Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
  tana acikin kitchen ɗin bayan ta kammala haɗa masa coffee din ta ruƙo cup ɗin a hannunta, sai ga haroon ya faɗo mata kamar daga sama cikin sauri taja da baya hankalinta atashe, daga shi sai vest da singlet, shu'umin murmushi ya saki yana kallonta yace "ke shine nasa ki kaimun abinci kika ƙi ko? Ke ga isassa mai walkin sa harni ɗan masu gida zan saki aiki, ki bijire mun," ya faɗi yana kallonta
 Murya na rawa sehrish tace "kayi hakuri dama na fara kaima babban yaya ne, kafin na kawo maka nakan......'
 Bata ƙarasa ba ya katse ta da cewa "Sorry for your self sehrish! wlh kin shiga uku ! kin jefa kanki cikin masifa, daga rana irin ta yau inaso kullum ki kasance cikin yin sallar dare kina rokan Allah akan ya kare ki daga Sharrina," zaro ido tayi tana kallonsa jin abunda yace cikin tsananin tashin hankali tace "saboda me zaka ce haka"? laifin me nayi maka, dan Allah kabarni inyi rayuwata cikin salama,"
 Fashewa da dariya yayi kafin ya tsagaita da cewa "kinsan wani abu?kina da kyau sosai musamman idan kika tsorata idanunki ba ƙaramin fizgata sukeyi ba, idan kika amince a shirye nake dana aure ki, kuma zan shiryu nadaina duk wani abu da nake yi, amma idan kika bijire mun I pity u wlh," cikin sanyin murya yake yi mata magana,.
 Tamkar zatayi kuka tace"Dan Allah na roƙe ka kayi hakuri nidai ka fita daga cikin rayuwata, kabarni dan Allah kaje can ka samu mace irinka ka aura, amma ni ina da wanda nake so," tayi maganar tare da bi ta gefensa gabanta na faduwa ta wuce cikin sauri,
 murmushi kawai haroon yayi tare da jinjina kansa aransa yace "nasan ba kowa take hari ba face wancan mai zubin ifritan, ni kuma ba zan ta6a bari hakan ta faru ba, target ɗina na farko da zanyi zan fara 6ata sunanki ne a wurinsa," yana fadin hakan ya saki shu'umin murmushi tare da wuce wa room ɗinsa
Â
Maganganun da haroon ya faÉ—a mata sun tsaya mata arai, tunaninta ya rayuwarta zata kasance nan gaba acikin gidan batasan me haroon zai yi mata ba,
tana tunanin tana tattaka stairs ɗin jiki amace, adai² lokacin Marshal ya shigo gidan cikin sauri saboda yarda yake agajiye shima, har sai da ta juyo daga saman stairs din ta ɗan kalle sa, ta other side ɗin yabi ya wuce part ɗinsa da hanzari sam bai lura a ita ba,
  bakomai bane ya faÉ—o mata arai face yaran da taji yace zasu zauna gidan Uncle Abusufyan É—insu, ko ya É—auko su? ta tambayi kantaÂ
cikin sauri ta wuce part É—insa bedroom É—insa ta shiga da sallama ya iznin shiga, a lokacin harya dawo gefen bed É—insa ya zauna yana cin abincinsa, yau ba sai ya jira anyi saving É—insa,
 ƙarasawa tayi kusa dashi sannan ta samu wuri agefen plate É—in abincinsa ta ajiye masa cup É—in,"Â
A hankali ya furta "thanks,' a tunaninsa zata tafi amma sai yaga tayi masa tsaye akansa, sam bata son ta tafi tabarshi saboda a ganinta in ta tafi bazai ƙarasa cin abincin bacci zai iya ɗakarsa,
Hannu yasa ya É—auki cup of coffee É—in data kawo masa sosae yasha, bayan ya kammala ya ajiye shi, sannan ya gyara kwanciyarshi ya kwanta luf abunsa, ya janyo blanket É—insa ya rufe har zuwa chest É—insa nan take bacci ya É—auke sa,Â
bata bar bedroom É—in nasa ba sai da ta tabbatar tayi masa addu'a tukunna tasa hannu ta kwashe kayan abincin acikin tray ta fuce dasu a hannunta,
  Kitchen ta koma da hanzari ta haɗa ma Marshal Omar nasa shima acikin tray sannan ta wuce masa dashi part ɗinsa,
tana shiga a lokacin ya fito sanye da jallabiya fara wuri ya samu asaman 3 seater ya zauna hannunsa ruƙe da wayarsa ganin sehrish yasa shi sakar mata murmushi tare da cewa "kamar kinsan a yunwace nake abunda nake jira kenan,"
 Murmushi ta saki tare da ƙarawa ta ajiye masa tray ɗin asaman table ɗin dake a gabansa sannan tace "Ya mai jiki ya omar, naji abunda ya faru Allah ya kiyaye gaba, ya tonu asirin su,"
 "Ameen Ameen," ya amsa mata, hannu tasa ta buɗe warmer tare da ɗaukar plate da saving spoon zata zuba masa abinci taji yace "baki tambaye ni twins ɗina ba"? Murmushi ta ɗanyi tare da ɗagowa ta kalle shi tace "dama ƴan biyu ne"? Yace "eh kamannin su ɗaya sak, ke ma haka fuskarki irin tasu ce sak komai da komai,"
  gabanta ne taji ya faɗi jin abunda omar yace dakatawa tayi da zuba mashi abincin tana son tunano wani abu arayuwarta amma sam takasa tunawa, tabbas tana jin cewa akwai wani abu da ta manta arayuwarta mai matuƙar muhimmanci agare ta, a duk lokacin da tayi ƙoƙarin tunawa sai taji zuciyarta tayi mata wani irin nauyi sosai,
"Wata rana zan kawosu ku ga juna, saboda inaso ki ga abun al'ajabin da nake son nuna maki,"
Cikin sauri tace "Shikenan ya Omar Allah ya kaimu lokacin nima zanso nagansu,"
ta jima suna dan fira dashi kafin daga bisani ta bar part É—in nasa ta koma É—akinta,Â
 Bayan Omar ya kammala cin dinner ɗinsa fitowa yayi tare da wuce wa ɗakin da suka kwantar da fawan
 Yanayin daya samu Twis zaune zun zuba mashi ido ga kanal yusif shima zugudum duk cikin jimami, gyaran murya yayi duk suka É—an É—ago kana yace "ku tashi ku je ku kwanta, tun da ya samu bacci"Â
 Amsa mashi su kayi da "toh" sannan suka miƙe tare da fuce wa daga ɗakin shima yusif yayi yabi bayansu, zama Omar yayi daga gefen fawan dake ta faman sharar bacci, addu'o'i ya shiga karantowa yana tatto fa masa, ya jima yana yi masa addu'a sannan ya tashi yabar ɗakin tare da tufe masa ƙopa,
****************
Wuraren ƙarfe sha biyu ya fito cikin sanɗa hannunsa ɗauke da pillow yana duddubawa yaga in ba kowa duk sunyi bacci lokacin murmushi ya saki tare da cewa "sheggu saboda wancan ɗan shilan shine duk suka susuce har suka gaza cin abinci, bari na ƙarasa shi lahira sai in ga ya zasu yi, zasu bi shi ne
 Yana faɗin hakan ya wuce ɗakin da suka kwantar da fawan cikin sanɗa ya tura ƙopar tare da sa ƙafa yashiga cikin, bin shi yayi da kallo jinjina kansa yayi sannan ya lalla6a ya haye saman gadon tare da ɗaga pillow ɗin ya taushe ma fawan hancinsa dashi , nan take fawan yafarka tare da zazzare idanunshi yana mutsu-mutsu sam bashi da sauran ƙarfi ajikinsa da zai iya kwatar kansa........... ... ...
sai faman kiciniya fawan yake yi saboda ya kwaci kansa daga hannun haroon wanda ya taushe masa fuska da pillow da mugunta ma yake kara danna masa shi, tun fawan yana wutsil wutsil da ƙafafunsa numfashinsa na kokarin daukewa gaba daya har jikinsa ya fara saki, suna cikin wannan halin aka kwankwaso kopar da karfin gaske,a wani irin tsorace haroon yayi wurgi da filon dake hannun shi, yayi wuff tamkar giftawar walkiya ya afka bayan labule ya boye yana faman zazzare idanun shi kamar na mujiya tsoran shi kar ace wani ne ya taso cikin daren nan,
Hannu yasa a hankali yaÉ—an buÉ—e labulen don yaga kowanene, gabansa ne yayi bugun bugu ganin Abbansu ya shigo ciki jikinsa sanye da jallabiya fara, cikin sauri haroon ya mayar da labulen ya rufe ruff tuni zufa ta soma tsattsafo masa a jikinsa tamkar wanda aka tsamo daga kogin maliya,
ï¿?
  ganin yarda fawan ya tashi zaune saman gadon yana faman hargowa yana fadin "zasu kashe ni ! bansan me nayi masu ba! Sun biyo ni don su kashe ni, ku ce musu su daina azabtar dani !!!! Gaba ɗaya ya zauce sai zuba sambatu yake yi yana zazzare ido,
  A hanzarce Abban nasu ya Æ™arasa tare da haye wa saman gadon dab dashi yana cewa"fawan sannu ya jikin? ka dawo cikin hayyacin ka ko? ka kwantar da hankalin ka, kana a gida yanzu babu wanda zai iya cutar da kai,'.Â
ï¿?
  girgiza kai fawan yashiga yi yana sake maimaita cewa "Har yanzu suna nan, bibiyata suke yi so suke su kashe ni, ni bansan me nayi masu ba," yana magana daker daker yake sakin numfashi, hancinsa har ya fara bleeding kaɗan jinin ke ɗigowa,
  tallabo fuskarsa Abban nasu yayi tare da ɗago da ita don ya kalle shi sosai yace "fawan Ni ne fa,Abban ku ina tare dakai, babu wani anan da zai cutar da kai,"
 A hankali fawan ke kallon Abban nasu yayin da idon shi ke rurrufe wa yace "Abba ruwa zan sha," ya faɗi agalabaice,
ï¿?
  Cikin sauri Abban nasu ya matsa tare da kai hannun shi saman bedside drawer ganin dakwai bottle water mai sanyi ajiye asama, ɗauko wa yayi tare da buɗe murfin ya kwafa masa abaki yana sha, jikin shi har wani kerma yake yi tamkar zai kwace roban ruwan daga hannun Abban nasu daya kwafa mashi, ganin yarda yake shan ruwan throat ɗinsa har wani sauti yake fitarwa kwattt!kwattt!! Saboda yarda yake kurbarsa a zafafe,
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.