Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
duk da ya mutu amma hakan bai masa ba saboda raÉ—aÉ—in da yake ji azuciyarsa, hannu yasa ya rarumi Æ™aton dutsin dake ajiye a Æ™asan wurin zai rotsa masa kai, cikin sauri matashin nan daya fita da husana ya faÉ—o É—akin ya tunkaresa tare da hanzarin ruÆ™o hannunsa yana cewa "Yalla6ai kabarshi haka mana, ya riga daya mutu," fisge hannunsa yayi yayin da idonsa ke cike tab da hawaye da wani irin huci yake cewa "Kabarni kawai na tarwatsa kansa ko zuciyata ta samu salama, kasan yarda nake ji acikin zuciyata kuwa, tamkar ana rura garwashin wuta acikinta saboda tsantsar baÆ™in cikin da nake ji, WANNAN MUTUMIN YA SHIGA HURUMINA !!!!!!!!!!!!!!!!!!!! â‰â—‼â—â“â“â“â“â“â“
*SHIN WANENE WANNAN MUTUMIN DAYA FARMAKI BABA ALAMU ACIKIN GIDAN GONARSA AYAYIN DA YAKE ƘOƘARIN KETA HADDIN HUSANA*â“â‰
*WANENE SHI*â“â“
_*amsar tana a wurin hafsat Bature muhammad Boss Lady domin son sanin wanene wannan sai ku antaya kuÉ—inku naira 300 kacal Vip kuma 700 a wannan acct number É—in 3196407426 first bank Bature hafsat Muhammad ku tura shaidar biya ta wannan layin da kuma masu tura recharge card 08103884440 kada ku bari abaku labari , masu karantawa ta facebook masu Æ™aramar waya Recharge card zaku tura koda digits É—insa ne 200 only in kun daure kun biya da dama zaku cigaba da samun posting insha Allah Ku fara biya da hanzari daga yau zuwa monday, har yanzu dae nice dae Hafsat Baturen da kuka sani mai sauÆ™in kai, ban canza ba, kaÉ—anne kawai zasu fahimce niðŸ‘ðŸ‘*
Alhamdulillah finally na kammala
*💋💋okay MAJOR ya sake ruƙo hannunsa tare da cewa"Sorry Sir! Nasan Abun da ciwo, Amma mu gode ma Allah da muka ƙaraso akan Lokaci batare daya kai ga Cutar da ita ba" huci kawai yake yi yana kallonsa da idanuwansa waɗanda suka canza Launi bakomai yake tunawa ba fa ce yarda Baba alamu ya yayyaga ma Husana rigar jikinta, in ya tuna wannan abun zuciyarsa Tafarfasa take yi saboda 6acin rai, muryar major ce ta katse shi da cewa" Allah ya huci zuciyarka yakamata mu hanzarta barin gidan gonar nan domin muyi gaggawar kai su asibiti,
Jin hakan yasa shi yin saurin zura hannu tare da curo wayarsa daga aljihun wandonsa, nan take ya shiga camera tare da saita gawar baba Alamu ya É—auke ta hoto da kyau, bayan ya ammala ya mayar da wayar cikin aljihun sannan ya kalli Major yace "Duba min aljihun wandonsa kona rigarsa kaga ko za'a samu waya,"
Cikin hanzari Major ya zura hannunsa cikin aljihun baba alamu daker ya lalubo wata ƙaramar waya nokia, taji duniya don bala'e batteryn wayar saida aka sanya robali sannan aka ɗaure shi baya cikon da akayi masa,duk ta rakwakkwa6e wayar,
"Sir ga wayar," ya faɗi tare da miƙa masa, bai kar6a ba bin wayr yayi da kallo kafin yace "Major cewa nayi ka ɗauko mun wayarsa ba wannan abun ba," ya faɗi yana nuna wayar hannun major ɗin
Ƙiris ya rage major ya fashe da dariya saboda ya lura cewa Boss Man ɗin nasa baya cikin hankalinsa,
"Sir wannan itace wayar, ka duba da kyau ta tsufa ne sosae shiya sanya ka ganta hakan,"
Ajiyar zuciya ya saki tare da cewa "Keep it in ur place, zan neme ta," yana faÉ—in hakan yakama hanyar fita daga É—akin,
Muryar Major ce ta dakatar dashi da cewa "yalla6ai rigar fa? zan iya É—auko maka ita," ya tambaya yana jiran amsa ,
Bai amsa mashi ba ya fuce kawai cikin sauri major ya ɗauko Jacket ɗinsa da yayi wurgi da ita sannan ya fito daga ɗakin ruƙe da ita a hannunsa a lokacin har yakai wurin motarsu da suka zo da ita, kai kana ganin yarda sukayi parking ɗinta kasancewa a tsiyace suka shigo da ita, domin kuwa har katakon ƙopar gidan gonar duk sun tarwatsa shi,
Cikin sauri Major ya rufa masa rigar abayansa shi kuma ya ƙara gyarata ajikinsa sannan ya zuge zeep ɗinta, buɗe motar yayi sannan ya shige back seat ɗin shikuma major ya shige driver seat sannan ya tayar da motar yayi baya² da ita kafin ya karya kwana ya fito daga gidan gonar da gudun gaske yake driving ɗinsu,
Sam ya gaza ɗauke idonsa akan hosana dake langwa6e asume kusa dashi, duk gashin kanta ya gama tarwatsewa dama a hargitse yake sai kuma aka ƙara hargitsar dashi, duk ya rufe mata fuskarta, lumshe idonsa kawai yayi har lokacin yana mamakin yarda akai wannan Lamarin ya afku amma yana da tabbacin cewa major yana da masaniya akan hakan,"
adai dai hanyar da baba alamu yayi wurgi da jahad Major yayi parking É—in motar, cikin sauri ya buÉ—e motar ya fito gabansa ne kawai ke faÉ—uwa tsoranshi kar ace ta mutu,
wani saurayi ne zuƙunne a inda jahad take yashe, da alama ba ƙaramin taimako yayi mata ba, domin kuwa ya ciccire mata ƙayoyin da suka soki ƙafarta sannan kuma yayi amfani da Mayafinta wurin kekketa shi izuwa kashi uku, ya ɗaure mata goshinta sannan kuma ya naɗe mata ƙafafunta dake zubar da jini,
Fitowa major yayi shima yana kallonsa,
"Major karfa ace yarinyar nan ta mutu," ya faÉ—i a tsananin tsorace
"Sir she's still alive, suma ce kawai," ya bashi amsa,
saurayin yace"yalla6ai tana buƙatar taimakon gaggawa saboda jinin dake bleeding a goshinta da kuma tafin ƙafarta,"
Cikin tsananin tashin hankali ya ƙarasa tare dasa dukkan hannayensa ya tallabo JAHAD ya ɗaukota da sauri Major ya buɗe masa motar ya shigar da ita a kusa da Hossana ya zunar da ita a sume, sannan shima yashiga motar, zuge glass ɗin yayi tare da kallon saurayin yace"Ka shiga mu tafi tare,"
saurayin yace"yalla6ai machine É—ina fa"?
tunkan ya bashi amsa major yayi saurin cewa"daraban kayima arziƙi ƙulli ana maganar arziƙi wake ta wani machine"?
Jin haka yasa saurayin tasowa sai da ya bari major yashiga, sannan shima ya shiga kusa dashi ya zauna, rufe motar su kayi sannan da gudu suka bar dajin suka miƙi santalelen titin da zai sadasu da inda suka dosa
Kallonsu kawai yake yi ransa na ƙara ƙuna ganin irin jigatar da yaran su kayi yaran daya kai Amana, sam kwalwarsa ta rikice yarasa gane ma wannan lamarin ba komai yake son ji ba face yarda akai har tsohon can ya ɗauko yaran izuwa cikin gidan gonarsa don ya lalata rayuwarsu! taya akai ya fito dasu daga gidan general Ishaq? taya akai Aunty laila tayi gangancin da har wani zaizo ya ɗauki twins ɗinsa? da sa hannun wa akayi wannan ƙulla-ƙullar, tabbas kowaye bazai ƙyale shi ba, muddin ya gano gaskiyar lamarin!!, ya ƙarasa zancen zucin nasa adai² lokacin da suka ƙetaro Abuja, kai tsaye suka wuce dasu izuwa katafaren asibitin SGR,
***************SEHRISH***************
Sam bata gane mai ake koyarwa acikin class É—in saboda wata irin yunwa dake jibgarta ga wani irin bacci da take ji, sai faman hamma take yi tana lumshe ido,
Wuraren ƙarfe tara da rabi, time ɗin break yayi gaba ɗaya ƴan class ɗin sai fita suke yi don suje cin abinci, Sehrish na kwance saman desk ɗin gabanta sai faman sharar bacci takeyi,
juyowa Amrish tayi daga seat É—inta tana kallonta, murmushi ta saki tare da sa hannunta taÉ—an bubbigi bayan sehrish tace "Get up baby ! time É—in break yayi, yakamata mu fita,"
daker sehrish ta buɗe ido tare da ɗago kanta daga saman desk ɗin tana kallonta biji², miƙewa Amrish tayi ta fito daga seat ɗinta, sannan ta ruƙo hannun sehrish tana cewa"Get up mana Let's go,ko bakya jin yunwa ne"?
ta tambaya tana kallonta, miƙewa sehrish tayi tare da biyota suka fito daga Class ɗin gabanta nata faɗuwa tsoranta kar ace siyen abincin zasuyi don ko sisi bata fito dasu ba, babu wanda ya bata kuɗi,
saukowa sukayi daga saman benen duk inda suka bi sai an samu wanda zai yi ma Amrish magana, kuma yawanci akan Sehrish suke tambayarta ko Æ´ar uwarta ce, sai dae kawai tace musu eh, saboda tasan son jin gulma ne kawai,
Hanya suka miƙa bada jimawa ba suka ƙaraso Lunch room ɗin makarantar wurin cin abincinsu, lokacin da suka shiga wurin mamaki ya kama sehrish ganin ɗalibai aciki kowa zazzaune saman dining tables masu mazaunin mutun 4, kowa wanne gabansa cike shaƙe da abinci sai ci suke yi,
Ruƙo hannunta Amrish tayi adai² wani tebur da bakowa tace ma sehrish tazauna sai faman zare ido take yi gabanta na faɗuwa tsoranta kar ace tabada kuɗin abinci,
"Me kike so na amso mana muci"? Amrish ta tambaya tana kallonta daga tsaye, zuru sehrish tayi tana tunanin yarda za tace ma Amrish bata da ko sisi,'
"Kin yi shiru baki ce komai ba"? Amrish ta tambaya a ƙagare, murya na rawa Sehrish tace "Ni bana jin yunwa, a ƙoshe nake,"
Cikin mamaki amrish tace "but alamu fa sun nuna cewa kamar kina jin yunwa? Yakamata ko Coffee ne kisha taya zaki zauna da yunwa acikin ki"?
sehrish tace"kada ki damu bana jin yunwa ne kawai," jinjina kai amrish tayi tare da cewa "its ok bazan takura maki ba, tunda kince bakya jin yunwa, ni bari naje na amso abunda zanci," tana faÉ—in hakan ta wuce wurin masu zuba masu abincin,
É—agowa sehrish tayi tana kallon students É—in dake zazzaune suna faman cin abinci hankalinsu akwance, haÉ—iyar miyau tashiga yi ganin yarda suke Cusa pancakes da zuma abakinsu,
sunnar da kai tayi gaba É—aya tarasa yaya zatayi ga yunwa tana ji amma tana tsoran taci musu abinci ba kuÉ—in biya, tana cikin wannan tunanin sai ga Amrish tadawo hannunta É—auke da plate guda biyu da murmushi afuskarta, ta ajiye su saman table É—in sannan ta juya ta koma domin amso masu abunsha,
Zuru sehrish tayi tana kallon plate ɗin mai ɗauke da banƙararriyar kaza ta gasu sosai hada ƙaramar knife wadda mutun zai yanka yaci, ɗayan plate ɗin kuma Snacks ne acikinsa shaƙe, runtse ido tayi tana ji tamkar takai ma plate ɗin hari, sai faman cixon la66a takeyi,
dawowa Amrish tayi hannunta ruƙe da Laca sera mai sanyin gaske roba biyu, wuri tasamu tana fuskantar sehrish tazauna tana cewa "Wai haryanzu kina akan bakan ki na ba zaki ci komai ba"? tun yanzu zamu fara haka dake?
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.