Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
A ƙarshe dae da abun ya fara yi mata yawa da kanta ta tunkari sayyadi a ɗakinshi lokacin yana a gida baije aiki ba,tunda ta shigo ɗakin ya ɗaure fuskarshi yana daga kishingiɗe saman gadonshi,
Wuri tasamu daga gefe ta zauna ta gaishe shi daƙyar ya amsa mata ma,yadda kasan auren ƙiyayya sukayi dashi,
"Meyasa kake barin mu da yunwa baka ajiye mana abinci acikin gidan nan yanzu?
ta6e bakinshi yayi tare da cewa"Yaushe rabon da kiban haƙƙina na aure?hakanan zan zauna ina ciyar dake da ƴa'ƴanki ne saboda haihuwata kukayi?
"Allah ya kiyaye in ƙara haɗa shimfiɗa dakai sayyad!rashin sani ne yasa ko lokacin baya nake baka haɗin kai,amma yanzu nagane ko kai wanene.... '
Murmushi ya saki yana kallonta batare da ya ƙara tanka mata ba,
Cigaba da magana tayi"bai kamata laifina ya shafe su ba,su fa ƴa'ƴanka ne jininka ne!meyasa zakayi masu horon yunwa saboda laifin da nina maka?haba sayyad sai kace ba ƴa'ƴanka ba?akan idonka ake wulaƙantasu amma ko ajikinka,narasa gane wannan abun.........'takaici ne yasa ta kasa ƙarasa maganar ta fashe mashi da kuka,cikin shessheƙar kuka taci gaba da cewa"tun da na haifi yaran baka ta6a nuna masu soyayya irin ta mahaifi ba,tun satin farko da suka zo duniya,ko ɗaukarsu bakason yi,me yasa dan Allah?kayan sawar su ma duk sun tsufa sunyi masu kaɗan,amma baka ta6a ɗaukar ko fallan atampha ba wannan kace gashi a ɗinka masu,wai kai wani irin mutun ne!?
Da buÉ—ar bakinshi sai cewa yayi"Dabba!"
Shiru abu tayi tana kallonshi kamar ta rufe shi da duka haka take ji,
 "Ko kin manta munanan kalaman da kika jefe ni dasu ne?da bakinki fa kika kirani da sunan dabba,"
 "Dan Allah to kayi hakuri komai ya wuce,ni so nake kawai ka daina yi mana horon yunwa ko dan saboda yaran nan,koda ace ni ba zaka bani ba,su yara ne basu san komai ba,ba zasu iya jurar yunwa ba,sannan kuma ya kamata ka sanyasu makaranta tunda bakinsu yafara buɗewa sosai suna magana,"ba don taso ba haka ta dinga lallashi akan ya taimaki yaran,
 Sai da ya mula ya sha iska sannan yace"ni bazan iya ɗaukar nauyin karatunsu ba,saboda ni ban fito gidan arziƙi ba kamar Abusufyan,kinsan cewa Ni malamin makaranta ne,makarantar ma ta islamiyya,salary ɗina bai wuci 20k ba,idan har kinason kula da yaranki ki tashi tsaye ki nemi kuɗinki mana,'
 Fuskarta ɗauke da damuwa tace"Meyasa zakayi mun haka sayyad!idan kasan cewa ba zaka iya ɗaukar nauyin su ba,meyasa ka bari na haifesu....  '
 Yunƙurawa yayi tare da miƙewa yabar mata ɗakin yana faman buga tsoki,ta jima zaune jugum aɗakin nashi,kafin ta miƙe ta koma bedroom ɗinta,zirga zirga tashiga yi tana neman mafitar yadda zata samu kuɗi don ta tallafama rayuwarsu,bakowa bane ya faɗo mata aranta ba face Ya haris,tana da tabbacin cewa in yaji halin da take ciki zasu iya taimaka mata duk da tana jin kunyar tunkararsu amman bata da wata mafitar data wuce wnn,addu'a ta shiga yi Allah yasa har yanzu da number shi data sani yake amfani,
Da wayar makwabciyarta tayi amfani wurin kiran Haris,cikin sa'a ta shiga,lokacin daya ɗaga kiran taji muryarshi sai ta fashe mashi da kuka,nan fa hankalinshi ya tashi ya shiga tambayarta ko lpy,bata 6oye mashi komai ba,game da halin rayuwar da suke ciki ita da ya'yanta,haris yayi mata al'ƙawarin zai taimaka masu,su bashi lokaci,
Bayan wasu ƴan kwanaki haris yayi mata aiken kuɗi masu yawa,dasu tayi amfani wurin nema masu makarantar boko da kuma islamiyya,wani lokacin har zama takeyi da kanta ta koya masu karatu,sun ɗan samu sauƙi a wannan lokacin kafin sayyadi ya sake ƙunsa masu wani baƙin cikin,ya kwashe mata Sehrish da jahad 6at aka neme su aka rasa,kamar abu zata yi hauka wurin nemansu,ashe zuwa yayi ya saida ma ƙungiyarsu yaran don suyi amfani dasu,shi kuma suka bashi makudan kuɗi,Mijin maman sadeeq ne ya tona mashi asiri a wurinta,saboda yaga lokacin daya gudu da yaran a 6oye ya tafi dasu,ranar kaca kaca sukayi dashi har bugunta sai da yayi saboda shaƙo kwalar rigarshi da tayi tana jifanshi da munanan kalamai,a ƙarshe tace zata haɗa shi da Allah in bai dawo mata da ƴa'ƴanta ba,tun daga ranar ta fara sallar dare tana kai kukanta wurin Allah,duk yadda sayyadi yaso ya juye mata tunani akan ta daina ibadar nan amma abun yaci tura,ko yayi nufin yi mata asiri babu abunda ke yin tasiri ajikinta,
A ƙarshe dae sae gashi a tsakar dare aka dawo mata dasu sun fita hayyacinsu sunyi jaga-jaga dasu,kamar an jefosu haka ta gansu sun faɗo ɗakinta,sae kuka sukeyi ko sutura babu ajikinsu,ga miyau na zalala abakunansu,hankalin abu ba ƙaramin tashi yayi ba,sai lokacin taƙara sanin wanene sayyadi,kuma ta fara kokwanton cewa Anya ƴa'ƴanshi ne,gaba ɗaya kuɗinta sae da suka ƙare wurin nema masu magani don tunda suka dawo ciwon kai,ciwon ido,ciwon ciki,ciwuka iri-iri haka suka dinga fama dasu,har gadon asibiti aka kwantar dasu sukayi jinya duk ita ke faman ɗawainiya dasu tare da Maman sadeeq,har mijin ta yana zuwa dubasu a asibitin sannan ya taimaka masu da wani abun hadi da addu'oi,amma Sayyadi kuwa ko leƙo asibitin baiyi ba,koda aka sallame su suka dawo gidama basu same shi ba,haka abu taci gaba da shan wahalar rayuwa,ko makarantarma acikin sati bai wuci sau biyu suke zuwa ba,saboda rashin lafiyar da suke ta fama da ita,kuma duk in sukaje makarantar da kuka suke dawowa,saboda yara dake tsokanarsu akan cewa mahaifinsu ɗan mafiya ne mai yankar kawunan mutane,wannan abun ba ƙaramin cutar da rayuwarsu yake yi ba,shiyasa duk suka tsani zuwa makarantar,
Akwai wani lokaci da Sehrish ta fito waje cikin unguwarsu ta miƙi hanya tana tafiya tana kuka abun duniya yayi mata,kwata kwata basu jin daɗin rayuwarsu ta ko'ina a ƙuntace suke,a daidai wannan lokacin Wata danƙareriyar mota tayi parking a gefenta,cikin sauri matashin dake cikin motar ya buɗe ya fito ya tunkareta,sam bata lura da shi ba har sae da ya ruƙo hannunta,a firgice ta juyo tana kallonshi da idanunta waɗanda sukayi jawur saboda kukan da tasha,ga majina duk fuskarta ta 6aci,zuƙunnawa yayi agabanta yana kallonta,gwanin ban tausayi ƴar ƙaramar yarinya ko kallabi babu akanta balle takalma,ga kayan jikinta duk sun 6aci,
Kamar yadda yake kallonta haka itama take kallonshi,É—an gayu dashi yasha wankan suit ajikinshi,
Cikin sanyin murya yace"Ya sunanki"?
..cikin shessheƙar kuka tace"dan Allah ni ka rabu dani,ka ƙyale ni in tafiyana,'
Abun yaso ya bashi dariya,shafo fuskarta yayi tare da cewa"FaÉ—amun me yasa kike kuka?idan kika faÉ—a mun zan taimake ki,'
A ƙule tace"Nidai ka ƙyale ni dan Allah,kawai ka rabu dani,kona faɗa maka babu abunda zaka iyayi mana saboda babu mai sonmu Allah ne kawai ke son mu,'
Tuni yaji hawaye sun cicciko mashi acikin idanunshi,Haris dake zaune cikin mota yana hangensu ta glass ɗin motar ba ƙaramin tausayi yarinyar ta bashi ba,
lallashinta ya shiga yi yana cewa"kiyi haƙuri kinji?bakowa ne baisonku ba,Nima gani kuma ina sonku sosai,ashirye nake dana taimake ku indae kunaso,zan ɗauke ku mu gudu mu bar ƙasar nan,in tafi tare daku can wani wuri mai daɗi kuyi rayuwarku ko baki so?
"dagaske kake"?muryarta tamkar zatayi kuka tayi maganar,
É—aga mata kai yayi alamar eh,tare da cewa"yanzu ki biyoni mu tafi batare da kowa ya ganmu ba,"
Girgiza mashi kai tayi tare da cewa"Su hosana fa?su bazaka tafi tare dasu ba?Oummanmu fa?itama anan zaka barta,
"Kada ki damu suma duk zanzo in É—aukesu daga baya,"
Maƙe mashi kafaɗa tayi tace"a'a ni bazan bika ba,sae dae inje in kirasu Johad da hosana,mu tafi atare,"
"Shikenan zan jiraki ki kirasu,kada ki faÉ—a ma kowa babu wanda zai san mun tafi,"
Amsa mashi tayi da toh sannan jiki na rawa ta juya da gudu ta koma gidan,
Sai lokacin haris ya fito daga cikin motar jikinshi a sanyaye ya ƙarasa inda abusufyan yake zuƙunne,hannu yasa tare da ɗan bubbuga kafaɗarshi yace"Yanzu ka tabbatar da abunda nake faɗa maka ko?
Muryarshi tamkar zai fashe da kuka yace"Haris yaran nan fa ƴa'ƴana ne!ina ji ajikina,hatta kamannin fuskarsu ma irin nawa ne,bansan ya akai hakan ya faru ba,mutumin nan baida Imani dama na jima ina zarginshi,kuma zanyi bincike akanshi,bazan ƙyaleshi ba haris,ni babban abunda yafi damuna yadda yake tafiyar da rayuwar yaran,kamar sunfi kowa rashin gata aduniya,ƴar ƙaramar yarinya kamar wannan har tasan cewa kowa baison su,tama rasa ina zata tsoma ranta saboda ƙuncin da take ji,so yake su kamu da ciwon zuciya tunda ƙuruciyarsu," ƙarasa maganar yayi tare da miƙewa tsaye yana share kwallar data zubo mashi,
"Akwai matsala fa,muddin rayuwar yaran nan taci gaba da tafiya ahaka,yakamata muyi gaggawar sanar da Abbanku domin ashawo kan matsalar tun kafin ka rasa yaran nan!amma inaso yanzu idan suka zo mu fara biyawa asibiti domin ayi masu gwajin jini don mu tabbatar da cewar Æ´a'Æ´anka ne,"
Yana kai ƙarshen maganar tashi,sae ga Sehrish ruƙe da hannun Hosana da jahad,ta ruƙo hannun kowannansu sun fito daga gidan,ko abu batasan da fitar su ba,saboda ta shiga makwabtansu wurin maman sadeeq don ta samo masu abincin da zasu ci,
Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyar abusufyan lokacin da yayi arba dasu,ruƙe da hannun juna,kamar jira yake yi su ƙaraso wurinshi,ya zuƙunna tare da haɗasu duka ya rungumesu a ƙirjinshi,ya jima dasu a haka kafin ya raba jikinshi da nasu,anan ne yayi masu hoto da wayarshi,ya ɗaukesu a yadda suke kaca kaca dasu da niyyar ya nuna ma gwaggon katsina don taga halin da yaran suke,ko zasu nemi mafita,
Akan idon mijin maman sadeeq mlm nura,abusufyan ya sanya su sehrish acikin motarshi,a back seat suka zauna,haris kuma shike driving É—insu,
Shi kanshi yayi mamakin yadda yaran suka amince suka biyo shi,ko mahaifiyarsu basu nema ba,duk irin shaƙuwar dake tsakaninsu da ita wannan zai tabbatar maka da cewar ta kansu sukeyi,sun gaji da komai,
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.