Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Fitowarsu kenan daga wanka atare kamar yarda suka saba kwatsam sai ga haroon ya turo ƙopar ɗakin nasu fuskarshi ɗauke da wannan shu'umin murmushin nashi, tsayawa yayi yana binsu da wani irin kallo jikinshi na sanye da Crazy jeans tare da wata figaggar riga daya sanya, ya tada kwalar rigar tsaye,sam haroon baya kama da musulmai ko a fuska, balle ma daya kasance yana sanya chain a wuyan shi da kuma earrings irin yarda jigunannun ƴan iska ke sakawa,
 Kallon juna su kayi atare kafin suka mayar da idanunsu akanshi,tuni ran Jahan ya 6aci ganin yarda yake bin jikinsu da kallo kamar wani tsohon maye, dama daga su sai short towels ajikinsu, farar surar ne mai jan hankali ta bayyana muraran,
 ɗaure fuska jahan yayi tare da cewa "me ya kawo ka É—akin mu? me kuma kake buÆ™ata,indai kuÉ—i ne suna nan zamu baka,"Â
 ta6e baki haroon yayi tare da yatsina fuska yace "yakamata kasan yarda zakayi magana dani with respect,ko don darajar wannan videon dake ajiye acikin wayata,'Â
 tsuke fuska su kayi atare zuciyarsu na tafarfasa tamkar su rufe shi da bugu haka suke ji,
  Cigaba da magana yayi "zuwa nayi don na ƙara tunasar daku, don na lura kamar kun manta da maganar dukiyata dake a wurinku, saboda waccan farin balbelen ɗan uwan naku da bai lfy na lura duk kun wani tashi hankali akanshi,'
 Buga tsoki ayaan yayi yace "kada ka sake kiran shi da sunan balbela kadaina haÉ—a sunayen mu dana dabbobi domin kuwa mu bamuyin munayen É—abi'un da za a haÉ—a sunan mu dana dabba, domin kuwa dabba yasan inda yake"Â
 waro ido waje haroon yayi jin abunda ayaan yace a tsananin mamaki yace "Ayaan ni kake kira da sunan dabba"?! Ya tambaya a dan fusace
 Cikin sauri jahan yace"kayi shiru ayaan kada kaja mana wani bala'en don na lura bai da Imani ko misƙala zarratin, tunda har bai damu da halin da ɗan uwansa ke ciki ba, burinsa kawai ya ƙuntata ma rayuwarmu," yayi maganar yana jefar haroon din da mugun kallo,
 fashewa da dariya haroon yayi hada dafe cikinsa kafin yace "Waye kuma ɗan uwana? ae ni bana ɗaukarku jini na,ko ajinsi ku farare ne ni kuma baƙar fata ne, in fact ni bani da wata alaƙa daku, Uba fa kowa muka haɗa uwa kuma kowa da tashi, bayan shi kuma sai me?
 shiru su kayi suna sauraron shi gaba É—aya tsanarshi Æ™ara ninkuwa take yi acikin zuciyarsu,Â
  juyawa yayi tare da cewa "Zan wuce ni ku huta lpy ƴan samari," yana faɗin hakan ya fuce yana sakin dariya kamar zautacce,
 Mayar da ido ayaan yayi kan jahan yace "bro i ave an advise abt that bastard, why not mu kashe shi kawai kowa ya huta, cos i don't think ko mun bashi kuɗin zai goge videon,"
  aɗan razane jahan ya kalle shi yace "ashe baka da hankali ayaan, kisa fa kace? Mu zamu kashe shi? In muka jefa kanmu cikin matsala fa? ya fadi yana kallon sa,
  Ayaan yace "ba wata matsala jahan, just lettus kill him kowa ya huta !!!!!!!!!
  "Mu bashi time in har muka bashi kuÉ—in bai goge videon ba, sai mu kashe shi kawai,don da abunda zai ta6a mutuncin family dinmu gwara abunda zai tada masu hankali na É—an wani lokaci ya wuce" Acewar jahan,Â
 Gaba daya sun amince da shawarar kashe haroon 😳
Duk mutanen da suka zo duba fawan duk sun ragu, har sun mai dashi daki sun kwantar dashi tun É—azu,
 Junaid kuwa lokacin da Abban su yashigo dashi É—akin shi ya wuce dashi tare da kwantar dashi ya farfaÉ—o daga suman da yayi amma ya dasa da bacci,Â
 Yanzu wanda suka rage a cikin gidan daga su matasan gidan sai abokin su sgr Shattima sun hallara a garden din gidan suna tattaunawa tare da marshal Omar dashi babban yayan,
  Cg Abbas ya jima da tafiya amma yabar Amani a gidan saboda yace zai dawo da daddare ya ɗauke ta, duk ita ta taya azmee rarraba ma masu zuwa dubiya lemun a cups har suka lafa,
  shigowa É—akin Abbansu yayi yana kallon junaid dake baje asaman bed dinsa yana ta sharar bacci, Æ™arasawa yayi wurin shi tare da zama daga gefen gadon nashi, sannan yaÉ—an sa hannun shi tare da bubbuga Æ™afar junaid kamar mai jira aikuwa a firgice ya tashi zaune yana faman zazzare kyawawan idanun shi da suka canza launi saboda bacci, yana jin muryar abbansu ya kira sunan shi nan take ya fashe da wani sabon kukan yana cewa "Abba yaya fawan ! Yana ina ! meya faru dashi.....'Â
Murmushi abbansu yayi yana kallon shi yarda yake kuka yana magana red lips din nan nashi na shagwa6a66u sun tatta6e,
  Cikin natsuwa abban nasu ya soma cewa "Calm down ur mind junaid,ɗan uwanka yana cikin ƙoshin lpy yanzu haka yana can medical room dinmu mun kwantar dashi, shima sai kiran sunanka yake yi yana cewa Abba ina junaid akawo mun shi in ganshi, inaso in ganshi,"
  jin wannan maganar ta abban nasu yasa junaid dakatawa da yin kukan nashi ya zuro da ƙafarsa zai sauko daga saman gadon, abbansu ya ruko hannun shi tare da cewa "pls junaid kada kaje mashi kana wannan kukan saika tayar mashi da hankali yaga kamar mutuwa zaiyi,
 Cikin sauri junaid yasanya tafin hannayenshi tare da share hawayen dake zubo masa sannan abban nasu ya saki hannun shi, jikin shi har rawa yake yi wurin saukowa daga gadon, bin shi da kallo abban yayi har cikin ranshi yana mamakin yarda junaid ke tsananin son ƴan uwanshi don ji yake yi da wani abu ya same su kwara shi ya same shi koda mutuwa ce,akwai wani lokaci da abbansu bazai ta6a mantawa ba in ya tuna abunda ya faru har dariya yake yi wani sa'in kuma yaji saukar hawaye, wannan ba kowane lokaci bane face lokacin da junaid yana da kananun shekaru, idan suka je masallaci tare dashi suke zuwa saiya bari an kammala salla an natsu liman na kora addu'a, sai shi kuma ya ɗaga hannayen shi sama ya ɗaga murya yana cewa "Ya Allah ya Allah kasa na riga Abbana mutuwa da ƴan uwana,ya Allah kafara ɗaukar raina kafin nasu," a lokacin kowa mamaki ya kama shi jin abunda ƙaramin yaron kecewa, har wasu ke tambayarshi dalilin dayasa yake son ya riga abban nasu mutuwa da yan uwan shi sai cewa yayi "Saboda idan na riga su mutuwa bazan ga tasu mutuwar ba in tazo,zuciyata zata samu salama akan na rasa su da raina," gaba daya mutanen dake a masallacin abun ya basu mamaki sosai, kuma ka'ida ne duk in suka je masallaci tare dashi dole liman ya jira shi ya kammala addu'o'in shi mutane na amsa mashi da ameen, kafin shi liman yayi tashi addu'ar saboda rigimarshi,
 Murmushi abbansu ya saki lokacin daya kammala tunanin nashi aranshi yace "Allah yabar mana kai junaid,ni kuma banaso naga mutuwarka nafiso nariga kowannan ku mutuwa don bazan juri ganin gawar ɗaya daga cikinku ba a kan idona," jikin shi a kasalance yake wannan zancen zucin,
 Wayarsa ce ta soma ringing daga cikin aljihun rigarsa ta yadi, cikin sauri ya zura hannu ya ɗauko ta tare da duba sunan mai kiran nasa sunan AMMI ne ya bayyana akan screen din wayar hakan na nufin mahaifiyarshi ce Ammi ke kiransa
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.