Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Tun yana cikin toilet wayar shi ke ta faman ringing,cikin sauri ya fito daga cikin toilet ɗin,jikinshi ɗaure da towel,ƙarasawa yayi inda ya ajiye wayar asaman pillow,ya miƙa hannunshi ya ɗauki wayar yana duba mai kiran nashi,murmushi yayi aranshi yace"Allah yasa jiya sun samu bacci,don na lura da yadda suke ta faman ɗokin son ganin ƴar uwar nan tasu,nima kaina a ƙagare nake dana haɗasu wuri guda,don su cigaba da rayuwa atare,
 Picking call ɗin yayi ya kara wayar a kunnanshi,
 Tun kafin yayi sallama muryar hosana ta katse mashi hanzarinshi da cewa"Ya omar!yaushe zaka zo ne!kai muke ta jira,jiya fa ko bacci ba muyi ba,
 Tana kai ƙarshen maganarta Jahad ta kar6e da cewa"ya Omar dan Allah ka tausaya mana,wlh ko breakfast ba muyi ba,kuma muna jin yunwa amma mun fi so muci abinci atare da ƴar uwarmu,"
Jin wannan maganar ta Jahad,yasa jikin shi yin sanyi,da alama ba ƙaramin so suke yi ma junansu ba,
 "Ya omar kayi shiru,"muryar hosana ce tayi maganar a ƙagare,
 cikin natsuwa ya soma magana"kuyi haƙuri kunji,insha Allah yau zaku ga ƴar uwarku,bazan samu zuwa ba,amma zan turo major ya ɗauko ku,abunda nake so daku yanzu,ku ci abinci ku ƙoshi,sannan kuyi wanka ku shirya ku sanya kaya masu kyau,a kowane lokaci zaku iya ganinshi yazo,"
 Yana jiyo muryoyinsu ta cikin wayar suna ta faman fadin Wayyo daɗi yau zasu ga rishi ɗinsu,'
 Sallama yayi masu bayan ya ajiye wayar,ya juya tare da wuce wa wurin closet ɗinshi,tsaf ya shiga shirya kanshi acikin rantsattsiyar shaddar shi.
SEHRISH,
Kwankwasa ƙopar ɗakin da akayi mata ne da ƙarfi,yasa ta tashi a firgice tana faman zazzare ido,ƙankame bargon jikinta tayi tana ƙara lullu6e jikinta dashi,fuskarta duk a yamutse saboda kukan da tasha jiya,amma yanzu Alhamdulillah tun da tafarka babu wannan ciwon cikin atare da ita,tamkar bata ta6a yin ciwo ba haka ta farka,taji sauƙi sosai,
  "Reesh,baby junaid ne fa,in shigo daga ciki"?
Muryar junaid ce taji yana magana daga waje,
 akasalance tace"eh,ka shigo,"
. tura ƙopar yayi tare da sanya kafa ya shigo cikin ɗakin hannunshi ɗauke da cup sae tiriri ke fitowa daga ciki,bakomai bane aciki face Corn flakes daya haɗo mata,yaji Uwar madara acikinshi,
  Sae faman murmushi yake sakar mata,wuri ya samu daga gefen gadonta ya zauna,sannan yace"reesh ya jikin naki?jiya ko bacci banyi ba saboda damuwa da halin da kike ciki,'
 "da sauƙi junaid,yanzu bana jin ciwo atare dani,na wartsake sosai,amma ina fata kaima kana cikin ƙoshin lafiya ko?naga fuskarka kamar ta canza kamanni,kayi haske sosai kuma fuskar ta ɗan sauya haka,Lips ɗinka sun ɗan kumbura kaɗan kalarsu ta ƙara cizawa sosai'tayi maganar yayin da take ƙare ma fuskar tashi kallo kamar wata malamar duba
 Junaid yace"farin cikin da kika bani jiya shine ya canza mun kamannin fuskata,ko kin manta abunda mu kayi jiya acikin Mota tare da ke?fuskarshi ɗauke da murmushi yayi maganar,
 Cike da mamaki sehrish tace"wane abu kenan?yaushe muka haɗu acikin mota?bayan bakazo ka ɗauke ni daga school ba,ni da ka manta dani junaid,nasha wahala jiya sosai,kamar bazan rayuwa ba,na neme ka na rasa.......'muryarta tamkar zatayi kuka tayi maganar,
 "Sehrish!me kike nufi da banzo na ɗauke ki ba?ko raɗaɗin ciwo yasa kin manta da abunda ya faru jiya atsakaninmu"?
 girgiza kai tayi alamar a'a tace"Nifa bakazo ka ɗauke ni ba,jiya da aka tashi daga school ciwon ciki ya kamani,shine na shiga toilet anan na yanke jiki na faɗi saboda azabar ciwon da nasha,gaba daya nafita hayyaci na.......'gaba ɗaya sehrish ta bashi labarin abunda ya faru da ita tun daga A har zuwa Z,abu ɗaya ne bata sanar dashi ba,shine zuwan waɗan nan matasan guda huɗu da suka ɗauketa a mota,
Tun da ta soma kora mashi bayani,hankalinshi yayi mugun tashi,jikin shi har kerma yakeyi wurin cewa"reesh dagaske ne duk abunda kika faÉ—amun"!.
 ɗaga mashi kai tayi alamar eh,sannan tace"ka faɗamun me ya hana ka zuwa ka ɗauke ni junaid?nayi tunanin zaka dawo ka ɗauke ni,in kaji shiru ban dawo gida ba,amma bakazo ba,'
 Gaba daya ta gama rikitar dashi duk yabi ya ruɗe,muryarshi har rawa takeyi wurin cewa"wlh nazo jiya school ɗinku,kuma naɗauke ki dakaina acikin motata.......'gaba daya junaid ya kwashe duk abunda ya faru tsakanin shi da jahad ya sanar ma Sehrish,
 Zuba mashi ido tayi tana kallonshi ita kanta hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba da jin labarin da junaid ya bata,
 "Junaid!ban karyata ka ba!amma anya ba gamo kayi ba?zai iya yiyuwa fa aljana ce in ba haka ba,taya za'a ce tana kama dani komai da komai har ka gaza gane cewa ni ce ko bani bace,"?a ruɗe tayi maganar tana kallon junaid,
Junaid sarkin tsoro tuni idanunshi sun cicciko da kwalla tsoranshi kar ace lokacin mutuwar tashi ne yayi shiyasa ya fara Æ´an gane gane,zai iya yiyuwa ma mutuwarce tafara kawo mashi ziyara kafin tayi wuff dashi,
 tuna wannan yasa shi fashe mata da kuka yana cewa"innalillahi wa'inna ilaihir raji'un shikenan lokacina yayi sehrish,dama nasan daƙyar zan wuce yau araye,....'
 Hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,ganin yarda junaid ya fashe mata da kuka,da alama ya tsorata sosai'
 "Junaid ya isa haka,ka daina kuka kaji,insha Allah ba yanzu zaka mutu ba,har sai mun yi aure mun haifi ƴa'ƴa,in ma zamu mutu atare mutuwar zatazo ta ɗauke mu,'
 Jin wannan zancen na sehrish yasa shi yin tsit yana faman sauke ajiyar zuciya,ga dariya na cinta amma tana tsoran karya kuma fashe mata da wani kukan,aranta tace"Tabɗijancan su junaid ansha soyayya da al'jana,da sauƙi ma tunda iya kiss suka tsaya,"
Miƙa mata cup ɗin hannunshi yayi tare da cewa"gashi kisha,corn flakes ne ni na haɗa maki da kai na,"wani irin tausayinshi ne taji ya kamata,musamman yarda ya nuna damuwarshi akanta,har ya haɗo mata cornflakes dakanshi don tasha,'
 zuba mashi ido tayi tana kallonshi,fuskarshi duk a yamutse babu alamun natsuwa atattare dashi,duk ya firgice da jin cewa ba ita bace ya ɗauko a school ba,kuma hankalinshi bazai ta6a kwanciya ba har sae ya tabbatar da cewa ba aljanu bane suka fara kawo mashi ziyara,
 Cikin sanyin murya tace"Junaid,dan Allah ka share hawayenka kaji?ko ka manta da alƙawarin da ka ta6a yi mun na cewa ba zaka ƙara yin kuka ba"?
 Muryarshi akasalance yace"nadaina,kiyi haƙuri bazan ƙara ba," yayi maganar yayin da yake miƙe mata cup din,
 "Ba zaka ban abaki nasha ba"?
É—agowa yayi yana kallonta jin abunda tace,tayi mashi hakan ne don ta kawar da damuwar dake a fuskarshi,
Matsawa yayi kusa da ita sosai,sannan ya zura hannunshi tare da dauko cokalin ciki,ya ɗebo cornflakes ɗin ya miƙa mata abakinta,
 Buɗe bakinta tayi ya zuba mata aciki,a hankali take murzar shi abakinta tana haɗiyar shi,yayi mata daɗi sosai saboda madarar daya zuba aciki,
Haka yaci gaba da bata abakinta tana sha,tun fuskarshi na aɗaure harya fara sakin wannan murmushin nashi,ganin ya washe daga damuwar da yake ciki yasa sehrish cewa"junaid,Wai jiya Uncle ɗin nan naku ya ƙaraso ne"?
 "Eh,yanzu haka yana acikin gidan nan ma,ya kamata kije ki gaishe su,hada aunty azeema kanwar Abbanmu itama tazo jiya,"
 wani irin farin ciki ne ya lullu6eta cike da zumuɗi tace"inaso naje na gaishe shi,amma ina jin fargabar zuwa wurin shi,"
 Junaid yace"meyasa toh?na gaya maki cewa basu da matsala,uncle dinmu mutun ne mai sauƙin kai fiye da tunaninki,haka Aunty azeemarmu ma tana da mutunci sosai,baki ga gift ɗin da takawo mun ba,zan nuna maki anjima,zaki sha mamaki,"
 murmushi sehrish tayi a lokacin harya kammala bata corn flakes ɗin,
"Bari nashiga toilet nayi wanka,idan na kammala shiryawa sai mu tafi tare da kai ka rakani wurinshi in gaishe dashi,'
Amsa mata yayi da toh,sannan ya miƙe tare da ɗaukar cup ɗin daya ajiye asaman side drawer dinta,ya fuce dashi,
Ajiyar zuciya ta sauke,bayan fitar shi ta sauko daga saman gadon tare da nufar dressing mirrow dinta ta tsaya tana kallon kanta ta cikin madubin,hannu tasa ta shafo sumar kanta da sgr ya datse mata shi,nan take ta tuna da abunda ya faru jiya lokacin daya shigo yi mata allura,wannan kallon da yayi mata ya tsaya mata aranta,da kuma kalaman da ya furta mata cikin sanyin murya,tabbas tana ji aranta cewa sgr ya fara jin abunda take ji agame dashi,duk da tasan cewa zaiyi wuya ya gane cewa akwai soyayya atattare dashi,kuma zaiyi wuya ya iya furta mata ita,
ta cikin mirror ta hango jacket din da sgr ya sanya mata,tana ajiye saman gadon,juyawa tayi cikin sauri tare da kai hannu ta É—auko rigar sanyin tana kallonta,
 tunani tashiga yi rigar wanene wannan?taya akai tazo bedroom ɗinta kuma asaman gadon nata!?
 ƙamshin Turaren jikin jacket dinne ya bata amsar tambayar da take nema,
Matse rigar tayi a hancinta,anan ta dinga jin ƙamshin turaren Sgr sosai ajikin rigar wannan ya tabbatar mata da cewa tashi ce,a hankali tashiga tunanin ta yadda akai jacket dinshi tazo bedroom ɗinta,kodai jiya ne daya zo yi mata allura..... '
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.