Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Around 3:30,sehrish ta farka tana faman murza idanu,ba ƙaramin bacci tasha ba,sai hamma take saboda wata irin yunwa dake cinta,dama ko a school bata wani ci abun kirki ba,hannu tasa tare da yakice hijabin dake jikinta tayi wurgi da ita gefe guda,sannan ta zuro ƙafafunta tare da saukowa daga saman gadon,tsayawa tayi tana kallon school bag ɗinta da tayi wurgi da ita ƙasa bakomai ya faɗo mata a rai ba face Ruwan addu'ar da Malamin nan mai farin glass ya bata,ƙarasawa tayi tare da zuƙunnawa ta janyo bag ɗin,tana dudduba cikinta sam babu roban ruwan aciki,abun ya ɗaure mata kai,hannu tasa tare da zazzage kayan cikin jakar duka amman babu robar ruwan,
 Tunanowa tayi da abunda Amrish ta faɗa mata"Ga ruwan addu'ar da malaman yace na baki,kuma yace indai bakiyi amfani dashi ba,ƙusumbi zai fito maki abayanki,"waro ido waje sehrish tayi tuna wannan maganar ta amrish nan take yatsun hannunta suka shiga kerma hatta la66anta,gaba ɗaya duk tabi ta rikice ba don komai ba sai don tsoran ƙusumbin da akace zai fito mata,mugun tsoran ƙumbin take yi saboda taji ana cewa aljanune ke ajiya a cikin ƙusumbin,ƙyamar abun take ji,
  Hawaye ne suka soma wanke mata fuskarta murya na rawa tashiga furta"innalillahi wa'inna ilaihir rajiun, nashiga ukuna!wayyo Allah na,yanzu ya zanyi?nan fa na ajiye robar ruwan nan amma yanzu na duba babu ita.....yanzu shikenan ƙusumbi zai fito min ya suffata zata koma tare da ƙoƙo abayana............'fashewa tayi da matsanancin kuka,anan wurin ta tsugunna tana matse kwalla duk tabi ta rikita kanta,sai da tayi mai isarta sannan ta miƙe tana faman shasshekar kuka takai hannu tare da tattara books ɗinta tana mayar dasu cikin school bag din,bayan ta kammala ta ɗauke jakar taje ta ajiyeta,
  Rage kayan jikinta tayi,ya rage daga ita sai white short da half vest,sannan ta shige cikin toilet cike da kasala,
 Ta jima acikin toilet din kafin ta fito jikinta ɗaure da towel,har lokacin idanunta na cike tab da hawaye,zulluminta ƙusumbin da akace zai fito mata,saboda tasan in hakan ta faru hatta Junaid sai ya guje ta,shi da yafi kusa da ita,da wannan yanayin ta kammala shirya kanta cikin wando palazzo maroon colour tare da halter shirt black colour,just imagine it ba ƙaramin kyau rigar tayi mata ba,ta ɗame jikinta sam rigar bata da hannu amma ta rufe ƙirjinta har neck ɗinta ta zagaye shi,komawa tayi gaban mirror tana feshe jikinta da turaren nan nata mai ƙamshin gaske,kafin daga bisani ta ɗauko ribbom launin wandonta maroon colour,tattare gashin tashiga yi zata ɗaure shi amma ina duk yadda taso ta haɗe shi wuri guda ta ɗaure abun yaci tura,har wani huci takeyi saboda 6acin ran yaƙi ɗauruwa,tana cikin dambe da gashin,taji ana kwankwasa mata ƙopa,dakatawa tayi da ɗaure gashin tace"Wanene,"
 "Auntynki ce,"muryar azmee ce ta bata amsa daga waje,
  ƙarasowa Sehrish tayi tare dasa hannu ta buɗe mata kopan,sanye take cikin hijabi hannunta ruƙe da cazbaha fuskar nan ɗauke da murmushi tace"irin wannan kyau haka?
. sunnar dakai sehrish tayi tare da cewa"Ina yini aunty azmee,"
 "Lafiyalou,tun ɗazu naso nazo na dubaki amma bansamu hali ba,ya school ɗin"?
 "Alhamdulillah Aunty azmee,"
"ina fata kina lafiya,naga kamar akwai damuwa a fuskarki"?
 girgiza kai sehrish tayi tace"a'a lafiyata lou,dana dawo ne bana ɗan jin daɗin jikina shine na kwanta nayi bacci sosai banjima da tashi ba,shiyasa fuskata take a haka,"
 Jinjina kai azmee tayi tare da cewa"okey,nagane ina fata kinyi sallah,
 "A'a yanzu nake shirin yi,"
Azmee tace"okey ya kamata ki hanzarta yi time har zai wuce,"
 Ta ƙarasa maganar tare da juya zata fita,tsayawa ta ɗanyi tare da jiyowa tana cewa"Oh namanta ban faɗa maki ba,ɗazu da safe da kika tafi school,hayaam ce taje kaima Sgr breakfast ɗinshi,'
 Jikin sehrish ne yayi sanyi tunkan ta ƙarasa jin abunda takeson faɗa mata tasoma jin jealous a zuciyarta,
 "Yanzu kenan itace zata cigaba da kula da part ɗinshi tana kai mashi abinci"?yarda sehrish tayi maganar taba azmee dariya,saboda a wani irin yanayi na tashin hankali tayi tambayar,
  "Kin tari numfashi na baki bari na ƙarasa maganar ba ai,Hayaam takai mashi abinci amma baici ba yace ta mayar dashi saboda shi ba'a sharing a aikinsa,yafison mutum ɗaya daya fara yi mashi aiki yaci gaba da yi batare da an canza mashi wani ba,ko kuma mutum biyu na mashi aiki at thesame time bayaso,"
  Wani irin ƙayataccen murmushi sehrish ta saki,farin ciki kamar anyi mata albishir da gidan Aljanna,tama rasa bakin magana sai faman zabga murmushi take,
  Azmee taci gaba da cewa"yanzu haka tun safe ba'a gyara mashi bedroom ɗinshi ba,na dai kai mashi breakfast ɗinsa,amma ban gyara ba saboda ba aikina bane,aikinki ne don haka da zarar kin kammala salla ki hanzarta zuwa ki gyara mashi part ɗinshi before ya dawo,"
  Dakyar Sehrish ta iya amsa mata da toh,kamar jira take azmee tabar ɗakin tana fita tashiga daka uban tsalle tana rawa don murna,
  Sam ta manta da maganar roban ruwanta da take nema,
  Sai da tayi salla sannan ta koma gaban dressing mirror ta shafa jan baki launin wandonta maroon colour ba ƙaramin kyau yayi mata ba,bayan ta gama ta kara feshe jikinta da turare sannan ta koma wurin wardrobe ɗinta tare da ɗauko mayafinta,ta yafa shi ajikinta,ta ɗauko takalmi baƙi ta zura a ƙafarta Open toe mai ɗan tsini,sai gashi ta fito ɗass da ita,
  hannu tasa tare da buɗe door din ɗakin ta fito tare da kama hanyar fita daga corridor din,
 Adaidai lokacin Hayamm ta fito daga masaukinta,itama ta ɗauki wankan lace mai ɗan karan kyau,riga da skirt ash colour,kayan sun matseta sosai,daga saman rigar kamar boobs ɗinta zasu fito waje gaba ɗaga,skirt ɗin kuwa wata tsaga gare shi tun daga guiwar ƙafarta tafara har wurin ƙafarta kana hangen fatar ƙafafunta,high heels ne a ƙafarta tana tafiya sautin na fita kwas kwas,ta cuge ɗaurin ɗan kwali abunta yarda kasan wadda zata gasar miss world
  jin takun tafiya yasa sehrish jiyuwa bayanta,har sai da gabanta ya faɗi da tayi arba da hayaam saboda wankan data ɗauka tayi uban makeup kamar wata aljana,bakin nan yasha jan janbaki ta wani cuno shi irin na masifaffu,
Tuni sehrish tasha jinin jikinta ganin irin wankan da Hayaam ta ɗauka,ba ƙaramin kyau tayi ba kuma zata ja hankali sosai,
kawar da kai sehrish tayi tare da juyawa zata tafi,muryar hayaam ce ta katse ta dacewa"Wait inason magana dake Æ´an mata,"
tsayawa sehrish tayi tana jiran jin me zata ce mata,
Koda Hayaam ta ƙaraso,bin sehrish tayi da wani irin matsiyacin kallo tun daga ƙasa har sama sannan tace"nasan gabanki ya faɗi kuma kin tsorata da ganin irin kyau da kuma kyawun sura da Allah yayi mun,"
É—aure fuska sehrish tayi batace komai,
Hayamm taci gaba da cewa"so nake ki fahimci cewa ni ba sa'ar yinki bace!bansan wani irin shisshigi kike ma Sg rafayet ba da har kika samu matsayi a wurinshi,inaso na gargaɗeki ne, kuma naja kunnanki akan ki fita daga sabgarshi saboda yafi ƙarfinki nesa ba kusa ba,don na lura abunda kike hari kenan,in ma banda haɗama irin taki ina zaki kai mutum kamarsa?dan Allah jibarki fa ƴar ƙarama dake amma sai kankanbar tsiya,wai ma menene connection ɗinki da mutanen gidan nan ne? tayi tambayar tana kallon sehrish yayin da fuskarta ke ɗauke da shu'umin murmushin nan nata,
jikin sehrish ba ƙaramin sanyi yayi ba don tuni idanunta sun cicciko da kwalla,daƙyar ta iya shanyesu sannan ta dake tare da cewa"Bansan meyasa kike gayamun waɗannan maganganun ba,da alama dae baƙin cikin ɗazu ne da sgr ya ƙumsa maki shine kikeson ki huce akaina,sannan kuma yaushe nace maki inason shi ne da har kike cewa yafi ƙarfi na?bama wannan ba,Naji kina magana akan cewa menene alaƙata da mutanen gidan to bari na baki amsa,"
matsawa sehrish tayi dab da Hayaam sannan tace"Ni yar aikinsu ce,biya na suke ina masu aiki kuma suna jin dadin aikina shiyasa nasamu kar6uwa a wurinsu,kuma ina alfahari da hakan,wannan shine alaƙata dasu,ke kuma fa?ƙanwar matar yayansu ce fa?ina alaƙa take anan?
Lokacin da sehrish takai ƙarshen maganarta,waro ido waje Hayaam tayi tana kallonta,bata ta6a tunanin cewa yarinyar zata iya mayar mata da martani ba ashe itama ba kanwar lasa bace,ranta ba ƙaramin 6aci yayi ba,tuni idonta sun canza launi saboda fusatar da tayi,
Sehrish kuwa murmushi ta saki tare da juyawa ta kama hanyar tabar wurin,
Wani irin tafarfasa zuciyarta keyi mata,tama rasa mai zatayi ma sehrish ta huce don tsabar takaicin maganar da ta yada mata,
"Da ace ban mayar mata da martani ba,dani zan kwana da baƙin ciki," sehrish ce tayi maganar a lokacin da take ƙarasa shiga part ɗin sgr,
Sai faman murmushi take saki abunta,wucewa tayi cikin bedroom ɗinshi,wannan daddaɗan ƙamshin turaren nasa ne yayi mata maraba da zuwa,duk da baya cikin ɗakin amma ƙamshinsa ya gauraye ko'ina,
Lumshe idonta tayi tare da buÉ—esu a hankali suka sauka akan shimfiÉ—eÉ—en gadonshi,tunawa tayi da abunda ya faru jiya atsakaninsu nan take taji wani irin yanayi atattare da ita,nan take tashiga tariyo dukkan abunda ya faru jiya a tsakaninsu,musamman lokacin daya kwantar da kanshi asaman chest É—inta sai taji shi tamkar babynta,hmmmmmm
shiga ciki sehrish tayi batare da 6ata lokaci ba,tashiga gyara mashi bedroom É—in nashi,tamkar sabo haka ta Canza mashi kamanni,bayan ta kammala da bedroom É—in,ta cire mayafinta tare da ajiye shi daga gefen gadon sannan ta koma cikin toilet É—insa don ta gyara mashi,
Bata jima da shiga ciki ba,sgr ya dawo cikin gidan,har yanzu wankan ɗazu ne ajikinshi,na warp shirt da black trouser,da alama a ɗan gajiye yake,kai tsaye ya nufi upstairs part ɗinshi,hankalin Hayaam ba ƙaramin tashi yayi ba lokacin data ga gifcinshi yana ƙarasa hawa upstairs ɗin,taso ta tarbe shi tayi mashi sannu da zuwa kota samu yasan ya idonshi acikin nata,amma bata samu damar yin hakan ba,saboda fargabarshi da take ji,
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.