Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Gaba daya an canzama gidan kamanni sai faman gyare-gyare akeyi mashi ta ko'ina,kwararrun ma'aikata aka ɗauko wurin tsara decoration ɗin da za'ayi ma gidan, yarda kasan za'ayi wani shagalin biki haka suka ƙawata gidan,duk wannan shirye shiryen da suke yi na tarbar manyan baƙinsu ne da zasu zo acikin kwanakin nan,a yau dae mutum biyu ne zasu fara zuwa,daga ciki akwai uncle Abusufyan da zaizo daga ƙasar turkey,sai kuma hajiya azeema da zata zo daga lagos,
gaba ɗaya tunanin matasan gidan Abbansu yasa aƙawata gidanne kawai saboda zuwan su Ammin sa ne,abunda basu sani ba shi da wata manufa yasa a gyara gidan, Tofah,
Wuraren ƙarfe 7:00am dai dai sehrish ta kammala shirinta na zuwa school,tana tsaye agaban mirror sai faman feshe jikinta takeyi da turare,bayan ta kammala ta koma wurin gadonta tare da kai hannu ta ɗauki hijab ɗinta data ajiye anan saman gadon ta zura ajikinta,
bata É—auki school bag É—inta ba saboda tana so tafara zuwa kitchen wurin su Aunty azmee ta kar6a ma babban yaya breakfast É—inshi takai mashi,
fitowa tayi daga cikin bedroom ɗin tana tafiya tana ƴan kalle kalle kamar zatayi tuntu6e,decoration ɗin da akayima gidan ba ƙaramin kyau yayi mata ba,don ba ƙaramin ɗaukar ido yake yi ba,
Ƙarasawa kitchen ɗin tayi tare da tsayawa daga bakin kopar tayi masu sallama,Azmee ce kaɗae acikin kitchen ɗin,jin muryar sehrish yasa ta juyowa fuskarta ɗauke da murmushi tace"Ƴan makaranta har an kammala kimtsawa ne?
murmushi sehrish tayi tare da cewa"ina kwana Aunty azmee,ya aiki"? Azmee tace"Alhamdulillah,shigo daga ciki mana in haÉ—a maki breakfast É—inki ki ci kafin ki tafi,'
"A'a Aunty azmee bana jin yunwa,idan naje school zanci acan,' har ta É—anyi shuru, cike da son jin gulma ta kuma cewa"Aunty azmee wai wanene zaizo zo yau"?
Murmushi azmee tayi tare da cewa"Masu kama dake ne zasu zo yau,'
"Masu kama dani kuma Aunty azmee"?ta tambaya fuskarta É—auke da mamaki,
azmee tace"kwarai kuwa kuna kama da azeema kanwar Abbansu junaid dake lagos,amman kinfi kama sosai da Uncle ɗinsu, Abusufyan dake zaune a ƙasar turkey shima zaizo yau,'
wani irin farin cikine taji ya lullu6eta,saboda ɗokin ganin wannan uncle ɗin nasu da take yawan jin suna ambatar sunanshi,a ƙagare take da ta sanya shi acikin idonta,
"Aunty azmee dagaske muna kama dashi?ko wasa kike yi mun"?
Azmee tace"dagaske nake mana,ban ta6a faÉ—a maki ba,amma maganar gaskiya kamanninki dashi har sun 6aci,kullum na kalli fuskarki sai ya faÉ—o mun araina,saboda komai na fuskarki irin nashi ne,tun daga kan idanuwanki,hancinki,da kuma bakinki duk irin nashi ne,ke hatta launin fatarki chocolate colour irin nashi ne,da ace Abusufyan ya ta6a yin aure,zan iya rantsewa cewa ke Æ´arsa ce'
tunda azmee ta soma magana sehrish ta saki baki tana sauraronta,
"abun ya jima yana É—aure mun kai,shiru kawai nayi,amma kamanceceniyarki da wasu daga cikin matasan gidan nan har taso tayi yawa,"
Cika da mamaki Sehrish tace"Aunty azmee wai dagaske"?
murmushi azmee tayi kafin taci gaba da cewa"na ta6a yi maki wasa ne irin haka"?
Girgiza kai sehrish tayi alamar a'a,
Cigaba da magana azmee tayi"kina yanayi da Abbansu junaid sosai kuma kina kama da Auntynsu Azeema,hatta junaid akwai kamanceceniya atsakaninku abunda yasa baza a gane ba saboda hasken fatarshi,amma kina kama da shi,bayan shi kuma sai Marshal Omar,shima akwai kamanninshi atattare dake,da kuma kanal yousouf,na jima da lura da hakan,"
tunda sehrish taji wannan jawabin na azmee take ta faman sakin murmushi,daÉ—i kamar ya kashe ta saboda ance tana kama da uncle Abusufyan É—insu,
"Aunty azmee naƙosa na ganshi,Allah yasa kafin nadawo daga school ya ƙaraso,da kaina zanje inyi mashi sannu da zuwa sannan in kai mashi abun sha,"
Dariya azmee tayi tana cewa"Allah yasa toh,amma kin manta baki ce insha Allah ba,"
cikin sauri sehrish tace"Insha Allah Aunty azmee,"
Suna cikin firar nan tasu,sai ga junaid ya faÉ—o cikin kitchen É—in ko sallama babu a firgice suka É—ago suna kallonshi,
daga shi sai gajeran wando fari ajikinshi,sai faman washe baki yake yi,kamar wanda akayima albishir da gidan Aljanna,
"Junaid anya lafiyarka kuwa?kaine yau kake yawo da short ajikin ka?ko ka manta akwai sehrish dani acikin gidan"? Acewar Azmee,
Murmushi ya saki tare da nuna sehrish da hannunshi yace"Wurinta nazo,inason magana dake reesh,in ba damuwa ki biyo ni muje bedroom É—ina,'
Kallon azmee tayi don taji me zata ce,
"kije mana,amma kada ki jima,"
Amsa mata tayi da toh sannan tabi bayan junaid suka fuce atare izuwa bedroom É—inshi dake a upstairs,
atare suka shiga cikin ɗakin nashi,har wurin gadonshi yakaita sannan ya tsaya tare da nuna mata shaddojin daya jera asaman gadon nashi yace"Pls reeshi ki za6amun ɗaya mai kyau,inaso yau nayi shigar mutunci don na burge uncle Abusufyan yasan cewa na girma yanzu,'ashagwa6e junaid ya ƙarasa maganar,
Sehrish kuwa zuba ma tsadaddun shaddojin ido tayi tana kallonsu,kala biyar ne sun sha uban aiki ajikinsu,hannu tasa tana É—aÉ—É—aga kayan tace"junaid ae ni nama rasa wadda zan za6a maka acikinsu,saboda kowacce kasa acikinsu kyau zatayi maka,bakasan cewa kaine keyi ma kayan kyau ba"? Tayi maganar tare da É—an juyawa tana kallon junaid dake tsaye yana ta faman sakin murmushin jin daÉ—in yarda sehrish ke hura mashi kai,
ta jima tana ruwan ido kafin ta cankar mashi wata haɗaɗɗiyar shadda gezner Ash colour sai faman salƙi take yi, mika mashi tayi tare da cewa"Wannan tayimun sosai kuma ina da tabbacin cewa in har ka sanyata ajikinka,sai uncle abusufyan ya razana da ganin irin kyan da zakai,'
Kar6ar shaddar yayi daga hannunta yace"thank u so much reesh,amma fa ba yanzu zan sanyata ba,sai zuwa anjima in zanzo É—aukarki daga school zaki ga kalar wankan da zan É—auka,"
murmushi tayi tare da kama hanyar fita daga cikin bedroom É—in nashi tana cewa"Allah ya kaimu lafiya,yanzu dae zan jiraka,in ka kammala shirin ka fito mu tafi kar nayi late,'
Amsa mata yayi da toh,bayan ta fita ya tattara shaddojin duka ya mayar acikin wardrobe É—inshi, ya zaro wasu jeans da t-shirt ya shiga zura su ajikinshi
_💋Boss Bature💋_
Lokacin da sehrish ta koma kitchen ɗin bata samu Azmee ba,sae dae Hayaam ta samu acikin kitchen ɗin,tana atsaye ta ruƙe qugunta kamar mai jiran wani abu,
Ganin sehrish yasata cewa"Sannu ko"
firgit Sehrish tayi tare da kai idonta inda hayaam ta ke atsaye tana sakin wannan shu'umin murmushin nata,
"Yawwa"ta amsa mata atakaice tare da wucewa wurin trayn da azmee ta ajiye mata saman table wanda ta shirya ma sgr breakfast ɗin shi aciki,hannu biyu tasa ta ɗauki tray ɗin sannan ta kama hanya tare da fucewa daga kitchen din,hakanan ta dinga jin kamar bata yarda da hayaam ba,anya ba wani abu takeyi acikin kitchen ɗin ba?in ba haka ba meyasa ta tsaya atsaye ruƙe da qugu,kamar mai jiran wani abu,
haka tayi ta wasiwasi acikin zuciyarta har ta ƙarasa part ɗin sgr,
Sallama ta fara yi mashi,jin shiru ba'a amsa mata ba,yasa tayi tunanin ko yana acikin bedroom É—inshi ne,
A hankali tasanya kafarta tare da shigewa cikin palourn komai agyare tsaf ta same shi,asaman table ta aza mashi tray din sannan ta tsaya tana jiran fitowarshi ko zai bukaci wani abu,
tana cikin tsayuwar nan tajiyo muryarshi daga cikin bedroom É—inshi yana tambayar wanene anan!"
Cikin sauri tace"Ni ce,dama breakfast ne na kawo maka,"
kusan minti biyar da yin maganarta sannan taji yace"A shigo min da coffee shi kawai nake buƙata,"
murmushi ta É—anyi tare da mika hannu ta É—auki cup of coffee É—in dake acikin kayan breakfast É—in nashi,ta nufi bedroom É—in hannunta É—auke da cup É—in,
sai da ta tsaya abakin ƙopar shiga Sgr ya bata izini sannan tasa kai tashiga,wani irin daddaɗan kamshin turarensa ne ya bugi hancinta,nan take taji wani irin yanayi atattare da ita,
lumshe donta tayi tare da buÉ—esu a hankali ta kallo inda sgr yake, a hakimce ya É—an kishingiÉ—a daga gefen katafaren gadon nashi,
Gaza janye idanunta tayi daga kallon kyakkyawar surar jikinshi,wankan daya ɗauka ba ƙaramin fisgarta yayi ba,white trouser ne na suits amma bai sanya coat ɗin sama ba,iya vest ɗin ciki ya bari tabi shape ɗin jikinshi,daga ƙasan vest ɗin ta ɗan tattare hakan ya bayyana farar fatar shafaffen cikinshi, ya harɗe kafafunshi wuri guda yayin da idanunshi ke a lumshe,
tafiya take tana tunkarar inda yake idonta akanshi har ta ƙarasa tare da ajiye mashi cup ɗin asaman bedside table ɗinshi tace"Gm sir,ga coffee nan na kawo maka,ko akwai wani abu da kake buƙata"?
Bai amsa mata ba,a hankali ya dan buɗe idanunshi sannan ya yunƙara tare da miƙewa daga zaune ya sauko da ƙafafunshi ƙasa,
Zaki iya tafiya,ya ambaci hakan ayayin da yakai hannu tare da É—aukar kofin coffeen yakai bakinshi yana kur6ar shi anatse,
Juyawa sehrish tayi ta kama hanyar fita daga bedroom É—in a hankali,ji take kamar karta tafi ta barshi,don bata gaji da kallon kyakkyawar fuskarshi ba,
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.