Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Shiru su kayi suna kallonta ba bakin magana, tsoki taja tare da cewa "if u can't talk to me, i will reject the call right now"!
Cikin sauri jahan yace "pls mommy don't reject the call, zamu yi magana, pls Ayaan kayi mata bayani" ya faÉ—i yana kallon Ayaan shima murya tamkar zaiyi kuka yace "Jahan i don't know what to say, kai kayi mata bayani pls," mamaki ne ya kama Alexandra ganin yadda suke ta jayayya akan wanda zaiyi mata bayanin dangane da kiran da sukayi mata,
tsawa ta daka masu tare da cewa "bana son shiriri James! kuyi mun bayanin kiran da kuka yi mun within 5 mins if not zan kashe kiran "
Natsuwa su kayi gaba É—ayan su sannan jahan ya soma cewa "Mom dama.....um......kuÉ—ine...muke....so...awurin ki, ki bamu,"
tana jin haka ta fashe da dariya hankalin su ba ƙaramin tashi yayi ba jin yarda mommyn nasu ke 6a66aka dariya,
Ayaan yace "mom why are u laughing pls, don Allah ki tausaya mana mommy muna cikin wani hali ni da Jahan....' dakatawa tayi sannan ta soma magana anatse "Har nawa ne kuÉ—in"?
Jahan yace "80million,"
É—an zaro ido tayi tare da cewa "har 80m? what are going to do with it?
Ayaan yace "mom dan Allah kada ki tambaye mu me zamuyi dasu, saboda ba zamu iya yi maki ƙarya ba, kawai ki taimaka ki ba mu,"
Murmushi ta ɗan saki tana kallonsu na wani lokacin kafin tace "Ni a wuri na miliyan tamanin tamkar naira tamanin take, naji zan taimaka na baku amma bi sa sharaɗi ɗaya"! Har sun fara sakin fara'a amma jin maganarta ta ƙarshe yasa su dakatawa da murna,
Jiki asanyaye Jahan yace "what mom"?
alexandra tace "Inaso ku sa ROMEO ya kira ni a waya, sannan ya kira ni da sunan mommynsa Kuma ya bani haƙura na bijire mun da yake yi, kiran yakasance video call ne, in har ku ka sa romeo ya amince ya kira ni awaya,i promise to give each one of u 50 50millions,' tayi maganar tare da jaddada musu,
Zaro ido suka yi gaba ɗayansu ga samu ga rashi, domin kuwa sunsan cewa Junaid bazai ta6a kiran mahaifiyarsu ba harya bata haƙuri kuma ya kirata da sunan mommynsu tabɗijancan,
gaba É—aya sun tafi zurfin tunani suka ji tace "i will be waiting to hear from u guys," tana faÉ—in hakan ta kashe video call É—in,
Hannu ayaan yasa ya rufe laptop din sannan ya kalli jahan wanda shima kallonsa yake yi yace "Yanzu ya zamuyi jahan? ga samu ga rashi ! duk da nasan junaid yana son mu sosai kuma yana yi mana biyayya zai iya yi mana komai amma banda wannan ALFARMAR,
zugudum su kayi cikin tsananin tashin hankali da kuma tunanin yarda zasu tunkari junaid da maganar! 😥
***********JAHAD***********"**
a hankali ta soma buɗe idanunta biji² ta dunga gani a idonta, daker take motsa su zata buɗe su, sai faman ambaton sunan Allah take yi a hankali,
lokacin da taƙarasa buɗe idanun nata mamaki ne ya kamata ganin ta kwance a wani ɗaki, komai na cikinsa fari ƙal a tsaftace, ga mutanen dake tsaye akanta farare fat hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba, gaba ɗaya ranta ya bata cewa mutuwa tayi ne, saboda yanayin wurin da ta gani fari ga mutanen dake tsaye akanta farare, hawaye ne suka soma zubo mata a idanunta cikin kuka take cewa "Ya Allah kasa ba mutu nayi ba,nabar hussana aduniya wurin wancan fasiƙin mutumin, nashiga uku wa zai taimake ta acan, meyasa mutuwa bata ɗauke mu, mu biyu ba atare? Sai ta ɗauke ni nikaɗae tabar hussana a waccen duniyar mai cike da ruɗani," gaba ɗaya jahad ta fashe musu da kuka, Hankalin nurse ɗin dake tsaye da likitan ba ƙaramin tashi yayi ba, cikin sauri su kayi kanta, ko da jahad tagansu sai ta ƙara sautin kukan tana cewa "innalallahi wa'inna ilaihirraji'un,! dan Allah su wanene ku farare haka, ina hussana take,
zama nurse É—in tayi daga gefenta sannan tace "Sannu da jiki Æ´ar uwata, ni ce nurse É—in dake kula da ku, sunana Camila ke fa"?
Jin tayi mata magana raÉ—au da hausa yasa jahad dawowa cikin hayyacinta sosai tana kallonta da mamaki, kana kallonta ka ga english woman, Cos majority na ma'aikatan asibin sgr daga u.s suke, wasu daga india, wasu kuma Æ´an nan nigeria, akwai kwararrun likitoci da nurses acikin asibitin,
ƴunƙurawa jahad tayi zata tashi cikin sauri Camila tasa hannu tare da mayar da jahad kwance tace "Ana miki ƙarin jini ne, ko baki lura ba ne"? ta faɗi tana kallonta da murmushi a fuskarta,
ɗan juyawa jahad tayi ta kalli ledar ƙarin jinin da akeyi mata,
sassauta muryarta tayi sannan tace "sister dan Allah ina ne nan? Kuma waya kawo ni nan?
Murmushi Camila tayi sannan tace "nan asibiti ne, sannan yayanki ne ya kawo ki domin mu baki kyakkyawar kulawa!"
Cikin mamaki jahad tace "Yayana kuma? ae ni bani da kowa aduniyar nan Æ´ar uwata ce kawai hussana nasani, dan Allah tana ina"? tayi maganar tana jiran amsa,
duk tattaunawar da suke yi dr Emran na tsaye yana jin su , kafin Camila ta buÉ—e baki tace wani abu sai ga MARSHAL OMAR ya shigo É—akin shida Major, gaisawa su kayi da dr emran, sannan ya matsa wurin da jahad ke kwance,
tsayawa yayi yana kallonta fuskarshi asake saboda ganin yarda ta wartsake alamar tasamu kyakkwar kulawa awurin Nurse É—in,
Sam jahad bata lura da marshal omar ba dake atsaye har sai da ya ambaci sunanta "JAHAD,"
A razane ta wurga kwayar idonta akan shi, ganin Ya Omar É—insu yasa ta zabura zata tashi zaune da sauri Camila ta mayar da ita, duk tabi ta zazzare idonta tana nuna shi da hannu tana ambaton sunan shi cikin tsananin mamaki,
tashi Camila tayi taba Omar wuri donya zauna kusa da jahad saboda ta lura yarinyar nason magana dashi,
Zama Omar yayi saman chair ɗin dake facing medical bed ɗin da jahad ke kwance asama sannan yace "Ya jikin naki"? tana jin haka ta fashe da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita, hannunta tasa ta ruƙe hannunsa tana cewa "Ya Omar ina ka shiga tsawan kwanaki kabar mu, bakasan halin da muke ciki ba..........' tana magana muryarta na shasshaƙewa saboda kukan da take, sam Omar ya gaza cewa komai tuni idonsa sun cicciko da kwalla,
Jahad taci gaba da cewa "Ya Omar har yanzu nagaza yarda cewa kaine! dan Allah kayi mun magana taya akai haka tafaru ya omar, kuma ina hossana take? mutumin nan ya gudu da ita ya omar..........." kasa ƙarasa maganar tayi saboda hannunsa daya sanya ya rufe mata bakinta........................................Bin idanunta yayi da kallo itama tana kallon nashi hawaye ne cike taf da idonta, bai janye hannunsa daga bakinta ba har sai da ya tabbatar cewa ta samu natsuwa sannan ya zame hannunsa yace "Jahad duk wani abu dake faruwa ni bansani ba,bani da masaniya akai,jiya ne aka turomin saƙo da privet number bansan ko wanene be,let me show the message,
Hannu yasa ya curo wayarsa daga trouser pocket ɗinsa kunna wayar yayi sannan ya shiga wurin messages ya buɗe saƙon ya nuna ma jahad don ta gani,
Zuba ma screen É—in wayar tayi da ido tana karantawa kamar haka
_"Omar ka yi ganganci daka bar rayuwar yaran nan a hannun Laila, ina baka shawarar ka hanzarta zuwa ka É—auko su, saboda naji cewa gobe goben nan za'a fitar dasu daga gidan_"
Janye wayar yayi sannan yace"lokacin da message ɗin ya shigo mun bana cikin natsuwa ta, saboda mun shiga tashin hankali,ƙanne na da aka tura aiki miyagu suka farmake su, mun samu nasarar ceto rayuwarsu kuma mun kama wasu daga cikin waɗanda suka farmake sun, yanzu haka da nake maki magana ɗaya daga cikinsu yana kwance a A&E ward, baisan inda kansa yake ba,saboda sai da suka banka mashi kayan miyagun ƙwayoyi sannan suka azabtar dashi, ba don Allah yasa an samu wani daga cikinsu ba yayi mana waya da shikenan ba'asan mai zai biyo baya ba,
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.