Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
ɗan murmushin yaƙe Sehrish ta saki tare da cewa "ba haka bane just bana jin yunwa ne shiyasa," ta faɗi tamkar zatayi kuka, Ido ya gani rai naso,
Murmushi kawai Amrish tayi kafin tasa hannu ta ɗauki ƙaramar wuƙar dake ajiye saman kazar tashiga yankar naman tana ci,
Ƙiris ya rage sehrish tasaki miyau saboda tsabagen kwaɗaituwa da tayi cikin sauri ta gyara natsuwarta gudun kar tayi abun kunya agaban sabuwar ƙawarta,
Muryar amrish ce ta katse ta da cewa "Ko lemun ba zaki sha ba"? Cikin sauri tace"eh a ƙoshe nake," giɗa kai tayi sannan taci gaba da cin abunta, suna cikin zaman nan sai gasu Naja'at da parveena sun shigo, kai tsaye wurinsu suka nufa suka samu wuri suka zazzauna,
Naja'at tace "Wlh da wata irin yunwa na fito Class ɗin can, sam bana gane ma karatun, dama can nifa ba gane math nake ba,' tayi maganar tare da sa hannu ta ɗauki robar lacasera tare da buɗeta ta kwafa abakinta tana kwankwaɗa, hankalin sehrish ba ƙaramin tashi yayi ba ganin tashanye mata lacasera ɗin da Amrish ta kawo masu, Ana cikin haka parveena ta tsoma hannu suka cigaba da cin roasted chicken ɗin da Amrish ta kawo masu, kafin kace mai tuni sun kwamushe komai, duk tana zaune tana faman haɗiyar yawu, sai da suka kammala sannan ma suka lura da ita, parveena tace "Au! Wai dama Yarinyar nan tana a wurin nan? Yo aini yunwa tasa nagaza gane ku nawa ne zaune a table ɗin muka tarar," ta faɗi da mamaki Naja'at ma tace"ko ni ban lura da ita ba, sai da kikayi magana Allah, sannu ko? Meyasa ke bakici komai ba ne,"
Tamke fuska sehrish tayi rai a6ace tace "bana jin yunwa," jinjina kai su kayi atare naja'at tace "halan kinyi breakfast dayawa ne a gida"?
A ƙule sehrish tace "Bansani ba," acikin zuciyarta tayi maganar a fili kuma tace "eh,"
daganan suka ci gaba da firar su har Parveena ta ƙaro masu abincin duk tana zaune suka zauna suka lamushe suka bar rishi da tanɗar baki, da lokacin komawa Class yayi kowa ya wuce Ajinsu naja'at da parveena class ɗinsu ɗaya don haka suka wuce atare, ita kuma tabi Amrish izuwa nasu Class ɗin,
Sehrish ba ƙaramin jiki taji ba, saboda azabar yunwa har wani jiri take gani, dishi² ta runƙa gani a idonta sam batasan me aka koya masu bama,
Lokacin da suka taso daga school tunani ta soma yi wa zai zo ya ɗauke ta, ga school bus tashigo cikin makarantar amma tsoranta kar ace kuɗi za'a biya,tsayawa tayi hannunta ruƙe da school bag ɗinta sai faman lullumshe ido take yi, suna cikin tsayuwar nan sai ga drivern Amrish ya iso, sallama tayi ma sehrish sannan ta shige cikin motar suka tafi,
Hankalin Sehrish ba ƙaramin tashi yayi ba, ganin sai zuwa ake ana kwashe sudents ɗin ita gatanan tsaye zugudum babu alamar wani zaizo ya ɗauke ta,
tana cikin wannan tunanin motar JUNAID tashigo cikin makarantar adai² inda take tsaye yayi parking ɗin motar tare da zuge glass ɗin motar yace "madam muje ko," ajiyar zuciya ta saki ba ƙaramin daɗin zuwan shi taji ba, buɗe motar tayi tashiga sannan yaja motar suka fita daga makarantar,
Miƙar hanya yayi dasu yana cikin driving ɗin yaji sehrish ta faɗo masa a kafaɗarsa ta langwa6e, saboda shock ɗin daya ji har saida yaɗan ci burki a tsakiyar titin, aza idonsa yayi akanta, wani irin wahalallan bacci ne ya ɗauke ta batare da saninta ba, shine ta faɗo masa a shoulder ɗinsa, gaza janye idonsa yayi akanta yadda take ta faman sharar baccin ta ba ƙaramin kyau tayi masa ba, ya jima yana kallon kyakkwawar fuskarsa, sam.ya manta cewa a tsakiyar titi suke, sai go slow suke haɗawa batare da saninsa ba, har sai da wani babban mutun yayi masa magana ta waje, sannan ya tashi motar yaci gaba driving ɗinsa cikin kasala,
har suka ƙaraso gidan adai² parking space ɗinsu ya ajiye motar, sannan yajuya ya kalli sehrish tare dasa hannunsa ya shafa gefen fuskarta tare da ambaton sunanta"Sehrish mun iso gida fa, wake up pls ," ya furta yana kallon yadda take motsi da idonta alamun zata tashi,
daker ta iya buÉ—e idonta tana kallon shi sunyi jawur dasu ga bacci ga yunwa, junaid yace "reesh kamar baki lafiya fa? Look at ur eyes fa sun janza kala,
A kasalance tace "yunwa nake ji sosai banci komai ba tunda naje school, ga wani wahalallan bacci da nake ji," ta ƙarasa maganar tana faman yin hamma, har time ɗin suna acikin motar,
Tun da tasoma magana junaid ya saki baki yana kallonta har sai da takai ƙarshen maganarta sannan yace "Kina nufin wai baki ci komai ba a school to saboda me? Ya tambaya yana kallonta
Yamutsa fuska tayi tare da cewa "junaid ban fa da ko sisi balle na sayi abinci, shiya sanya,"
Wani irin kallo junaid ke bin ta dashi kallon na tausaya maki, ga takaicin daya hanasa yin magana,jin yayi shiru yasa ta cewa "ka tashi mu shiga ciki, kuma naga kana kallonta,"
A ƙule yace "Haushi kika ban ne,shiyasa nagaza magana, reesh waya ce maki sai kin biya kuɗi zaki ci abinci? An fa riga anbiya kuɗin komai na school ɗinki, tun daga school fees har kuɗin abincin ki dana school bus da zaki dunga hawa har na tsawon 3 months fa,"
Jin haka yasa sehrish zaro ido waje baki asake tana mamakin ashe itace shashashar batasani ba ta hana kan ta cin haƙƙinta, ashe an biya kuɗin komai ita kanta takaicin ne yasa ta yin kasaƙai,
Fitowa sukayi daga motar atare suka shige cikin gidan a babban falon suka rabu ta wuce bedroom É—inta shi kuma ya wuce upstairs É—akinsa, babu kowa acikin gidan abunda ya É—aure mata kai,
tana shiga ciki tayi wurgi da school bag É—in sannan tashiga tu6e uniform É—in suma duk nan tayi watsi dasu saman gadonta, bayan ta kammala ya rage daga ita sai half vest da gajeran wando, toilet tashige shaf shaf tayi wanka tare da É—auro alwala tafito, cikin hanzari ta buÉ—e wardrobe É—inta ta zumbula doguwar riga, sannan ta zura hijabi tare da shimfiÉ—a darduma ta kabbara sallar, tana kammala sallar ko addu'a bata tsaya yi ba, ta haye saman gadonta ta baje tashiga sharar bacci maganar yunwa kuma wata'kil saita tashi sannan tashiga neman abinci,
Turo ƙopar Azmee tayi ta sameta tana ta jan minshari bin ko'ina tayi da kallo ganin yarda tayi wurgi da school bag ɗinta ga uniform ɗinta data watsar saman gadon, murmushi kawai tayi tare da girgiza kai tace "ƴan makaranta kenan, tun yau anfara wurgi da shool bag ga uniform a watse saman gadon maimakon ta ninke su," ta faɗi da murmushi a fuskarta sannan taja mata ƙopar ta fuce,
ta jima tana bacci sai wuraren sallar la'asar sannan tafarka da wata irin matsiyaciyar yunwa ba arziƙi ta fito ta wuce kitchen, har time ɗin babu kowa, roƙon da take yi Allah yasa babban yaya ba us suka koma ba,
Acikin tray ta haÉ—a abincinta sannan ta zauna a kitchen É—in tana ci tana tunanin duniya,'
**********Twins***************
Duk yinin ranar ba inda suka je saboda tashin hankali sam sun rasa inda zasu tsoma ransu, tun da sanyin safiya bayan sun dawo daga sallar asuba, haroon ya faɗo masu ɗaki domin ya ƙara jaddada masu akan buƙatun daya nema a wurinsa, Jahan ya tsawatar masa akan cewa ko nawa yake so zasu bashi amma kada ya sake yayi kuskuren cewa zai ƙara kusantar ɗaya daga cikinsu, da jin wannan maganar sai haroon yace ya amince amma bisa sharaɗin cewa zasu ƙara mashi miliyan 80 in har suna son ya daina bibiyarsu Kuma cikin sati guda kacal ya basu in ba haka ba zai tona masu asiri 😥😳
tun safe basu ci komai ba, ko fitowa ba suyi ba daga bedroom ɗinsh, kuma babu wanda ya lura da hakan illa junaid da yayi ta tambayarsu har ɗakinsu sai da yazo yayi ta faman knocking yana kiran sunan su, suna jin shi tamkar zasu yi kuka amma basu amsa mashi ba,ƙarshe yayi tunanin cewa basa nan yayi tafiyarsa,
Ayaaan ya sha kuka aduk lokacin daya tuna abunda ya faru dasu daren jiya sai yayi yunƙurin amai, yanzu haka ma yana zaune gefen gadon idonsa jawur ya ɗago ya kalli jahan dake ta faman safa da marwa acikin ɗakin yace "Dan Allah jahan mu hanzarta mu sama mashi kuɗin daya buƙata, if not wlh so yake ya kashe mana rayuwa," ya faɗi yana faman matse hancinsa da yayi jawur saboda matsar daya sha da hannunsa,
Jahan ya dubesa cikin damuwa tare da cewa "Ayaan bansan ya zanyi ba ! Wa zan fara tunkara game da kuɗin nan? duk wanda zamu tambaya acikin brothers ɗin mu ko Abban mu dole sai sunji me zamuyi dasu kafin su bamu, daga baya ma zasu tambaye mu ina abunda muka siya dasu, don haka Mommy ce kawai nake tunanin zata iya bamu kuɗin amma matsalar shine tana fushi da mu saboda bama kiranta a waya muna gaishe ta," Jahan ya ƙarasa maganar tare da samun wuri ya zauna kusa da Ayaan ɗin,
"Jahan mom ita kaÉ—ai ce solution, mu jaraba kiranta kawai mu sanar mata mu ji mai zata ce,"
"Video call zamu kira ta, may be tafi tausaya mana in taga yanayin mu" Acewar jahan, yayi maganar tare da miƙewa ya ɗauko laptop ɗinsu dake ajiye saman drawer ɗinsu, komawa yayi ya zauna dab da Ayaan sannan ya zaro wayarshi tare da buɗe laptop ɗin, duk ayaan na zaune zugudun yana jiransa ya kira,
zama su kayi suka ƙurama screen na laptop ɗin ido suna jiran mommyn nasu ta ɗaga kiran cikin sa'a ta ɗaga masu kiran, har haɗa baki suke yi wurin cewa "Mommy," tana zaune cikin haɗaɗɗen garden saman gujera hannunta ɗauke da cup na coffee da alama sha takeyi, ta jima tana kallonsu sai daga bisani tace "sai yau kuka ga damar kira na"?
"Sorry mom ba haka bane.....," suka faɗi atare, girgiza kai alexandra tayi tare da cewa "to menene? halan wani abu ku ke buƙata shiyasa kuka kira ni"?
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.