Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Koda Sgr ya ƙaraso wurinsu, a tsakiyar inda kowannansu yake,sai ya sauko da ita,Kamar dama jira takeyi ya sauke ta ƙasa da gudu ta kama hanya zata bar wurin,aikuwa a zafafe ya damƙo waist ɗinta da ƙarfi ya maido ta jikinshi,
Har Abbanshi na cewa"ka bi ta a hankali don Allah,ta tsorata sosai,bansan meke damunta bane, ko Æ´an uwan nata ne ke batasan gani "abusufyan kuwa runtse idanunshi yayi,har cikin ranshi yake jin soyayyar yaran,
Cikin shessheƙar kuka take faɗin"Na bani,na shiga uku!Na lalace!dan Allah ku rabu dani!ku barni na tafi, banason ganinsu!ni ba ƴan uwana bane!ciwon kai suke sani idan ina kallonsu,raɗaɗi nake ji acikin zuciyata kamar ana ƙonata...."
Hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba jin abunda sehrish ke cewa,yanayin yadda take maganar zai tabbatar maka da cewar da gaske take tana jin duk wani abu da ta faɗi,musamman Sgr daya ruƙota,yaji jikinta da wani irin Zafi,har shi kanshi zafin na shafar jikinshi,
Abusufyan ne yace"kuyi mata addu'a don Allah,zai iya yiyuwa akwai sihiri ajikinta,wani zai iya shiga tsakaninta da Æ´an uwanta saboda ni shaidane akan yadda suke son junansu!nagani da idona,basa rabuwa da junansu kullum suna manne da juna,banta6a ganin Æ´an uwa masu son junansu ba irin yaran nan,tun kafin su mallaki hankalinsu suke tsananin son junansu.....'
Cike da mamaki Abba yace"meyasa kake tunanin cewa akwai sihiri ajikinta?
kowa ya kasa kunne yana sauraronshi,
"In har da gaske sune ƴa'ƴana kamar yadda nake hasashe to tabbas an shiga tsakaninsu ne,saboda mutumin da suka taso awurinshi,nayi bincike akanshi,bama haka ba shi da kanshi ya rabani da bibiyar rayuwarsu da nake yi,kowa zaiyi mamakin taya nabar yaran rayuwarsu ta wulaƙanta batare dana taimaka ma rayuwarsu ba,ko kuma na sanar ma wani daga cikin dangina don a taimaki rayuwarsu,ba laifina bane tursasamun akayi........'
Kasa ƙarasa maganar yayi saboda hawayen da suka shiga kwaranyowa daga cikin idanunshi,
Abbas yace"Akwai sauran labari kenan, bari mu gyara zama don a idasa warware mana komai,"
ɗagowa yayi da idanunshi da suka yi jawur har sun dan fara kumbura ya kalli sgr tare da cewa"idan ba damuwa,inaso ka zauna tare da ita akusa dakai,saboda ka ruƙeta karta gudu,in yaso sai kayi mata addu'ar koda bata dawo hayyacinta ba,zataji sauƙin radaɗin ciwon kan da takeyi,
"Okey,"ya amsa tare da samun wuri ya xauna,asaman laps ɗinshi ya zaunar da Sehrish,sosai ya ruƙota jikinshi,tunda ta kwantar da kanta asaman wide chest ɗinshi,numfashinta ya fara daidaita,a hankali kuma zafin jikinta ya soma raguwa,saitin kunnanta yakai ƙaramin bakinshi yana karanta mata addu'o'i,bugun zuciyarta ne ya soma raguwa,jikinta kuma ya rage kermar nan da yake yi,
"Ina gwaggon take ne?naga bata fito ba inaso ayi komai agabanta tare da Dr haris kuma"abusufyan ne yayi maganar yana kallon Abban nasu
Fawan ne ya kuma miƙewa tare da cewa"Bari naje na kirasu,'
cike da zolaya jahan yace"Messenger,aikinka na kyau,"murmushi kawai yayi tare da wucewa ciki,ae yau ji yake kamar ya zuba ruwa ƙasa yasha don murna don kuwa ranshi ya gama bashi cewa su jahad din yan'uwansu ne.
Ba da jimawa ba,sae ga Gwaggon katsina ta fito har yanzu undin nan ne ajikinta Allah ma yasa irin dogon nan ne mai kauri,tana biye da bayan fawan tana dungurin keyarshi tana cewa"Shegen bisa,da kanshi kamar na tamola,baccin ma baza abar mutun yayi ba,matsalar mutun yazo gidan jikoki kenan duk subi su addabi rayuwarshi.....'
Muryar Abba ce ta katse ta da cewa"gwaggo ku samu wuri ku zauna,magana ce mai muhimmanci zamuyi,"
Har zata zauna idonta suka sauka karaf akan Sehrish dake zaune asaman laps É—in Sgr,hankali tashe tace"mun shiga uku!yanzu agabanku ake wannan aika-aikar amma babu wanda ya tanka?hosana ce ko jahad?wacece acikinsu?wlh bazan bari a lalatamun Æ´a'Æ´an Abusufyan É—ina ba,dasu zamu koma katsina ayau.......'
..da sauri Haris ya katseta da cewa"Dan Allah gwaggo kidaina wannan sambatun naki,bakiji abunda abba yace ba!magana mai mahimmanci za'ayi,ki samu wuri ki zauna kuma kiyi shiru,'
Wurga mashi harara tayi kafin ta wuce tare da samun wuri ta zauna,shima haris ya zauna agefenta,sai da suka xauna sannan ta lura da hosana da jahad dake zaune gefen hajiya azeema,
Da sauri ta mayar da idonta kan sehrish don taga wacece ita,ko dae idanunta ne suka fara samun matsala don taga kamar kamanninsu iri É—aya sak,
"Harisu,kana ganin abunda nake gani kuwa,wai yaran nan har nawa ne masu fuska iri É—aya"?
A dan ƙule haris yace"Eh,su uku ne!ko kinmanta su nawa ne,na faɗa maku Abu ta haifa!wannan ae cikon ƴar ukun tasu ce,'
"Oh to,yanzu nagane"ta fadi tana faman gyara zamanta,
Sae da kowa ya natsu sannan abusufyan ya kalli su hosana da jahad yace"Ya sunan mahaifiyarku ne?kuma waye mahaifinku"? Yayi masu tambayar ne don ya fara tabbatar da cewar sune É—in dai dagaske,
Har suna haɗa baki wurin cewa"Sunanta Zainab,amma anace mata abu ƴar buzuwa,sannan mahaifinmu kuma sunanshi Sayyadi.......'tunkan taƙarasa maganar kowanne daga cikinsu ya shiga sakin murmushi,jin sun ambaci dai dai da sunayen da abusufyan ya gama bada labari akansu,tunkan aje ko ina suka tabbatar da cewar sune dae ƴa'ƴan abusufyan ɗinsu,
"Ina mahaifiyarku take yanzu"?ya kuma tambayarsu,
Jahad tace"bamu son inda take ba,amma koma a ina take bata acikin hayyacinta,lokacin da tabarmu tasamu ta6in hankali,'
jiki asanyaye ta ƙarasa maganar,
"Yanzu zaki iya bamu labarin abubuwan da suka faru arayuwarku gaba daya,har izuwa lokacin da kuka rabu da junanku"?
É—aga mashi kai tayi alamar eh,
Kafin abusufyan ya ƙara cewa wani abu,Abba ya katse mashi hanzarinshi da cewa"Yakamata,ka fara sanar dasu game da alaƙar da take tsakaninka da mahaifiyarsu"
Jinjina kai abusufyan yayi kafin yace"zaku iya tunawa da mutumin daya ta6a zuwa wurinku lokacin kuna ƴan ƙanana,har ya ɗauke ku hoto a wayarshi?lokacin da zan tafi kuka dinga kuka kuna cewa na tafi daku baku son zama da mahaifinku"?
A razane hosana da jahad suke kallonshi yayin da suke ƙoƙarin tunawa da wannan lokacin......'
Murmushi abusufyan yayi tare da cewa"nasan ba zaku iya tunawa da wannan lokacin ba!,amma mun sha haÉ—uwa daku wani lokacin kuna ku kadae,wani lokacin kuma tare da mahaifiyarku........'
Batare da 6ata lokaci ba,abusufyan ya basu labarin rayuwarshi da abu a takaice yadda zasu fahimta,sai lokacin suka san asalin mahaifinsu da kuma kakansu baba buzu daya rasu,da kuma irin rayuwar da abu tayi tare da abusufyan kafin su rabu,ta auri ya sayyadi,sunsha kuka sosai,aransu suna jin ƙuncin abunda mahaifiyarsu tayi masu,ashe duk itace taja masu bala'en da suka fuskanta,
Kowa yayi shiru na wani lokaci suna sauraron kukan dasu hosana da jahad sukeyi gwanin ban tausai,banda sehrish wanda tayi lamo ajikin Sgr,duk wani abu da suke faÉ—i acikin kunnanta,amma bata É—ago ta kallesu ba,har yanzu dae bata dawo dai dai ba,
Daƙyar su Omar suka lallashe su,kafin daga bisani Abbansu yace"Jahad yanzu ke muke sauraro!munaso muji irin rayuwar da kukayi a hannun mutumin nan!"
Duk wannan abun dake faruwa akan kunnan Haroon,ya jima da shigowa batare da sanin kowa ba ya la6e yana jin labarin da abusufyan ke ba su jahad,na rayuwarshi da mahaifiyarsu,hankalin shi yayi mugun tashi,gaba ɗaya ya tsorata ya rikice,wata irin zufa ce tashiga gangarowa a fuskarshi,bakomai ya razanar dashi ba face ganin Ƴan ukun gaba ɗayansu sun haɗu acikin gidan kuma ga Ubansu da kanshi ya gane cewa ƴa'ƴanshi ne wannan alama ce dake nuna cewar asirinsu ya kusa tonuwa,
Tuni zufa tasoma tsastsafo mashi acikin jikinshi,sharkaf ta jiƙa t shirt ɗin jikinshi duk kuwa da ba zafi,jan ƙafarshi yayi tare da lalla6awa cikin sanɗa ya wuce bedroom ɗinshi,
Zagaye ya shiga yi acikin ɗakin,gaba ɗaya jikinshi sae faman rawa yakeyi,yama rasa inda zai tsoma kanshi kamar wani zautacce haka ya koma,a fusace ya dunƙule hannunshi tare da kai ma madubin ɗakin naushi,nan take glass ɗin jikinshi ya tsastsage ya zube ƙasa,
Hannunshi ya shiga fitar da jini,ko kaÉ—an baiji xafin hakan ba,raÉ—aÉ—in da zuciyarshi ke yi mashi yafi raÉ—aÉ—in glass É—in daya shige shi,
Da ƙarfi ya furta"That's impossible!ƙaryane ba gaske bane!!wlh bazan rasa rayuwata ba!dole na rayu ko da kowa zai rasa ranshi,zanyi komai zan yi don ganin na kwaci kaina!!
Yana magana yana sakin huci,idanuwan nan nashi sunyi jawur dasu luhu luhu,
Cikin sauri ya zura hannunshi tare da ciro wayarshi daga cikin aljihun jeans dinshi ya danna ma wata number kira,cikin sa'a aka É—aga kiran!
Wata irin muryace ta karaÉ—e kunnanshi mai tsoratarwa"Ba saida nace maka karka sake kira na ba!Tun farko ya mukayi dakai?
hankali atashe haroon yace"Ni ba wannan maganar tasa na kira ka ba!ka faÉ—amun taya akai kukayi gangancin barin yaran nan har suka haÉ—u da danginsu!!!!!!!
"Wasu yara kenan!"
Haroon yace"Ƴan ukun nan!na gansu da idona acikin gidan nan!yanzu haka gasu can a falon gidan nan sun taru suna jin labarin rayuwar yaran nan!
Nan take muryar mutumin da suke waya dashi ta canza,
"Wai kana nufin hosana!jahad!sehrish!duk sun haÉ—u anan cikin gidan naku ko mi"?
A ƙule haroon yace"Eh mana!akansu nake magana,wlh kowa yayi ta kanshi!saboda yarinyar nan dole ta ambaci sunanka acikin labarin da zata bayar kuma kasan cewa muddin waɗannan namun dawan guda biyu sukaji mugayen abubuwan da kuka aikata dole su binciko ka duk inda ka shiga kuwa,kuma koda a ƙarƙashin ƙasa ka 6oye,!
Fashewa da dariya mutumin yayi kafin ya tsagaita da yin dariyar yace"Baza su ta6a iya gano ni ba!nafi ƙarfinsu nesa ba kusa ba!zanyi amfani da ƙarfin sihirina wurin dakatar da tunaninsu.......'
Tun kan ya ƙarasa maganar haroon ya daka mashi tsawa tare da cewa"Ya Isa haka!!zancen ku iri ɗaya da ita!daga kai har ita daga anyi magana sai kuce ƙarfin sihiri,zakuyi amfani da sihiri ku asirce mutun!angaya maku cewa kowane lokaci sihiri ke yin tasiri ne!sam babu Allah aran kowannanku don haka babu wanda zai tsira acikinmu!ko ka manta da irin mutuwar da mahaifinku yayi ne?duk wani sihiri da kuke taƙama dashi ae a wurinshi kuka gado shi,akan idon kowannanku yayi mummunar mutuwa sakamakon farmakar shi da kakanmu salahuddeen sukayi,ku baku da tunani ne?me yasa shi a lokacin baiyi amfani da ƙarfin sihirin shi ba don ya hana kanshi mutuwa?ko don saboda ya tsufa ne yasa nashi sihirin baiyi aiki bane?
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.