Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Lokacin da fito har azmee ta kammala jera masu breakfast É—in asaman dining,junaid ta samu tare da fawan zaune suna yin breakfast dinsu,kamar waÉ—anda yunwa ta koro sai faman turawa suke yi abakinsu suna ci,
  dagowa junaid yayi tare da kallonta nan take ya sakar mata murmushi tare da kiran sunanta"sehrish,"Â
 Juyowa fawan yayi tare da kallonta yace"ke zo nan,"Â
 nan da nan taji gabanta ya faɗi dama basu ta6a magana dashi ba,
 jiki asanyaye ta ƙarasa inda suke dai dai kusa dashi sannan ta tsaya tana faman ƴan kame kame,
  cikin sanyin murya yace"jira kike na fara gaishe ki ne"?
 cikin sauri sehrish tace"ina kwana,ka tashi lafiya,"
 fashewa da dariya junaid yayi yana kallonsu,harara fawan ya watsa mashi tare da mayar da idonshi kan sehrish yace"lafiya lou,haka yadace daga yanxu basai nace ki gaishe ni ba,daga zarar kin ganni kiyi hanzarin gaidani amatsayina na yayanki,"
 Murmushi sehrish tayi tare da amsa mashi da"toh,"
  junaid yace"bismillah ki zauna muyi breakfast atare mana," girgiza kai tayi tare da cewa"a'a inaso zan shiga kitchen ne wurin aunty azmee,"
 Amsa mata yayi da"okey,"
 Sannan cikin sauri ta juya tare da nufar kitchen din,
  time din da taƙarasa kitchen ɗin azmee ta kammala gyare kitchen din tsaf, dakyar ta iya cewa"ina kwana aunty azmee,"
  sai lokacin ta lura da ita,murmushi tasakar mata tare da cewa"lafiya lou babyn junaid,sai yanzu kika tashi daga baccin naki?dazu nashiga ɗakin naki na sameki kina bacci,
  ciki sehrish ta shiga tana cewa"Aunty azmee ae da kinsani kin tashe ni,nikaina banasan yawan baccin nan da nake yawan yi,"
 Azmee tace"ai baida amfani atlease yakamata ace duk in kika kammala sallar asuba ki daure kina karanta al'qur'ani, sannan ki dinga yawaita yin azhkar,insha Allah duk wani abu dake damunki Allah zai yaye maki shi,"
 "Insha Allah zan yawaita yinsu kamar yarda kikace,yanzu inaso in kaima babban yaya breakfast ɗinshi,bansani ba ko kin kai mashi,
  Azmee tace"a'a ban kai mashi ba,bari na haɗa maki sai ki kai mashi,"
  Tsayawa sehrish tayi tana jiranta,
 Bayan azmee ta kammala shirya mata breakfast din nashi acikin tray ta miƙa mata,hannu biyu tasa ta kar6a tare da kama hanya ta fuce daga kitchen ɗin,
 Da sallama abakinta tashiga part din nashi,
  har time din bai fito ba,yana acikin bedroom ɗinshi,ƙarasawa ciki tayi tare da ajiye mashi tray din asaman table,sannan ta wuce izuwa bedroom ɗinshi daga bakin kopar ta tsaya tare da maimaita sallamar,
  daga cikin bedroom ɗin tajiyo muryarshi yana cewa"wanene nan"
 tuni tasha jinin jikinta,musamman data tuna abunda ya faru jiya ba ƙaramin tsoro ya bata ba,
  murya na rawa tace"Ni ce,breakfast nakawo maka,"
  "Okey,come in,"
a hankali tasa ƙafa tare da shiga ciki zuciyarta nata faman ɗar ɗar,
 tsayawa tayi daga bakin ƙopan tana kallon shi,har lokacin yana kishingiɗe kamar yarda Omar ya barshi,
  ganin ta tsaya abakin ƙopar yasa shi cewa"lafiya?
  cikin sauri tace"bakomai,"
"Okey shigo ciki,ki fara gyara min toilet É—ina,"Â
 ƙarasawa ciki tayi a hankali take tafiya tana satar kallon shi,eyes ɗinshi na'a rufe tamkar mai jin bacci,duk wani motsinta acikin kunnanshi yake jinshi,tura ƙopar toilet ɗin tayi tare da shigewa ciki,
  Sai bayan da ta shiga ciki sannan ya buɗe idanun shi tare da bin ƙopar toilet ɗin da kallo,tunawa da abunda ya faru jiya tsakaninsu yayi,mayar da idonshi yayi tare da lumshe su,
  ba da jimawa ba sehrish tafito daga cikin toilet tare da cewa"na kammala gyarawa,saura bedroom din,"
  buɗe idanunshi yayi ba tare da ya kalleta ba yace "okey,ki duba cikin closet ɗina,ki ciro mun kayan da zan sanya,"
 Cike da mamaki ido waje sehrish tace"dani kake"?Â
 "Ni da waye" ya tambaya a ataƙaice,d'an murmushi tayi tare da wuce wa can ciki wurin wardrobe ɗinshi,mai girma da faɗin gaske gaba ɗaya glass ne ta gabanta,daga waje kana iya hango kayan sawarshi dake aciki gasunan abun kamar a company jeri jeri komai a tsare,tana ɗauke da sliding doors ajikinta,
 Hannu sehrish takai ajikin wardrobe ɗin nan take ƙopar ta zuge da kanta,abun ba ƙaramin burgeta yayi ba,ruwan ido ta tsaya yi tama rasa wanne zata ɗauko mashi,saboda kowanne acikin kayan sawar nashi kyau suke yi mata,wata ƙopar ta zuge anan taga jerin kayan hausawa ta jima tana mamakin ashe yana dasu amma bai ta6a sanyawa ba,hannu tasa tare da ɗauko mashi haɗaɗɗiyar shadda gezna sky blue mai ɗaukar ido,
  ruƙowa tayi a hannunta tare da dawowa wurin gadon Shi a lokacin harya gaji da jiranta ya sauko da ƙafafunshi ƙasa yana ƙoƙarin tashi,jin takon tafiyarta yasa shi ɗagowa yana kallon kayan data ruƙo a hannunta,
 tsayawa tayi dab dashi sannan ta miƙa mashi,
  ƙin kar6a yayi saima nuna mata hanya da yayi tare da cewa"basu nakeso ba,ki canza mun wasu bana sa kalar wannan,"Â
   Jiki asanyaye sehrish ta koma ta maida shaddar sannan ta ɗauko mashi jeans da t shirt baƙa,
 Â
 Komawa tayi tare da miƙa mashi,hannu yasa ya kar6a tare da furta"thanks" a gefen shi ya ajiye kayan sannan ya miƙe tare da kai hannu ya zame bathrobe ɗin jikin shi,cikin sauri sehrish tayi hanzarin barin bedroom ɗin takoma daga waje tana faman sauke ajiyar zuciya,ƙiris ya rage sgr ya saki murmushi don ba ƙaramin dariya ta bashi ba,ita duk atunaninta babu shorts ajikinshi shiyasa tayi saurin guduwa daga ɗakin nashi,
 Tsaf ya kammala zura kayan ajikinshi bayan ya gama ya koma gaban dressing mirror ɗinshi tare da kai hannu ya ɗauki kwalbar turarennan nashi shumukh yabi ko'ina na jikinshi ya feshe shi da shi,sannan ya koma wurin shoe rack ɗin shi tare da zaro takalma ya zura a ƙafarshi,
  tana atsaye tana jiran fitowarshi muryarshi ta ratsa kunnanta da cewa"ki shiga ciki ki gyara mun,"
 Sannan ya wuce ta izuwa cikin falon nashi,
  Shiga ciki sehrish tayi anatse ta soma gyara mashi bedroom ɗin nashi,
  **************
A hankali motarsu tashiga cikin gidan abusufyan major ne ke driving É—inshi yayin da yake zaune a back seat na motar,
 Bayan yayi parking ɗin motar omar ya fito tare da wuce wa ciki,
 Koda yashiga cikin falon samun su yayi azune saman 3seater sun haɗa kai sun kurawa plasma tv ɗin dake manne abango suna kallon tashar bollywood,
  ba ƙaramin burgeshi su kayi ba,gyara muryar yayi tare da yi masu sallama,atare suka dago tare da kallon shi,hossana na ganin shi ta miƙe da gudun gaske ta tunkare shi,dakatar da ita yashiga yi da hannun shi amma ina sai da ta faɗa mashi,sosai ta rumgume shi tare da kwantar da kanta a saman wide chest ɗinshi,lokaci guda yaji wani irin yanayi atattare dashi,
 Jahad kuwa a fusace tace"hossana menene haka wai?ba zaki bari ya ƙaraso ciki ba?
  tamkar bata jita ba,haka ta ƙara ƙanƙame shi tana cewa"ya Omar nayi missing ɗinka sosai,jiya ko isasshen bacci bansamu ba saboda ban saka a idona ba,
 hannu omar yasa tare da janyeta daga jikinshi suna kallon juna ido cikin ido yace"Am sorry pls,amma yanzu ae gashi nan nazo ko?
 daga mashi kai tayi alamar eh,sannan tasanya hannunta cikin nashi suka ƙarasa ciki atare suka zauna kusa da Jahad saman 3 seater ɗin da take,
 Cikin sanyin murya tace"sannu da zuwa ya omar,yasu abba da sauran mutanen gidan,
 Fuskarshi dauke da murmushi yace"yawwa jahad,duk suna lafiya,ina fata kuma nasame ku cikin Æ™oshin lafiya,"Â
 Amsa mashi tayi da eh,sannan tace"namanta ban tambayeka ba,yasu Aunty zainab,"?
  kafin yace wani abu hossana tace"ya Omar wai dagaske kana da aure"?a shagawa6e tayi maganar tamkar zatayi kuka,
  cikin natsuwa ya soma kora masu jawabi"Ni banta6a aure ba,saurayi ne ni,ko budurwa ban ta6a ajiyewa ba,"
 Jahad tace"amma ya Omar wacece ta ɗaga kiran wayarka da mukayi a lokacin?
  shiru ya danyi kafin yace"ina tunanin younger brother ɗina ne Junaid,ya cika zolaya sosai,"
Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!
ï¿?
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.