Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Haihuwar tazo mata cikin sauƙi,a ranar aka sallame ta,suka koma gida,bakomai yafi damun abu ba face yadda mutane suka ƙi zuwa yi mata barkan samun ƴan uku,ko leƙo gidanta babu wanda yayi,tayi tsammanin danginshi zasu zo amma abun mamaki babu wanda ya leƙo da sunan ɗan uwanshi yazo duba yaranta,jikinta yayi mugun sanyi,duk taji ta tsani kanta,amma daga ta kalli ƴan ukunta sai taji farin ciki aranta,suka dae ne dangin da take dasu aduniyar nan,su take gani taji daɗi aranta,lokacin da yaran suka kai wata ɗaya aduniya,aranar wata ƴar uwarshi tazo kawo mata ziyara,ita ta taimaka wurin yi mata wankan jego,da kuma yi ma yaran wanka,duk yadda abu taso taja ta da fira don taji a ina suke da zama suna da dangi,amma matar nan da shegen wayau ko uffan bata ce mata ba,a haka har suka kammala wankan jegon matar ta koma garinsu,
Abu ba ƙaramar wahala tasha ba,wurin rainon ƴan ukunta,babu mai taimakonta,itace yi masu wanka har sau biyu arana safe da kuma dare in zata kwantar dasu,wankin kayansu da suka 6ata,ɗawainiyarsu da kuma ɗawainiyar kanta,abun duk ya jagule mata,ga sayyadi ko tsinke bai ta6a sanya hannu ya kawar mata ba,bayan kafin suyi aure shi da kanshi yake sanar da ita cewa in sukayi aure duk ranar da yake hutu bai aiki har girki sai yayi mata ashe duk ƙaryace yake yi mata,Abusufyan kuwa muddin yana agida bai barinta tayi aiki,sai dai yayi shi kaɗae ko kuma suyi atare,da kanshi yake cewa"Abuna idan har kika haifa mana ƴa'ƴa ni da kaina zan dinga yi masu wanka,idan mata ne zan dinga sharce masu gashin kansu ina gyara masu shi,bazan bari kisha wahala ba,'in ta tuna waɗannan kalaman nashi sai ta fashe da kuka,dama ita dana sani bata da daɗi,Allah ka rabamu da aikin dana sani,Amin
Kunji yadda akai Abusufyan ya auri abu,da kuma yadda akai yabar nigeria da kuma yadda akai ta haifi Æ´a'Æ´anshi agidan wani wanda ya taso amatsayin ubansu,
💋Boss Bature💋
Lokacin da Abusufyan yakai ƙarshen labarin nashi sai ya fashe da matsanancin kuka kamar ƙaramin yaro,cikin sauri Abba ya janyoshi jikinshi yana lallashin shi,bashi kaɗae ba hatta su fawan,jabeer,irfan,khaleed dasu twins sai da idanunsu suka cicciko da kwalla,Sgr da Omar kuwa jinjina kai kawai sukeyi,Abbas ne yace"Yanzu ina ƴa'ƴan suke?suna raye ko sun mutu ne"?
"Nima abunda nakeso na tambaya kenan,"acewar hajiya azeema da jikinta ya gama mutuwa,kowa mamakinshi ta yadda akai waÉ—annan abubuwan suka faru batare da Abusufyan da kuma goggon katsina sun sanar ma kowa ba,
cikin sanyin murya Abba yace"ka faÉ—a mana ina Æ´a'Æ´an suke yanzu"?
ɗagowa abusufyan yayi da idanunshi waɗanda sukayi jawur yace"ni kaina bazan iya cewa ga inda suke ba,a lokacin can baya ina bibiyar rayuwarsu,ta hanyar haris shiya kira ni a waya yake sanar dani cewa abu ta haifi ƴa'ƴa kuma yaran dani suke kama sosai,tun daga lokacin na sanya shi akan ya dinga bibiyar rayuwar yaran yana sanar dani duk wani abu dake faruwa arayuwarsu,shine yake turo mun da hotunansu ina ganinsu a wulakance,yara ne mata guda ukku wani lokacin babu kallabi a kawunansu kuma babu takalma a ƙafafunsu,tun lokacin nake tsananin jin tausayinsu,kuma raina yake bani cewa tabbas ƴa'ƴana ne su.....saboda akwai wani lokaci da nazo nigeria zuwan bazata batare da sanin kowa ba............."
Bai ƙarasa maganar ba suka jiyo muryar goggon katsina tana sambatu tana cewa"ƙarfen nasara ba tabbas,Allah ka tsine ma baturen daya ƙirƙiri motar harisu,shegiyar motar kamar da katako akayita,tun safe muke a hanya take ta bamu matsala mtsswwwwww haba ina dalili,tafiya daga katsina zuwa abuja sai kace mutun zashi saudia a ƙasa?ae dana san haka zata faru da a kafa na tako wlh,shegen maƙo irin nashi,maimakon ya biya mana kuɗin jirgi,ya nace sai mun hau waccen rugwagwar motar tashi..........'kasa ƙarasa maganar tayi ganin yadda matasan gidan suka taru a falon gidan,ga kuma Abusufyan ɗinta dake ta faman sharar kwalla,
Don bala'e,a hannu ta ruƙo zaninta daga ita sae dogon undi fari ajikinta,ta cire zanin gaba ɗaya,ranta ba ƙaramin 6aci yayi ba,da alama,
Tsayawa tayi cak baki asake tace"Na shiga uku ni yau,abun dae ba sa'a,Allah yasa dae ba wani ya mutu ba,wlh yanzu inyi kwana in koma katsina don ni ban shirya ganin gawa ba,dan Allah ku faÉ—a mun maiya faru"?
Miƙewa sukayi gaba dayansu suna kallonta cike da tuhuma,adaidai lokacin kuma Dr haris ya shigo tare da Saude,suma duk suka tsaya cirko-cirko ana kallon kallon,
Koda Abusufyan yayi arba da goggon katsina,jiki na rawa ya tunkareta,tare da faÉ—awa jikinta ya rungumota sosai yana cigaba da kukan,
Nan fa hankalin goggon katsina ya tashi,hannu bibbiyu tasa tare da É—ago da fuskarshi daga jikinta tana cewa"Abusufyan É—ina meya faru?meyasa kake kuka?kai da zanga kana farin ciki?ko Omar bai nuna maka Æ´a'Æ´anka bane.....?
cike da mamaki kowa ya zuba ido yana kallonta,Abusufyan dake kuka nan take ya dakatar da kukan nashi yana cewa"Mommyna...ina abu take ne?ina yaran da ta haifa suke?suna ina?
Bata bashi amsa ba,sae ta kalli Omar dake tsaye yana kallonsu tace"Omaru ina kakai mashi Æ´a'Æ´anshi ne?yaran nan fa da kazo dasu gidana Æ´a'Æ´an abusufyan dina ne dama saida na faÉ—a maka,dan Allah ku nuna mashi Æ´a'Æ´anshi ya gansu yaga yadda suka girma ko hankalinshi ya kwanta banson ganinshi yana kukan nan"
Tashin hankali!
Nan fa kowa ya ruÉ—e yana tunanin su wanene yaran da gwaggon katsina take magana akai,
"Gwaggo kina nufin cewa hosana da jahad Æ´a'Æ´an abusufyan ne!"?Omar ne yayi mata tambayar fuskarshi É—auke da mamaki,
goggo tace"Eh mana,sune Æ´a'Æ´an abusufyan É—ina,suna ina ne.....'
Kafin wani ya buɗe baki ya ƙara magana,sai ga Jahad da hosana sun fito da gudun gaske jin muryar gwaggon katsina data karade gidan,tana ganinsu ta washe baki tana cewa"Yawwwa ga ƴa'ƴan abusufyan ɗina nan sun ƙaraso,maza ku ƙaraso in rungume ku ajikina,'
ƙarasawa sukayi tare da faɗawa jikinta,ta hada su duka ta rungume ajikinta,tana ta faman murmushi,
Fawan ne yace"Anya gwaggo tasan me take cewa kuwa?taya waɗannan yaran zasu kasance Ƴa'ƴan uncle ɗinmu?hakan na nufin cewa Sehrish itama ƴar shi ce kuma,su jinin mu ne?
Cikin sanyin murya abusufyan ya juya tare da kallon fawan da yayi maganar yace"Tabbas su Æ´a'Æ´ana ne!nasan zakuyi kokwanton maganarta ne saboda tana da ta6in hankali,to inaso ku sani cewa mommyna tana acikin hayyacinta,tasan me takeyi duk da akwai ta6in hankalin atare da ita,amma ba kowane lokaci bane take kasancewa dashi ba,'
Jin maganarshi yasa Hosana da jahad suka juyo suna kallonshi yayin da zuciyoyinsu ke cigaba da bugawa da ƙarfi da ƙarfi,
Kowa fa ya shiga ruÉ—ani,wasu ma saboda tsabar mamaki sun gaza magana,irin su Sgr da kuma su Jahan,
"Yanzu duk ba wannan ba!dole muji ya akai kasan cewa su ɗin ƴa'ƴanka ne!kuma ya akai kuka bar rayuwarsu ta wulaƙanta batare da kun sanar mana ba!sannan dole muji ta bakin yaran game da irin ruƙon da wannan mutumin yayi masu!'acewar Abbansu junaid,ranshi a6ace yake maganar,
Gwaggo dae bata gane inda zancen nasu ya dosa ba,amma tana da tabbacin cewar abusufyan ya fasa abunda suka jima suna 6oyewa,hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba,dama ta gaji da 6oyon al'amarin da sukeyi,saboda ganin irin wahalar da yaran suke sha a hannun mugun mutumin nan,
Omar yace"Abunda ya kamata shine,yanzu naga anata kiran sallar isha'e yakamata muje muyi sallah,kafin mu dawo nasan gwaggo ta ɗan rage gajiya,sai mu zauna ayita taƙare kawai,in yaso sai jahad tayi mana bayanin komai tunda itace mai cikakken hankali acikinsu,Sehrish ita kanta bana tunanin tana acikin hayyacinta yanzu,
Kowa ya amince da maganar omar,batare da 6ata lokaci ba,suka wuje bedrooms É—insu domin yin alwala,hajiya azeema ce ta shigar da Gwaggon katsina cikin É—akinta tare da saude kafin agyara masu inda zasu zauna,
Yau dae gidan Abban sojoji a hargitse yake,Wlh ni kaina a hargitse nake,sai addu'a kawai,
Abbansu na fitowa daga cikin toilet,junaid ya faÉ—o mashi acikin ranshi,nan fa gaban shi ya faÉ—i rasss,sae lokacin ya tuna da cewar babu junaid fa acikin gidan tun É—azu,duk wannan budurin da akeyi babu shi acikinsu,
Hankalinshi amatuƙar tashe ya tunkari wayarshi dake ajiye saman side drawer ya dauketa,tare da lalubo numbar junaid ya danna mashi kira cikin sa'a wayar tashiga tana ringing amma ba'a ɗaga ba,kusan sau huɗu yana kira ba'a ɗagawa,
Ana biyar É—inne aka É—aga wayar,kara wayar yayi kunnanshi yana cewa"Junaid ina ka shiga ne!!"shiru yaji ba'a tanka mashi na,nan fa yabi ya rikice,
"Junaid wai baka jina ina magana ne?bazaka amsa mun ba?junaid kodae wani abu ya faru da kaine?
Nan ma shiru ba'a bashi amsa ba,
Muryarshi tamkar zaiyi kuka ya kuma cewa"don Allah babyn Abbanshi kayi mun magana mana!
Muryar mace ce ta amsa mashi da cewar"ka duba whatsapp É—inka,zaka ga video mun tura maka,"
Jikinshi har kerma yakeyi wurin katse kiran ya shiga whatsapp É—inshi,new number ya gani tayi mashi message da video,
Saboda tsabar fargaba,tun kafin ya buÉ—e video É—in zufa tashiga gangarowa a fuskarshi,dukkan ilahirin jikinshi ya shiga yin kerma,idanunshi sukayi jawur tsoranshi kar a videon yaga junaid cikin wani yanayi,bazai iya jurar wannan ba,
Runtse idanunshi yayi yana karanto addu'o'i abakinshi,kafin daga bisani ya daure ya cije ya buÉ—e videon,
Zazzare idanunshi yayi waje tamkar kwayar idanunshi zata faɗo ƙasa,
A ƙarshe kuma ya fashe da dariya,tare da zubewa saman guiwowinshi yana tikar dariya,
Bakomai bane acikin video É—in nan ba,face Mommynsu junaid Alexandra rungume da junaid asaman gado,suna kwance abunsu,da alama ma kamar bacci yake yi ajikinta.......
Â
*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃
*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*
*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*
*LOCATION KANO*
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.