa mu shirya ma zuwanta don in ta tashi zuwan bazata zata yi kuma ba zata tafi ba har sai taga An shafa fatihar kowannan mu.....' ya ƙarasa maganar da dariya a fuskarshi,
Suna tafiya suna nufar bedroom É—in sgr yayin da suke fira a tsakaninsu,
Abban nasu yace"Albishirinka,"
Cike da zumuÉ—i Omar yace"Goro,"
"Fari ko ja"? Abban nasu ya tambaya fuskarshi É—auke da murmushi,
Omar yace"Fari,"
ƙayataccen murmushi Abban nasu ya saki kafin yace"Uncle ɗinku Abusufyan shima yana nan tafe insha Allah,sannan Auntynku azeema tana nan tafe,uwa uba kuma Ammynku itama tana nan tafe,don haka ku shirya don ta sanar dani cewa muddin tazo sai an ɗaura auran kowannanku,da alama zata zo tayi yaƙi da tazuranci ne acikin gidan nan.....'ƙarasa maganar yayi muryarshi ɗauke da dariya,shima Omar dariyar yayi yana girgiza kai yace"Abba Allah yaso ni,ina da wadda nakeso,don haka ni bani da matsalar komai wlh,Alhamdulillah Allah ya kawota Lafiya musha biki,'
Cike da mamaki Abban nasu yace"wai dagaske Omar kana da wadda kakeso?hakan na nufin kayi budurwa baka sanar dani ba"?
É—aga kai Omar yayi alamar eh,wani irin farin cikine ya cika abban nasu har ya gaza magana sai faman sakin murmushi yake yi yana cewa"Ikon Allah,"
A ƙopar shiga bedroom ɗin sgr suka tsaya suna cigaba da tattaunawa cike da nishaɗi atsakaninsu,
Saboda tsabar tashin hankali har wani zazza6i ya lullu6e sehrish tuni temperature É—in jikinta yayi wani irin zafi,zuciyarta har wani bugu takeyi daram!daram!!fargabarta karsu shigo su same su a wannan yanayin ita da sgr,
Hayaniyar da suke yi ce,ta fara disturbing É—in baccin nashi,hakan yasa ya fara motsi alamar zai farka,waro ido waje sehrish tayi cike da fargaba jin alamar zai farka,
Hannunshi ya janye daga ruƙon da yayi ma sehrish,hakan ne ya bata damar kufcewa daga jikinshi,kamar walƙiya haka ta mirgina tare da faɗawa ƙasan gadon,sam bata ji zafin buguwar da tayi ba,tana faɗowar nan ta yunkura tare da miƙewa tayi wuff ta faɗa bayan labulan ɗakin shi,
Shigarta ke da wuya,Abba da marshal suka shigo cikin É—akin nashi atare bakunansu É—auke da sallama,
A hankali sgr ya soma buɗe idanunshi dake cike da bacci ga wata irin kasala data mamaye shi don baccin bai ishe saba,daƙyar ya iya sa hannunshi tare da dafa mattress ɗin ya tashi daga zaune tare da jingina back ɗinsa asaman pillow yana kallon Abban nasu tare da Omar sai faman lumshe ido yake yi,
Zama Abban yayi daga gefen gadon nashi yana kallon fuskar kyakkywan yaron nashi yace"Rafayet bacci kuma a irin wannan lokacin?ko baka ga time bane?
Sai lokacin sgr yakai idonshi akan diamond clock ɗin dake manne a bangon ɗakinshi ƙarfe 6:30 na yamma,
lumshe idonshi yayi kafin ya waresu akan Abban nasu yace"Abba bansan time É—in da baccin ya É—auke ni ba"
jinjina kai abban nasu yayi
kafin yayi yunƙurin cewa wani abu karaf idonshi suka sauka akan jan bakin sehrish dake zane asaman breast ɗinshi,
waro ido waje abban nasu yayi tare da cewa"Kai me nake gani haka kodai idona ne"?yarda yayi maganar a ruɗe yasa marshal Omar ɗan matsowa daga tsayen da yake ya russina yana ƙare ma Ƙirjinshi kallo,cike da mamaki Omar yace"ba shakka Abba,ba idonka bane wannan alamar sumbata ce,ga zanen la66an mace nan raɗau asaman fatar kirjinshi,
Gaba daya sun gama confusing É—in Sgr,sam bai gane inda zancen nasu ya dosa ba,"
Hankali atashe Abbansu yace"Rafayet tell me the truth!wa kayi feeding haka har ta goga maka jan baki asaman breast dinka!!!"
Saboda tsabar kiÉ—ima tuni jikin sehrish ya soma tsastsafo da wata irin zufa,duk da sanyin ac dake gauraye da ko'ina,
Ganin yarda sgr ya dabarbarce kamar bai gane kan me suke magana ba,hakan yasa omar ƙarasawa gaban dressing mirror ɗinshi,yasa hannu tare da ɗauko ƙaramin madubin dake ajiye asaman shi,
Ƙarasowa yayi wurinshi tare da saita mashi madubin yarda zai gani da kyau,
Ware manyan idanunshi yayi yana kallon zanen la66an dake asaman chest É—inshi cike da tsananin mamakin a ina ya same shi.......
*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃
*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*
*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*
*LOCATION KANO*
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.