Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
A ranar da baba alamu zai tafi dasu hossana, akan idon osman Aunty babba ta fito tare dasu jahad da hossana,ta buɗe masu motar hafsat suka shiga, duk yana kallonsu, daga bisani kuma sai yaga hafsat tafito hannunta ɗauke da trolley hakan na nufin wani ne zaiyi balaguro, bayan hafsat ta shiga cikin motar taja motar tafito dasu daga cikin gidan, cikin sauri osman ya hau mashine ɗinsa da yake ajiyesa acikin gidan yabi bayansu a hankali yake tuƙa mashin ɗin don kar su ganshi, da hafsat ta tsayar da motar abakin titi tana jiran ƙarasowar baba alamu, sai osman ya dakata da tukin mashin ɗinsa, cikin sauri ya sauka tare da samun wuri ya cire rigar jikinsa ta kakin sojoji ya 6oyeta a ƙarƙashin wani benci dake agaban wani shago dake rufe, sannan ya tu6e wandon jikinsa ma, ya ajiyesa a ƙarkashin bencin bakomai yasa shi yin hakan ba face don karsu ganshi da kakin sojoji yana binsu, Asirin shi zaiyi saurin tonuwa ne,
Sai daya rage daga shi sai farar shirt da gajeran wando ajikinsa a lokacin motar baba alamu taƙaraso,cikin sauri Osman ya zuƙunna agaban mashin ɗin tamkar ya samu matsala yana gyaransa, alhalin nan duk salon dabaru ne na jami'ae,
yana gyaran mashin ɗin yana satar kallonsu, akan idonshi hafsat ta buɗe ma jahad da hossana mota suka fito sannan ta ɗauko masu trolley ɗinsu da food basket ɗinsu ta basu,bayan hafsat ta tafi, baba alamu ya amshi akwatin Su hossana da jahad ya wurga cikin boot ɗin motarsa, daga nan jahad da hossana suka shiga cikin motar, shima ya shiga tare da tashin motar suka tafi, cikin sauri Osman ya haye mashin ɗinsa tare da tashinsa yabi bayan motar baba alamu da gudun gaske amma bai bari ya ƙurewa motarsa ba kasancewar Motar baba alamu glass ɗin jikinta duk ya fashe, muddin osaman ya ƙurewa motar tofa zasu iya hango shi, hakan yasa ya basu tazara sosai, yana cikin tuƙin mashin ɗin ya ɗan jinkirta tare da zura hannu cikin aljihun wandonsa ya zaro wayarsa tare da bugama major kira, bayan ya ɗaga yake sanar dashi duk abunda ke faruwa,
Hankali tashe major yace "Osman kada ka bari ya kubce maka, kaci gaba da bin motarsa, sannan kabar wayarka a kunne zamu biyo diddigin layinka, mu zo inda kuke," bayan osman ya amsa masa, ya mayar da wayar, sannan ya ƙara ma mashin ɗinsa gudu, a lokacin da motar baba alamu tashiga dajin da gudun gaske, jahad na ƙoƙarin fitowa tana ihu bayan ta samu ta harba murfin motar ya buɗe, sai baba alamu ya girgiza motar da mugunta, ta faɗo ƙasa timmmm goshinta ya bugu, ta taso da gudu tana bin motar tana kiran sunan hossana daga bisani ta yanke jiki ta faɗi, adai-dai lokacin shi kuma osman ya ƙaraso ba komai yasa shi yin jinkiri ba fa ce wayar da yayi da major shiyasa bai ƙaraso akan lokaci ba har baba alamu ya kubce mashi,
ganin jahad da yayi yashe a ƙasa ta sume ga jini, ba ƙaramin razana yayi ba, cikin hanzari yayi wurgi da mashin ɗinsa ya nufe ta hankali atashe, ya zuƙunna gabanta yana faɗin "ke!ke!! tashi ki tashi dan Allah, kada ki mutu,"
Adai-dai lokacin kuma motarsu Marshal Omar ta faso cikin dajin ta hanyar tracking layin osman da sukayi yasa har suka ci nasarar cimma inda yake,
Osman na ganin motarsu Marshal yasan cewa sune aciki, a lokacin omar ya zuge glass ɗin motar a tsorace ganin jahad kwance duk jini a goshinta, harya harzuƙa zai fito daga cikin motar, cikin sauri Osman yace "yalla6ai ya gudu da ɗayar, gashi can ya miƙi hanyar dama da ita, don Allah ku ceci rayuwarta," jin haka yasa Omar fasa fitowa daga cikin motar, cikin sauri major yaja motar da gudun gaske suka bi motar baba alamu a lokacin ya ɗanyi masu nisa, hayaƙin da bayan motar baba alamu ke fitarwa shine yasa suka gane hanyar da yabi,
suna isa basu tsaya buɗe kopar katakon gidan gonar ba, kai tsaye major yabi ta ƙopar atsiyace ya tarwatsa katakon gidan gonar suka shige,
Tamkar zaki haka omar ya fito daga cikin motar ya afkawa É—akin da baba alamu ya shige da hossana,
*Wannan shine abunda ya faru taƙaice kenan*
"Ya omar ina hossana take ita'? Omar yace"hossana tana cikin ƙoshin lafiya, itama ƙarin jini akeyi mata, yanzu haka bacci take sha tana a kusa da ɗakin nan," ajiyar zuciya jahad ta saki kafin ta kuma cewa "ya omar kullum hossana saita ambaci sunanka, komai akayi sai tace "ya Omar fa," ita bata son rabuwa da yaya omar ɗinta,"
Murmushi Omar ya saki jin abunda jahad tace,
"Amma ya Omar ba zaka ƙara rabuwa damu ba ko? dan Allah kada ka haɗamu da kowa kabarmu kawai a wurin ka, kai kaɗai ke son mu," tayi maganar idonta akansa tana jiran amsar shi,
Omar yace "ko wancan time ɗin bada son raina nabar ku ba, jahad you're always in my mind ina jin ku araina,amma yanzu komai ya wuce just forget about the past, ku ƙaddara cewa wani abu bai ta6a faruwa da rayuwarku ba na ƙunci, saboda yaya omar ɗinku ya shirya maku kyakkyawar rayuwa ta jin daɗi da walwala, masarauta ce wadda ku kaɗai zaku mulketa sai yadda kuka ga dama zakuyi acikinta, hatta yaya omar ɗinku zai zama tamkar bawa agare ku,"
dariya kawai jahad ke faman tiƙa saboda murnar jin abunda omar ke cewa, hatta dr Emran da Camila dake tsaye murmushi kawai suke saki, shima major dake tsaye daga ƙopar ɗakin murmushi ne a fuskarsa, ƙarasa shigowa ciki yayi yana cewa "Sir idan ba damuwa inaso a bani muƙami acikin masarautar nan, zanso na zama sojan dake kula da princesss ɗin dake acikinta, bama ni kaɗai ba ga abokina osman nan shima yana roƙon gimbiya jahad da ta bashi damar zama ɗaya daga cikin masu kula dasu,"
Abun sai ya zama tamkar shirin wasan kwaikwayo gaba ɗayansu dariya ce a fuskarsu, hakan ba ƙaramin farantawa omar rai yayi ba ganin yadda jahad ke faman tiƙar dariya, sai yaji sanyi aransa sam ya gaza janye idonsa akanta,
Muryar Camila (kameela) ce ta katse su da cewa "Yalla6ai nima idan ba damuwa ina neman alfarmar zama É—aya daga cikin masu yi ma gimbiya jahad hidima, ko da a matsayin jakadiya ne mafi kusanci dasu,"
Fashewa da dariya jahad ta ƙara yi daga kwancen da take har omar na cewa "Bi a sannu my baby, kada ki shaƙe,"
gaba É—ayansu sun natsu sai raha akeyi, suka ji Muryar hosana kamar daga sama tace"YA OMAR,"
Atare suka juya suna kallonta, tsaye take a bakin ƙopar ɗakin daker take buɗe idanunta tana kallonsu, hannu tasa ta murza idonta sannan ta ƙara buɗe su da kyau donta tabbatar da abunda idonta ke gane mata, tabbas kuwa shine wato yaya Omar ɗinta,
tsananin farin ciki ne yasa hossana ƙarasa shigewa ciki da gudun gaske tana isa inda Omar yake ta zube saman guiwowinta tare da kifa kanta asaman laps ɗinsa tana kuka,
Shiru su kayi gaba ɗayansu na wani lokaci suna sauraren kukan da hossana ke yi, gaba ɗaya jikin omar ya gama mutuwa saboda yasan yarda yarinyar ke tsananin ƙaunarsa dole tayi kewarsa, hannu omar yasa tare da shafa gashin kan hossana cikin muryar lallashi yace "Am so sorry hossana,nasan nayi laifi ban ma san da wane baki zan iya baki haƙuri ba,"
Maimakon ta É—ago sai ta daddage ta gartsa mashi ciwo a laps É—insa, runtse ido omar yayi saboda yaji zafin cizon, babu wanda ya lura da abunda ke faruwa sai jahad, tun da taga omar ya runtse ido tasan cewa Hossana Cizon shi tayi,
tayi mashi hakan ne don yasan irin raɗaɗin da suka ji acikin zuciyoyinsu na ƙin zuwan da yayi ya tafi dasu,
buɗe idonsa yayi a hankali yana sauke ajiyar zuciya ya kalle ta, a lokacin itama ta ɗago tana faman huci ta ɗaure masa fuska tare da haɗe masa girar ƙasa da sama tana kallon shi,
Cikin sanyin murya ya sake maimaita "Am sorry again," ya furta tare da kai hannunsa a fuskarta yana share mata hawayenta dake kwaranyowa daga idonta,
Cikin kuka tace "Ya omar yanzu ka kyauta abunda kayi mana? ka tafi kabarmu cikin tashin hankali ko waiwayon mu, ba kayi ba yanzu da mun mutu shikenan bazan sake ganin Ka ba sai dai a lahira ko?
Æ´ar dariya omar yayi tare da cewa "Amma ae yanzun baku mutu ba ko? Kuna raye kuma ga yaya Omar É—inku atare daku, mai yayi saura yanzu"? ya tambaya yana kallonta
Hossana tace "sai ka kaimu gidan ku inda kake rayuwa, don wlh duk inda zaka je, ƙafarka ƙafarmu, mu da kai mutu ka raba takalmin kaza," ta ƙare maganar tana zumbura baki,
Gaba É—ayansu na cikin É—akin dariya kawai suke yi, Kallon dr emran omar yayi kafin yace "yanzu mai ya rage dr?yaushe kake tunanin za'a sallame su, in yaso sai acigaba da basu kulawa acan gida?
dr emran yace "zuwa night, ae jikinsu yayi ƙarfi yanzu saboda ƙarin jinin da akayi masu, idan ma ba damuwa Camila zata iya cigaba da kula da lafiyarsu, in har kana buƙatar hakan, tunda dama naji tace tana son zama hadimar princess ɗin naka,"
Murmushi suka saki gaba É—ayansu banda hossana don batasan zancen ba, tuni ta mayar da kanta akan laps dinsa tana faman sauke ajiyar zuciya,
dukkan tsanani yana tare da sauÆ™i, mahaÆ™urci kuma mawadaci ne wata rana, babu wani yanayi na rayuwa da yake kasance wa na dundundun, Innallaha ma'assabirin tabbas wannan haka yake, iya haÆ™uri dae su hossana sunyi kuma sun jurema duk wata jarabawa da suka fuskanta na Æ™uncin rayuwa, basu fasa yin addu'a ba suna kai kukan su ga Allah ba kuma basu fidda rai da cewa Allah zai kawo masu É—auki ba, idan muka sa haÆ™uri kowa zai cimma nasara, gashi yanzu zamu iya cewa Masha Allah ðŸ˜ðŸ‘‘
**************Twins *******************
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.