Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
  "Aunty azmee bana tunanin sehrish tana cikin hayyacinta ne!saboda nima nasan da maganar ƴan uwan nata,da wayata takeyin amfani wurin kiransu tun a lokacin baya,akwai ma last message da sister ɗinta ta turo mata a wayana,nacewa suna buƙatar taimakonta har a lokacin naso na tura masu kuɗi amma lokaci guda wayarsu tadaina shiga kwata kwata,sehrish da kanta ta nemi na kaita garinsu tagansu,nace mata Sai babban yayanmu ya koma Us sannan zan kaita amma yanzu kuma ace ta manta komai? Yyi tmbyar yana kallon azmee itama kallon nashi takeyi,
 Cikin mamaki tace"junaid naji kace tana amfani da wayarka wurin kiransu,kuma har message sun tura maka dan Allah idan wayar na'a kusa inason gani,'
  cikin sauri junaid ya zura hannu acikin aljihun wandon jeans ɗinshi ya curo wayar,dannata yashiga yi can cikin messages ɗin shi yashiga sai ga saƙon da Jahad ta tura mata,
 Ƙarasawa yayi dab da azmee ya miƙa matar wayar yana cewa"kin ganshi nan,"
 Hannu tasa ta kar6i wayar tashi ta zuba ma screen ɗin wayar ido tana karanta saƙon,
Jinjina kai azmee tayi tare da cewa"Tabbas ƴan uwanta ne,idan bazan mantaba ta ta6a ambaton sunan JAHAD da HOSSANA amatsayin ƴan uwanta na jini,amma meyasa sehrish take ƙoƙarin mantawa dasu?ko don saboda tana cikin wannan daular ne......'
 Junaid ne yayi hanzarin katse ta da cewa"i don't think so!rishi bazata ta6a mantawa da ƴan uwanta ba saboda abun duniya,na yarda da sehrish sosai kuma nayi imanin cewa rishi bazata ta6a yi maki ƙaryaba!tabbas akwai wani abu dake faruwa ne!!amma rishi bata cikin hayyacinta!!,
.. azmee ta gamsu da bayanin shi amma har lokacin tana mamakin yarda akai hakan ta faru,
  jinjina kai kawai tayi tace"yanzu ya zamuyi da ita junaid?inaso ni nasan awane hali ƴan uwan nata suke ciki ne,saboda inaso na haɗata dasu tun a lokacin naci burin hakan,nayi alƙawarin zan haɗata da ƴan uwanta,saboda yarda naga tana shiga damuwa akansu,
  "Aunty azmee,yanzu babu halin yin wannan,in ma muka ce zamu cigaba dayi mata magana akansu to fa za'a samu matsala saboda zata iya samun ta6in hankali,amma in muka bi komai a hankali insha Allah dakanta zata dawo cikin hayyacinta wata rana,addu'armu kawai take buƙata,
  Ajiyar zuciya azmee tayi maganganun junaid sun sa ta fara saukowa daga fushin da tayi da ita,
  amsar wayarshi yayi daga hannunta sannan ya kuma cewa"pls aunty azmee karki ce zaki juya mata,ko kice zaki canza mata hakan zai iya haifar mata da damuwa,saboda ta saba dake sosai ta ɗauke ki tamkar mahaifiyarta,"
 murmushi azmee tayi tare da cewa"shikenan junaid romeo insha Allah hakan ma bazata ta6a faruwa ba,kana da hankali sosai junaid shiyasa kake shiga ran mutane,ni nagaza fahimtar rishi,amma kai gashinan ka fahimce ta,"
  murmushi shima yayi tare dasa kai ya fuce daga kitchen ɗin,
*************
Agalabaice Amal ta kammala wanke uban kayan da suka tula mata,kaf sai da ta wankesu,ba ita ta kammala wankin ba sai wuraren la'asar,da zazza6i taƙarasa shi,gaba ɗaya ga66an jikinta ciwo suke yi mata,
  ɗakinsu tashiga ganin babu kowa aciki saboda duk suna can É—akin mamynsu hayaam da abra wadda bata jima da dawowa ba,tana jiyosu acikin É—akin suna ta faman ciye ciyen kayan daÉ—in da abra tadawo masu dashi,babu wanda ya tuna da ita duk wannan uban aikin da tayi masu,shiga ciki tayi jikinta na kerma ta faÉ—a saman lumbutsetsiyar katifarsu,bargo taja ta lullu6e jikinta dashi,dakyar take numfashi,da wani irin hucin masassara numfashin ke fita,rayuwarta gwanin ban tausayi tun safe ko wanka batayi ba,saboda babu lokacin yin wanka,koda tayi niyyar yin wankan,sun riga da sun hanata amfani da sosonsu ko sabulun wankansu,wani lokacin in jikinta ya soma yi mata tsami,ruwa kawai take É—iba tashiga ta watsa,daga bayane tayi dabarar yankar buhu tayi amfani dashi amatsayin soso, ba sabulu haka take gurje jikinta dashi,ðŸ˜
 Cike take da tsoran karsu shigo su same ta acikin ɗakinsu,saboda sun hana ta shiga ko'ina na gidan in ba kitchen ba,shima ɗin in zatayi masu girki ne,
tana acikin wannan yanayin tajiyo murya abra tana cewa"ke!uban mi ya kawo ki cikin ɗakin mu?ba mamynmu ta hanaki shigar mana ɗaki ba!! A fadace tayi maganar,tana a tsaye bakin ƙopar ɗakin,yarda kasan photocopy ɗin aunty babba haka kamanninta suke,
 Shiru Amal tayi batace komai ba zuciyarta ce kawai ke ta faman bugawa,
 Rai a6ace abra tace"ko ki tashi kona zonan inyi wurgi dake ƙazama kawai,"
  har lokacin Amal tagaza motsawa saboda nauyin da jikinta yayi mata,jinjina kai abra tayi tare da shiga ciki azafafe don tayi wurgi da ita,har takai hannu zata fisgi bargon da ta lullu6e dashi,jin muryar hayaam yasa ta dakata daga ƙoƙarin cire mata bargon da take yi,
 Shigowa cikin ɗakin tayi tare da cewa"meya haɗaki da ita ne,naji kina ta faɗa,"?
  turo baki abra tayi tare da nuna Amal É—in da hannu tana cewa"baki ga yarda ta haye mana katifarmu ba da wannan baÆ™in jikin nata duk dauda,"Â
 Sai lokacin Amal tasamu damar buÉ—e bakinta daÆ™yar murya na rawa tace"dan Allah kuyi haÆ™uri bani da lafiya,banjin daÉ—in jikina,"ðŸ˜ï¿?
dakatar da abra hayaam tayi tare da cewa"ki rabu da ita,wahalar tayi yawa just for to day ta huta,tunda bata da lafiya," sam ba haka taso ba,bata ji daÉ—i da Hayaam ta hanata hukunta amal ba,a fusace ta fuce daga É—akin tana huci
Shiga ciki hayaam tayi tare da samun wuri daga gefen katifar ta zauna,jin muryar Amal tana sambatu na raɗaɗin ciwo yasa ta kasa kunne tana sauraronta,
ï¿?
  "Ina jin cewa bazan rayu ba,dan Allah ku kaini wurin auntyna,inaso naganta kafin na bar duniya,"
  dariya Hayaam tayi tare da cewa"aikuwa dae ba zaki ta6a ganinta ba adae nan duniyar, ae kin ɗaura aure da wahala tunda kika bari aka haifoki acikin gidan nan," tayi maganar tana ƙarashe dariyarta,
 Amal kuwa fashewa tayi da kuka mai cin rai,Â
 tsawa hayaam ta daka mata tare da cewa"yi mun shiru, kuka baya maganin komai sai ma ya ƙara jaza maki wani ciwon," shiru Amal tayi tana shassheƙar kuka ƙasa ƙasa
Shigowa abra ta sake yi hannun ta ɗauke da wayar amani iphone 13 sai faman ruri take yi,miƙa mata wayar tayi tare da cewa"Sofwan ne ke kiranki,"
 "ɗan wahala," ta fadi tare da kai hannu ta amshi wayar,juyawa abra tayi ta kalli Amal dake ƙumshe cikin bargo,guntun tsoki taja tare da cewa"salon ki sakarwa mutane miyan bacci asaman katifarsu,sai kin shanye shi don ubanki," ta ƙarasa maganar tare da kama hanya ta fuce daga ɗakin,
Kara wayar tayi a kunnanta bayan tayi picking call ɗin,magana suka shiga yi dashi akan tafiyarta,duk wulaƙancin da tayi mashi hakan baisa ya rabu da ita ba, sai ma kiranta da yayi akan cewa gobe yanaso su tafi tare yakaita abujan,
Sun jima suna waya kafin daga bisa ni su kayi sallama,
tana ƙoƙarin ajiye wayar wani kiran ya sake shigowa,tsoki ta ɗanja tare da cewa"wani jarababben ne kuma yake kira na"!?
  Duba screen ɗin wayar tayi Sunan AMANI ne ya bayyana,ɗan juyawa tayi ta saci kallon Amal dake ƙumshe cikin bargo alamu sun nuna cewa bacci yayi awon gaba da ita,hakan ne yasa ta ɗaga kiran tare da karawa a kunnanta tare da yin sallama,
 On the other hand amani tace"wa'alaikum salam,hayam y kk ya gida yasu mammy"?
  yatsina fuska tayi tare da cewa"duk suna lafiya,"
  Amani tace"labarine ya same ni daga wurin aunty laila nacewa zaki koma gidansu Abbas da zama,sam abun bai dace ba wannan abun kunyar har ina?menene alaÆ™armu dasu da har zaki koma gidan surukan mu da zama?amatsayin Æ™anwar matar yayansu!Â
Jin wannan maganar ta Amani yasa ran hayaam 6aci,miƙewa tayi daga zaunen da take saboda tsiwa tamkar zata fasa screen ɗin wayar haka tashiga cewa"Ki tsaya iya matsayinki AMANI!!babu ruwanki dani, iya sa idone kawai naki kada kice zakiyi mun shisshigi acikin lamarina! Ni ba kamar Aunty laila bace data saba jan ki ajiki har tayi maki sanadin auren Abbas,kina magana ne da HAYAAM!!!yakama ki iya bakin ki!!!!
ï¿?
 jin yarda hayaam ke zazzaga mata rashin mutunci yasa tayi rejecting kiran,
 tsoki hayaam ta saki tare da cewa"matsoraciyar banza!!ae banso kika kashe kiran ba,so nayi na sauke maki kwandon rashin mutunci shashasha kawai," rai a6ace ta ƙarasa yin maganar tare da yin wurgi da wayar saman katifar,kama hanyar fita ɗakin tayi domin taje ta sanarwa mamaynsu yarda su kayi da Amanin,
 fitarta ke da wuya, Amal ta buɗe idanunta waɗanda suka kumbura jawur saboda raɗaɗin ciwo, ta samu bacci amma tsiwar hayaam ce tafarkar da ita, gaba ɗaya duk wayar da su kayi da amani tana ji a kunnanta,saboda taji lokacin da hayaam ta ambaci sunan Amani,
Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!
ï¿?
  A hankali ta sanya hannunta tare da yaye bargon,a galabaice ta ɗan tashi zaune, hannu takai tare da ɗaukar wayar hayaam wadda tayi wurgi da ita asaman katifar kuma cikin sa'a wayar bata kai ga shiga security ba,
  jiki na kerma ta shiga wurin kiran,sai ga sunan amani ya bayyana a list ɗin farko da tayi waya dasu,cikin sauri Amal ta buɗo numbarta, zuba ma numbar ido tayi tana tunanin yarda zata ɗauki numbar,babu wurin da zatayi copying dinta,tuni hawaye sun soma zarya a fuskanta, wannan shi ake ce ma ga ƙoshi ga kwannan yunwa,
 runtse idonta tayi tare da buɗe su akan screen ɗin wayar,nan take taji cewa zata iya haddace numbar akanta,muddin taci gaba da bitarta akanta, a hankali take ƙarewa numbers ɗin kallo tana naɗarsu akanta,motsin mutun taji alamar an tunkaro ɗakin cikin sauri Amal ta fita daga wurin numbar amanin ta danna power ɗin wayar tayi duhu sannan ta ajiyeta,da hanzari tashige cikin bargon ta lullu6e dukkan jikinta, Hayaam ce tashigo kai tsaye ta ƙarasa inda wayar take tasanya hannu ta ɗauka tare da fucewa daga ɗakin,
 ajiyar zuciya Amal tashiga saukewa,har lokacin tana cigaba da bitar numbar amani akanta,
*******************
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.