Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
ta ko'ina Allah ya bata ga dogon wuya,
Bin ta da kallo saurayin yayi sam yagaza janye idonshi akanta sai kace batare suke rayuwa acikin gidan ba,
Towel ne kawai ta ɗauro ajikinta cikin hanzari ta miƙa hannunta tare da kar6ar wayar tana cewa"nashiga ukuna Aunty laila kuma a awaya?yanzu zata rufe ni da faɗan ba gyara ba dalili mtswwwwww
ï¿?
 Ta ƙarasa maganar tare da ɗaga kiran ta kara a kunnanta tana faman zazzare manyan idanunta,
A ƙule aunty babba tace"ina kika je ne inata faman kira ba'a ɗagawa?
Cikin en ina tace"Nashiga toilet ne yanzu na fito na sami wayar tana ringing asaman gado,
aunty babba tace"hmmmm kina a gida ko kina awaurin yawon gantalin naki?
Cikin sauri tace"am....ina a gida......" bata bari ta ƙarasa ba a tsawace tace"Karki kuskura kiyimun karya Hayaam ina sane da duk wani yawon gantali da kikeyi ana sanar mun da komai,saboda tsabagen iya shege da fitsara idonki ya buɗe wuyanki ya isa yanka hada tattara kaya da komawa gidan saurayi da zama koba haka akai ba? Ta tambaya azafafe tamkar tana a gabanta,tuni ran Hayaam ya 6aci juyawa ta ɗanyi ta kalli Sofwan dake kallonta bai sauraron me suke cewa amma ya lura da yanayin fuskarta daya canza saboda hayaam bata iya 6oye 6acin ranta duk mun ƙanƙantarsa,
 sassauta muryarta tayi tare da cewa"Aunty layla mgnr da kika faÉ—a gaskiya ne,i can't hide it 4 u ni bazan iya rayuwa a cikin gidan nan ba saboda baida marar raba da kwango a wurina,fentin gidan duk ya Æ™oÆ™e kamar munfi kowa talauci a layinmu,bama wannan ba É—akinmu bai da banbanci da kwankon ashana katifa ce kawai duk ta gwaigwaye sai akwatin kayan mu, ko na fidda kuÉ—i na siyi furnitures mommy bata barin komai sai dae kawai nadawo na taras ta siyar da komai ta hanani jin daÉ—in rayuwa kuma kinsan ni macace mai son rayuwar hutu rayuwar Æ´anci wannan shine dalilin dayasa nabar masu gidan don wlh ko abincin da suke ci ynx 6ata mun ciki yake yi saboda wannan yarinyar Æ™anwar Amani ita suke ba girkin gidan,yarinyar da bata wuci 14years duk wani aiki na gidan ita take yin shi har yanzu mommy bata haÆ™ura ba akan É—aukar fansar abunda mommynsu tayi mata" yadda take magana kaÉ—ai ya isa ya tabbatar maka da cewa ba Æ™aramar Æ´ar duniya bace magana take tana faman wurga ido tana kora jawabiÂ
Jinjina kai aunty babba tayi tare da cewa"ae ni tayimun dai dai,wato wayewa tasa kin manta da irin azabtarwar da matar nan tayi mana shine har kike ganin laifin mommynmu,kwara su kashe yarinyar ma kowa ya huta ae ni nafison su wulaƙantata," ta fadi tana faman huci kamar tana agabanta,
Download>>>Â Yaro Ne Complete Document
Ganin wayar tasu ba mai ƙarewa bace yasa Sofwan tasowa daga saman bed dinsa ya sauko, takawa yayi izuwa bayan Hayaam dake atsaye ya rumgumota tare da zagayo da hannayen shi ta waist ɗinta sannan ya kwantar da kanshi daga gefen wuyanta yana cewa"babe yaushe wayar zata ƙare?nifa a ƙagare nake,
Æ™asa Æ™asa da murya tayi tare da cewa"pls karkaja min bala'e,"Â
ï¿?
Muryar aunty babba ce taci gaba cewa"Yanzu abunda nakeso dake kibar komai da kike yi ki tafi abuja gidan surukaina acan nakeso ki cigaba da zama,
 Ƙiris ya rage hayaam ta saki wayar dake a hannunta saboda jin sa6on da auntyn nata ke faɗi, cikin ruɗu tace"haba dae Auntyna amma dae wasa kike yi ko?if not ni mai zai kaini gidan in-lows din mu da zama abun ma babu daɗin ji........,
Tsawa aunty babba ta daka mata tare da cewa"ke dalla yi mun shiru!duk ƙoƙarin da nakeyi akanki bakya gani!kina nan sake da baki ga wata can a gidan matsayin yar aiki Abbansu ya mayar da ita ɗiyarshi sun gatanta yarinyar har makaranta take zuwa,idan har kikayi gangancin rasa wannan damar ta komawa gidan da zama ina mai tabbatar maki da cewa Kin rasa cikar burinki na har abada," shiru hayaaam ta ɗanyi gabanta na faɗuwa saboda ba abunda ta tsana fiye da ace zata Rasa SURGEON GENERAL RAFAYET saboda mutuwar son da take yi mashi ta kwallafa rai akanshi a lokacin baya tasa naci sosai akan shi sa'adda suke zuwa gidan sosai,amma tun da ta lura cewa kafin ya ma ɗaga idonshi ya kalli mace aiki ne don sai da ta share 2 weeks a gidan sau ɗaya suka ta6a hada ido shima ɗin by mistake ne ya ɗago a lokacin,abun ya tsaya mata arai, yadda take da kyawun surar nan babu namijin da zaiganta ya kawar da ido batare da ya neme ta ba sai akan SGR,tun a lokacin ta soma fidda rai akan shi amma yanzu aunty laila ta soma dawo da ita kan network,
lumshe idonta tayi tana tuna kyakkyawar fuskarshi har lokacin sofwan na manne da jikinta ya lafe mata kamar wani maye,
 ƙara kara wayar tayi akan kunnanta tace"Aunty laila komai zan iya yi akan na mallake shi,saboda shine namijin daya haɗa komai da nake kwaɗayi nake tsananin so a jikin ɗa namiji,amma abunda bansani ba aunty layla shin kina ganin zasu kar6e ni in naje gidan a matsayina na ƙanwar matar yayansu?
Wani irin shu'umin murmushi Aunty babba ta saki wato anzo dai dai wurin da tafi so, miƙewa tayi daga zaunen da take agaban mirror tashiga zagaye bedroom ɗin nata tana cewa"Hayaaam baki da Matsala indae a gidan nan ne! Kinsan yarda Abbansu ke da son ƴa'ƴa hannu biyu zai kar6eki abu daya kawai nasani shine dole sai da iznin Abi sannan zai kar6eki don haka kibarmun wannan a hannuna ni zanyi magana da mommynmu tunda ita ke juya shi da zarar tayi mashi magana zai amince!abunda kawai nakeso dake hayaam shine kiyi gaggawar komawa gidan da zama acikin watan nan!Ke bama sai kin je da komai ba tsurarki zaki tafi batare da trolly na kayanki ba,saboda inaso ki fara fakewa da cewa kinje duba Fawan ne da bashi da lafiya daga nan kawai saikiyi zaman ki dirshan babu mai tanka maki saboda duk matasan gidan miskilai ne babu ruwansu,da ace dae yana da ƴa'ƴa mata shine za'a samu matsala kinsan mu mata da bakin ciki da hassada muke....'
 Murmushi kawai hayaam ke saki tana faman lumshe ido tare da cizon pink lips dinta saboda shock ɗin da takeji na sofwan dake bin jikinta da hannun shi yana shafa ko'ina,Auntyna indae ni ce just karki samu damuwa,ki ƙaddara cewa gani can ma acikin gidan ina watayawa ta,ita kuma wannan yarinyar da kika sanar mun cewa tana zaune a gidan tuni zansa su yi mata checking out badai ni bace ba hmmmmmm,
 Dariya aunty babba ta saki tare da cewa"har naji sanyi araina,burina na dab da cika,"
Download>>>Â Yar Harka Complete Document
 Sun jima suna wayar kafin daga bisani suka yi sallama da junansu,
  Buge hannun sofwan tayi tare da cewa"duk kabi ka takuramin wai kai wani irin jarababben mutun ne mai nacin tsiya haba mtwww,"taja dogon tsoki
 Baki asake yabi ta da kallo tare da cewa"ni kike ma tsoki wai?wato wannan haɗamammar auntyn taki takira duk ta tunzuraki akan abunda bazai ta6a faruwa ba,duk naji mai kuka tattauna da ita,
 ya fadi yana faman sakin hucin 6acin rai,murmushi hayaam ta saki tare da cewa"Sofwan zamana dakai ya ƙare!!!!!!!
ï¿?
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.