Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
08062073990
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining.
Snack
Awarah
Farah
Zobo
Samosa
Cup cake etc
Contact me 09063302182or 09012179727.
*💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة ØØ¨ رومانسية بين Ø³ØØ±ÙŠØ´ ÙˆØ§Ù„Ø¬Ø±Ø§Ø Ø§Ù„Ø¹Ø§Ù… Ø±ÙØ§ÙŠØªðŸ’‹ðŸ’˜â¤ðŸ¤â¤ðŸ’•💖*
*Ga duk maison karanta littafin Abban sojoji,zai biya 300 ne,za'a tura mashi tundaga farko har inda muka tsaya,kuma zai cigaba da samun update dinshi akai akai,ga wanda ke buƙata zai tura mun message ta whatsapp ɗina (08103884440) kada ku bari abaku labari*,
😔
Abunda ya faru,lokacin da wata mata ta kira junaid da sunan mommynshi don yazo ya ɗauketa a airport,jiki na rawa junaid ya shige cikin motarshi ya kama hanyar zuwa airport bayan ya fita daga gidanne ya tuna da tace in ya fito ya sanar da ita,fiddo wayarsa yayi da niyyar kiranta,tunanin taya zai kirata ma ba number ya shiga yi,adaidai lokacin ta sake kira tambayarshi tayi ya fito ne,ya amsa mata da eh yana a akan hanyar zuwa,cigaba da tafiya yayi zuciyarshi cike fal da son ganin mommynshi,driving yake yi yana ayyana farkon haɗuwarshi da mommynsu baisan wani irin runguma zaiyi mata ba,yayi zurfi acikin tunaninshi kwatsam sae ga wasu jerin motoci sun kusa goma sha biyu,baƙaƙe kuma da black tinted,da gudun gaske suka nufo inda junaid yake,koda junaid ya lura da motocin nan fa hankalinshi yayi mugun tashi,ƙarasowarsu ke da wuya suka zagaye motar shi,yadda bazai iya kubce masu ba,nan fa hankalin junaid yayi mugun tashi,jikinshi ya shiga rawa,tsoranshi kar ace mutanen da mommy azeema ta sanar dashi cewa suna bibiyar rayuwarshi ne,zama yayi acikin motar hankali a matukar tashe,
É—aya daga cikin motocin aka buÉ—e,sae ga wani gabjejen mutun faffaÉ—an gaske sanye cikin suits,kai tsaye ya nufi motar junaid hannu yasa tare da knocking glass É—in motar,zuge glass É—in junaid yayi atsorace yana kallonsu sae faman haÉ—iyar yawu yake yi da kyar,
kafin yayi wani yunƙuri Mutumin nan ya buɗe motar tashi,gaba ɗaya ya cakumi junaid ya toshe mashi baki,ya nufi cikin motarshi dashi,bayan ya sanyashi acikin motor,atare suka tashi motocin da gudun gaske suka bar wurin,
junaid dake a back seat na motar tuni ido ya raina fata,hawaye suka shiga wanke mashi face ɗinshi,muryar shi tamkar zaiyi kuka yace"Su wanene ku?laifin me na aikata maku?dan Allah kada ku rabani da rai na,inason na sake ganin Abbana.....'bai kai ƙarshen maganar tashi ba,ɗaya daga cikinsu ya daka mashi tsawa tare da cewa"Shut up!ko tari ka ƙara yi saina fille maka kai,"
Jin haka yasa junaid yayi tsit zuciyarshi na bugawa da ƙarfi da ƙarfi,
Wani katafaren gida suka shiga tare da shi,bayan sunyi parking É—in motocin,É—aya daga cikinsu ya buÉ—e motar tare da É—auko junaid asaman kafaÉ—ar shi,ya wuce dashi cikin gidan,a babban falon gidan ya sauke shi,sannan ya juya ya fuce,
To fa,tsayawa junaid yayi cikin tashin hankali yake kallon haÉ—aÉ—É—en falon komai a gyare tsaf,tunani ya shiga yi mai yasa suka kawo shi nan suka ajiye shi?ko dae kidnapping É—inshi sukayi ne?hannu yasa yana share hawayen shi,bai kammala wiping É—insu ba,yajiyo takun takalmi kwas kwas,
A firgice ya ɗago don yaga wanene,zuba mata ido yayi yana kallonta,daga saman stairs take saukowa down,jikinta na sanye da doguwar riga fara mai shegen kyau tabi shape ɗin jikinta,ƙafafunta kuma na sanye da takalma high hills farare duk da tsayin da take dashi don sam ba gajera bace,ba ƙaramin kyau shigan tayi mata ba,kasancewarta farar fata,wuyanta na sanye da ziririyar sarƙa fara ta diamond,hannunta kuma na sanye da Zobe ɗaya kacal a middle finger,shima na diamond ne,ta ɗaure gashin kanta abaya,mai tsayi wanda launinsa yake tamkar golden yellow,
A hankali ta ƙarasa saukowa daga saman benen,sannan ta tsaya tana kallonshi daga inda yake tsaye,duk da akwai tazara atsakaninsu amma suna iya ganin juna sosai,ƙare mashi kallo tashiga yi,burinta junaid ya fara shaida ita wacece kafin ta sanar mashi,
hakanan ya dinga jin gabanshi na faɗuwa rass rasss,batare da jin tsoro ba ya tunkareta sai da ya kusa kaiwa inda take sannan ya tsaya yana kallonta,ƙwayar idanunta yabi da kallo blue colour wanda hakan ya tabbatar mashi da cewar mommynsu ce, dama kuma yasan ta a hoto,komai na fuskarta irin na Babban yayansu ne,duk da ta kwana biyu aduniya amma hakan bai 6oye kyawun fuskarta ba,tamkar ƴar shekara 30 haka fuskarta take,hatta jikinta yana nan yadda yake da kyau da kuma diri,
A hankali junaid ya furta"Mommy!is you?
jinjina mashi kai tayi alamar eh,da gudun gaske ya ƙarasa tare da faɗawa jikinta,sosai ya ƙankameta saboda tsabar farin ciki ya fashe mata da kuka,nan take itama kukan yazo mata atare suka shiga yin kukan babu mai lallashin wani,tamkar zasu haɗe jikin junansu su koma ɗaya haka suka ƙanƙame kansu,daƙyar Alexandra ta iya dakatar da kukan nata,ta sanya hannayenta tare da ɗago da fuskar junaid tana kallonshi,hawaye sun wanke mashi fuskarshi tass,
muryarta na rawa ta ambaci sunan shi"Ro..meo.É—ina,'
Cikin shessheƙar kuka junaid yace"Mommy,ashe zan sanyaki acikin idanuna,bansan da wasu kalmomin zan bayyana maki irin farin cikin da nake ciki ba,i luv u so much mom....'
Jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba,duk irin watsin da tayi dashi tabar Nigeria,hakan bai hana shi sonta ba,
Kwantar dashi ta sake yi asaman ƙirjinta,ta sanya hannayenta tana ɗan bubbuga bayanshi,kafin ta mayar da hannunta ɗaya acikin sumar kanshi,ta jima tana mamakin girman shi,ta tafi ta barshi a lokacin da yake ɗan jinjiri dashi,amma yanzu tadawo ta same shi ya girma ya zama babba,ba ƙaramin farin ciki taji ba,mara misaltuwa,
ɗago dashi ta kuma yi daga jikinta cikin sanyin murya tace"romeo ɗina,kayi haƙuri ka daina wannan kukan duk da nasan na farin cikin ganina ne,ni kaina bazan iya misalta farin cikin dana ji ba,wai yau ni ce tare da babyn dana bari yana jinjirinshi,ya girma ya zama babba,nayi danasanin tafiya nabarka romeo,nayi kewarka sosai,hakanan na raba kaina dakai,ba don bana sonka ba romeo,zan iya cewa nafi sonka fiye da kowa aduniyar nan.....na godema Allah daya nunamin wannan ranar....inaso na sake neman yafiya a wurinka saboda na cutar da rayuwarka sosai,ko wani yaro lokacin da yake jinjiri burinshi yaji dumin mahaifiyarshi,ya kasance atare da ita don samun kulawa daga gareta a koda yaushe,koda ace yana da uba,amma kai baka samu wannan gatancin ba,ka tashi hannun maza ba'a hannun mahaifiyarka ba,baka samu soyayyar nan ba,duk da mahaifinka yayi ƙoƙari sosai wurin gina rayuwarka tayi kyau,haka ƴan uwanka ma ba su bari ka zubar da hawayenka ba,amma duk da haka nasan abun ya jima yana maka Ciwo..."
Tana ƙarasa maganar,ta zube saman guiwowinta agabanshi,tana roƙon yafiyarshi,hakan ba ƙaramin tayar mashi da hankali yayi ba,cikin sauri shima ya zube saman guiwowinshi suna fuskantar juna ita dashi,
"Mommy dan Allah ki tashi,banason kina duƙamin,komai ya wuce yanzu tun da kin dawo wurinmu da ranki kuma da lafiyarki,har yanzu kina da sauran damar da zaki gyara kuskuren da kikayi abaya mommy," ashagwa6e ya ƙarasa maganar,murmushi ta saki tana kallonshi,ji take yi da tana da ikon da zata mayar dashi cikin cikinta,taƙara haifo shi da tayi,don kawai ta bashi wannan kulawar daya rasa,
Sun jima a wannan yanayin,kafin daga bisani suka miƙe tare,ta ruƙo hannunshi cikin nata,ta wuce dashi upstairs ɗaya daga cikin bedrooms ɗin dake a wurin suka shiga,ɗakin ya haɗu sosai,
"Mommy me yasa ba kije gidaba?wurinsu Abba su ganki? Yayi tambaryar yana kallonta,
"I just came because of u junaid,inaso mu samu lokaci sosai atare,ka ganni dakyau nima na ganka da kyau,tun yanzu in fara aikina na baka kyakkwayar kulawa kamar jariri,in yaso gobe zamu shiga gidan da safe ko?
Murmushin jin dadi junaid yayi tare da cewa"Eh,mommy,dama ni yakamata in fara ganinki tunda dama nine ban sanki ba a zahiri"
"Bansani ba ko kana jin yunwa,amma zansa akawo mana abinci,in baka abaki kaci ka ƙoshi,yau dae atare da babyna zamu kwana,'
Dariya junaid yayi,ba ƙaramin daɗin maganarta yaji ba,sosai mommynshi ta shiga bashi kulawa a wannan lokacin,
Kunji yadda akai junaid ya kasance tare da mommynshi,har ta É—auko ma Abbansu video É—insu saman gado ta tura mashi,abunda yasa kuma Abban bai gane Voice É—inta ba,shine da kanta tayi amfani da wayarta wurin canza muryarta don ta tsoratar da Abbansu.
💋Boss Bature💋
fitowa Abbansu yayi daga cikin ɗakin nashi fuskar nan tashi awashe saboda tsabar farin cikin dawowar Alexandra,bakomai yafi faranta mashi rae ba face Junaid daya gani rungume ajikinta,yaji daɗi sosai,ko ba komai Junaid dae ya haɗu da mommynshi,hankalinshi zai ƙara kwanciya,
Bai sanar masu da zuwan nata ba,saboda sunyi waya da ita ta sanar dashi cewar till tomorrow zasu shigo gidan don tana bukatar kasancewa da junaid don su kara fuskantar juna sosae,hakan yasa ya bari kawai sae goben sannan su ganta unexpected,duk da a kagare idanunshi suke da suyi tozali da ita.
Gaba daya suka haÉ—u atare suka wuce masallaci,
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.