Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
(Banji daɗi da ruwan addu'ar nan ya zube ba,wlh nima ina buƙatar shi don nasha)
Yanayi mara daɗi,a daren ranar Omar ya kwana yana kukan zuciya saboda abunda yayi ƙoƙarin aikata ma Hosana, ya kwana da tunanin wane hali suke aciki?sunyi bacci kuwa?baida amsar tambayoyin shi dole sai inya gansu,gashi baya jin zai iya takawa yaje dubasu saboda fargabar karsu gane cewa shine yayi masu wannan abun kunyar,matsananciyar damuwar daya sa ma ranshi ne da tunane-tunane ya haifar mashi da wani irin severe headache na 6arin kai,yaji jiki adaren nan har magani yasha amma bai sauka ba,a haka ya kwana yana juyi asaman gadonsa,
 Adaren ranar nan dai abubuwa dayawa sun faru masu daÉ—i da marasa daÉ—in ji,dama haka rayuwa take ba kullum ake jin daÉ—in ta ba,idan yau anyi farin ciki,gobe zai iya kasancewa baÆ™in cikine,idan yau anyi dariya gobe zai iya kasancewa kuka ne,haka rayuwar ke tafiya babu wani yanayi da yake kasancewa permanently,Allah yasa mu dace,yasa mu fi Æ™arfin zuciyoyinmu,kuma ya kare mu daga aikata aikin danasani,wasu sun É—auki rayuwar duniya wani abu,da har suka É—auke ta da zafi suna aikata abunda suka ga dama,sun manta da cewa acikin seconds za'a iya zare ransu su bar duniyar gaba É—aya suje su fuskanci abunda suka shuka,duka nawa ne jin daÉ—in duniyar?basa tuna donme aka halicce su,ta wace Æ™opa suka faÉ—o duniyar nan,taya zasu koma ga mahaliccinsu?daga kai fa sai likkafaninka za'a binne ka cikin Æ™abarinka,sai kuma halinka daka je dashi,na gari ne kona banza,😢Allah yasa mu cika da kyau da imaniðŸ™
Wuraren sallar Asuba Sgr ya farka daga dogon baccin daya ɗauke shi,a hankali ya buɗe eyes ɗinshi,yayin da bakinsa ke ambaton addu'ar tashi daga bacci,a kasalance ya miƙe daga kwancen da yake saman doguwar kujerar,mamaki ne ya kama shi ganinshi kwance a palour ɗinsa yana bacci instead of saman gadon shi,ya jima yana mamakin yarda bacci yayi awon gaba da shi adaren jiyan nan,sauko da ƙafafunsa yayi ƙasa,idanunshi suka sauka akan tray ɗin da sehrish ta kawo mashi na dinner ɗinsa da baici ba jiya,tsayawa yayi yana ƙoƙarin tuna abunda ya faru adaren jiya,yunƙurawa yayi tare da tashi tsaye daga saman sofa din ya soma takawa walking slowly,jin sul6in wani abu a ƙasan tafin kafarshi yasa shi yin saurin kai idonshi wurin yana kallo,mamaki ne ya kama shi ganin Mayafin yarinyar nan yashe a kasa,yasan cewa shiya cire mata mayafin amma abunda ya ɗaure mashi kai zaman me gyalenta keyi acikin part ɗinsa?
  russunawa yayi tare da kai hannunshi ya ruƙo gyalen tare da ɗagowa dashi yana kallon shi,sai lokacin ya tuna abunda ya faru jiya tsakanin shi da ita,na commanding ɗinta da yayi akan tayi tsallen kwaɗi,to ina yarinyar take,tambayar daya jefa ma kanshi kenan,
  Cikin sauri ya zagayo ta bayan sofas ɗin tunkan ya ƙarasa ya hangi yarinyar kwance magashiyyan a sume bata motsi,tasha wahala sosai sam baiyi tunanin cewa zata cigaba da yin frog jump ɗin ba,yasan ba komai ne yaja hakan ba face tsananin tsoronshi da take ji,shiyasa bata yi tunanin ta tafi ba,tunda taga bacci yayi awon gaba da shi,
    A hankali ya ƙarasa takawa inda take sannan yaɗan zuƙunna agabanta yana kallon sumar kanta data rufe mata fuskarta,hannu yasa tare da ruƙo gashin kan nata,ya janye mata shi daga saman fuskarta ixuwa gefe guda,
  Zuba ma kyakkyawar fuskarta ido yayi yana kallon yarda tayi jaga jaga da hawaye duk ta yamutse saboda kukan da tasha,idonta sun kumbura,haka la66anta ma sunyi suntum dasu,tsananin tausayinta ne ya kama shi,baiji daɗin baccin daya ɗauke shi ba,da baibari tasha wahalar nan ba,ba da nufin ya cutar da ita yayi hakan ba,kawai yaso ya ɗan hukuntata ne donta kiyaye shi sosai,
   miƙewa yayi tare da nufar wurin fridge ɗinshi,ya buɗe ya ɗaukko bottle water daga ciki mai sanyi,sannan ya dawo inda sehrish take ya cire murfin tare da ɗebo ruwan a hannunshi ya yayyafa mata shi a fuskarta,ruwan na sauka asaman fuskarta,taja dogon numfashi tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya,a hankali tashiga mutsu mutsu zata buɗe idanunta,
  "Get up" yace,jin muryarshi yasa sehrish ware idanunta akan sgr dake zuƙunne agabanta,jikinta har kerma yake yi wurin yunƙurawa tare da tashi daga kwancen da take ta zauna,tun kafin taji me zaice ta shiga bashi haƙuri tana cewa"dan Allah ka yafe mun babban yaya,bazan ƙara maimaita kuskuran da nayi....,.'
  Kasa ƙarasa maganar tayi,a firgice ta shiga girgiza mashi kai ganin yadda ya ɗago da hannunshi,duk a tunaninta marinta zaiyi amma sai taga akasin hakan,a hankali ya aza tafin hannunshi a saman lallausar fatar gefen fuskarta,ɗan zaro ido sehrish tayi tana kallon fuskarshi,yayin da shi kuma yake kallon brownish lips ɗinta dake ta faman kerma,
  Almost 5 mins sannan yace"Tashi ki tafi,"ya ambaci hakan tare da zame hannunshi daga gefen fuskarta sannan ya miƙe tsaye hannunshi ruƙe da bottle water ɗin yana maida murfin robar,daddagewa sehrish tayi tare da yunƙurawa daƙyar ta miƙe,aikuwa nan take ƙafafunta suka bada wani irin sauti ƙasss!,a gigice ta saki wata irin razananniyar ƙara nan take ƙafafun suka gaza ɗaukarta,gaba ɗaya ta tafi zata kife ƙasa,sai dai ina kafin takaiga ƙasan tuni hannun sgr ya damƙi qugunta kwakkwaran ruƙo yayi mata da hannu ɗaya,gabanta ne taji yayi wani irin bugu daga bisani kuma ta shiga sauke ajiyar zuciya ba ƙaramin tsorata tayi ba,har lokacin hawaye ne ke zubowa daga cikin idanunta,janyota Sgr yayi ta faɗo saman jikin shi gaba ɗaya,sannan ya ɗan russinar da kanshi tare da ɗago da ita,ya sanyata a saman kafaɗarshi,yadda kasan ya ɗauki wannan ɗiyar robar ƴar tsana,haka ya sa6i sehrish asaman shoulder ɗinshi,tafiya ya soma yi ɗauke da ita,ya ƙarasa wurin fridge ɗinshi tare da ajiye roban ruwan dake hannunshi,sannan ya juyo tare da kama hanya ya fito daga part dinshi kai tsaye ya nufi downstairs,ajiyar zuciya sehrish ke ta faman saukewa tayi lamo abunta,yadda take jin daɗin kafaɗar tashi tamkar ta hau Jirgin sama,
  A natse yake taka matattakalar benen ɗauke da ita har ya ƙarasa saukowa da ita cikin Main palour ɗin nasu,bin ko'ina yayi da kallo babu kowa da alama basu kammala shirin zuwa yin sallar asubahin ba,duk da dama lokaci bai ƙarasa yi ba,a lokacin ake ta haramar fara kiran sallan,
Tunani ya shiga yi a ina zai sauke yarinyar,don shi bai ta6a sanin ma a ina yarinyar take rayuwa acikin gidan ba,har wani lumshe ido sehrish take yi saboda yanayin da ta shiga wata irin kasala ga baccin da take ji,ta gaza yarda cewa sgr ne da kanshi ya sa6ota asaman kafaÉ—arshi,jin abun take kamar a mafarki,duk da halin da take ciki amma har addu'a take yi cikin ranta Allah yasa dagaske ne ba mafarki bane,
  Yana cikin wannan tsayuwar ɗauke da sehrish a kafaɗarshi,kwatsam Abbansu ya fito daga bedroom ɗinshi ya tunkaro main palour din,sai faman sauri yake yi don yaje ya tashi sauran su tashi su kimtsa lokacin sallah yayi,tunɗazu yake trying numbers ɗinsu don ya tashe su amma mutum ɗaya ne kawai yayi picking call ɗin,wato kanal yousouf,amma sauran babu wanda ya ɗaga alamar basu tashi daga bacci ba,
  Da wa Allah ya haɗa shi?ae yana fadowa babban falon karaf idanunshi suka sauka akan Sgr dake ɗauke da Sehrish a kafaɗarshi,har sai da gabanshi ya faɗi,cikin sauri Abba ya ɗan ja da baya saboda kar Sg rafayet ya ganshi,har wani murza idonshi yake yi da hannayenshi don ya ƙara tabbatarwa da kanshi abunda yake gani,wai ko idanunshi ne ke nuna mashi ba dai-dai ba,lamarin ya ɗaure mashi kai,tsananin mamaki ne matuƙa ya kama shi,har ƙara leƙawa yake yi don ya tabbatar ma kanshi wanene acikin matasan nashi ya ɗauko mace a kafaɗarshi,
  Hasken fatar sgr,da kuma wannan doguwar ƙirar tashi ne suka tona mashi asiri,uwa uba doguwar sumar kanshi,
 Doubting ya shiga yi yana cewa"Anya kuwa shine?kodai idona ne ke nuna min ba dai dai ba,kodai tsufa ne yazo mun gadan gadan harya sa nake ganin hakan!kai wannan fa Rafayet ne ba wani ba,yarinyar daya ɗauko a kafaɗarshi kuma wannan yarinyar ce sehrish!ita kaɗae ce ƴar matashiya acikin gidan!idan har zargina ya tabbata toh me ya haɗa shi da yarinyar ne harya ɗaukko ta saman kafaɗarshi?Hakan na nufin a bedroom ɗinshi ta kwana"? Ya jefa ma kanshi tambaya,gaba ɗaya ya kuma ruɗewa,
 Can dai yace"Ina yi mashi kyakkyawan zato,amma tabbas akwai alamar tambaya anan!"
 Shiru ya ɗanyi yana ƙara leƙensu,abunne ya daure mashi kai sosai tunda yake bai ta6a ganin sgr da mace haka ba,aranshi ya shiga cewa kodai Ya fara kula mata ne?wata'ƙil akwai wata alaƙa atsakanin shi da yarinyar,'
 Jinjina kanshi yayi tare da cewa"Biri yayi kama da mutum tabbas!sai yanzu na gane inda ya samu jan baki asaman ƙirjinshi,Oh ni hussein ina nan sake da baki ana mun aika aika acikin gidana!nagode ma Allah daya nunamin wannan abu akan idona,nasan me zanyi!"
 Yana fadin hakan ya juya tare da komawa part ɗin nasu,don ya tashi sauran dama Upstairs ya nufa don ya tashi Omar,abunda yasa ya koma saboda baison sgr ya ganshi ya gane cewa ya ganshi ɗauke da Yarinyar a kafaɗarshi,
  Jin takun tafiya yasa Sgr juyawa don yaga wanene,Azmee ce ta fito tana ta faman ƴan waige-waige,bakomai ne ya fito da ita ba face neman Sehrish, taje bedroom ɗinta donta tashe ta daga bacci taga babu kowa,hakan yasata fitowa don ta nemeta acikin gidan,
  "Ke,zonan,"a ɗan firgice Azmee ta kallo inda yake,dama tunda taji an ambaci hakan tasan cewa Sgr ne,saboda shi kaɗai ke mata wannan kiran kai tsaye kamar wata ƙaramar yarinya,ko sunanta bai iya faɗi sai dae ke,don shi a yadda ya ɗauka duk wata mace ƙarama take awurinshi,
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.