Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
  tuni zufa tasoma tsatstsafo mata a fuskarta, takawa sgr yayi yana matsawa kusa da ita, ja da bayan da zata Æ™ara yi ke da wuya , gaba É—aya ta faÉ—a asaman gadon shi, bin ta saman gadon yayi gadan gadan ya tunkareta, hakan yasa ta fashe da matsanancin kuka atsorace ta dinga girgiza mashi kai tana cewa"wlh bani bace na É—auko allurar ba ! Bani ita akayi....ba zan iya cutar dakai ba.......!!" sai faman sambatu takeyi ita kanta batasan me take cewa ba saboda ya Æ™ureta sosai ta runtse idanunta zuciyarta nata faman harbawa, sam batasan cewa sgr yana cikin hayyacin shi ba,da gangan yayi mata haka saboda akwai abunda yakeson ganowa game da daren jiya da kuma abubuwan da ya gani na canji a bedroom É—inshi da kuma body É—inshi, yasan cewa itace last person daya kasance tare da ita,Â
   jin shiru baice komai ba yasa ta ɗan buɗe idonta, ba komai yake kallo ba face doguwar sumar kanta, sai yanzu ya gane inda ya samu siraran gashi guda uku masu tsayi, hakan na nufin gashin kan Yarinyar ne ya tsinta asaman gadon shi ɗazu da safe, acikin sambatun da tayi mashi ta ambaci cewa ba ita bace ta ɗauko allurar ba, ba ta ita akayi, nan ma ya gane cewa kwa6a tayi mashi jiya har ya ɗirka ma kanshi allura, that's why omar ya tambaye shi akan cewa shi ya dauko allurar, natsuwa yayi a hankali yana ƙare ma fuskar sehrish kallo, ita kuwa sai faman haɗiyar yawu take yi saboda tsoro ga zufa dake gangarowa ta cikin gashin kanta kamar mara gaskiya, duk da sanyin A.c dake gudana aciki,
  rufe idanuwanta tayi tana faman karanta addu'oi' acikin bakinta,
  for the first time daya ƙarewa wata ƴa mace kallo irin wannan aduniyar nan, yana kallon kyakkyawar fuskarta ne aƙoƙarin shi na ya tuna abunda ya faru jiya,amma yarda take motsi da siraran la66anta tana karanta addu'oi'n neman tsari hakan ba ƙaramin burge shi yayi ba, sai ya samu kan shi da shagala wurin kallon bakinta, tunanowa yayi da ranar daya turketa amatsayin mace yarda ta tsorata har ta sume mashi, shi kuma rayuwarshi mace mai shegen tsoro ba ƙaramin burgeshi takeyi ba,ba don komai ba sai don ya ruƙa tsorata ta don ya samu nishaɗi,
  ɗan gyara muryarshi yayi tare da cewa"jiya kin ban allura nayi ma kaina har nayi Æ™oÆ™arin yin raping É—inki, ko ba haka akayi ba? ya tambaya fuskarshi a É—aure,.Â
  hankali tashe sehrish ta shiga furta"innalallahi wa'inna ilaihirraji'un. Nashiga uku, kasan Allah ni bani bace na É—auko allurar ba bansan komai akai ba,.Â
  shiru sgr yayi yana kallonta har lokacin taƙi buɗe idanunta, abunda bata sani ba shi guessing yayi bai tuna komai ba, amma yayi mata rijiya ta faɗa,
  cigaba da magana yayi anatse"then tell me who brought it to u"?
  shiru tayi lamo saboda tasan ba zata iya furta sunan haroon ba, ganin taƙi magana yasa shi daka mata tsawa tare da cewa"ba magana nake maki ba!!," wannan tsawar da yayi mata ne yasa ta sume mashi, dama sai da ranshi ya bashi,
 Saukowa daga saman gadon yayi tare da fucewa izuwa palour dinshi, kai tsaye ya wuce wurin fridge ɗinsa tare da buɗewa ya ɗauko bottle water mai sanyi, sannan ya koma cikin bedroom ɗin nashi,zama yayi daga gefen gadon tare da sanya hannu ya buɗe roban rubar saida ya fara sha sannan ya ɗebo a hannun shi ya yayyafa mata a fuskarta, a gigice ta ware idanunta kai tsaye suka shiga cikin nashi a lokacin ya mayar da bottle din abakin shi yana ƙara shan ruwan, tamkar a mafarki take ganin abun har lokacin jikinta bai daina kerma ba, cire roban ruwan yayi daga bakin shi sannan ya mayar da murfin ya rufeta tare da ajiyewa saman side drawer ɗinshi,
  sannan yayi mata nuni da hanyar fita yace"zaki iya tafiya," cikin sauri ta sauko daga saman gadon nashi, hanyar fita ta nufa da sauri da sauri, jinkirtawa tayi tare da ɗan juyawa don ta saci kallon shi, samun shi tayi a kashingiɗe saman gadon ya aza head dinsa asaman pillow, eyes dinshi a lumshe tamkat zasu rufe amma hasken kwayar idonshi blue ya ɗan fito alamar bai runtse idanun duka ba,
  Muryarshi ce ta ratsa kunnanta da cewa"akwai wani abu ne"? Cikin sauri ta girgiza kai alamar a'a sannan ta fuce daga ɗakin, sai da tafara ɗaukar mayafinta dake zube a ƙasa, ta yafa shi akanta sannan ta fuce daga part ɗin nashi, tafiya take anatse fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi tayi mamakin yarda akai Sgr bai tuhumeta ba,bayan ya tuna duk abunda ya faru atsakaninsu jiya, tayi tunanin zata sha mari ne a wurin shi amma sai gashi abun yazo mata da sauƙi, har yau tana mamakin sauƙin kai irin nashi da ba kowa zai fahimta ba, amma tabbas bai da girman kai ko kaɗan, jan ajine kawai dake gare shi ko jinin sarauta bazai nuna mashi wannan ba, Domin kuwa shi kanshi Sarki ne mai cike da ƙarfin iko👑
 a hankali take taka steps ɗin down stairs zata sauko, jin alamar shigowar mutun cikin babban falon yasa ta tsagaitawa da tafiyar tana kallon shi, jahan ne ya shigo cikin falon hannun shi ruƙe da jakar kuɗin da zasu ba haroon, ganin yarda yake tafiya cikin sanɗa yasa ta gane cewa bai son wani ya ganshi cikin sauri ta ja da baya tare da samun wuri ta la6e,
  sai faman ƴan waige waige yake yi yaga ko akwai mutun amma wayaam ba kowa hakan yasa cikin sauri ya wuce bedroom ɗinsu, ajiyar zuciya sehrish ta sauke tare da lalla6awa ta fito kai tsaye ta nufi kitchen tana zullumin ko menene Jahan ya ɗauko acikin jakar hannunshi, da alama dae wani mugun abunne tunda har yake sanɗa don kar aganshi, ta faɗi acikin ranta a lokacin da take ƙarasawa cikin kitchen ɗin don ta zuba ma kanta abincin da zata ci,
  turo ƙopar yayi a hankali yashiga daga cikin ɗakin nasu, jin alamar shigowar mutun yasa ayaan dakatawa daga zirga zirgan da yake yi acikin ɗakin,
 Cikin sauri ya nufe shi yana cewa"Jahan ka tabbata babu wanda ya ganka"? Amsa mashi yayi da cewa"eh babu da alama duk sunyi bacci, kazo yanzu mu hanzarta mu kai mashi kuÉ—in,"Â
 Atare suka fito daga bedroom ɗin nasu, duka suna sanye cikin jallabiya, ɗakin haroon suka nufa, koda suka ƙaraso ƙopar ɗakin a rufe take, kwankwasawa Jahan yashiga yi a hankali,
 "Su waye ne"? Ya tambaya daga ciki,
Har suna haÉ—a baki wurin cewa "twins ne ",
  kwance yake daga saman gadonshi,daga shi sai shorts ajikinshi ba riga, tasowa yayi tare da nufar kofan yasa hannu ya buɗe masu tare da cewa"ku shigo daga ciki," kallon juna su kayi kafin daga bisani suka shiga daga ciki,
 tunda haroon yayi arba da jakar kuÉ—in dake hannun jahan yashiga sakin murmushin nan na shu'umanci yana cewa"ince dae kuÉ—ina ne acikin jakar nan ko"? yayi maganar tare da miÆ™a hannu zai kar6i jakar,janye ta jahan yayi tare da cewa"ka fara goge video É—in tukunna mu damÆ™a maka su,"Â
 ta6e baki yayi yana kallon su,kafin ya juya ya nufi saman gadonshi inda wayar shi ke ajiye ya É—aukota, yatsan shi yasa ta buÉ—e sannan ya shiga wurin videos É—inshi ya lalubo nasu daya É—auka sannan ya miÆ™a masu tare da cewa"Gashi nan ku goge da kan ku,ina ga hakan zai fi ko"? Kallon juna suka sake yi duk jikinsu yayi sanyin, tsoransu karya cuce su,ayaan ne ya kar6i wayar tashi yayi deleting É—insa gaba É—aya, sannan ya kalli haroon É—in dake ta faman sakin murmushi yace"ka tabbata babu wani videon namu dake gare ka bayan wannan!?Â
 ɗaga mashi gira yayi alamar eh, jahan yace'laptop É—inka fa babu wani aciki"? nan ma ya sake cewa"babu wannan ne kawai gare ni,"Â
 ajiyar zuciya suka saki gaba ɗayansu,
 Miƙa mashi wayar Ayaan yayi, sannan jahan ya damƙa mashi jakar kuɗin, kar6a yayi yana cewa"kun tabbatar cewa miliyan 80 ɗinne"?
 ayaan yace"ka Æ™irga su mana sai kaga in sun cika,"Â
Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!
ï¿?
Zuƙunnawa haroon yayi tare da zuge zeep ɗin jakar, sai ga bandir bandir ɗin ƴan dubu dubu, dami dami shaƙe acikinta, hannu yasa tare da curo bandir guɗa ɗaya yakai a saitin hancin shi yana shinshinasu yace"Anya wannan ba kuɗin ganye bane?harara suka watsa mashi jahan yace"a'a na bishiya ne," dariya haroon yayi yana faman shaƙa kuɗin a hancin shi,
 gaba ɗaya ransu ya gama 6aci burinsu ya ƙirga kuɗin yaga in sun cika, amma ya tsaya yi masu shegantaka,
  tass ya fiddo da kuÉ—in ya Æ™irga su, duk dami É—aya na dubu É—ari ne, a haka yayi counting É—insu 80 millions ne bayan ya kammala Æ™irgasu, ya shiga cusa su acikin jakar kaf ya kwashe su, sai da ya zuge zeep É—in sannan ya É—ago ya kalle s u cike da shaÆ™iyanci yace"Au na manta ban baku la'ada ba,"Â
 atare suka haÉ—a baki wurin cewa"mun fi Æ™arfinsu,kai ke buÆ™atarsu kai daga ganin mu kasancewa ba matsiyata bane,"Â
 "Wow," ya furta yana tafa hannunshi "abu yayi kyau Æ´a'Æ´an billionaire,karfa kuce zaku gayamin magana!ku fuce mun daga É—aki cikin salama,"Â
 Jahan yace"ba sai ka kore mu ba, mukan mu aƙagare muke da mu fita mubar maka wannan ƙazamin ɗakin naka wanda ko numfashi mutun daƙyar yake iya fitarwa!!kuma inaso ka sani Haroon baka ci bulus ba, zamu rama duk wani wulaƙancin da kayi mana!!
 yana kai Æ™arshen maganar tashi ya ruÆ™e hannun ayaan suka juya zasu fita daga É—akin karaf idonsu ya sauka akan mutumin dake shigowa cikin É—akin, A wani irin firgice suka ja da baya gaba É—ayansu, shi kanshi Haroon ya sha jinin jikin shi saboda basu son da mutun ba, gaba É—aya duk abunda suka tattauna acikin kunnanshi kaf ya gama naÉ—ar komai,Â
 hankali tashe suke kallon shi,kamar yarda shima hankali atashe yake kallon suÂ
Follow my tiktok acct 👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.