Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
  Jikin Ayaan har kerma ya keyi wurin ɗaukar jug ya zuba lemu mai sanyi acikin cup yana kwankwaɗa, abun ya ɗaure ma junaid kai ashe dai da gaske yunwar suke ji,
  Shima jahan jiki na rawa ya shiga zubama kansa abincin, cikin sauri junaid ya wuce wurin freezer ɗinsu ya buɗe tare da ɗuko masu cool drinks ya kawo masu agabansu,
 Hannu jahan yasa ya É—auki bottle water yana kwankwaÉ—a har yana kusa shaÆ™ewa, agalabaice ya ajiye robar ruwan sannan ya kalli Junaid dake tsaye akansu yace "Allah yayi maka albarka junaid, kaje ka ci gaba da wasan ka,"Â
 Juya junaid yayi ya koma kitchen wurinsu sehrish, tana ganinsa tace "Za'a a ƙara masu abincin ne"? Girgiza kai junaid yayi tare da cewa "zuwa nayi na taya ku aikin, bana jin daɗin zama ni kaɗai ne,"
 Azmee tace"so kake kaja mana ko? taya za'a ganka acikin kitchen kana tayamu aiki, kaima kasan ba zaiyiyu ba,"
 turo bakinsa yayi tare da cewa "Aunty azmee nifa ba wani abu zanyi mai yawa ba, kawai zan taya sehrish yanka kayan lambun ne,"
  "Ban amince ba junaid, wai ni yau ba ka zuwa wurin buga ball ɗinka ne? ina laptop ɗinka ne? kaje ka kunna kallo kayi mana ko ka buga game,"
  Ruƙe qugu yayi tare da cewa "Aunty azmee korata kawai kike son yi ne, to Allah ba inda zani ƙafata ƙafar sehrish, tazo mu tafi tare," ya faɗi da shagwa6a
 Dariya su kayi gaba ɗayansu, sai lokacin sehrish tace "junaid ɗina shigo ciki ka samu wuri ka zauna, zan haɗa maka Cornflakes, kana sha kana kallon yarda muke girki,"
  Murmushi ya saki sannan ya shige ciki tare da samun wuri saman dinning chairs na kitchen din ya zauna yana jiranta,
 Jinjina kai azmee tayi tare da cewa "Shaƙuwarku fa da junaid ƙara gaba take yi, don na lura kema bakyaso yayi nisa dake,"
 Sehrish tace "Aunty azmee yana ɗebe mun kewa sosai, ina jin shi tamkar ƙanina ne shiya sanya.... . '
Muryar junaid ce ta katse ta da cewa "Wanene Æ™anin naki"?Â
 Cikin sauri sehrish tace "bafa maganarka muke yi ba" tayi maganar yayin da tasa hannu a cup board ta zaro kofin tare da wuce wa wurin dispenser saboda ta ɗebi ruwan zafin da zata haɗa masa dashi,
"Koma meye dae zanji ne," ya faÉ—i yana É—an hararar ta daga inda yake,
Bayan ta haÉ—a masa takai masa nan ya zauna yana sha suna fira tare dashi,
________________________________
After magrib prayer motocinsu suka dunga shigowa cikin gidan da gudun gaske atare suka yi parking ɗinsu, Abbansu ne tare da SGR suka fito, motar dake bayansu kuma Su irfan ne tare da jabeer da khaleed, kana ganin su kasan sunji jiki, amma su da sauƙi babu alamar rauni ajikinsu sun dai jigata ne,
 buɗe motar dake bayan tasu suka yi wadda fawan ne kwance acikinta, gaba ɗaya jikinsa sahun bulali ne ta ko'ina, saboda hasken fatarshi duk zanen bugun da miyagun su kayi mashi ya fito raɗau jawur wani wurin ma harya fashe, amma da yake ya samu emmergency treatment duk ansanya mashi magani awurin, babu riga ajikinsa gajeran wando ne kawai guntu suka barshi dashi, asaman ƙirjinsa hada ɗinki akayi masa, ba ƙaramin jiki ya ji ba yaji gata sosai,
Amstrong ne babban na hannun daman SGR ya fiddo shi tare da Irfan suka tallabo shi sannan suka wuce dashi cikin gidan, har lokacin bai dawo cikin hayyacinsa ba saboda hodar da suka shaƙa mashi,
  Suma sauran mutanen da suka halarta domin yi masu jaje duk suka harhaɗu nan suna tayi ma Abbansu Allah kyauta, daga bisani suka haɗu gaba ɗayansu izuwa cikin gidan,
  Tun da Sehrish taji dirar motaci tarasa samun kwanciyar hankali burinta taga su wanene suka zo, a lokacin sun kammala aikace-aikacensu na kitchen fitowarta kenan daga wanka, ta buɗe closet dinta ta zura doguwar riga sannan ta matsa jikin window tana leƙensu bata samu damar ganinsu da kyau ba saboda mutanen dake zagaye ta ko'ina,
Jiki asanyayae ta rufe window in gabanta na faduwa tsoranta kar ace wani ne ya rasu, hannu ta aza akanta tana ambaton "innalallahi wa'inna ilaihirraji'un ya Allah kasa ba wani bane ya mutu,"Â
Cikin sauri ta bar wurin tare da buɗe kopar ɗakin nata ta fito waje a lokacin itama Azmee tafito daga ɗakinta a ruɗe jikinta na sanye da zumbuleliyar hijabi alamar salla ta kammala yi, ko addu'a bata tsaya yi ba ta fito saboda jin jiniyar shigowar motocinsu,
  tsayawa su kayi gaba ɗayansu suna son ganin abunda ke faruwa, gaba daya sun rikice ganin yarda Amstrong da irfan suka shigo da Fawan duk ciwuka ajikinsa saman 3 seater suka zaunar dashi saboda masu zuwa dubiya,
Fitowa Ayaan da jahan sukayi daga ɗakinsu suma jin hayaniyar dake cikin gidan ganin fawan a wannan yanayin yasa su ƙarasawa da gudun gaske suka zube saman guiwowinsu agaban shi cikin tsananin tashin hankali suke cewa "fawan meya faru dakai haka? Waye yayi maka haka? Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un,
 Daker fawan ke iya kallonsu duk da baya iya tantance su wanene agabansa amma yaji muryarsu, juyawa su kayi suna kallon Irfam da jabeer don son jin ƙarin bayani,
  Jabeer yace "Fawan bazai iya yi maku magana ba a halin yanzu baima san ko ku su wanene ba, addu'a kawai zakuyi masa,' jin haka yasa hawaye soma zuba daga idanunsu,
 Shigowar da mutane suka soma yi ne yasa su samun wuri Æ™asa suka zauna kowa ya zabga tagumi, kana kallon fuskar Abbansu kasan cewa acike take da tashin hankali saboda arayuwarsa ya tsani abunda zai ta6a masa jininsa,Â
Ganin SGR ya shigo yasa sehrish jin faÉ—uwar gaba, gaba É—aya babu annuri a fuskarshi, white shirt É—in dake ajikinsa duk shedar jini ne daya fallatsar masa hada hannunsa,
ba jinin kowa bane face jinin waÉ—anda suka farmaki su fawan, mugun bugu sukayi masu na fitar shari'a gaba É—ayansu suna a headquater dinsu an killace su can domin horar dasu da kuma yin bincike akansu,
Tuni jikin sehrish ya soma yin kerma saboda tashin hankalin da tagani ajikin SGR tunaninta ya gama bata cewa ko harbinsa akayine da bindiga shiyasa taga jini, hannu tasa ta rufe fuskarta tana kuka da gudun gaske ta juya ta koma É—akinta saman gadonta ta faÉ—a tana cigaba da kukan,"
 Abun ya ɗaure ma azmee kai ganin yarda sehrish ta gudu tana kuka kuma tasan ba don komai bane fa ce sai don ganin jini a jikin rigar sgr da hannunsa,
  Ganin manyan mutane sun fara cika babban falon yasa azmee komawa cikin ɗakinta jiki asanyaye, zama tayi tana jiran mutane su ragu sai taje ta dubo shi,
  Hannu Abbansu yasa ya ruƙo na Ayaan yace "taso ina son magana dakai,"
 Tasowa ayaan yayi daga zaunen da suke yabi abbansu suka ɗanyi nisa da mutane sannan ya kallesa yace "Ina junaid yake"?
 Ayaan yace "ina ji yana a ɗakinsa bana tunanin ya fita, Amma abba tayaya hakan tafaru da Fawan? Suwaye suka yi mashi haka? ya fadi idonsa cike tab da hawaye,
 Dafa kafaɗarsa abbansu yayi shima fuskarshi tamkar zaiyi kuka yace "Ayaan bamu son ko su wanene ba, Babban yayan ku da Omar sune suka je wurin da suka farmake su, kuma sun samu nasarar kashe wasu daga cikinsu, yanzu haka akwai mutun 3 daga cikin miyagun suna a headquater ɗin mu,"
  "Abba don Allah karku kyalesu akashe su kawai," ayaan ya faɗi cikin jin ɗaci aransa
 "Ba zamu Æ™yalesu ba ayaan, mutanene masu haÉ—arin gaske, babban tashin hankalin É—aya daga cikinsu da muka aza shi saman kujerar lantarki muka bashi horo ya bamu wasu bayanai nacewa macace take basu Umarni duk wani kashe-kashen da suke yi a Æ™asar nan,"!Â
  waro ido Ayaan yayi cikin tsananin mamakin abunda Abban nasu ya faɗa masa, aruɗe yace "What! Mace kuma Abba? mace wannan dana sani?
 "Of course Ayaan, ba kai kaɗae ba kowa daga cikin mu yayi mamakin jin hakan, yadda akasan mata da rauni amma har acikinsu asamu wata mai ƙarfin halin haɗa tawagar ƴan ta'adda masu farmakar mutane suna kakkashe su, Amma koma wacece insha Allah zamu ganota bi'iznillah zata ɗanɗani kuɗarta!"
  Jinjina kai Ayaan yayi yana cewa "Insha Allah Abba, Allah ya tonu asirinsu aduk inda suke, abun yayi yawa wlh rashin imanin nan har ina? mutun baya tuna cewa shima wata rana zai mutu yabar duniyar ne?shin menene ribarka idan ka kashe wani bayan kai baka isa ka hana kanka mutuwa ba?
  Kafin Abbansu yace wani abu muryar kanal yusif ta katse su da cewa "Abba ka matso kusa mutane suna son magana dakai,"Â
 Amsa mashi yayi da "toh gani nan zuwa" sannan ya kalli ayaan yace "Abun dayasa na tambaye ke game da junaid kasan halin shi, muddin ya fito yaga halin da fawan ke ciki tofa zai iya sume wa ko ya zauce, dan Allah kusan yarda za'ae ku hana shi fitowa daga É—akinsa indae yana ciki,"Â
  Ayaan yace "Shikenan abba bari naje na duba shi," cikin sauri ayaan ya wuce upstairs É—akin junaid, a hankali ya tura Æ™opar É—akin cikin sanÉ—a ya shiga, abun mamaki samun shi yayi saman gadon shi zaune ya toshe kunnan shi da headphone yana kallo acikin laptop É—insa baya jin duk wata hayaniya da akeyi acikin gidan,Â
  Murmushi Ayaan ya saki sannan ya ƙara ja mashi ƙopar ɗakinsa dakyau ya rufe masa ita, sannan ya juya ya sauko down wurin su,
Har wurin dare mutane suna ta zarya agidan sai wuraren Æ™arfe 9:30 sannan suka fara raguwa, tuni Sgr ya wuce part É—insa saboda ya gyara jikinsa ga matuÆ™ar gajiyar da yayi idonsa ma kansu daÆ™er yake buÉ—esu ga yunwa ga bacci, har lokacin zuciyar shi tafarfasa takeyi duk in ya tuna irin artabun da su kayi tare da miyagun nan, duk da sunci nasara akansu sosai, bakomai bane ya tsaya masa aran shi ba face wannan maganar nace wa macace take É—aukar nauyin tawagar miyagun dake kashe-kashen, yaci alwashin cewa sai ya gano ko wacece ita,Â
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.