Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
A hankali Motarsu tashiga babban gate din gidan Abusufyan,major ne ke driving dinshi yayin da Omar ke hakimce a seat ɗin baya,sai faman zullumin haɗuwarshi da hossana yake saboda yasan cewa ba ƙaramin fushi take dashi ba,saboda ƙin zuwan da yayi,
Parking ɗin motar major yayi sannan ya fito tare da buɗe mashi motar,a hankali Omar yasa ƙafa tare da fitowa daga ciki,sannan cikin sauri batare da 6ata lokaci ba ya wuce cikin gidan,
Tunkan yasa ƙafarshi cikin parlourn nasu yajiyo shessheƙar kukan hossana,tsayawa ya ɗanyi yana sauraron abunda suke cewa,
  "Hossana wai ba zaki daina kukannan ba?salon ki 6ata kwalliyarki ko"?
 "Jahad ba zaki gane bane,bakisan yarda nake ji bane,saboda ya omar nayi kwalliyar nan,amma ta tashi a banza,yau ma bazaizo wurin mu ba...'cikin shessheƙar kuka ta ƙarasa maganar,
ƙayataccen murmushi Omar ya saki a fuskarshi,kafin yasa kai tare da shiga cikin palourn,samunsu yayi zaune asaman 3 seater,hossana ta kwantar da kanta asaman hannun sofa ɗin,yayin da jahad ke gefenta tana rarrashinta,gaba daya duk sunyi wanka sun canza kayan jikinsu,riga da skirt ne ajikin jahad,hossana kuma gown ce mai kyan gaske,
  jin alamar motsin mutum yasa jahad ɗagowa tana kallon shi,cike da mamaki ta buɗe baki zatayi mashi magana,da hanzarin gaske ya dakatar da ita ta hanyar yi mata nuni da hannunshi alamar ta tashi ta tafi,murmushi jahad tayi tare da miƙewa cikin sanɗa tabar saman sofa ɗin ta koma saman 1 seater ta zauna tana kallon dramar da ya Omar ɗinsu zai shirya,cikin sanɗa ya lalla6a tare da komawa wurin da jahad ta tashi ya zauna,sannan yakai hannunshi tare da ɗan janyo wutsiyar gashinta,
A fusace tace"dan Allah jahad ki rabu dani inji da abunda ke damuna,ki tashi kiban wuri,"
Murmushi Omar yayi tare da cewa"zan tafi amma ki fara faÉ—amun meyasa kika damu da yaya Omar É—inki har haka"?
Sam hossana bata gane voice É—inshi ba saboda ranta a6ace yake,
"Saboda inason shi sosai,jahad nasan ni kawai nake haukana,yana can wurin hayatyn shi,suna shan soyayya.....'
Katse ta Omar yayi da cewa"kina kishi ne"?
A faɗace tace"saboda me bazanyi kishi ba,nima ae zuciyata ce a ƙirjina ba dutse ba,"
Wannan maganar ta hossana ba ƙaramin dariya taba marshal Omar ba,hatta jahad sai da ta murmusa daga inda take,
Kwantar da kanshi ya ɗanyi abayanta yana cewa"am really sorry babyn Omar,nayi missing ɗinki sosai,nasan nayi laifi ayimun afwa bazan ƙara ba..."jin muryar Omar raɗau a kunnanta yasa tayi hanzarin ɗagowa tana kallonshi da idanunta da suka cicciko da kwalla,
Waro ido Omar yayi yana kallonta ba ƙaramin tsorata yayi ba da ganin makeup ɗin da ke a fuskarta,ta dambara Uwar foundation kamar wata aljana,Jan bakin da ta shafa ya 6ata fuskarta har wurin cheeks ɗinta saboda uban kukan da tasha,ga maskara ta zazzago mata a ƙasan idonta,
Hankali tashe Omar yace"subhanallahi,kuke ganinmu bamu muke ganinku ba,Babyn Omar wannan kwalliyar fa?dama itace kwalliyar da ake cewa anyimun don inzo in gani,"cike da zolaya yayi maganar,amma tamkar ya tunzura hossana nan take ta 6are baki itare da fashewa da wani sabon kukan,
Dariya jahad ta dinga tiƙa kamar kamar me har tagaza dakatar da kanta,
Yama rasa ta inda zai fara shawo kanta don ya lallashe ta,hakan ya ƙara hasalata,kamar wata ƙaramar yarinya,ba ƙaramin tausayi ta bashi ba yasan duk don saboda rashin zuwan shi ne,hannu yasa tare da janyota jikinshi yayi hugging ɗinta sosai yana ɗan bubbuga bayanta,lokaci guda ta nemi kukan da takeyi ta rasa,sai gata tana faman sauke ajiyar zuciya,
a hankali ya furta"am really sorry hossana,bazan ƙara 6ata maki rai ba,kullum zan dinga zuwa idan ma bansamu halin zuwa ba zan kira ku awaya mu gaisa,"
Ya ƙarasa maganar tare da cewa"kin yafe mun"?
ƙasa ƙasa tace"na yafe maka,amma karka ƙara,"
murmushi yayi tare da É—agota daga jikinshi yana kallon fuskarta,sai faman cin magani takeyi tana haÉ—e mashi fuska,
"Kin ci abinci kuwa"?
"A'a banci ba,"
"Why"? Ya tambaya yana kallon bakinta da take ta faman turowa irin na shagwa6a66u,
"Kai nake jira kazo ka bani abaki,"
"Really"? É—aga mashi kai tayi alamar eh,
Juyawa ya É—anyi tare da kallon jahad dake zaune tana kallonsu gwanin burgewa yace"dagaske hossana bata ci komai ba"?_
Amsa mashi tayi da eh,jinjina kai yayi sannan yace"ki kawo mata dinner ɗinta anan,sai na tabbatar da taci ta ƙoshi sannan zan tafi,"
Murmushi jahad tayi tare da miƙewa ta wuce downstairs don pta shiryo masu dinner din,"
_💋Boss Bature💋_
Yau da wuri suka dawo cikin gidan wuraren karfe goma dai dai,wani irin tsoro da fargaba sehrish taji,musamman da azmee ta sanar da ita cewa ga dinner É—in sgr can taje takai mashi,bakomai ya faÉ—o mata arai ba face abunda ya faru É—azu tasan cewa dole ya tuhumeta saboda ita kaÉ—ai ce macen da take shiga part É—insa,sai faman zarya takeyi acikin bedroom É—inta,tana tunanin yarda zata tunkare shi ayau É—innan,
Hayaaam
Tafiya takeyi cikin sanÉ—a tana waige waigen ko akwai wani a main palour din cikin sa'a taga babu kowa,murmushin mugunta ta saki tare da nufar kitchen din,tana shiga tayi arba da tray na abincin da Azmee ta shirya ma Sgr,asaman dogon table na kitchen É—in ta ajiye mata,jinjina kai hayaam tayi tare da cewa"hmmmmm yarinya kenan yau zaki fara sanin koni wacece wurin iya makirci,"
Tana faɗin hakan ta shiga ciki kai tsaye ta tsaya wurin tray din,hannu tasa tare da buɗe warmer ɗin dake ɗauke da chicken ppr soup,sai faman ƙamshi yake yi,murmushi hayaam tasaki tare da kai hannu cikin sumar kanta,ta cinko gashin kanta sannan ta jefa acikin chicken ɗin hadasa hannu ta motsashi aciki,sannan ta rufe murfin,duk hakan bai mata ba sai da tabi komai na abincin ta sanya gashi aciki,sannan cikin sanɗa tabar kitchen ɗin,tana faman sakin dariya don tasan cewa da zarar sgr yaga gashin nan yarda yake da tsaftar nan ba ƙaramin ƙyamatar yarinyar zaiyi ba,kuma tasan dole ya koreta daga yi mashi aiki,bama wannan ba dole ya hukuntata, tashin hankali da ba'a sama shi date,
💋💋💋
Fitowa sehrish tayi bayan ta gama zullumin nata,kitchen ɗin ta nufa batare da 6ata lokaci ba ta ɗauko tray ɗin a hannunta tare da wuce wa upstairs,hakanan tadinga jin gabanta na faɗuwa kamar wani mummunan abu zai faru da ita,tsayawa tayi abakin ƙopar shiga falon nashi,sai da ta dai²ta natsuwarta sannan ta zabga sallama,tana jiran jin amsawar shi,
Jin shiru yasa ta ƙara maimaita sallamar,har kusan sau uku ana huɗun ne tajiyo muryarshi yace"Come in,"
Ae tunda taji Voice ɗinsa jikinta ya shiga yin kerma,addu'o'in neman tsari tashiga karantowa abakinta,ta jima atsaye tana faman zullumin abun da zaibiyo baya kafin daga bisani ta daure tare da shiga cikin falon nashi,ƙamshin turaren nan nasa ne ya wanko mata hancinta har saida ta lumshe idanunta,tunkan taƙarasa ta hango shi kwance ya miƙe kafafunshi asaman 3 seater,jikinshi na sanye da pyjamas yellow,ba ƙaramin kyau su kayi mashi ba,kunnanshi na kare da wayarshi alamar waya yake yi,
  Gabanta na faɗuwa haka ta nufe shi tare da ajiye mashi tray ɗin asaman table dinsa,saboda tsabar rashin gaskiya,tana ajiye tray ɗin ta juya cikin sauri zata bar parlourn nashi,kamar daga sama taji anyi ma mayafinta kwakkwaran ruƙo ta baya,nan take mayafin ya sulale daga jikinta,zazzare ido waje sehrish tayi jikinta na kerma,nan take tashiga haɗiyar yawu,tsayawa tayi tana jiran maizo biya baya,
  Jin alamun motsin shi abayanta ya tabbatar mata da cewa shine yaja mayafinta daga jikinta,tsayawa tayi tana ambaton sunan Allah abakinta,ganin kusan minti biyar bata ji ya ƙara motsawa ba yasa tayi hanzarin juyawa a wani irin firgice sam bata tsammaci yana tsaye abayanta ba sai dai kawai taji ta kai mashi karo,ja da baya ta ɗanyi tana faman zare ido,tunkan ya tambayeta ta shiga cewa"dan Allah kayi haƙuri,nasan na 6ata maka rai,wlh nima bada son raina hakan ya faru ba,nashiga na gyara maka bedroom ɗinka ne,bayan na kammala shine na ɗan cire mayafina na ajiye asaman gadonka don naji daɗin yin aikin,ashe kafin na fito daga cikin toilet ɗin ka dawo,shine na same ka akwance kana bacci saman mayafina,saboda ina tsoran ka farka ka ganshi yasa nayi ƙoƙarin janshi daga jikinka,shine...cikin bacci batare da saninka ba ka...........'kasa ƙarasa maganar tayi saboda jin yatsun hannunshi da tayi asaman lips ɗinta,alamar tayi mashi shiru,sannan ya hankali ya ɗan ware eyes ɗin nashi akan fuskarta............
*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃
*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*
*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*
*LOCATION KANO*
08062073990
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining.
Snack
Awarah
Farah
Zobo
Samosa
Cup cake etc
Contact me 09063302182or 09012179727.
💋BOSS BATURE💋
Follow this link to join my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.