Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
 Amani taci gaba da cewa"Tun yaushe kika fara aiki a gidan nan ne"? Saboda ni ban ta6a ganinki ba gsky,"  Sehrish tace"banjima da farawa ba,"  "Amma nayi mamamkin yarda shaƙuwa ta shiga tsakanin ki da mutanen gidan har abbansu ya mayar dake ɗiyarshi,kuma naga kina da kusanci ssae da junaid har yana ruƙe maki hannunki kamar wata ƙanwarsa, bayan matsayinki bai wuce na ƴar aiki ba," ɗagowa sehrish tayi a ɗan rikice tana kallonta jin abunda tace,   Murmushi amani ta kuma saki kafin tasanya hannu ta dafa kafaɗar sehrish tace"idan ba damuwa inaso in baki wata shawara wadda zata amfane ki, domin na lura kinason jefe kanki cikin hatsari, karfa ki ruɗa kan ki,".  Jinjina kai sehrish tayi tare da cewa"ina sauraronki," amani taci gaba da cewa"ki nisanta kanki daga kowa na cikin gidan nan,ka da ki bari wani ya so ki acikin matasan gidan nan,kuma kada ki kuskura ki bari zuciyarki ta faɗa tarkon son wani,idan da hali ma ki tsaya a iya matsayinki na ƴar aiki,zaki fi samun kwanciyar hankali,"  Tun da tasoma magana sehrish ke bin ta da kallo fuskarta ta nuna alamun rikicewa don sam batasan inda zancen matar ya dosa ba,  "Kada kice na cika ki da surutu,its just an advise in kinyi amfani da ita ke zata amfana,but if u don't hmmmmm u can even lost ur life........' Wani irin bugu zuciyar sehrish taji saboda abunda amani tace, na cewa zata iya rasa rayuwarta, tuni jikinta ya shiga yin kerma alamomin tsoro sun bayyana a fuskarta, hankali atashe take cewa"meyasa kika ce haka?saboda me zan rasa rayuwa ta?don kawai naso wani ko wani ya so ni acikin gidan nan"? Ta tambaya tana kallon Amanin,   Kafin Amani tace wani abu, muryar Azmee ta katse mata hanzarinta da cewa"tsayuwar me kuke yi ne, ke da nace ki kira mun ita don tazo mu haɗu mu fara girkin da wuri"? Ta tambaya tana kallon Amani, . cikin sauri Amani ta dan basar tare da sakin fara'a a fuskarta tace"dama muna ɗan tattaunawa ne,kinsan bata sanni ba nima kuma haka, so ina gabatar mata dakaina ne don musan juna,"  Zuba mata ido sehrish tayi kawai baki asake tana kallonta,  Azmee tace"Hakan na da kyau, sehrish wannan matar yayanku ce Abbas sunanta AMANI,ina fata zaki saki jiki sosai da ita domin kuwa tana da mutunci sosai,  daƙer sehrish ta ƙaƙalo murmushi tace"Insha Allah aunty azmee,"   tayi maganar tana kallon Amanin ita ma kallonta takeyi har lokacin, Azmee ta lura da kallon kallon da suke yi don haka tace"Amani mu wuce kitchen,ke ma sehrish ki ajiye hijabin jikinki ki zo mufara aiki,"  Juya ciki sehrish tayi su kuma suka wuce kitchen ɗin, kanta ya gama ɗaurewa da maganganun da Amani ta gaya mata,amma duk da hakan ba tajin zuciyarta zata karaya saboda wasu ƴan kalamanta,hannu tasa tare da tu6e hijabin ta ajiye ta nan saman gadon, sannan ta ɗauko ɗan mayafinta cikin wardrobe tayi rolling ɗinsa,  A dai dai lokacin da ta fito daga ɗakin ta tunkari hanyar kitchen ɗin sai ga haroon ya fito daga part ɗinsu,sai da taji gabanta ya faɗi don ita yanzu kallon shaiɗan take yi mashi saboda ƙahone kawai babu akanshi,   Ƙarasowa yayi inda take suna facing ɗin juna yace"mutuniyar ba hello ba hi,laifin me nayi maki ne"? Yayi maganar yana ɗaga mata gira tare da kashe mata ido,  Tsuke fuska tayi tare da bi zata wuce cikin sauri yasha gabanta tare da ware hannayensa yace"daga kin ƙara motsowa zan rungume.........' kasa ƙarasa maganar yayi gabansa na faduwa ba don komai ba sai don ido biyun da su kayi da SGR wanda ke shigowa cikin babban falon su biyu ne tare da shattima suka shigo,banda omar wanda tun a masallaci suka rabu,  Cikin sauri haroon ya canza kalamansa da cewa"kin gane dole kisa tsoran Allah acikin zuciyarki idan kinason rayuwarki tayi kyau,amma in kika ce zaki biye ma ƙawayen banza zasu kaiki ne su baro ki," ya dage sai zuba yake yi mata,juyawa tayi don taga wanene ya shigo saboda ganin yarda haroon yabi ya susuce ya sauya magana,   hada ido su kayi da shi adai dai lokacin yana ƙoƙarin kawar da nashi idon daga na haroon,har cikin zuciyarta taji wani irin sanyi aranta dama da kewarshi tadawo gidan,ganin shattima na kallonta yasa tayi saurin cewa"ina yinin ku"? "Lafiyalou Alhmdllh ƴan mata," ya amsa mata fuskarshi asake,sannan suka wuce upstairs part dinshi,sam takasa janye idonta daga kallon Bayan sgr da takeyi ko kyaftawa ba tayi har suka 6ace ma ganinta,hakan ba ƙaramin fusata haroon yayi ba rai a6ace tace"Ke!!kina a gabana kuma kike kallon wani"?  ƴar dariya sehrish tayi kafin tace"Namiji nake kallo," tana faɗin hakan tabi ta gefenshi ta wuce izuwa kitchen,baki asake haroon ya tsaya yana huci jin abunda tace,aransa yace"lallai ma ƴar shilan can harni zata ce ma Namiji take kallo,hakan na nufin ni kallon ɗan daudu takeyi mun,zan yi maganinta ne! Watan fara shan uƙubarki yayi acikin gidan nan !!zan 6ata maki suna a wurin shi dama kowa na gidan nan"!!! Yana gama faɗin hakan ya gyaɗa kanshi yana sakin shu'umin murmushi ya fuce daga falon. Shiga kitchen din tayi ta same su har sun fara aikin girkin,sallama tayi masu suka ɗago suna kallonta atare, azmee tace"sannu da zuwa za'a fara aikin ne,"  Ɗaga kai tayi tare da cewa"eh amma inaso nafara kaima su babban yaya abunsha naga sun shigo tare da wani ynx," zuru amani tayi tana kallon ikon Allah,  Azmee tace"toh bari na haɗa maki tare da snacks ki kai masu,"  ɗan murmushi sehrish ta saki tana jiranta duk in ta ɗago sai sun haɗa ido da Amani,sai tayi saurin kawar da idonta,  Bayan azmee ta kammala haɗa mata two cups na coffee a saman tray tare da plate mai ɗauke da snacks ta miƙa mata,kar6a sehrish tayi ta rike da kyau a hannunta sannan ta juya ta fuce daga kitchen ɗin tana faman sauke ajiyar zuciya,   Wuce wa tayi upstairs tayi a bakin falon ta tsaya tare da yin sallama,muryar wannan abokin nan nasa taji ya amsa mata da cewa"wa'alaikum salam," sai da ta dai dai ta natsuwarta sannan tashiga ciki gaban ta na faɗuwa kamar kullum,   Shattima ne kawai ta samu zaune saman 3 seater yana danna wayarshi, Ƙarasawa tayi tare da ajiye tray din saman table din gabansa,maimakon ta tafi saita tsaya tana faman wasa da yatsun hannunta burinta kawai taga sanyin idaniyarta tasan cewa zai fito shiyasa ta tsaya,  Hannu shattima yasa ya ɗauki cup of coffee din yakai bakinsa yana kurba da alama ba ƙaramin daɗi yayi masa ba,sam takasa tafiya saboda bata ga sgr ba,ganin tayi masa tsaye yasa shi jinkirtawa da shan coffee ɗin da yake yi yace"Ya sunanki ne"? firgit ta ɗanyi tare da kallon shi tace"Sehrish," jinjina kan shi yayi kafin ya ƙara cewa wani abu sai ga Sgr ya fito sanye da short ajikinshi tare da singlet,nan da nan sehrish ta shiga natsuwarta, wuri ya samu ya zaune gefen shattima, cikin sauri ta ɗauki cup ta miƙa masa hannu yasa tare da kar6a yana dan sipping dinshi a hankali,  Mayar da idon shi yayi kan sgr yace"wannan fa ban ta6a ganinta ba is she ur sister? Ya tambaya yana kallon shi,  "U can ask her," ya faɗi batare da ya dago ya kalle shi ba, murmushi shattima yayi tare da mayar da idon shi kan sehrish yace"kina da connection dasu ne,ko yar wurin Aunt dinsu ce ko uncle dinsu"?  ɗaga mashi kai tayi alamar"eh" sunnar da kai tayi cikin jin kunyar ƙaryar da tayi,  Shattima ya kuma cewa"amma Abba yayi maki miji kuwa"? ɗagowa tayi tare da dan zare ido saboda jin abun yace mata,mamakin ta yadda yake ta tambayarta bayan sam ko a fuska baiyi kama da mai son surutu ba shima,   girgixa kai ta kuma yi tare da cewa"a'a bai mun ba" "Because of what?ko babu wanda kike so acikin matasan gidan nan"? maimakon ta bashi amsa sai ta ɗan saci kallon Sgr dake kur6ar coffee din hannun shi,  Wani irin murmushi shattima ya saki saboda yaga inda sehrish take kallo, acikinsa ransa yace"hmmmm dama nasani,"  A fili kuma yace"yana da kyau ko'? A firgice sehrish ta mayar da idonta kan shattima tace"Wa"? da ido yayi mata nuni da Sgr, sunnar da kai tayi tana murmushi tace"eh,"   "Shi bai yarda da mace ba,yace mata matsala ne arayuwar namiji,but i want to ask u something a misali mace ta samu righteous husband kamar wannan lu'u lu'un,wanda ya haɗa komai ga kyau ga ilmi ga dukiya, kina tunanin akwai macen da zata yi gangancin Mallakarsa har ta zama matsala arayuwarshi balle ta 6ata mashi rai"?  jikin sehrish tuni ya soma kerma saboda tsoran dogon sharhin da abokin sgr ɗin ke yi mata,babban tashin hankalin ma gashi a kusa duk da yayi tamkar baya jinsu,ammma ae kunnan shi a buɗe suke ba'a toshe ba dole ne yaji abunda suke cewa,muryarta na rawa ta buɗe baki zatayi magana kenan kwatsam taji wannan sanyayyiyar muryar tashi tace"ba kowace mace bace zata so ni dan Allah in fact duk macen da zata soni sai don waɗannan abubuwan daka lissafa," yayi mgnar again batare da ya kalle su ba, sai ma hannun shi daya zura cikin short pocket dinsa ya ciro wayarsa dake ringing tare da yin picking ya kara a kunnan shi yana magana cikin harshen turanci,  gaba ɗaya jikin sehrish yayi mugun sanyi kalamansa akwai ƙamshin gsky acikinsu,yanzu ta ƙara gane dalilin dayasa mace sam bata agabanshi,saboda yasan cewa duk wadda zata so shi,ba zata so shi dan Allah ba face sai don wani abu daya mallaka,kamar wannan kyakkyawar surar tashi mai matuƙar jan hankali,da dukiyarsa kuma, ga kuma ilmi duka dai😇 Amma har ga Allah ita ba don dukkan waɗannan abubuwan ba take son shi ba,ataƙaice ma tunkan taga fuskarshi tunkan tasan koshi wanene ta afka ma tarkon son shi ta hanyar sunan shi kawai da taji suna faɗi BABBAN YAYA,  gaba ɗaya ta tafi zurfin tunani muryar shattima ta dawo da ita daga dogon
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.